LALLAI AKWAI TAMBAYA DANGANE DA NI'IMOMIN RAYUWA

“Sa'annan kuma haƙiƙa lallai sai an tambayeku game da ni'imomi.” 

Duk wata ni'ima ta shiga cikin wannan, don haka idan Allah ya yiwa bawa wata ni'ima to tabbas ya shirya amsa tambayoyi ranar alƙiyama akan wannan ni'imar.

Cikin hadisi ingantacce riwayar muslim, Annabi Muhammad (S.A.W) da manyan sahabbansa da kuma mafi kusancin abokanansa (Abubakar da Umar) (R.A) yunwa ta fito da su, a ƙarshe suka samu abinci a gidan ɗaya daga cikin sahabbai mawadata, suka ci suka ƙoshi kuma Annabi ya basu tabbacin cewa sai an tambayesu dangane da wannan ni'imar.

Idan har abincin da ba kai ka nemo da guminka ba za'a tambayeka to ni'imomin da akai maka na lafiya da ƙwarewa a wani fanni na rayuwa sune mafi aula da'a tambaya.

Idan kanada ƙarfin tunani da hangen nesa to tabbas za'a tambaye ka akan wannan ni'imar.
Idan kana da fasahar tsara rubutu to tabbas za'a tambaye ka akan hakan.
Idan kana da balagar magana, ka iya yin magana wadda za'a fahimta kuma ka isar da saƙon da kake so, to tabbas za'a tambayeka akan wannan shima.
Kai hatta wayar hannu da social media accounts da kake da su sai an tambaye ka akansu. 
Kuma duka tambayar da za'ai maka shine ta wacce hanya ka tafiyar da su, shin ka taimaki addinin Allah da su ko kuwa more rayuwa kawai kayi da su.

Ka duba rayuwar mu ta yau, mutum ya samu lafiyayyan abinci yana ci, gaban sa ya zubawa akwatin telabijin ido yana kallon mata suna tiƙar rawa ko suna kaikomo cikin tsiraici, wataƙila ma kiɗa yana tashi. Ya manta da cewa duka wayannan ababen tambaya ne.

Allah muna roƙonka daka sadamu da rahamarka, ka rabamu da faɗawa tarkon shaiɗan.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.

Comments

  1. Shukran wa jaxakhallahu bi jannah aqee Allah y bamu ikon aiki d tunatarwa ameeeen

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.