Halin ko in kula.

Illar rashin kula da tarbiyya da ilmin yara.
Iyaye da dama suna mutukar kokari wajen bawa yayansu tarbiyya, saidai kuma kash, suna nuna halin ko in kula ga rayuwar yara marasa galihu basa tunanin cewa yaransu da suke bawa karatu da kulawa da tarbiyya suna fuskantar kalu-bale da yawa anan gaba a rayuwarsu...

Tabbas wayannan yara da ba a bawa tarbiyya ba, indai suka girma tabbas zasu addabi wayannan yara da aka ilmantar domin kuwa dole dai tare zasu rayu, ba za'a raba musu duniya ba.

Tamkar kashi ne idan aka yishi a cikin aji, sai wari ya dami mutanen cikin ajin, sai aka bukaci yan aji dasu kawar da wannan kazanta don a daina jin wannan warin ko za a sarara, sai kawai wasu sukace su iyakar kashin bangarensu zasu kwashe.... Alhalin kuwa akwai kashin bajaja a ko'ina.
Shin kana tunanin in suka kwashe iyakar kashin bangarensu zasu daina jin kashin cikin aji? Ko kuwa sai an hada karfi da karfe an kwashe na ko'ina?

Sign
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.