SHUGABANCHI 1

                          SHUGABANCHI....

Sabuwar hanya na bi, don wayar da kan al'umma akan halin da suke ciki a rayuwar yau. Na tsara bayanin nawa ta sigar labari ta yadda yan'uwa zasu karantashi cikin nishadi da kuma walwala. Ina fatan hakan bazaisa yan'uwa su kasa gane darussan da yake dauke da su ba.

                          **         **          **

Farko

Duk da iskar da take kadawa mai karfi hakan bai hana mutane fuskantar inda suka saka gaba ba. Mafi yawansu zaka iske cewa matasa ne kuma an zana kalmar FUSHI a fuskokinsu.... Suna tafe wasu basa ko magana yayinda zakaga wasu suna musayar magananganu a tsakaninsu......

Suka tsaya sukai cirko-cirko a gaban wata mota wadda ta kife sakamakon kaya data dauko wanda yafi karfinta, dadin-dadawa kuma hanyar bata da kyau ko kadan domin cike take da ramuka da gargada wadda tafiyar da zakayita cikin minti sha biyar ba tare da yin gudun ganganci ba indai a wannan hanyar ne sai kayi kusan minti arba'in da biyar.....

“Laifin matukin motar ne,” wani mutum ya furta hakan, “Ya za'ai ya debo kaya irin wannan tsabar hadama.”

“Laifin gwabnati dai ko?” wani daga gefe ya sako kansa cikin maganar, “Domin kuwa hanyoyin da suke a gyare ai irin wayannan motocin basa faduwa.”

“Laifin duka biyun ne” cewar wani dattijo. “Muma kuma munada namu laifin na rashin taimaka musu.”

Yayin daya gama furta hakan saiya nufi motar da kansa yana mai sanya dukkanin karfinsa don tayar da motar daga kwanciyar shan iska da tayi a tsakiyar hanya.

Ba tare da yace wani abuba matasan sukai caa suka tayashi, ai kuwa cikin kankanin lokaci suka tayar da motar nan ta zama ta tsaya qiqam da kafafunta.

Duk abinda ke faruwa akwai wani matashi a gefe yana kallo. Ko motsawa baiyi donya taimaka ba, bai kuma maida hankalinsa ga masu taimakon ba. Domin kuwa a cikin zuciyarsa akwai abubuwa da dama da suke damunsa..... Akwai damuwa da dama da take zagaye da zuciyarsa.....

Matashin ya kalli wani tafkeken agogon hannunsa a firgice ya murza idonsa ya sake dubawa, 5:00pm agogon ya nuna masa. Yasan kuma sunada jarrabawa karfe hudu na yamma.

Sau da dama sai lokacin shiga jarrabawar yayi yake tafiya amma baya haura minti talatin yake zuwa, kuma dayaje ake barinsa ya shiga, amma tabbas yau yasan ya dade.

“Da na sani ban biyo ta wannan hanyar ba wallahi,” ya fadawa kansa. “ni ban samu abin hawa ba kuma ban tafi da kafata ba, gashi lokaci harya fara kulewa... Bari kawai in fara tafiyar da kafata tunda dai kudi na biya ai babu wanda ya isa ya hanani zanawa...”

Take ya fara tafiya cikin gaggawa, saboda rashin kyawun hanyar bai samu abin hawan ba, ya sake duba agogo yaga 5:20pm sai kawai ya daina saurin ya fara gudu. Yana cikin gudun ne ya zame sakamakon cabalbali daya mamaye kasar wajen wadda ta juye zuwa yumbu ko tabo. Yayi maza ya mike duk ya bata jikinsa.

“Yaufa English za'ai, kuma kasan shekara uku kana nemansa, amma tsabar sakaci ace har yanzu baka karasa makarantar ba harma an kusa gamawa, tabbas wayannan malamai cutarku suke, domin kudin da kuke basu suke baku satar amsa shiya janyo kuka rainasu kuke kin bin dokarsu, sannan kuma kuke kin mayar da hankali akan jarrabawar tunda amsar kawai ake kawo muku ku kwafa ku bayar.... Ta yaya ilmi bazai gurbace ba..... Hatta kannenku kansu da suke bayanku ganin yadda ake muku yasa basa kokarin yin karatu....” Duk wannan zuciyarsa ce take gaya masa.

Tunaninsa yazo karshe sakamakon ganinsa da yayi a kofar makarantar; “Alhamdulillah” ya ambata lokacin daya afka cikin makarantar....

Amma yau yanayin makarantar ya sauya, domin ya saba a duk lokacin daya fara hango dakin jarrabawar tasu, zaiga sunata harkokinsu wasunsu har suna dago masa hannu. Yau kam ya tarar da sabanin hakan.

“Yau jarrabawar gaske ake ne?”
Tambayar da yayiwa kansa kenan wadda shi kansa baida amsarta.

Jikinsa a sanyaye ya karasa bakin kofar dakin jarrabawar.

“kai! Me kake anan?" Wani figigin mutum fari mai karamin jiki ya tambayeshi cikin kumbura murya, fuskarsa kuwa babu annuri a cikinta.

“ja..ja... Jarrabawa...n ...n.... nazo yi.” matashin ya furta lokacin da yake sunkuyar da kansa.

Are you nonsense" mutumin ya maidawa matashin martani cikin karaji.

No sir,” matashin ya fada yana mai sunkuyar da kansa, yayinda kuma gumi yake keto masa.

Wannan kuma wanne irin mai kula da masu jarrabawa ne haka? Suda suka biya kudi ai bai dace ayi musu irin wannan ihun ba....

“Yanzu ko na barka ka shiga kana jin cewa zaka iya wani abin arziki bayan saura minti 15 a kammala jarrabawar?” maganar mutumin ta katse masa tunaninsa.

“a..... eh, insha Allah.”
Matashin ya bada amsa, cikin yanayin nuna isa da jin kansa cewa shi wani ne.

Mutumin yayi masa inkiya daya shiga, harya kai kafarsa zai shiga sai mutumin ya damko wuyan rigarsa ya wurgashi baya, matashin ya fadi kasa. Cikin mamaki da kuma murmushin karfin hali ya mike.

“Aiba dakin uwarka bane da zaka shiga baka nuna katin jarrabawarka ba, anya kuwa ba shaye-shaye kayi kafin ka taho ba?” mutumin ya fada yana mai zazzaro jajayen idanuwansu.

Sorry sir,” matashin ya sake fada a karo na biyu.

Daga bisani ya dauko katin jarrabawar ya nuna, bayan gajeran nazari sai mutumin ya matsa masa hanya shi kuma ya shige.

Shigarsa keda wuya, wani mutum a ciki ya daka masa tsawa yace “fice waje” shi kuwa ya tsaya kikam yana kuma tunanin lokaci fa yana ta tafiya.

Bai aune ba sai ji yayi wancan mutumin ya hankadashi baya yana cewa “Bakaji ne?”

“Sorry sir,” ya fada a karo na uku, “zan baka wani abu.” ya fada kasa-kasa.

Mutumin ya harareshi, daga bisani kuma ya matsa masa hanya gami dayi masa inkiyar yaje ya zauna a wani mazauni wanda aka ware.

Bisa ga mamakinsa saiyaga an kawo masa takarda wadda an gama zanata, abinda kawai zaiyi shine ya saka sunansa da kuma lambar jarrabawarsa.

Ya godewa Allah, sannan ya zauna jim kadan kafin a fara karbar takardu.

Bayan an gama karba ne gaba daya sai wannan mutumin daya bashi takardar yazo kansa ya tsaya yace “Gani nazo.”

“Kazo me? Anfa karbi tawa.”
“Tab, nufinka aikin banza akai maka, ka makara an barka ka shigo, kuma an baka rubutacciya amma kace duk a banza akai maka....”
“Na zata don Allah aka taimaka min.”
“kaga mallam bana son bata lokaci in zaka bayar ka bayar, in kuma bazaka bayar ba to ka bani takardata kawai.....”

Matashin ya dan zazzaro idanu daga bisani ya zaro dubu daga alhajinsu itama duk ta zama baka saboda kudundunewa da yawo da tasha a hannun mutane masu dauda.
“Ya hakuri ka karbi wannan sir.”
“Ko a hanya ka ganni kasan na girmi dubu dayanka ko?” mutumin ya furta yana mai bata rai.
“Ai saboda ka girmeta shiyasa nace na zata don Allah ka bani ita.” matashin ya bada amsa.

“Mtsw”, mutumin yayi tsaki gami da fizgar duba dayan.

Matashin ya mike, ya karkade rigarsa saboda zama da yayi a benchi mai kura da datti.

Babban dakin jarrabawar cike yake da datti, saman kuma wata dankareriyar yanar gizoce baibaye dashi, tagogin dakin kuwa duk a kakkarye suke, babu wadda take dauke da gilashi duk an zubar dasu. Wasu ma an cire har karafan su....

Ina makomar al'ummar da ilminta yake cikin wannan yanayi, bata dauki ilmi da daraja ba, don haka shima ilmin bazai waiwayi al'ummar ba.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

MUTUM DA HANKALI

EYE OPENER... (SIWES)

LIKITAN ZUCIYA...