SHUGABANCHI 3
Umar ya nufi waje daga cikin gidan yana rike da takardar da mahaifiyarsa ta bashi.
Soron cike yake da kashin dabbobi wayanda suke kiwatawa, tare da cewa kullum sai an share soron amma hakan bai hana kasar wajen cakuduwa da fitsari gami da kashin dabbobin ba, sanadiyyar haka yasa zakaji yanayin soron wani iri.
Ya sanya hannunsa ya jawo kofar gidan wadda take a sakaye, duk tayi tsatsa. Tayi wata kara gami da tirjewa, amma sai gogan naka ya sanya karfi ya fincikota, karfin jan dayayi mata ya sanya kofar ta sallama ta budu tare da cewa tana tirjewa game da kartar kasa tamkar bata son motsawar.
Ya kalli layin nasu wanda yake cike da ledoji barkatai, dududu fadin layin ko keke napep bazai iya shigowa ba. Tsakiyar layin kuma wata kwata ce wadda gurbataccen ruwa ya dankare ya tsaya a cikinta, a haka yaci gaba da tafiya kansa a kasa daga bisani ya samu guri kebantacce a gefen layin inda aka ajiye wani kututture, ya zauna akai.
Ya kalli dama da hauni, yaga babu kowa inka dauke tattabaru da suke kokawa wajen cin hatsi da aka zubar musu a kasa. Cikin nutsuwa ya zaro takardar da mahaifiyarsa ta bashi wadda yar gidan mallam jatau ta bashi.
Assalaam Alaikum
Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan sarkin nawa ya tashi lafiya, kamar yadda na gaya maka ina mai farin cikin sanar da kai cewa Baba ya siyar min wayar hannu, kirar Nokia rakani ...... , da fatan zaka rinka kirana kamar yadda mukai alkawari.
Sannan ina tayaka murnar kammala jarrabawa, Allah ya bada sakamako mai kyau.
Tabbas a kowane bugun zuciya akwai radadi, jimami da kewar rashinka, duk sanda na kwanta da zummar bacci idanuwana sukan rufe dauke da kyakkyawar fuskarka, gamida murmushin da babu irinsa.
Ina godiya ga Allah daya bani kai a matsayin abokin rayuwa.
Daga taka
Fatima Jatau.
Umar ya ninke takarda, gami da yin murmushi kana yace “Yanzu banda abin yarinyar nan, aida saita bari idan mun hadu saita bani takardar nan, amma kacokam ta dauka ta bawa mahaifiyata, kuma banda abinta ko mahaifiyata bata iya karatu ba, ai zata gane sakon menene saboda adon fulawar da ta yiyyi a jiki.....” daga bisani kuma yabi takardar da kallo, yana mai nazarin fulawar da aka zana guda biyu gami da wasu tsuntsaye a saman fulawar dauke da wani allo a bakunansu, a jikin allon an rubuta lambar waya.
Anyiwa zanen kala, inda fulawar ta kasance koriya da ja, yayinda su kuma tsuntsayen akai musu kalar rawaya tare da ratsin baki. Allon da suka dauka kuma fari zanen cikinsa kuma ja ne amma mai duhu.
Zamu dakata anan
Tare da ni
Naseeb Abu umar Alkanawy.
Comments
Post a Comment