ABOKIYAR ZAMA

"Kafin in kara aure ban fuskanchi wata matsala da uwargida ba, asalima ita take min kwalliya ko kuma ta zabo min kayan da zan saka idan ta fuskanchi zanje zance." Matashin mutaumin mai kimanin shekaru 35 yake fada a dai-dai lokacin da nake gab da shi a cikin keke napep.

"Ranar daurin aure ma ita tayi min kwalliya, mukayi hotuna daga bisani na tafi wajen daurin auren, da safiyar washe garin daurin auren ita tazo har bangaren amaryar ta shirya mana kayan breakfast gamida wasu lemuka data ajiyewa amarya wanda ni banma san ta tanade suba...." Ya dan dakata yana mai lalubo hotunansa da matan nasa gamida da nuna mini.

Yaci gaba da cewa; "lokacin da nakuda ta zowa amaryar, uwargidan ita ta kaita asibiti a motarta, bananan lokacin sai kawai waya tayo min tace amarya ta sauka suna asibiti kaza, dana je asibitin abinda na gani ya burgeni domin hatta yan'uwan amaryar duk yan kallo suka zama duk abinda ake bukata kafin suyi uwargida tayi... Hatta kayan da aka sanyawa jaririn nata ne...."

Yana bani labarin ina jinjina al'amarin gami da tuno irin labaran da nake ji a radio na kishin hauka da jahilchi.....

Ya katse min tunanina ta hanyar cigaba da bada labarin "Da ranar suna ta zagayo, amarya tace ita sunan uwargida take so a saka, da safiyar sunan uwar amarya ta kirawoni gefe tace don Allah shin an zabarwa yarnan sunan da za'a saka mata? Ni kuwa nace eh baba an zaba, saidai wanne suna da kikai niyyar a saka mata? Babar amaryar tace ita dai ko an saka don Allah alfarma take nema a chanja... Na tambayeta wanne suna take son a saka? Sai tace ita sunan wannan uwargidan yar Aljanna take so a saka.... Ina jin haka nayi murmushi nace ai itama firdousi (amaryar) sunan da tace a saka kenan..."

"Mallam anzo inda zaka sauka" mai keke napep ya katse mana hirarmu.

Sign.
Naseeb Auwal

Comments

Popular posts from this blog

MUTUM DA HANKALI

EYE OPENER... (SIWES)

LIKITAN ZUCIYA...