SHUGABANCHI 2

Tun bayan fitowar matashi Umar daga dakin jarrabawar yake ta sake-sake a zuciyarsa gami da tunanin makomar wannan jarrabawa tasa, amma abinda yafi damunsa shine dubu dayar da aka karba daga hannunsa.

“Idan naje gida me zan cewa Baba, tunda dai da ita suka dogara a matsayin cefanen gobe.” saurayin ya fada yana mai zurfafa tunani akan mafita.

Duk da wasu daga yan'uwansa masu zana jarrabawa suna ta iface-iface domin kuwa yaune ranar kammala jarrabawar, yayinda wasu masu adadin shekaru basa wannan iface-iface, wasunsu ma tuni sun bar harabar makarantar... Tabbas wayanda suke baki a wajen zana wannan jarrabawar sunfi kowa murna da hauka gami da wauta.

“Gaskiya ka burgeni da naga ka ware gefe ba'a wannan shirmen da kai,” wani mutum wanda yake da kimanin shekara 35 ya fada lokacin da yake mikowa matashi Umar hannu.

Murmushi kawai umar yayi gami da amsa sallamar wannan mutumin.

“Nifa wannan shine zana jarrabawata ta shida, kuma abu daya kawai nake nema. "Maths", shiyasa na yanke shawarar zuwa wannan makarantar don ance ana ci sosai....” mutumin ya fada lokacin da yake kallon matasan da suke iface-iface don murnar kammala jarrabawar.

Umar yaja gwauron numfashi ya mike sakamakon ganin yadda gari ya fara duhu ga kuma kiraye-kirayen sallah daga kowanne sashe.

“Ni kuma yina na biyu kenan, kuma ina saka ran zan wuce a wannan karon, kaima kuma yayana ina maka fatan nasara.... Amma kuma..... Koda yake dai sai Allah ya kaddara saduwarmu...” Umar ya fada lokacin da yake sassarfa don fita daga makarantar....

Matashin mutumin ya bishi da kallo kawai yanata sake-saken abinda yasa wannan saurayi yake sassarfa haka kamar zai tashi sama.

★         ★          ★

Kwance yake a dakinsa shi kadai bisa kan tabarmarsa, ya kurawa fankar saman dakin ido wadda take kuka ita kadai.

Tunanin Umar ya luluka dashi zuwa ga rayuwarsu ta makarantar sakandire a inda ya rike mukamin shugaban dalibai, ya tuno irin gudummuwar daya bayar tare da badakalar daya aiwatar. Ya kuma tuno yadda ya tara jama'a da abokai iri-iri wayanda yanzu babu lalllai a kuma haduwa, wasu zasu mutu, wasu kuma dama adadin haduwar da za'ai iyakar ta makarantace, wasu kuwa za'a gamu bayan dogon lokaci.

Tunaninsa ya katse, sakamakon dauke wuta da akai, ga zafi da ake fama dashi don haka ya mike yayi mika ba tare da ambaton Allah ba, ko akwai wani nassi daya tabbata cewa in anyi mika a ambaci Allah ko ayiwa Annabi Muhammad (S.A.W) salati? Shidai bai sani ba.

“Umaru, yaufa ka makara,” mahaifiyarsa ta fada lokacin da suka ci karo akan hanyarta ta shigowa dakin nasa.

“Jiya na gaji ne” Ya fada yana mai rufe bakinsa sakamakon hamma, sannan yaci gaba da cewa "jiya muka gama jarrabawa.”

“Allah dai yasa wannan karon kayi nasara.”
“Ameen umma”
“Ga wannan sakone ance a baka,”
“Injiwa.”
“Inji yar gidan mallam jatau”.

Umar ya dan sunkuyar da kansa yana mai jin kunyar mahaifiyar tasa, daga bisani yace; “Allah sarki maganar karatu ce na sani.”

Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

Tare da ni
Naseeb Auwal

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.