Zuwa ga matasa

Zunzurutun tsananin tsantsar tsabagen tsagwaron rashin imani da wasu mazan suke nunawa a gidajen su na aure yana mutuqar bani mamaki.

Matarka amana ce a wajenka, kuma za a tambayeka irin kiwon da kayi mata kamar yadda za a tambayeka irin yadda kayi sallah da azumi, kai bari madai tambaya akan hakkin mata yafi hatsari akan tambaya akan hakkin sallah da azumi da sauran bauta.... Sallah, azumi da zakkah duk Allah zai iya yafe maka idan baka yi yadda ya dace ba, amma ka sani hakkin wani Allah baya yafewa......

Ka daukota, ka rabata da iyayenta, ka rabata da gidansu ka kawo ta naka wulakantaccen gidan kuma a haka ka mayar da ita baiwarka, baiwar ma mara yanci mara kan gado duk a tutiyar cewa kaike shugabantarta.... Kuma Allah ya wajabta mata tayi maka biyayya.....

Kaje waje kaci abinda kake so, nan kuma ka barta da wulakantaccen lamin abinci wanda bazai gina jiki ba, Dan karfin dayake dashi zai taimaka ne kawai wajen toshe wata bazawarar yunwa da take fama da ita.

Ba ruwanka da lafiyarta kaidai indai buqatarka zata biya shikenan.....

*Bata da damar ta tasheka daga bacci face ta tsokanowa kanta.

*Bata da damar ta gaya maka sabulu ya qare face ta fusato ka.

*Bata da damar ta gyara maka kuskurenka face ta zinguroka.

*Da yawa mata su suke biyan kudin magani idan su ko yayansu basu da lafiya.....
Ni nasan hakan da dama.

Ina yiwa iyaye magiya da don Allah su rinqa bincike wajen aurar da yayansu mata, sannan su rinqa bibiyar gidan auren yayansu maza.

**       **       **
Zuwa ga mata (1)

Alkaluma sunata kai kawo, yayinda kowa yake tofa albarkacin bakinsa akan irin rashin mutuncin da maza suke tafkawa a gidajen aure, saidai kuma ance in bera da sata, tofa daddawa ma na da wari......

Mata da yawa su suke janyo abubuwa da yawa da suke faruwa dasu, kamar yadda da dama daga ma'auratan suka nuna.

*Sauda dama zaka kawo abinci gida sai kaga wannan mata ta nuna cewa ta raina.

*Zaka kawo mata magani bata da lafiya saita nuna bashi take so ba, tafi son Mai tsada ta _tashin sense_......

Babban abinda yake damun mata shine kallon fina-finai da kuma karanta novels na hauka au uffararan na hausa... Wanda wannan yasa suke raina duk wani kokari da mijin yake wajen kyautata musu.

Wata bata bawa mijinta kulawa kwata-kwata, maimakon ta koyo kulawar a littafan haukan tofa saidai ta koyo rashin kunya da raini....

Ya kawo abinci tace itafa ta gaji da wannan irin abinci na wulaqanchi.
Yasai magani daidai qarfinsa tace ita tafison na kamfanin gsk (England) ko na kasar waje.
Ya kuma yi mata dinki tace itafa wannan tsohon yayi ne, rabonta da taganshi a jikin wani tun tana rabon katin bikinta.

In ba mai imani kika samu ba, da anyi haka sau daya sau biyu saiya daina hidima, in mai imani ne shine zai daina yin mustahabbai ya tsaya iyakar wajibai.....

Don haka yana da kyau mata da maza duka a gyara.

Banzan, gurbataccen, yasashshen, wulakantaccen, bahagun shaidanin tunanin da muke ya kamata ace mun fitar dashi daga cikin kawunanmu.

Sign
Naseeb Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.