AUREN DOLE.
Wannan takaitaccen fadakarwa ce akan auren dole, hukuncinsa a addini da kuma shawarwari....
Mun tattara bayanan ne don amfanuwar Malamai, Dalibai, Iyaye, matasa da wasunsu.
Aikin da mukai na dai-dai daga Allah ne, wanda mukayi na kuskure kuma dama mu yan Adam ne, muna rokon Allah daya gafarta mana. Ya kuma sanya littafin ya zama mai amfamarwa ne ga daukacin yan'uwa musulmi.
Tare da mu
Dan uwanku.
Naseeb Abu Umar Alkanawiy.
Da yar'uwarku.
Shifaa khamis Adam.
AUREN DOLE 0⃣1⃣
Tabbas soyayya jigo ce mai girma a zamantakewar auratayya. Shiyasa Allah da kansa yake cewa...
"Yana daga cikin ayoyinSa ne, ya halitta muku matan aure daga rayukanku, domin ku nutsu zuwa gareta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani."
Rum:21
Hakanan Annabin rahama yake fada cewa "Banga abinda yafi dacewa da masoya biyu ba sama da suyi aure".
Anan zamu gane cewa soyayya jigo ce a cikin aure kuma da itane aure yake zama.
Auren dole wani aure ne, da ake tilastawa wani sashe donya auri wani ba tare da yana sonsa a zuciyarsa ba.
Shin me musulunchi yace gami da auren dole?
Kamar yadda muka fada cewa soyayya jigo ce a zamantakewar auratayya kuma mukaji daga fadin Allah da manzonSa, hakan zai nuna mana cewa musulunchi baya goyon bayan auren dole, baya ga hakan kuma akwai dalilai da sukafi wayannan fitowa fili.
1. An karbo hadisi daga Abu Huraira (R.A), Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa "Ba'a aurar da bazawara harsai an nemi umarninta, kuma ba'a aurar da budurwa har sai an nemi izininta". Sai sahabbai sukace " Yaya za'a gane izininta?" Sai Annabi Muhammad (S.A.W) yace "Idan tayi shiru".
Bukhari da Muslim
2. A wani hadisin Nana Aisha ce tace "Ya Ma'aikin Allah, hakika budurwa tana da kunya" Sai yace "Yardarta shine shirunta".
A karkashin wayannan hadisai malamai suka tafi akan cewa ana neman izinin budurwa, dalilin da yasa ita bazawara za'a nemi umarninta shine; ita bazawara bata da na'in kunya irin wadda budurwa take da shi.
Imam sufyan yana cewa "Ana cewa budurwa idan kin yarda kiyi shiru, in baki yarda ba kiyi magana. Har sau uku..."
Imam san'aniy kuma cewa yayi "Wannan hadisi (na neman izinin budurwa) gamamme ne akan dukkan waliyyai uban budurwar ko waninsa. Kuma babu makawa sai an nemi izininta".
Subulus salaam Vol:3/167.
Don haka baya halatta ga iyaye su yiwa yarsu auren dole barinma ace idan muka duba irin wannan zamani da muke rayuwa a ciki.
Da soyayyar ma ya auren ya kasance bare babu?
Aika iya cewa "Me neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki."
Shin akwai wani hukunci daya bayyana zamanin Annabi akan wayanda akaiwa auren dole na tabbatarwa ko hanawa.
Zamuji wannan a rubutu na gaba.
AUREN DOLE 0⃣2⃣
Ko akwai wani abu daya faru a zamanin Annabi akan auren dole, kuma me Annabi ya zartar shin ya tabbatar da auren ko kuma ya raba shi?
_Amsa_.
1. Akwai hadisi daya tabbata cewa khansa'a bnt khudaam Al'ansariyya babanta ya aurar da ita lokacin tana bazawara ita kuma bata son auren. Saitaje wajen Annabi ta sanar dashi. Sai ya raba auren.
Irwa'ul galeel 1830.
2. Ibn Abbas ya rawaito cewa wata tazo wajen Annabi ta sanar dashi cewa babanta ya aurar da ita ga wanda bata so, sai Annabi ya bata zabi.
Ibn majah 1520
Kaga anan kai tsaye zamu fuskanci Allah da manzonsa basa goyon bayan auren dole.
Da'ace auren dole ya abin sone fa Annabi ya zartar dashi ga bareera, wadda aka yanta ta, ta rabu da mijinta... Ya rinka binta hawayensa yana satatuwa yana biyowa ta gemunsa saboda yawa akan ta soshi ta dawo wajensa amma tace bata sonsa🤦🏻♂.. Sai Annabi yace mata "Dama dai ki koma wajensa tunda shine uban danki", sai tacewa Annabi "Umarni kake bani?" Sai Annabi yace mata "a'a ninazo shawara ne ko ceto" sai tace "Bana bukatarsa".
Kaga anan tausayi ne yasa har Annabi ya sanya baki yayi biko, amma data ce bata sonsa Annabi bai takura mata yace saita so shi ba.
A karkashin wannan ibn qayyim yake cewa " Wannan ceto ne daga shugaban masu ceto, ga masoyi izuwa abinda yake so, wannan kuwa shine mafi girman ceto kuma mafi girman lada a wajen Allah".
Raudatul muhibbeen
A cikin wannan littafi babi guda ya bude akan hada masoya da Annabi da sahabbansa sukai da kuma taimakawarsu wajen hada masoyan da suka rabu.
Ko a iyakar nan zamu gane cewa a addini babu auren dole babu kayansa.
Tambaya?
Shin yaya kuma zamuyi da aikin wasu sahabban kamar yadda sayyadina umar ya aikata wajen zuwa wajen sayyadina usman da sayyadina Abubakar akan ya auri yarsa nana hafsat?
Eh wannan ya halatta yana da kyau mutum ya bijirowa yarsa mutanen kirki saidai kuma hakan ba yana nuna auren dole bane. Domin kuwa in suka zo din dai sai an nemi izininta.
Tambaya
To ai wani lokacin laifin matan ne, domin basa zaben nagari, su kuma iyaye saboda rashin dacewar wanda yayan suka zabo ko suke zabowa saisu zartar da hukunci su bada su ga wanda suke ganin ya dace a wajensu. Me zakuce akan hakan.
AUREN DOLE0⃣3⃣
A wasu lokutan akwai laifin mata ko maza domin kuwa basa zaben wayanda suka dace, saika samu budurwa tana kula samari barkatai kuma cikinsu babu na kirki ko guda don haka wani lokaci iyayen suke zabo mata wanda suke ganin na kirki ne. Kuma su dau alwashin koma menene zai faru saisun aura mata shi domin shine zai iya kama hannunta yakaita zuwa ga Aljannar Allah.
Shi ice tun yana danye ake tankwarashi, don haka iyaye tun yayansu suna kanana ya kamata su gina musu rayuwarsu, akwai hanyoyin dabam dabam na bada tarbiyya wanda yana da kyau dukkan iyaye su sansu...
Zamu fadesu a rubutunmu kebantacce akan tarbiyyar yara.👌🏻
Tarbiyya itace zata saka ita kanta budurwa bazata kula wanda bai cancanta ba, tarbiyya ita zata saka budurwa da kanta ta zabo wanda iyayenta zasu yaba dashi.
Wasu iyayen kuma son abin duniya ne yake sanyawa suke yiwa yayansu auren dole. ....
Tabbas ana samun haka, da yawa akan samu budurwa akwai wanda take so kuma ya cancanta, amma saboda iyayenta sunga wani mai kudi saisu biyewa wannan mai kudin basu damu da cewa wannan budurwa tana sonsa ko bata sonsa ba. Wanda irin wannan auren zalunchi ne. Domin sun raba yarsu da abinda take so, kuma sun jefa rayuwarta cikin wata sarkakiya wanda tana rayuwarne tsakanin mutuwa-da-rayuw.
Don yarsu ce hakan ba shine ke nuna sunada ikon suyi komai da sukaga dama akanta ba domin hadisi ya tabbata cewa "Dukkaninku makiyaya ne (masu kiwo), kuma dukkaninku za'a tambayeku abinda kuka kiwata."
Sa'annan shima wanda aka aurawa din yana da laifi mutukar yasan bata sonsa. Domin an hada kai dashi an zalunceta kenan.
Abinda ya dace shine idan ya fuskanchi bata sonsa da gaske to ya janye ya kyaleta. Idan yayi haka to tabbas zai samu sakamako mai kyau.
Ahmad ya rawaichi wani hadisi Annabi yake cewa "Wanda yabar wani abu saboda Allah, Allah zai musanya masa da wanda ya fishi alheri".
Sannan abin sani a gurin masoya na gaskiya shine
Masoyi yana sadaukar da jin dadin zuciyarsa, don samuwar jin dadin abinda yake so, koda kuwa hakan zai cutar dashi. Don haka idan har masoyin kwarai ne, idan har yasan zama dashi zai cutar da ita tabbas zai hakura ya janye.
Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta. Ya kuma nuna mana karya karya ce, ya bamu ikon guje mata.
Ameen
AUREN DOLE 0⃣4⃣
Kamar yadda mukaji layfin iyaye da mata dasu ke taimakawa wajen auren dole.a wata gabar kuma zaka samu cewa akwai wasu samarin da su din sun cancanta kuma yarinyar tana sonsa amma cikas din kawai shine suna ta qoqarin qulla wannan alaqar kwata kwata ba tare da sanin magabatan yarinyar ba, haka zaka ga da lokaci yayi da iyayen wannan yarinyar suke sonsu aurar da yarsu yayi kuma su kaga yarsu bata fito da wani da take so ba, sai kaga kuwa sun bijiro mata da mijin aure daga bangarensu, koda kuwa bata sonshi in an tambaye ta sai kaji tace tana so sakamakon wancen din baiyi shirin aure ba.
To anan shawarar mu itace ,da saurayin da yaga yarinyar da ta kwanta mishi kuma ya tabbatar yayi addua har ma yana kyautata zaton ita din alkhyri ce agareshi kuma suka sami fahimtar juna da wannan yarinyar to abu na farko da mutum ya dace yayi shine ya sami hanyar sanar da magabatan wannan yarinyar tun da dama can sun fahimci juna da ita.
Duk da wannan hanyar ba itace hanyar da addini ya tanada ba.
Hanyar da addini ya tanada itace in ka ga yarinya kafin ka fara doso mata da wata magana ya dace ka fara da neman iznin iyayenta.su
Kuma iyayen wannan yarinya alhakinsu ne su duba nagartar ka su ga ka dace ka nemi auren yarsu ko ko a'a.
To anan inka dace sai su sanar da yarsu cewa akwai wane zaku gana to anan yadace ma ita yarinyar har tai kwalliya sbda kwalliya ta halarta ga mai neman aurenta.to daga nan insuka gana kamar na dan lokaci sai a tambaye ta in yayi mata to sai anfara zancen aure in kuma bai yi mata ba kuma ba dole shikenan.
Wannan shine ya dace da hadithin da Annabi S.W.A yake cewa "idan wanda kuka yarda da addininsa da amanarsa yazo muku to ku aura masa idan baku aikata hakan ba fitina zata faru a aban qasa."
Amma yanxu a irin wannan lokacin zaka iske cewa saurayi da budurwa sun shafe wani lokaci me tsayi suna alaqa irinta soyayya ba tare da sanin mahaifanta ba.sai daga baya kuma idan lamari ya cakude sai kaga abu sam baiyi dadi ba.
Kusan yanzu abunda yake faruwa shine gudanar da alaqar soyayyah tsakanin masoyan biyu ba tare da sanin manya ba.ta inda zaka ga an shafe shekaru da dama ana gafara sa amma baa ga kaho ba.
Su kuma iyayen sai su zubawa yarinya ido almajirai suyita sintiri ana fadin wai wance tazo inji wane kamar ajiyar ta yabayar.sai bayan wani lokaci ne zakaji iyaye sun cewa yarinya acikin masu zuwannan ki fito da wanda kike so kice ya aiko....
Da zarar ya aiko kuma sai kaji ana za'ai binkice, idan ko akai binkice cikin rashin saa bai dace ba,to a sannan uba zaicewa yarsa bai yadda da alaqarta da wannan yaron ba daganan sai ya fito mata da wani yace shi zai aura mata dasunan auren dole kenan ,ita ko yarinya,tuni ta gama narkewa a son wane.
Don haka ya dace iyaye su fito da tsarin hana yaransu kule kulen samari ba tare da binciken dabi'un wannan saurayi ba.
AUREN DOLE 0⃣5⃣
Kamar yadda muka ji hukuncin auren dole da kuma matsalolin da suke sanyawa ayiwa wasu auren dolen yana da kyau mu waiwaya ga wayanda suka samu kansu a cikin halin auren dole.....
Lokacin da ya zamana iyaye sun miki auren dole to abinda ya dace shine kiyi hakuri kiyi biyayya mutukar babu hanyar kaucewa auren dolen. Hanyar kaucewar kuma bawai ina nufin yi musu tawaye ba ko kuma aibatasu. Ina nufin zuwa wajen wani nagaba da su, ko amininsu da neman ya bayyana musu irin halin da suke kokarin sanyaki.
Hakika an rawaici hadisi cewa "wanda yabar wani abu yayi hakuri akai saboda Allah, Allah zai musanya masa mafi alkairi".
Hakanan kuma wanda ya miqawa Allah lamuransa yabi abinda iyayen nasa suka zartar tabbas zai samu lada mai yawa tare da samun sakamako. Domin kuwa sauda dama Allah yana jarrabar mutane domin yaga shin zasu gode ko zasu kafirce. In suka yi hakuri suka godewa Allah sai ya sauya musu sannan kuma ya mayar da wannan abin daya jarrabesu dashi mafi girman ni'imominsa a garesu.
Ta iyayiwuwa kuma akwai wani matsayi da Allah yake so ya basu a lahira wanda aikinsu bazai kaisu wajenba don haka saiya bijiro musu da wannan jarrabawa don in sukayi hakuri sukai wannan matakin a Aljanna.
Amma azabtar dakai ta hanyar sanya damuwa a cikin zuciya bazai amfanar ba, saidai ma ya kore ladan jarrabtar da Allah yayiwa wanda aka jarraba din, kaga anyi biyu babu ga jarrabawa ga rashin sakamako mai kyau.
Wanda kuma ya kai ga matakin kashe kansa wannan Annabi ya fada a ma'anar wani hadisin bukhari cewa; wanda ya kashe kansa da wani abin kisa karfe, guba, ko rataya to za a halittar masa wannan abin a wutar jahannama ayita azabtar dashi da abin zai dawwama a ciki a haka.....
Allah yana tare da masu hakuri, kuma yana son masu hakuri, hakanan shi hakuri haske ne anan duniya da can kiyama.
A karshe zamu bawa mata shawarar cewa Duk lokacin da kika ga wani har alaqar soyayya ta shiga tsakani to kai tsaye kiyi masa maganar cewa yaje ya samu iyayenki, don su san da maganar tunda wuri.
Wannan zaisa su kuma suji daga gareshi, anan zasu fuskanchi zai iya aurenki ko kuwa wasa yazo yi. Sannan sunada wadataccen lokaci da zasu bashi harma suyi bincike a nutsu.
Misali kina level 1 su kuma sunaso sai kinyi degree zasu aurar da ke, to kinga anan zasu gaya masa nanda shekara uku zuwa hudu suke buqatar aurar dake.... Duk da dai ana sukar alaqa mai dogon zango irin wannan. Amma duba da yanayi yasa ake yin uzuri da wasu abubuwa da dama.
Allah muke roko ya karbi wannan aiki, ya sanya ya amfanar da yan'uwa musulmi.
Wannan shine karshen wannan rubutu Insha Allah.
Anan zamu dakata, sai kuma a wani rubutun dabam tare da mu.
Naseeb Abu Umar Alkanawy
&
Shifaa Khamis Adam
Masha Allah, Allah y zaba Mana Mafi alkhairi.
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDelete