IYAYEN KO MALAMAN?

ƊALIBAN, MALAMAN KO IYAYEN?

Rubutawar

Naseeb Auwal (Abu Umar Alkanawy)

                    Da

Shifaa Khamis Adam  

★      ★      ★     ★       ★

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin rahama, shugaban farare da baƙaƙe.

Bayan haka.
Taɓarɓarewar ilmin addinin musulunchi da kuma rashin ganin girmansa abune daya samo asali daga wasu abubuwa da zamu tattaunasu a wannan rubutu, kafin nan yanada kyau muyi waiwaye wanda ake cewa adon tafiya.

WAIWAYE ADON TAFIYA
Lokacin zuwan turawan mulkin mallaka, sun tarar da sarakuna na wancan lokaci suna kula da alarammomi da sauran dalibai masu neman ilmin addini, sa'annan masu ilmin ababen girmamawa ne da kuma girma da kima a idon mutane.

Da dama daga cikin dalibai na wancan lokacin suna barin garuruwansu a kafafuwansu bisa jagoranchi ko goyon bayan mahaifansu zuwa wani garin don kwankwaɗar ilmi daga wani hamshakin malamin. Wayannan ɗalibai ana kiransu da Almuhajirun mutum daya kuma sai a kirashi da Almuhajiri, sai Bahaushe ya sauƙaƙe kalmomin zuwa Almajirai da Almajiri.

Bayan turawa sun kammala abubuwan da zasuyi saiya zamana karfi, iko da kuma haraji da ake karɓa atun jen mutanen gari gaba ɗaya yana tafiya gurin turawa, don dole sarakuna suka daina kula da ɗalibai na makarantun islamiyyu (Allo) saboda ƙaranchin kuɗin shiga da suke samu.....

Hakan tasa wasu suka daina tura ya'yansu wasu garuruwan, wasu kuma a cikin almajiran (Almuhajirun) sai suka dogara da abinci da mutane suke basu inda a ƙarshe shekaru suna wucewa har abin ya koma bara, shima baran akwai asalinsa amma lokaci bazai bamu dama ba......

Anan ina jan hankalin gwabnati da ya kamata itama ta samar da wani tsari na kula da kuma zamanatar da ilmin addini kamar yadda aka zamanantar dana boko kuma aka kallafawa kowa shi.

KALLO YA KOMA SAMA.
Wannan ilmi abin girmamawa na addini sai da ya kai ya kawo ƙimarsa ragaggiya a wajen al'umma. Domin kuwa ilmin boko shine wanda ya maye gurbinsa, ta yaya bazai ture na addini ba alhalin shuwagabanninsu shi suka fi girmamawa.

Daga ina matsalar take kuma ta yaya za'a gyarata?

Matsalar inka cire shugabanchi zaka iya rabata gida uku.
1. Iyaye
2. Malaman islamiyyu
3. Ɗaliban islamiyyu

Bari mu dauki daya bayan daya don saukaka bayanin da kuma fito da bayanan.

IYAYE
Iyayen yanzu da dama daga cikinsu basu da wadatar ilmin addini, don haka da yawansu sun taso sunga iyayensu suna girmama shine shiyasa suma suke girmamashi. Sauda yawa zaka iske iyayen yanzu basa gaza izu uku zuwa biyar.... Kuma ɗaiɗaikune zaka iske suna tilawar wannan karatun, asalima wasu iyayen zakaga a sallah kawai zaka iske suna karatu.

Hakanan a cikin gidajensu zaka iske basa ɗabbaƙa abubuwan da addinin ya koyar yadda ya kamata...
To a irin yanayin zakaga yaro koda yaje islamiyyar idan ya tarar gidansu ba'a  amfanin da abinda ya koyo tun anan zai fara tunanin ilmin addinin yanayi ne kawai amma aiki dashi ba dole bane.

Sa'annan iyaye da dama sukan fifita ilmin boko a aikace ta yanda zaka iske koda yaushe ana yiwa yaro maganar karatun boko ne. Da ace za'a ce masa “Anya kuwa ka karanta littafinka yau?” abinda zai fara zuwa ƙwaƙwalwarsa shine littafin boko.

Hakanan da sassafe za'asan yanda za'ayi zai an turashi makarantar boko ko an kaishi, amma a lokacin islamiyya ba'a damu ba don an aikeshi ya makara. Kai wani lokacin ma zakaga anfi bawa games da kallon t.v muhimmanchi akan karatun islamiyya, mafi lalacewar iyaye kuwa sune wayanda suka gina yayansu akan wasa, kallo da games......

Kai akwai yaran dana sani da basa fashin makarantar boko amma islamiyya sai sunga damar zuwa.

Yarinya zataje malami ya gaya mata irin shigar da zatayi a musulunche amma a gida idan za'aje unguwa tayi irin wadda malamin ya fada sai kaji ance mata haba wance ya naganki haka a hijabi kinata faman yawo a ciki sai kace matar liman.......
To yanzu an koya mata iyaye sun rushe gobe an koya sun ruguza, jibi an koya sun hargitsa, gata an koya sun wancakalar, citta an koya sun antayar... To ta ina zataga girman ilmin?

Hakanan wata yarinyar da ta kai wani limit na karatu, ko wasu shekaru saita kauracewa zuwa islamiyyar iyayen kuwa babu abinda zasu ce mata.....
Idan ma sunyi maganar ba ji zatayi ba, domin kuwa su suka nuna mata rashin amfani da darajar ilmin.

MALAMAI

Malamai masu koyarwa a islamiyyun suma suna sunada nasu matsalolin domin ba ma'asumai bane.

Yana da kyau ace a zamantar da islamiyyu ta yadda ɗaliban zasu sosu fiye da soyayyarsu ga boko, hakanan suma iyayen ta yanda zasu san da gaske wannan koyarwar, koyarwa ce ta gaske... Abin nufi ya zama an tsara jadawalin karatun domin akwai makarantun islamiyyun da zaka iske karatun da yaro zaiyi a shekara hudu ya kaishi har shekara goma, wani ma ka tarar yayi shekara goma yana zuwa islamiyya amma bai iya larabchi ba, hakanan idan yanayi maka sallah saika kusa yi masa kuka.

Sa'annan yana da kyau asan malamin dazai kula da yara, da kuma wanda zai koyarda manya. Misali yanzu idan ka dauki wanda baya daukar tension ka sakashi ya koyar da yara kuma ka bashi bulala tare da bashi damar ya dakesu, ai ba sai na gaya maka abinda zai faru ba.

Alhamdulillah akwai islamiyyu da suke ta yin irin wannan tsare-tsare.

Hakanan a matsayinka na malamin islamiyya ya zama dole ka kiyaye mutuncinka, domin mutuncinka shine mutuncin abinda kake koyarwa...

Ko kasan da yawan ɗalibai kana ce musu Manzon Allah (S.A.W) yace.... Amma su ba manzon Allah suke dubawa ba, kai suke dubawa....

Kana malamin islamiyya amma yammata kusan biyar ko goma a makarantar yan matanka ne, kuma a haka kace addini kake koyarwa.

Ko kuma ya zamana kana warewa tsakanin masu kudi da yayan talakawa don roƙo, kwadayi da neman abin duniya.

DALIBAI
Su kuma yaran dama tun suna ƙananu iyayensu sun gama saka guba a cikin ƙwaƙwalwarsu da zuƙatansu, ta yanda basa ganin girman ilmin addini ko kadan, gashi dai suna da sanin wani yankin na ilmin addini amma basa taɓa ɗaukarsa a matsayin wani abu mai gagarumin amfani.

Yarinya ta yarda ta kwaikwayi wata ballagazar ƴar film ko mawaƙiya amma bata yarda ta kwaikwayi matan ma'aiki da salihan bayi ba... Saboda tafi so da ganin girman waƴanda suke film din, duk da dai akankin kanta tana jin kamar tafison Nana Aisha akan su Lady gaga, Nickie minaj, Rihanna da sauransu... Amma ƙarya take domin tana yaudarar kanta ne kawai, idan kuma tafi son Nana Aisha to ta ajiye abinda ta koyo a wajen Rahama sadau ko watanta tayi aiki dana Nana Aishar.

Yaron ya yarda ya kwaikwayi Ronaldo, Messi ko Bolotelli, amma bai yarda ya kwailwayi masoyina (S.A.W) ba, kuma a haka yake yaudarar zuciyarsa wai yafi son Annabi... Idan yafi son Annabi me yasa ya kasa ajiye abinda Wizy, lilwaine ko Akon da wasunsu sukeyi yabi na Annabi ba?

Kammalawa
Yanada kyau gwabnati ta taka tata muhimmiyar rawar don kawo gyara.

Amma rawar gwabnati ba abar jira bace, domin yanzu ne kidan ya ɗau zafi, idan kuwa aka daina kiɗan lokaci ya wuce rawar bazata taku ba.

Don haka mu ya kamata mu miƙe a matsayinmu na ƙanne, yayye, ƴaƴa, abokai ko ƙawaye kuma iyayen gobe...... Mu nusar da kawunanmu. Sannan mu sanya abinda muka sani ya zama aiki.

Ina jimami da kuka idan nayi tunanin cikinda muka yiwa yau, wanda zata haifeshi gobe, ina tausayawa ƴaƴanmu da tunanin irin zamanin da zasu rayu a ciki mutuƙar muka ci gaba da tafiya a haka.....

Yanzu yaranda basu san darajar addini ba, mezai faru idan suka haifi nasu ƴaƴan kana tunanin basu san darajarsa ba zasu sasu a gaba suga sun san addininsu?

In kuwa kuwa haka ne, ana rayuwa a haka zamu riski mutane daga cikinmu wayanda basu yarda akwai Allah ba wanda tuni mun fara ganin irinsu.

Allah ka shiryar damu, ka kuma bamu kariya!

Rubutawa
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy
Tare da
Shifaa Khamis Adam

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.