ƘARYA

ƘARYA.
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA ANNABIN RAHAMA SHUGABA JA GABA DA AHALINSA TARE DA SAHABBANSA DA WAYANDA SUKA BIYO BAYANSU DA KYAUTATAWA.

NA SHAIDA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH KUMA ANNABI MUHAMMAD BAWANSA MANZONSA NE. 
HAKIKA MAFI GASKIYAR ZANCE SHINE LITTAFIN ALLAH, KUMA MAFI ALHERIN SHIRIYA ITACE SHIRIYAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W), MAFI SHARRIN AL'AMURA KUWA SUNE WAYANDA AKA FARAR, KUMA DUKKANIN FARARREN ABU BIDI'A NE, KUMA DUKKANIN BIDI'A ƁATA CE.

BAYAN HAKA, WANNAN WANI TAƘAITACCEN RUBUTU NE DA NAKE SO IN BIJIROWA YAN UWA SHI DON TUNATARWA DA KUMA FAƊAKARWA AKAN WANI MUHIMMIN ABU MAI GIRMA WANDA SABO DA SHI YA SANYA DA YAWANMU MUN DAINA GANIN GIRMANSA. BA WANI ABU BANE WANNAN FACE ƘARYA. 
INA ROƘON ALLAH DA YA SANYA WANNAN AIKI YA ZAMO DON SHI AKAYI, YA KUMA KARƁI AIKIN, HAƘIƘA SHI MAI IKO NE MAI KUMA KARAMCHI NE.

ƘARYA
Ƙarya dai sananniyar aba ce, domin kuwa koda yaushe tana kaikawo a cikin mutane, sai dai duk da haka zamu so muji mecece ƙaryar da kuma abubuwan da ta ƙunsa.

Idan akace ƙarya ana nufin kishiyar gaskiya, kuma gaskiya mun sani itace faɗar abu a bisa yanda yake, ko bada labarin abu a bisa yanda yake a zahiri. Idan muka gane wannan shine gaskiya, to ƙarya kenan zata zamo faɗar abu ko bada labari saɓanin yanda yake. Shahararren malamin nan na musulunci Imam Nawawi yana cewa a cikin sharhin sahihul Muslim.

 الإخبار عن الشيء على خلاف ما هو، عمدًا كان أو سهوًا، سواء كان الإخبار عن ماض أو مستقبل
Ma'ana 
Bada labarin wani abu bisa saɓanin yadda yake. Da gangan ko cikin rashin sani, kodai akan abin da ya wuce ko kuma wanda zai zo nan gaba.
Har ila yau ƙarya tana shiga cikin kore gaskiya, a zo a gaya maka gaskiya ka wancakalar da ita, ko a nuna maka gaskiya kaƙi karɓarta, ko kayi rubutu don saɓanin gaskiya duka wannan yana cikin ƙarya.
Dangane da ayoyin Qur'ani da sukai magana game da ƙarya kuwa suna da mutuƙar yawa. 

Idan mun fahimta zamu gane cewa ƙarya tana iya kasuwa gida uku. 
1. Ƙarya ta magana.
2. Ƙarya ta ayyuka.
3. Ƙarya ta niyya.

Ƙarya ta magana itace ƙarya irin wadda mutum zai bada labarin wani abu wanda ba gaskiya ba, kamar wayanda suke ƙaryata ayoyin Allah hakanan masu rubuta ƙarya suce daga Allah take suma zan iya sakasu a wannan gidan domin rubutu ɗan uwan magana ne. Idan munzo maganar matakan ƙarya zamu tattauna akan hakan Insha Allah.

Ƙarya ta ayyuka kuma shine bayyana wani aiki wanda ba gaskiya ba, kamar kukan ƙarya, lanjarewa don a zaci mutum baida lafiya ko nakasashshe ne. A hausance dama in aka ce abu na ƙarya ne to ana nufin na boge ne ko baikai zuci ba, misali a wasan kwaikwayo zaka iya ganin mutum yana kuka shaɓe-shaɓe amma a zahirin gaskiya ba kukan gaske ne, kukan ƙarya ne kawai.

Ƙarya ta niyya kuma shine yin wani aiki da nuna cewa don Allah ake maimakon ba don Allah ake wannan aikin ba.

Dangane da ayoyin QUR'ANI, Akwai ayar da take magana akan masu gaskiya take cewa:
{لِيَسْأَلَ الصَّادِقِينَ عَن صِدْقِهِمْ} 
[الأحزاب:8].
Ma'ana
Lallai za'a tambayi masu gaskiya akan gaskiyarsu.

A ma'anar wata magana ta Ibn Qayyim Rahimahullah yana cewa "Idan har masu gaskiya za a tambayesu kuma za ai musu hisabi akan gaskiyarsu to ina kuma ga masu ƙarya?"
Mai gaskiya abinda yake faɗa haka yake, amma tare da hakan za a tambaye shi, ballantana kuma wanda ya karkace ya saki ƙarya.

A ma'anar wata aya data maimaitu a cikin suratul An'aam, A'araf da kuma Yunus. Allah yake cewa "Shin wanene yafi zalunchi fiye da wanda ya ƙirƙiri ƙarya ya jinginawa Allah ko kuma ya ƙaryata ayoyinSa?"
Tabbas babu wanda yakai wannan zalunci, domin kuwa zalunci shine ajiye wani abu ba a bigirensa ba, wanda kuwa ya ƙirƙiri ƙarya yace daga Allah take to lallai ya zo da zalunci mai girma.

Hakanan a ma'anar wata ayar dabam cikin surar Ɗaha Allah yana cewa "Hakika anyi mana wahayi cewa akwai azaba ga wanda ya ƙaryata kuma ya juya baya (barin karɓar gaskiya)."

A cikin suratul Baƙara Allah ya tabbatar da cewa "Haƙiƙa wayanda suka kafirce kuma suka ƙaryata ayoyinmu wayannan sune ma'abota wuta (Yan wuta)."

A cikin suratu Jathiya Allah yana cewa:
وَيْلٌ لِّكُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ
Ma'ana: "Azaba ta tabbata ga dukkanin mai ƙarya kuma mai yawaita zunubi."

A taƙaice dai, Qur'ani yana cike da ayoyi da suke maganar narko na azaba ga wanda yake ƙarya. Sawa'un shine ya ƙirƙireta ko kuma gujewa gaskiya yayi.

Dangane da Hadisai kuwa, zamu fara da hadisin Abu Huraira da yake cikin Bukhari (33) da Muslim (59) wanda a cikinsa Annabi ya ambaci alamomin munafiki a cikinsu kuma na farko shine "Idan yayi zance sai yayi ƙarya..."

Hakanan akwai wani Hadisin dai daga Abu Huraira (R.A) da yake cewa Annabin rahama yace "Ya ishi mutum ƙarya, ya bada labarin duk abinda yaji." Muslim (4)
Malamai suka ce wannan hadisin yana da ma'ana guda biyu.
Na farko: Mutumin da yake bada labarin da yaji alhalin yasan ƙarya ne.
Na biyu: Mutumin da baya bincike akan labaran da suka zo masa, komai ya ji kawai zai ɗorar ya kama bada labari.

Kowanne sashe daga cikin wayannan fassarori guda biyu laifi ne, musamman ma na farkon. Hakan kuma ba shine yake tseratar da na biyun ba, domin ayar Qur'ani sukutum tayi jan kunne da idan anzowa da mutum labari to ya tabbatar.

Akwai tabbataccen hadisi da Annabin rahama (S.A.W) yake cewa "Na haneku da ƙarya domin ƙarya tana shiryarwa izuwa fajirci, shi kuwa fajirci yana shiryarwa ne izuwa wuta. Mutum ba zai gushe yana ƙarya ba har sai an rubutashi a wajen Allah 'Maƙaryaci'." 
Bukhari da Muslim duka sun fitar da shi.

Ƙarya abace mai munin gaske kuma zaka iske kusan koma ince dukkanin lokacin da mutum yayi ƙarya guda ɗaya to sai wasu ƙarairayin sun biyo baya, ko don ƙawata wannan ƙaryar ta farko ko kuma don bata kariya.

Zartaccen abune a duniya kuma dukkanin addinai da al'adu suna zargin ƙarya, tun a lokacin jahiliyya an san ƙarya abace mara kyau, kamar yadda tarihi ya nuna mana. Shin akwai wani mutum mai lafiyayyen hankali da zai goyi bayan ƙarya bayan shi kansa mai ƙarya ƙayata ta yake don tayi kama da gaskiya?
In ƙarya aba ce mai kyau me yasa wani babban mutum idan yayi bayani ba a cewa ƙarya ne, koda ƙaryar yayi sai dai a faɗa a bayan idonsa?

Ƙarya tana zubar da kimar mai yinta a idon duniya, shiyasa ko masu mulki ado ne ace mutum yana da gaskiya amma ba zaka taɓaji ance ai wane ko sarkin gari kaza yana burge duniya saboda ƙaryar sa ba.

Baya ga hadisai da ayoyi wayanda muka tsakoro wasunsu akwai maganganun magabata da dama wayanda da zamu ambace su da rubutun zai tsayi. Amma bari mu tsinto yan tsirari daga ciki.

A cikin littafin Adabud dunya wad deen na Imam Mawardiy yake cewa Sayyadina Umar (R.A) yana cewa "Gaskiya ta zubar min da kima hakan yafi soyuwa a gare ni da ƙarya ta ɗaukaka darajata, kuma hakan da wuya ko faruwar hakan ta ƙaranta."

Abin nufi da ace wani abu zai faru da idan yayi gaskiya kimarsa zata zube kuma idan yayi ƙarya kimarsa zata ƙaru to bazai wannan ƙaryar ba, shine yake maganar kuma irin wannan yanayin ma zai wahala kaga yazo. 

Hakanan na taɓa cin karo da maganar Abdullahi Ibn Mas'ud yana cewa "Mafi girman laifuka itace ƙarya."

Wani daga cikin magabata yake cewa "Abubuwa biyu basa haɗuwa, Ƙarya da dattako."

Ƙaryar da akai rangwame a kanta itama zaka iske ƙarya ce ta maslaha kamar ta ceton rai, za'a kashe wani mara laifi an biyo shi kai kasan inda ya ɓuya aka tambayeka kace baka ganshi ba, ko mata da mijin da suke bada labari don bawa junansu kariya a abinda yake halastacce, ko suke yabon juna... Fuskarki tana haske kamar farin wata. Ko wanda yake ƙoƙarin sasanta wasu, ko wanda ya miƙa lamuransa da Allah yake ɓoyewa bayi wata damuwarsa wadda bayyanata bai da fa'ida, don haka in aka tambayeshi kaine kai kaza ko kaza ne yake damunka sai yace a'a. Da sauransu wayanda idan akwai tsawon rai kuma da dama insha Allah zamu keɓantasu da rubutu na musamman.

Mafi girman ƙarya itace yin ƙarya zuwa ga Allah, kamar masu sauya abinda Allah ya saukar, ko masu da'awar mafarki an basu wata shari'a, ko musu halatta abubuwa da haramtawa ba tare da sanin hukuncin addini akai ba. Yin ƙarya ga Allah bisa duba ga nassin ayoyi yana gadar da shigar mutum wuta. 

Ƙaryar da take biyewa wannan baya itace ƙarya zuwa ga Annabi Muhammad (S.A.W) kamar yadda hadisi mutawatiri yazo cewa "Duk wanda yayi min (Annabi) ƙarya, to ya tanadi mazaunin sa a wuta." 

Bayan kuma sai ƙarya zuwa ga malaman addini ababen koyi wannan kuwa ya haɗe harda yiwa maganar su kwaskwarima da amfani da ita a inda bai dace ba. Wannan ne yasa Ibn Taimiyya Rahimahullah yace cewa "Bai dace ba mutum ya ɗauki maganar wani mutum ya fassarata bisa abinda bashi mai maganar yake nufi ba."

A taƙaice dai ita ƙarya gwargwadon girmanta da matsalar da zata janyo gwargwadon alhakin da mutum zai samu.

Dangane da masu tsara labarai kuma malamai sunyi sauƙi cewa indai rubutun mai ɗauke da darussa ne sannan cikinsa babu cin mutunci ko zarafin wata al'umma ko wani abu da haramcinsa yake sananne to babu laifi cikin hakan.

Allah ya kare mu daga faɗawa cikin maƙaryata.
Maƙaryaci tun a duniya yake kunyata.

Allah nake roƙo daya duba wannan aiki ya kuma sanya ya zama sanadin shiriyar mu. Allah ka jiƙan mabatanmu wayanda muke tare dasu Allah ya rabamu lafiya.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.