Matan Aure a Musulunci: Hakki, Daraja da Kyakkyawar Mu’amala.

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.


Kowanne abu ba cikakke ba ne, duk halittar da Allah ya yi babu kamar mutum, amma shi kansa mutum tara yake bai cika goma ba, a dabi'ance, lafiyance da addinance. To haka idan ka duba abubuwan da suke kewaye da mu, masu rai da marasa rai za ka iske kowanne yana da bangaren da ya cika yana da kuma bangaren da ya ke da tawaya.

ALLAH Buwayi Gagara Misali shi kadai ne cikakke, kuma gwargwardon kusancin bawa zuwa ga Allah gwargwadon cikarsa, kimarsa da darajarsa. Shi yasa Annabin Rahama ﷺ ya fi kowa zama cikakke domin ya fi kowa kyakykyawar alaka da Allah Mai Girma.

Idan muka dauki ayyuka da kuma tsarin rayuwa za mu iske cewa cike take da kalu-bale mai yawa, kuma cike take da misalai ga masu hankali na irin hanyoyin da ta bi ta dilmiyyar game da hallakar da wayanda suka daukaka sha'aninta, kamar kuma za mu ga ba ta bar na kirkin ba, domin kuwa kowa akwai irin matsalolin da ya yi fama da su, kuma ya ke fama da su, kuma zai yi fama da su a nan gaba. Hanya guda daya ta kaucewa wannan shi ne mutum ya yi rayuwa yanda Allah ya tsara, idan mutum ya yi haka to zai samu saukin rayuwa, zai samu ribar rayuwa a nan duniya, zai kuma samu dacewa a Ranar Alkiyama.

Kamar yanda Allah shi ne cikakke, to haka ma addininsa shi ne cikakke, kuma shi ne ya zo mana da cikakkiyar rayuwa wadda babu tawaya ko nakasu a cikinta. Don haka duk abin da mutum zai yi, idan yana son dacewa kuma ya yi shi gwanin sha'awa ba tare da cin karo da munanan matsaloli ba, to mutum ya koma zuwa ga abin da Allah ya turo masoyinsa da shi; wato Musulunci.

Daga cikin abubuwan da suke bayar da ciwon kai a Kasar Hausa dama duniya baki daya akwai zaman aure. Musamman a wani zamanin da wasu abubuwa da yawa sun faru a baya wayanda su ne sukai cikin da yawa yau ta haife wasu munanan matsaloli masu wuyar gyaruwa. Sannan kuma shaidan ya samu wani karfi wanda ba shi da shi a shekarun baya, wannan karfi na social media da wayoyin hannu...

Don haka naga dacewar tattara wasu daga ayoyi da hadisai a matsayin takaitacciyar nasiha zuwa ga yan uwa da kuma fahimtar da su abin da ya kamata su fahimta.

Na zabi takaita rubutun zuwa ga mata da abin da Musulunci ya yi wasiyya da shi a kansu na kyautatawa da tausayi. Musamman saboda a gidan aure su ake mulka, Idan akwai tsohon rai da dama In Shaa Allah rubutu zai biyo baya akan Mazan Aure.





Kyakkyawar Mu’amala da Mata a Musulunci


Addinin Musulunci ya bayar da muhimmanci sosai ga yadda namiji zai mu'amalanci matarsa. Aure ba yarjejeniya ce ta zama tare ba kawai; Allah Ya gina shi ne a kan nutsuwa, soyayya da rahama.

Allah سبحانه وتعالى Ya ce:

وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنْفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
[الروم: 21]


Ma'ana:
“Daga cikin ayoyinSa ne Ya halitta muku mata daga jikinku domin ku samu nutsuwa a wurinsu, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani.”

Allah Mai Girma da Daukaka da kansa saboda muhimmancin mu'amalantar mata da kyautatawa sai ya bayar da umarni kai tsaye...

Allah Ya ce:

 وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ فَإِن كَرِهْتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ اللَّهُ فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا
[النساء: 19]

Ma'ana:
“Ku zauna da su (matanku) cikin kyakkyawar mu’amala. Idan kun ƙi wani abu daga gare su, to watakila kuna ƙin wani abu ne alhali Allah Ya sanya alheri mai yawa a cikinsa.”

Wannan aya tana ɗauke da muhimmin darasi. Allah bai ce miji ya jure da matarsa ba kawai, sai Ya ce:

وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ

Wato ku mu’amalance su cikin alheri.

Imamul Al-Qurṭubi ya bayyana المعروف da ma’anar kyakkyawar mu’amala, kamar kyautata magana, kyautata aiki, da ba wa mace hakkokinta, wannan kuma babu sabani daga malamai, domin dai duka maganganunsu idan ka bibiya ka tattare wannan ma'anar suke nufi. Ba don gudun tsawaitawa ba da mun ambaci wasu daga cikinsu.

Kuma wani abin lura shi ne cewa Allah Ya kawo wannan umarni ne bayan ya ambaci yiwuwar mutum ya ƙi wani hali daga halayen matar ko siffar matar.

Wato: abin da mutum bai so a cikin matarsa bai kamata ya zama dalilin da zai manta da sauran alherinta ba. Idan ta bata masa ta wata fuskar, to sai ya tuna alheranta ta wasu fuskokin. Shi mumini koda yaushe yana yiwa mutane uzuri, kuma ba ya manta alheransu akan sharri dan kadan da suka aikata. Domin kuwa ko a rayuwar mu ta yau da kullum idan ka ce kowa kuskuransa kawai za ka rinka kalla kuma ka yi masa hukunci da shi to za a wayi gari ba ka tare da kowa.

Kada ka ƙi mace saboda hali ɗaya, don haka ne ma Annabin Rahama ﷺ ya ke cewa cikin hadisi ingantacce riwayar Imam Muslim.


 «لَا يَفْرَكْ مُؤْمِنٌ مُؤْمِنَةً، إِنْ كَرِهَ مِنْهَا خُلُقًا رَضِيَ مِنْهَا آخَرَ»

Ma'ana:
“Bai kamata mumini ya ƙi mumina ba; idan ya ƙi wani hali daga gare ta, zai yarda da wani hali nata.”

Wannan hadisi yana koyar da adalci wajen kallon mutum. Babu cikakken mutum kamar yanda muka ambata. Mace tana da abubuwan da za ta yi kuskure a cikinsu, kamar yadda namiji yake da nasa. Don haka idan mutum ya ga abin da ba ya so, bai kamata ya manta da dukkan kyawawan halayen da matar ta mallaka ba.


A wata ayar Allah Madaukaki Ya ke cewa:

وَلَهُنَّ مِثْلُ الَّذِي عَلَيْهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ وَلِلرِّجَالِ عَلَيْهِنَّ دَرَجَةٌ
[البقرة: 228]


Ma'ana:
“Kuma su ma (mata) suna da hakkoki kamar yadda ake da nauyin hakkoki a kansu, bisa ga abin da ya dace; kuma maza suna da matsayi na kula da al’amari a kansu.”

Ayar nan idan muka kula ta kafa wani babban ƙa’ida: aure yana da hakkoki da nauye-nauye a bangarorin biyu. Namiji akwai abubuwan da ake bukatar ya sauke, kamar yanda ita ma mace akwai su, kuma hakki ne kowa yana da shi akan kowa.

Wannan ba yana nufin cewa hakkokin namiji da na mace iri ɗaya ne a kowane fanni ba. Amma yana nuna cewa bai dace namiji ya kalli abin da yake so a ba shi kawai, ya manta da abin da ake buƙatar ya bayar ba. Shi aure zaman tare ne, zaman farantawa juna ne, zaman samarwa da juna nutsuwa ne, kauna da kuma rahama.

Saboda ka da namiji ya muzantawa mace, kuma saboda kar idan ta yi laifi ya munana wajen yi mata hukunci ko ramuwa, Sai Manzon Allah ﷺ ya yi wasiyya akan mata inda ya ke cewa cikin hadisi ingantacce:

 «اسْتَوْصُوا بِالنِّسَاءِ خَيْرًا»
Ma'ana:
“Ku yi wa juna wasiyya da kyautatawa mata.” Hadisin Bukhari da Muslim duka sun rawaito shi.

Wannan hadisi yana nuna cewa kyautatawa mata ba wata dabi’a ce kawai da mutum zai yi idan yana so ba; Manzon Allah ﷺ ya yi wasiyya da ita. Kuma dai mun san ya girman Manzon Allah ﷺ ya ke a wajen musulmi. Idan mutum zai girmama wasiyyar iyayensa, to wasiyyar Annabin Rahama ﷺ ya kamata ya fi kiyayewa.


Mafi alherin mutum shi ne wanda ya fi alheri ga iyalinsa, kamar yanda ya zo a hadisi riwayar Imam Tirmidhi Manzon Allah ﷺ ya ce:

«خَيْرُكُمْ خَيْرُكُمْ لِأَهْلِهِ، وَأَنَا خَيْرُكُمْ لِأَهْلِي»


Ma'ana:
“Mafi alherinku shi ne wanda ya fi alheri ga iyalinsa, kuma ni ne mafi alherinku ga iyalina.”

Wannan magana tana buƙatar mutum ya yi tunani a kanta kuma ya rinka tuno ta a koda yaushe, hakan zai ba shi kwarin gwiwa wajen ganin yayi koyi da Masoyi ﷺ.

Abin mamki, wasu mutanen suna da kyakkyawar mu'amala da abokai, makwabta da mutanen waje, amma idan sun shiga gidansu sai su zama masu tsawa, zagi, wulakanci da rashin hakuri. Tabbas wayannan sun yi hannun riga da koyarwar Annabin Rahama ﷺ, wannan hadisin ya nuna cewa gidanka ma wurin gwajin kyakkyawan halinka ne. Duk kyawun halinka a waje indai ba ka da kyan hali a gida to kyan halin na ka ya zama na gulma da munafunci. 


Ma'anar hadisin tana kara fitowa idan muka hadata da wannan hadisin da Annabin Rahama ﷺ ya ke cewa:

«أَكْمَلُ الْمُؤْمِنِينَ إِيمَانًا أَحْسَنُهُمْ خُلُقًا، وَخِيَارُكُمْ خِيَارُكُمْ لِنِسَائِهِمْ خُلُقًا»

Ma'ana:
“Mafi cikar muminai wajen imani su ne waɗanda suka fi kyawun hali, kuma mafi alherinku su ne waɗanda suka fi kyautata hali ga matansu.”

Saboda haka kyakkyawar mu'amala da mata tana da alaka da imani da kyawawan halaye, ba kawai al'adar zaman gida ba.


Mu dubi girma irin na Sayyadina Umar رضي الله عنه amma ka duba alakarsa da matansa za ka iske akwai saukakawa, tausasawa, kawar da kai da kuma tausayawa.  An ruwaito cewa wani mutum yana korafin cewa matarsa tana masa magana da ƙarfi. Sai ya tafi wajen Umar domin ya kai ƙara. Da ya isa ƙofar gidan Sayyadina Umar, sai ya ji matar Sayyadina Umar tana yi masa magana da karfi, shi kuma Sayyadina Umar ya yi shiru yana saurare. Sai mutumin ya juya yana son tafiya.
Sayyadina Umar sai ya tambaye shi dalilin tafiyarsa. 
Sai mutumin ya bayyana cewa ya zo ne saboda yana korafin matarsa, amma sai ya ga matar Umar ma tana yi daga masa magana, kuma Umar yana jurewa.

Sai Sayyadina Umar ya ce da shi:

Ita mace an halicceta ne da kashin hakarkari, idan ka ce za ka mikar da shi to karyashi za kai, idan ka kyaleta da wannan karkacewar ta kashin hakarkarin kuwa to sai ka ji dadin zama da ita duk da a karkace take.

Wannan yana daga cikin ma'anar hadisin da Manzon Allah ﷺ ya koyar, kuma Umar yana amfani da shi wajen nuna cewa mace tana da dabi'un da suke bukatar hakuri, juriya da fahimta. Mun fadada bayani a karatun mu na wannan hadisin a channel din mu ta WhatsApp.

Amma fa wannan hadisin da maganar Sayyadina Umar ba wai yana nufin a bar mace akan kuskure ba. Ma'anarsa ita ce mutum ya fahimci halittar mutum, ya yi hikima da hakuri, maimakon ya nemi tilasta komai ya zama yadda yake so.


Hausawa suna cewa "Idan ka san halin mutum sai ka sha maganin zama da shi." Idan ka karanci halin matarka to sai ka san ta hanya mafi kyau da za kai mata gyara da kuma lokacin da ya kamata kai mata gyaran.


Aure ba Wajen Cutar da Juna ba ne

Kada a yi amfani da aure wajen cutar da mace, domin aure ba wajen cutarwa ba ne, ba kuma wajen mugunawa juna ba ne.
Allah Ya ce:

وَلَا تُمْسِكُوهُنَّ ضِرَارًا لِّتَعْتَدُوا

Ma’ana:
“Kada ku riƙe su da nufin cutar da su, har ku ketare iyaka.”

Wannan aya tana da matukar muhimmanci. Idan mutum ya samu sabani da matarsa, bai kamata ya yi amfani da matsayinsa na miji wajen azabtarwa, wulakanci, ko matsa mata ba. Domin ba haka muka riski Annabin Rahama yana aikatawa ga matansa ba. Idan an yiwa mutum laifi ya dauki matakan gyara masu kyau wayanda shari'a ta yarda da su, wayanda kuma za su kawo gyaran ba wayanda za su kara hargitsa abubuwa ba.

Ko lokacin rabuwar aure, akwai umarnin rashin cutarwa, Allah Ya na cewa:

أَسْكِنُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ سَكَنْتُم مِّن وُجْدِكُمْ وَلَا تُضَآرُّوهُنَّ لِتُضَيِّقُوا عَلَيْهِنَّ
[الطلاق: 6]

Ma’ana:
“Ku zaunar da su a inda kuke zaune, gwargwadon ikonku, kuma kada ku cutar da su domin ku matsa musu.”

Mu lura da yadda Qur'ani yake kula da wannan al’amari: har ma lokacin da aure ya kai ga rabuwa, ba a bayar da damar muzgunawa mace ba.


Manzon Allah ﷺ ya kasance abin koyi


Sayyada Aisha ta na cewa:

«مَا ضَرَبَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ شَيْئًا قَطُّ بِيَدِهِ، وَلَا امْرَأَةً وَلَا خَادِمًا...»

Ma'ana:
“Manzon Allah ﷺ bai taɓa dukan wani abu da hannunsa ba, ba mace ba, ba bawa ba…”

Wannan yana nuna irin girman tausayi da kyakkyawar mu'amala da yake da su ﷺ. Kuma dai matansa ba ma'asumai ba ne, suna yi masa laifi, suna yin kuskure, amma yana amfani da hikima wajen yi musu gyara, ba duka ba zagi.


Za mu dakata a nan, Allah ya datar da mu.

Abu Umar Alkanawy

Comments

Popular posts from this blog

KNOWLEDGE AND ITS NEGATIVE EFFECT...

JAN HANKALI GA ƊALIBAN KIMIYYA

PUBLIC DANCE!!!