TSARABA DAGA SHEHU USMAN DAN FODIO


*Tsarabar Abu Umar Alkanawy*

Shehu Usman Dan Fodio yana cewa...
“... Daga cikin bidi'o'i akwai addu'a bayan idar da kowace sallah ta wata fuska abar sani, itace liman ya rinka addu'a su kuma mamu su rinka amsawa da ameen, wannan bidi'a ce makruhiya a mazhabar imam malik, wasu malaman kuma sukace bidi'a ce mustahsana, wasu sukace bidi'a ce abar so. 

Shehu Usman Dan Fodio yaci gaba da cewa...

“...Sai dai abin da yake na asali shi ne kowane mutum yayi addu'arsa, sai dai fa ba a yi saɓani ba cewa ba a rawaito daga Annabi (S.A.W) yayi sallama daga sallah sannan ya ɗaga hannunsa yayi addu'a mamu kuma sukace ameen ga addu'arsa ba, hakanan ba a rawaito wani daga halifofinsa shiryayyu yayi haka ba, Gaba ɗayansu. 

Shehu Usman ɗan Fodio bai tsaya haka ba sai ya ci gaba da cewa...

“...Shi kuwa duk abin da Annabi (S.A.W) bai taɓa aikata shi ba, haka nan ko ɗaya daga cikin sahabbai. Babu shakka barin wannan abin shi yafi akan aikatashi...

كتاب بيان البدع الشيطانية التي أحدثها الناس في أبواب الملة المحمدية
للشيخ المجدد عثمان بن فودي (ص) ١١

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.