TSARABAR JUMA'A DAGA ABU UMAR ALKANAWY



*Tsarabar Abu Umar Alkanawy*. (3)

Lokacin Khalifancin Sahabi Abubakar (R.A) ya shugabantar da Khalid bn Walid, bayan Sayyadi Abubakar shi kuma sahabi Umar bn Khaddab (R.A) saiya cire Khalid (R.A) ya maye gurbinsa da Abu Ubaida bn Jarrah (R.A)...

Ko menene dalili?

Shaikhul Islam Ibn Taymiyya (R) yace “Shi Abubakar (R.A) mutum  ne mai sanyi mai sauki, saboda haka saiya shugabantar da Khalid (R.A) wanda mun sani cewa shi mutum ne mai tsanani. Shi kuma lokacin da Sahabi Umar ya hau Khalifanci, mutumne mai tsanani don haka saiya sauya Khalid ya shugabantar da Abu Ubaida (R.A) wanda shi kuma mutum ne mai sanyi...
A tsari na shugabanchi haka akafi bukata a hada zafi da sanyi, kada a hada zafafa biyu sai tsaurin yayi yawa, hakanan kada a hada sanyaya biyu sai sanyi ko sakaci yayi yawa.

Nace: Ka duba lokacin da Allah ya turo Annabi musa mana, saboda yasan yanada tsanani sai ya sanya masa dan'uwa mai sanyi wato Haruna (A.S). 

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.