AUREN DOLE.


Wannan takaitacciyar fadakarwa ce a kan auren dole, hukuncinsa a addini da kuma shawarwari...


Mun tattara bayanan ne don amfanuwar al'umma baki daya.

Aikin da mukai na dai-dai daga Allah ne, wanda mukayi na kuskure kuma dama mu yayan Adam ne, muna rokon Allah da ya gafarta mana. Ya kuma sanya rubutun ya zama mai amfamarwa ne ga daukacin yan'uwa musulmi.


Dan uwanku.
Abu Umar Alkanawy
Da yar'uwarku
Shifaa Khamis Adam


AUREN DOLE 

Tabbas soyayya jigo ce mai girma a zamantakewar auratayya. Shi yasa Allah da kansa yake cewa...
"Yana daga cikin ayoyinSa ne, ya halitta muku matan aure daga rayukanku, domin ku nutsu zuwa gareta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani."
Rum:21

Hakanan Annabin rahama yake fada cewa "Banga abin da ya fi dacewa da masoya biyu ba sama da suyi aure".

Wannan hadisi ne shahararre wanda matasa da dama suke amfani da shi, kuma lalle yana nuna darajar aure da matsayinsa a Musulunci. 

Hadisin daga Sayyidina Abdullah bin Abbas (R.A) ya zo mana, ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce:

لَمْ نَرَ لِلْمُتَحَابَّيْنِ مِثْلَ النِّكَاحِ

"Ba mu ga abin da ya dace da masoya guda biyu ba (domin karkata soyayyar zuwa ga yardar Allah) kamar aure."

 

Sunan Ibn MajahHakim a Mustadrakh, Baihaqi a Sunan Al-Kubra da Tabarani a Mu'ujamul Kabir duk sun fitar da hadisin    

Malamin Hadisi Muhammad Nasiruddeen Albani ya tantance hadisin a matsayin Sahih (ingantacce) a cikin littafinsa Silsilat al-Ahadith al-Sahihah (Hadisi na 624). Imam Al-Hakim ma kafin nan yace hadisin ya cika sharudan Imam Muslim, koda yake shi Muslim din bai kawo shi ba.


Darussan cikin Hadisin 

Malamai sun yi sharhi mai ratsa jiki a kan wannan hadisi:

  • Ma'anar Soyayya: Malaman sun bayyana cewa, idan zuciyar mace da namiji ta karkata ga juna, babu maganin da zai warkar da wannan shauki ko ya sanya shi a tafarki madaidaici sai aure. Domin ita soyayya kamar wata guba ce da ba ta da magani face kara kwankwada daga wannan gubar.

  • Kariya daga Zunubi: Malamai kamar Al-Munawi a cikin Faydul Qadir sun nuna cewa, soyayya kafin aure tana da hadarin fadawa cikin haramun. Don haka, aure shi ne kadai hanyar da za ta halatta wannan shauki, ya zama lada maimakon zunubi.

  • Nasiha ga Waliyyai: Wasu malaman sun yi amfani da wannan hadisi wajen kwadaitar da iyaye cewa, idan aka ga saurayi da budurwa suna son juna kuma sun dace, to kada a kawo musu cikas, gara a hada su aure domin kiyaye mutuncinsu da imaninsu.

Wannan hadisi gaskiya ne, kuma yana nuna cewa Musulunci bai hana soyayya ba, sai dai ya samar mata da kyakkyawar tashar da za ta gudana, wato Aure.


A nan zamu gane cewa soyayya jigo ce a cikin aure kuma da ita ne aure yake zama.


Auren Dole

Auren dole wani aure ne, da ake tilastawa wani sashe don ya auri wani ba tare da yana sonsa a zuciyarsa ba.

Shin me musulunchi yace gami da auren dole?

Kamar yadda muka faɗa cewa soyayya jigo ce a zamantakewar auratayya kuma muka ji daga fadin Allah da manzonSa, hakan zai nuna mana cewa Musulunci ba ya goyon bayan auren dole, ba ya ga hakan kuma akwai dalilai da suka fi wayannan fitowa fili.

1. An karɓo hadisi daga Abu Huraira (R.A), Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa "Ba a aurar da bazawara har sai an nemi umarninta, kuma ba a aurar da budurwa har sai an nemi izinin ta". Sai sahabbai sukace  " Yaya za a gane izininta?" Sai Annabi Muhammad (S.A.W) yace "Idan ta yi shiru".
Bukhari da Muslim

2. A wani hadisin Nana Aisha ce ta ce "Ya Ma'aikin Allah, hakika budurwa tana da kunya" Sai ya ce "Yardarta shi ne shirunta".

A karkashin wayannan hadisai malamai suka tafi a kan cewa ana neman izinin budurwa, dalilin da yasa ita bazawara za a nemi umarninta shi ne; ita bazawara ba ta da nau'in kunya irin wadda budurwa take da shi.

Imam Sufyan yana cewa "Ana cewa budurwa idan kin yarda kiyi shiru, in baki yarda ba kiyi magana. Har sau uku..."
Imam San'aniy kuma cewa ya yi "Wannan hadisi (na neman izinin budurwa) gamamme ne a kan dukkan waliyyai uban budurwar ko waninsa. Kuma babu makawa sai an nemi izinin ta".
Subulus salaam: 3/167.

Don haka ba ya halatta ga iyaye su yiwa yarsu auren dole barin ma ace idan muka duba irin wannan zamani da muke rayuwa a ciki.
Da soyayyar ma ya auren ya kasance bare babu?
Ai ka iya cewa "Me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki."

Shin akwai wani hukunci da ya bayyana zamanin Annabi a kan wanda aka yi wa auren dole na tabbatarwa ko hanawa.


Auren Dole a Zamanin Manzon Allah

Ko akwai wani abu da ya faru a zamanin Annabi a kan auren dole, kuma me Annabi ya zartar shin ya tabbatar da auren ko kuma ya raba shi?

Amsa.
1. Akwai hadisi da ya tabbata cewa Khansa'a bnt Khudaam Al'ansariyya babanta ya aurar da ita lokacin ta na bazawara ita kuma ba ta son auren. Sai taje wajen Annabi ta sanar da shi. Sai ya raba auren.
Irwa'ul galeel 1830.

2. Ibn Abbas ya rawaito cewa wata tazo wajen Annabi ta sanar da shi cewa babanta ya aurar da ita ga wanda ba ta so, sai Annabi ya ba ta zabi.
Ibn majah 1520

A nan kai tsaye za mu fuskanci Allah da manzonsa ba sa goyon bayan auren dole.

Da ace auren dole abin so ne da Annabi ya zartar da shi ga Bareera, wadda aka yanta ta, ta rabu da mijinta... Kissar Barira (R.A) da mijinta Mugith tana daya daga cikin labarai mafi ratsa zuciya da aka samu a tarihin sahabbai, wanda har Manzon Allah (S.A.W) ya yi mamakin girman soyayyar da ke cikinta.


Barira bawa ce (baiwa) a gidan wasu mutane, kuma tana da aure da wani bawa mai suna Mugith. A wancan lokacin, shari’ar Musulunci ta tanadi cewa idan baiwa mace ta samu yanci, tana da zabin ko dai ta ci gaba da zama da mijinta (idan shi bawan ne har yanzu) ko kuma ta rabu da shi.

Sayyada Aisha (R.A) ta fanshi Barira ta 'yanta ta. Bayan Barira ta zama yantacciya, sai ta zabi ta raba aurenta da Mugith.

Shi kuwa Mugith yana matukar son Barira da matsananciyar soyayya. Bayan ta rabu da shi, sai abin ya zama masa babban kalubale. An ruwaito cewa:

  • Mugith ya kasance yana bin Barira a cikin lungunan Madina yana kuka.

  • Hawayensa har jiƙa gemunsa suke yi domin tsananin bakin cikin rabuwa da ita.

  • Yana rokonta da ta dawo gare shi, amma ita kuma tuni ranta ya karkata ga rashin son ci gaba da zaman.

Abin ya kai ga har Manzon Allah (S.A.W) ya ga halin da Mugith yake ciki, sai ya ce wa kawunsa Al-Abbas:

"Ya Abbas, ba ka mamakin tsananin son da Mugith yake wa Barira, da kuma tsananin ƙin da Barira take wa Mugith?"

Manzon Allah (S.A.W) saboda tausayawa Mugith, sai ya je wajen Barira ya ce mata:

"Da za ki koma wajen mijinki (Mugith)?"

Barira ta san matsayin Manzon Allah (S.A.W), amma kuma ta san hakkinta na yanci da musulunci ya ba ta. Sai ta tambayi Manzon Allah (S.A.W):

"Ya Manzon Allah, umarni kake ba ni (wanda dole in bi) ko kuma ceto kake yi (shawara)?"

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya amsa mata da cewa:

"A'a, kawai ina yin ceto ne (ina nema masa alfarma)."

Sai Barira ta ce:

"To ba ni da bukatar sa."

Manzon Allah (S.A.W) bai matsa mata ba, kuma bai nuna fushi ba, domin ya san cewa aure bukatar zuciya ne kuma hakki ne na mutum ya zaba wa kansa.

Darussan da ke Cikin Kissar

  • Iyakokin Soyayya: Soyayya ba tilas ba ce; ko mutum yana sonka sosai, idan ba ka jinsa a ranka addini bai tilasta ka zauna da shi ba. Idan ba a sonka ka hakura kawai, ka da ka yi ta tilastawa a kan dole sai an so ka.

  • Adalcin Manzon Allah (S.A.W): Shugaban halitta bai yi amfani da matsayinsa na Annabi ya tilasta wa baiwar da aka 'yanta ta koma wa tsohon mijinta ba.

  • Hakkokin Mata: Kissar ta nuna cewa mace tana da ikon fadin ra'ayinta a kan wanda take so ta aura ko wanda take so su rabu.

Wannan labarin yana nuna mana yadda Musulunci ya gina zamantakewa a kan yarda da gaskiya, ba a kan dole ba.


A ƙarkashin wannan Ibn Qayyim yake cewa " Wannan ceto ne daga shugaban masu ceto, ga masoyi izuwa abin da yake so, wannan kuwa shi ne mafi girman ceto kuma mafi girman lada a wajen Allah".
Raudatul muhibbeen

A cikin wannan littafi (Raudatul Muhibbeen), babi guda ya buɗe a kan haɗa masoya da Annabi da sahabbansa su kai da kuma taimakawarsu wajen haɗa masoyan da suka rabu.

Ko a iyakar nan zamu gane cewa a addini babu auren dole babu kayansa.


Shin ya Halatta Uba ya Zabawa Yarsa Miji?

Tambaya
Shin yaya kuma za mu yi da aikin wasu sahabban kamar yadda Sayyadina Umar ya aikata wajen zuwa wajen Sayyadina Usman da Sayyadina Abubakar a kan ya auri yarsa Nana Hafsa?

Eh wannan ya halatta yana da kyau mutum ya bijirowa yarsa mutanen kirki sai dai kuma hakan ba yana nuna auren dole ba ne. Domin kuwa in suka zo din dai sai an nemi izininta.

Tambaya
To ai wani lokacin laifin matan ne, domin ba sa zaben nagari, su kuma iyaye saboda rashin dacewar wanda yayan suka zabo ko suke zabowa sai su zartar da hukunci su bayar da su ga wanda suke ganin ya dace a wajensu. Me zakuce a kan hakan?

A wasu lokutan akwai laifin mata ko maza domin kuwa ba sa zaben wayanda suka dace, sai ka samu budurwa tana kula samari barkatai kuma cikinsu babu na kirki ko guda don haka wani lokaci iyayen suke zabo mata wanda suke ganin na kirki ne. Kuma su dau alwashin koma menene zai faru sai sun aura mata shi domin shi ne zai iya kama hannunta ya kai ta zuwa ga Aljannar Allah.

Shi ice tun yana danye a ke tankwara shi, don haka iyaye tun yayansu suna kanana ya kamata su gina musu rayuwarsu, akwai hanyoyin dabam dabam na bayar da tarbiyya wanda yana da kyau dukkan iyaye su sansu...


Zamu ambato su a rubutunmu kebantacce a kan tarbiyyar yara.

Tarbiyya ita ce za ta saka ita kan ta budurwa ba za ta kula wanda bai cancanta ba, tarbiyya ita za ta saka budurwa da kanta ta zabo wanda iyayenta za su yaba da shi.

Wasu iyayen kuma son abin duniya ne yake sanyawa suke yiwa yayansu auren dole. ....

Tabbas ana samun haka, da yawa a kan samu budurwa akwai wanda take so kuma ya cancanta, amma saboda iyayenta sun ga wani mai kudi sai su biyewa wannan mai kudin ba su damu da cewa wannan budurwa ta na sonsa ko ba ta sonsa ba. Wanda irin wannan auren zalunchi ne. Domin sun raba yarsu da abin da take so, kuma sun jefa rayuwarta cikin wata sarkakiya wanda tana rayuwarne tsakanin mutuwa-da-rayuwa.


Don yarsu ce hakan ba shi ne ke nuna suna da ikon suyi komai da suka ga dama a kanta ba domin hadisi ya tabbata cewa "Dukkaninku makiyaya ne (masu kiwo), kuma dukkaninku za a tambayeku abin da kuka kiwata."

Sa'annan shima wanda a ka aurawa din yana da laifi mutukar ya san ba ta sonsa. Domin an hada kai da shi an zalunceta kenan.

Abin da ya dace shi ne idan ya fuskanchi ba ta sonsa da gaske to ya janye ya kyaleta. Idan yayi haka to tabbas zai samu sakamako mai kyau.

Ahmad ya rawaichi wani hadisi Annabi yake cewa "Wanda ya bar wani abu saboda Allah, Allah zai musanya masa da wanda ya fi shi alheri".

Sannan abin sani a gurin masoya na gaskiya shi ne

Masoyi yana sadaukar da jin dadin zuciyarsa, don samuwar jin dadin abin da yake so, koda kuwa hakan zai cutar da shi. Don haka idan har masoyin kwarai ne, idan har ya san zama da shi zai cutar da ita tabbas zai hakura ya janye.

Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta. Ya kuma nuna mana karya karya ce, ya bamu ikon guje mata.
Ameen


Akwai Wata Matsalar 

Kamar yadda mu ka ji laifin iyaye da mata da suke taimakawa wajen auren dole. A wata gabar kuma za ka samu cewa akwai wasu samarin da su  din sun cancanta kuma yarinyar tana sonsa amma cikas din kawai shi ne suna ta kokarin kulla wannan alakar kwata kwata ba tare da sanin magabatan yarinyar ba, haka za ka ga da lokaci yayi da iyayen wannan yarinyar suke sonsu aurar da yarsu ya yi kuma su ka ga yarsu ba ta fito da wani da take so ba, sai kaga kuwa sun bijiro mata da mijin aure daga bangarensu, koda kuwa ba ta son shi in an tambaye ta sai ka ji tace tana so sakamakon wancen din bai yi shirin aure ba.

To a nan shawarar mu ita ce, duk saurayin da ya ga yarinyar da ta kwanta mi shi kuma ya tabbatar ya yi addu'a har ma yana kyautata zaton ita din alkhairi ce a gare shi kuma suka sami fahimtar juna da wannan yarinyar to abu na farko da mutum ya dace ya yi shi ne ya sami hanyar sanar da magabatan wannan yarinyar tun da dama can sun fahimci juna da ita.

Duk da wannan hanyar ba ita ce hanyar da addini ya tanada ba.

Hanyar da addini ya tanada ita ce in ka ga yarinya kafin ka fara doso mata da wata magana ya dace ka fara da neman iznin iyayenta. Su kuma iyayen wannan yarinya alhakinsu ne su duba nagartar ka su ga ka dace ka nemi auren yarsu ko ko a'a.

To a nan inka dace sai su sanar da yarsu cewa akwai wane za ku gana to a nan ya dace ma ita yarinyar har tai kwalliya saboda kwalliya ta halatta ga mai neman aurenta, to daga nan in suka gana kamar na dan lokaci sai a tambaye ta in ya yi mata to sai a fara zancen aure in kuma bai yi mata ba kuma ba dole shi ke nan.

Wannan shi ne ya dace da hadithin da Annabi S.W.A yake cewa "idan wanda kuka yarda da addininsa da amanarsa ya zo muku to ku aura masa idan ba ku aikata hakan ba fitina za ta faru a ban kasa."

Amma yanzu a irin wannan lokacin za ka iske cewa saurayi da budurwa sun shafe wani lokaci me tsayi suna alaka irin ta soyayya ba tare da sanin mahaifanta ba. Sai daga baya kuma idan lamari ya cakude sai ka ga abu sam bai yi dadi ba.

Kusan yanzu abin da yake faruwa shi ne gudanar da alakar soyayya tsakanin masoyan biyu ba tare da sanin manya ba. Ta inda za ka ga an shafe shekaru da dama ana gafara sa amma ba a ga kaho ba.

Su kuma iyayen sai su zubawa yarinya ido almajirai su yi ta sintiri ana fadin wai wance ta zo in ji wane kamar ajiyar ta ya bayar. Sai bayan wani  lokaci ne za ka ji iyaye sun cewa yarinya a cikin masu zuwan nan ki fito da wanda kike so kice ya aiko...
Da zarar ya aiko kuma sai a ce za ai binkice, idan ko a kai binkice cikin rashin sa'a bai dace ba, a sannan uba zai cewa yarsa bai yarda da alakarta da wannan yaron ba... Daga nan sai ya fito mata da wani ya ce shi zai aura mata da sunan auren dole. Ita ko  yarinya tuni ta gama narkewa a son wani.

Don haka ya dace iyaye su fito da tsarin  hana yaransu kule kulen samari ba tare da   binciken dabi'un samarin ba.


Za ai min Auren Dole ya Zan yi

Kamar yadda muka ji hukuncin auren dole da kuma matsalolin da suke sanyawa a yiwa wasu auren dolen yana da kyau mu waiwaya ga wayanda suka samu kansu a cikin halin auren dole.....

Lokacin da ya zamana iyaye sun miki auren dole to abin da ya dace shi ne ki yi hakuri ki yi biyayya mutukar babu hanyar kaucewa auren dolen. Hanyar  kaucewar kuma ba wai ina nufin yi musu tawaye ba ko kuma aibata su. Ina nufin zuwa wajen wani na gaba da su, ko amininsu da neman ya bayyana musu irin halin da suke kokarin sanya ki.

Hakika an rawaici hadisi cewa "wanda ya bar wani abu yayi hakuri a kai saboda Allah, Allah zai musanya masa mafi alheri".
Haka nan kuma wanda ya miƙawa Allah lamuransa ya bi abin da iyayen nasa suka zartar, tabbas zai samu lada mai yawa tare da samun sakamako. Domin kuwa sauda dama Allah yana jarrabar mutane domin ya ga shin za su gode ko zasu kafirce. In suka yi hakuri suka godewa Allah sai ya sauya musu sannan kuma ya mayar da wannan abin da ya jarrabesu da shi mafi girman ni'imominsa a garesu.

Ta iya yiwuwa kuma akwai wani matsayi da Allah ya ke so ya b asu a lahira wanda aikinsu ba zai kai su wajenba don haka sai ya bijiro musu da wannan jarrabawa don in sukayi hakuri su kai wannan matakin a Aljanna.

Amma azabtar da kai ta hanyar sanya damuwa a cikin zuciya ba zai amfanar ba, sai dai ma ya kore ladan jarrabtar da Allah y ayi wa wanda aka jarraba din, ka ga an yi biyu babu ga jarrabawa ga rashin sakamako mai kyau.

Wanda kuma ya kai ga matakin kashe kansa wannan Annabi ya fada a ma'anar wani hadisin bukhari cewa; wanda ya kashe kansa da wani abin kisa karfe, guba, ko rataya to za a halittar masa wannan abin a wutar jahannama a yi ta azabtar da shi da abin zai dawwama a ciki a haka...

Allah yana tare da masu hakuri, kuma yana son masu hakuri, hakanan shi hakuri haske ne a nan duniya da can kiyama.

A ƙarshe za mu ba wa mata shawarar cewa duk lokacin da kika ga wani har alakar soyayya ta shiga tsakani, to kai tsaye ki yi masa maganar cewa ya je ya samu iyayenki, don su san da maganar tunda wuri.

Wannan zai sa su kuma su ji daga gareshi, a nan za su fuskanchi zai iya aurenki ko kuwa wasa ya zo yi. Sannan sunada wadataccen lokaci da za su ba shi harma su yi bincike a nutse. Kuma da yawan wayanda ba nagari ba a na cewa su fito ko su turo magabata ake nemansu a rasa.

Misali kina level 1 su kuma sunaso sai kinyi degree za su aurar da ke, to kinga a nan za su gaya masa nan da shekara uku zuwa hudu suke buqatar aurar da ke.... Duk da dai ana sukar alaka mai dogon zango irin wannan. Amma duba da yanayi yasa ake yin uzuri da wasu abubuwa da dama.

Allah muke roko ya karbi wannan aiki, ya sanya ya amfanar da yan'uwa musulmi.

Wannan shi ne karshen wannan rubutu Insha Allah.

A nan zamu dakata, sai kuma a wani rubutun dabam tare da mu.

Abu Umar Alkanawy
&
Shifaa Khamis Adam

Comments

  1. Masha Allah, Allah y zaba Mana Mafi alkhairi.

    ReplyDelete
  2. Allah yasa mu dace Ya haɗa mu da abokan zama na gari

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

KNOWLEDGE AND ITS NEGATIVE EFFECT...

JAN HANKALI GA ƊALIBAN KIMIYYA

PUBLIC DANCE!!!