MUTUM DA HANKALI


Mutane da Hankali
01
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaba, Ja gaba, tare Ahalinsa da Sahabbansa. 

Hankali shi ne mafi girman abin da Allah ya bawa ɗan Adam, ba wai don bai bawa sauran halittu shi ba, sai don yanda ɗan Adam yake amfani da hankalin na sa ya sha bambam da yanda sauran halittu suke amfani da na su hankalin.

Hakan kuma ya samo asali ne saboda shi tunanin ɗan Adam yana samun jagoranci ne daga shari'a wadda Allah ya aiko manzanni da ita, don haka sai ɗan Adam ya zamana yayi fintinkau a ɓangaren kowace ɗabi'a mutuƙar. 

Wani zai ce ai tun kafin a saukar da Shari'a mutum ya ke da hankali, sai mu ce, Allah da ya halicci Annabi Adam, ya halicceshi ne akan fiɗira, kuma haka aka ɗorawa Annabi Adam nauyin ɗora ƴaƴansa akan wannan tafarki wanda aka ɗorashi a kai. 
Allah Mai Girma da Ɗaukaka ya na cewa:
كَانَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً فَبَعَثَ اللَّهُ النَّبِيِّينَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِيَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ فِيمَا اخْتَلَفُوا فِيهِ ۚ وَمَا اخْتَلَفَ فِيهِ إِلَّا الَّذِينَ أُوتُوهُ مِن بَعْدِ مَا جَاءَتْهُمُ الْبَيِّنَاتُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۖ فَهَدَى اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا لِمَا اخْتَلَفُوا فِيهِ مِنَ الْحَقِّ بِإِذْنِهِ ۗ وَاللَّهُ يَهْدِي مَن يَشَاءُ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ 
Suratul Baƙara aya ta 213

Wannan ayar abin da take nunawa shi ne mutane sun kasance akan tafarki guda ɗaya a farkon al'amari, da sukai saɓani sai Allah ya turo da Manzanni don su yi wa mutane hukunci akan abin da sukai saɓani a kai... 
Malaman tafsiri a ƙarƙashin wannan ayar sun magantu, amma magana mafi inganci ita ce wadda aka rawaito daga Ibn Abbas, Ubayyu Ibn Ka'ab, Ibn Mas'ud, Ikhramata, Abul Aaliya, Mujahid, Ƙatada da wasunsu Allah ya yarda da su ya kuma yi musu raha. Idan ka haɗe ruwayoyin za su nuna maka cewa; Asali mutane suna kan Shari'a ne da Shiriya wadda suka gada daga Kakansu Annabi Adam, bayan shuɗewarsa sai sukai saɓani, wasu ruwayoyin suka nuna cewa kusan ƙarni goma ne tsakanin Annabi Adam da Annabi Nuhu (A.S) kuma dukkaninsu suna kan shiriya, sai sukai saɓani, suka saɓawa shiriyar suka koma bautar wanin Allah, Sai Allah ya turo musu da Manzanni... Mai son ƙarin bayani sai ya duba littafan tafsiri kamar Tafsirin Ibn Kathir ko kuma littafin Da'awatut-Tauheed na Dr. Muhammad Khalil Harras shafi na 90-102, ya faɗaɗa bayani kwarai, kuma ya tattara ilmi mai yawa a shafuka ƴan kaɗan.

Idan haka ne to ashe mutum tun farkon halittarsa Shari'a ce ta raineshi ta samar masa da hankalin da yake taƙama da shi, kuma da ace da aka saukar da shi haka aka barshi to da bambancinsa da sauran dabbobi zai zama kaɗan idan an samu kenan.

Idan muka ɗauki ɗaiɗaikun halaye zamu iske yanda ɗan Adam yake da hankalin neman aminci, samarwa da kansa kariya, shugabanci da iyakance rayuwarsa a wani waje zamu iske sauran dabbobi suma suna da irin wannan sai dai a samu bambamci wajen yanda suke aiwatar da rayuwarsu, yanda suke samar da shuwagabanninsu, da kuma yanda suke zaɓar abokan rayuwarsu. Tare da cewa zaka cika da tsananin mamaki idan kaga irin kamanceceniya da take tsakanin mutane da wasu dabbobin, wanda idan da rai In Shaa Allah zamu tsakuro wani abu daga ciki.

An rawaito daga Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda take cewa "Wanda Allah ya bawa hankali to lallai ya rabauta."  Ibn Qayyim (R) ya kawo athar ɗin a farko-farkon littafin Raudatul Muhibbeen.

Gida nawa mutane suka rabu ta fuskar hankali?
Menene banbancin hankalin ɗan Adam dana dabbobi?
Wanne hankali ne ingantacce?
Shin Allah ya bawa mutum ƙarfin hankalin da shi akankin kansa zai iya tsarawa kansa rayuwa ba tare da aiki da Shari'ar da Allah ya tsara masa ba?

Dama wasu abubuwan da dama sune zamu tattauna a cikin wannan rubutu da yardar Allah.

 MUTANE DA HANKALI
02
Alaƙar mutane da hankali alaƙa ce wadda samuwarta shi ne yake bambamta mai hankali da mahaukaci. 

Irin hankalin da mutum yake da shi yasha bambam da na sauran dabbobi, kamar yadda hanyar isar da saƙon mutum ya sha bambam da na sauran dabbobi. Don haka ne masana kimiyya suka ce koda ace dabbobi suna magana ba zamu fahimci abubuwa da yawa na su ba, saboda yanayin yanda kake jin kanka a matsayin mutum ya sha bambam da yanayin yanda suke jin kansu a matsayin dabbobi... Shi yasa babban kuskuren da masu bincike a kan halayyar dabbobi su kai shi ne aunawa da kuma gwada fahimtar dabbobin a mizanin mutum, maimakon su auna fahimtar dabbobin a mizaninsu, Wannan wani babi ne da shi kansa yana buƙatar rubutu idan aƙwai tsawon rai da yardar Allah, tsawaita bayani a nan zai jawo tsayin rubutun.

Akwai abubuwa da suke da tasiri wajen hankali da tunanin mutane, daga ciki akwai addini, al'ummar da mutum yake rayuwa a ciki da kuma ilmi. 

Addini shi ne shari'a wadda dama Allah ya kawo ta ne don ta gyara tunanin mutane domin tunani shi kaɗai ba zai iya jagorantar rayuwa mai kyau da inganci ba, kamar yadda muka bayyana a wasu rubuce-rubucenmu na baya. A taƙaice kamar yanda Shaikul Islam ya ke kamantawa; shi hankali kamar ido ne, ita kuma shari'a haske ce; komai ƙwarin idon mutum idan aka ce ana cikin duhu to tabbas babu amfani ga wannan idon, amfanin idon yana zuwa ne idan akace akwai haske.

Al'ummar da mutum ya taso a cikinsu suna da tasiri wajen ba shi irin tunanin da zai girma da shi, yanzu sau nawa zaka iske wasu al'umma ko wata ƙabila suna aiwatar da wani abu, kai a wajenka wannan abin bai dace ba amma su a wajensu wannan abin ya dace, kuma su a wajensu dai dai ne, yayin da kai kuma koda kuɗi ba zaka aiwatar da abin ba. Hatta dabbobi suna ɗabi'antuwa da irin wannan ɗabi'a. 

Cikin wani littafi "Thinking animals", marubuciyar ta tattauna akan wasu birirrika da kuma yanda suke gudanar da rayuwarsu wasu sun saki jiki da mutane, wasu kuma tsoron mutane suke yayin da wasu tsakaninsu da mutane sai mugunta da kallon banza... A binciken da tayi bayan duba tarihin kowannensu sai ta tabbatar da cewa al'ummar da suka taso a ciki itace ta taka muhimmiyar rawa wajen sanyawa kowannensu irin tunanin da yake kai da kuma yanda yake kallon duniya.

Haka nan ilmi yana taɓa hankali ko dai ya saita shi ko kuma ya bauɗar da shi, domin ba dukkan ilmi ne mai amfani ba... Zamu taƙaita don gudun tsawaitawa.

Kamar yadda muka ambata cewa zamu ambaci rabe-raben mutane bisa alaƙarsu da hankali to zamu fara da kashin farko.

1. Mai hankali a cikin masu hankali; Wannan shi ne wanda yana da hankalin da idan abubuwa guda biyu suka zo masa kuma duka biyun masu illa ne ko masu cutarwa to zai iya aunawa yaga mai dama-dama a cikinsu. 

Mafi yawan hakan yana kasancewa idan aka ce rashin ɗayan abubuwan da suka zo masa zai haifar da matsalar da tafi samuwarsu.

Misali 1
Mutum ne yana ɗaki akan bene sai wuta ta kama, a ilahirin benen bai da inda zai bi ya tsira, sai kawai ya tuno da tagar (window) ɗakin, sai dai kuma tunda a bene yake idan ya biyo ta tagar ya diro zai iya jin rauni, idan da tsaursayi ma, zai iya karyewa. 
To anan yana da zaɓi guda biyu; kodai ya tsaya wannan wutar ta ƙone shi ya mutu ko kuma ya faɗo ta wannan tagar in yaso ya ji ciwon.

Shin da mutuwa da jin ciwo wanne yafi wani muni a gare shi?

To a al'amuran rayuwa irin wayannan sukan afku.

Misali 2.
Ilmin boko da ake yi, an san yazo da wasu abubuwa da sun saɓawa musulunci kamar cakuɗuwar maza da mata da sauransu. To a nan sai muga akwai abubuwa guda biyu.

1. Kodai ayi wannan karatun ayi ƙoƙarin kiyaye abubuwan da suka saɓawa musuluncin tare da cewa mun sani dole wasu in sun kiyaye wasu zasu afka. Kuma muna sane da tarin alheri da yake cikin yin karatun.
2. Ko kuma ace ai tunda ya saɓawa Musulunci ta wasu guraben dole a ƙyale shi. In aka ƙyaleshi sai ragamar komai ta koma wajen wayanda ba Musulmi ba. Sojoji su ne, likitoci su ne da sauransu.

A nan duka hanyoyi biyun suna da sharri sai dai ɗaya tafi ɗaya.

Misali 3
Kamar malami da aka bijiro masa da wata kujera musamman ta wani muƙami kaga shima cikin barinta ko karɓarta akwai sharri makamancin wanda muka ambata a misali na farko da na biyu.

Akwai misalai da dama, shi mumini baya hangen iyakar yanzu, yana rayuwa ne yana duba daga ina aka taso, a ina ake kuma ina za a je. Don haka za ka iske shi da ilhama, hangen nesa da wasu abubuwa wa'yanda ba zaka same su ga waninsa ba.


 MUTANE DA HANKALI
03
Kamar yadda mukai bayanin mai hankali a cikin masu hankali tare da buga misalai a rubutun daya gabata, inda muka tabbatar da cewa mai hankali shi ne wanda yake iya bambamce abin da yafi alheri a cikin masharrantan abubuwa guda biyu. Kuma idan ba a manta ba maganar tamu idan aka waiwayeta tana kai komo ne akan maganar sahabi Umar (R.A) kamar yanda muka ambata a rubutun farko.

Nau'i na biyu shi ne mutumin da yake da hankali; na kira shi da mai hankali sabo da bai kai na farkon hankali ba, idan ma ya kamata mu kira shi mai hankalin kenan.

Abin da nake son mai karatu ya gane shi ne wannan rabe-raben ban riski wani daga cikin magabata da yayi shi ba, kuma bance dole a haka rabon mutane yake ba dangane da alaƙarsu da hankali, kawai na aikata hakan ne don sauƙaƙa fahimtar mai karatu.

Idan nace mai hankali nayi shiru (ba kamar mai hankali a cikin masu hankali ba). To ina nufin mutumin da yake iya bambamce mai kyau da mara kyau, amma idan marasa kyau guda biyu suka zo masa baya iya tantance wanda yafi sauƙin sharri a cikin su.

A cikin mutane muna da irin waƴannan da yawa. 

Bari mu buga misali don bayanin yafi fitowa fili.

Misali (2)
Mutum ne ya saka fararen kaya yana tafe akan gadar jirgin ƙasa gefensa na dama muggan namun dawa ne, gefen sa na hagu kuma wani ruwa ne mai datti. Sai kwatsam jirgin ƙasa ya biyo wannan gadar, sai yake tunanin idan ya sauka ya koma gefen namun daji tofa zasu cinye shi, idan kuma ya sauka ya koma ɗaya gefen fararen kayansa zasu ɓaci, don haka sai ya kasa tantance inda zai yi sabo da duk inda yayi cutuwa zai yi, ko mutuwa ko ɓata kaya, sai kawai ya tabbata akan wannan hanyar a ƙarshe har wannan jirgin ƙasa yazo yayi awon gaba da shi. 
Tare da cewa cutarwar mutuwa gare shi tafi ta ɓata kaya muni nesa ba kusa ba.

Wannan shine irin abin da masu kushe ilmin zamani suka faɗawa inda a ƙarshe suke kore shi tare da kafirta wanda yayi shi ko yayi amfani da shi. Tare da cewa alheran dake cikin amfani da shi sunfi sharrukan da suke cikin barin sa.

A kula, idan abubuwa guda biyu suka zo masu sharri bawai ina nufin a dubi wanda yafi sauƙi a cikinsu a yi shi ba, a'a barin su duka biyun shi yafi, ana amfani da mafi sauƙin cikin su ne idan rashin yin ɗaya daga cikin su zai haifar da matsalar da tafi yin ɗaya daga cikinsu.

Misali (3)
Matashi ne iyayensa guda biyu suke saɓani har ta kai uwar ta fita daga hayyacinta ta ɗauko wuƙa sabo da fushi ta nufi mahaifinsa da zummar caka masa, sai mahaifin ya umarceshi da cewa ya ƙwace wuƙar daga hannunta ya ɓoye, ita kuma mahaifiyar tace kada ya sake ya ƙwace inba haka ba zata tsine masa...
Shin anan barin mahaifiyar ta kashe mahaifin shi ne maslaha ko kuwa saɓa mata ya ƙwace wuƙar?

Misali (4) 
Da kuma ace mahaifi da mahaifiyar rigima suke, sai mahaifiyar tace ɗan ya mari uban ko uban yace ɗan ya mari uwar...
Kaga anan barin duka sharrin guda biyu shi ne abin da yafi.

To mai hankali da baya aunawa ko baya iya gane lokacin da zai amfani da wannan da wancan ba zamu kira shi da cikakken mai hankali ba.

Zamu sake juyowa kan wannan bayanin idan akwai kwanaki masu yalwa a gaba Insha Allah.

Nau'i na Uku; Wannan shi ne mara hankali. Baya banbance mai kyau da mara kyau, baya zaɓar alheri akan sharri.

Wani abu da nake son mai karatu ya fahimta shi ne komai siffar kamala da cikar hankalin mutum a zahirance mutuƙar baya aiki da shi to wannan ba shi da shi.

Shin mayunwacin da yake da ajiyayyen abinci amma yaƙi ci za a kira shi da ƙosashshe? Sai dai ko ƙoshin yunwa.
Malamin da yake aiki irin na jahilci za a kira shi da malami? Sai dai ko ga wanda bai san menene malanta ba.

Shi mara hankali shi ne wanda ya sakarwa son zuciyarsa ragamar rayuwarsa don haka duk inda ta tura shi nan yake bi ba tare daya auna abin alheri ba ne ko sharri.

Misali (5)
Ana tsananin sanyi, mutum yana jin ɗumi sai yaga ya dace yaje bakin wuta don shan ɗumi, ai kuwa yaji daɗin ɗumin nan ya ratsa shi, sai zuciyarsa ta ƙaddara masa cewa ya shiga cikin wutar domin zai fi jin ɗumin da kyau, inda ma ɗumin bai kai ba duk zai kai. Ai kuwa wannan mutum sai ya faɗa cikin wannan wuta...
Shin ina hankali ga wannan?
To wannan shi ne misalin mutumin da yake afkawa sharri alhalin yasan sharrin ne, ya sayar da lahirarsa saboda jin daɗin duniya.

Nau'i na huɗu: Mara hankali cikin marasa hankali, wannan shi ne wanda ba son zuciyarsa yake bi ba, son zuciyar wasu yake bi, kuma yasan ba akan dai dai suke ba.

Misali (6)
Mutum ne uban gidansa ya bashi fetur, yace da shi yaje wani ɗaki da ake ajiye kuɗin wasu mutane, idan ya shiga ya bulbula fetur ɗin a kowanne saƙo na ɗakin sannan ya rufe kansa a cikin ɗakin ya kunna wuta, dalili kuwa wayancan yan adawa ne idan aka bar ɗakin a buɗe to zasu zo su kashe wutar kafin ta ƙone komai.
Shin wanda yaji wannan umarni yaje ya aikata bai zama yafi kowa wauta ba? A kan farantawa wani yaje ya hallaka kansa.

Wannan shi ne karshen rabe-raben sai dai idan yan'uwa suka kula zasu ga rubutun ya fi tafiya da zallar hankali tunda dama maganarsa ake.

Sai dai kuma wanne matsayi hankali yake da shi a shari'a?

Shi ne abin da rubutu na gaba zai ƙunsa da yardar Allah.

Allah ya shiryar damu, ya azirtamu da halal, ya bamu lafiya mai inganci.
Ameen 


MUTANE DA HANKALI
04
Idan mai tambaya ya tambayeka cewar "ya kake jin rayuwarka a matsayin jemage?"
Amsar da zaka ba shi ba zata zama gamsashshiya ba, sabo da zaka ba shi amsa ne a matsayinka na mutum ba jemage ba. Kuma ba zaka iya ƙiyasta rayuwar jemage a matsayin rayuwa dai dai da kai ba domin kuna da bambamci a waje dabam dabam. 
Misali, kai a rayuwarka kusan ido shi ne gaba, da shi ne kake neman abinci, da shi ne kake gane nisan  tafiyar da zakai ka cimma abin da kake nema kuma dai idon shi ne kusan abin da kafi ji da shi. Don girma da darajar ido hadisai da dama suka tabbata cewa wanda Allah ya jarrabta da rashin ido kuma yayi haƙuri to bai da sakamako sai aljanna. 
A ɗaya ɓangaren kuma idan muka dubi jemage shi da kunnensa yake amfani wajen gano nisan dake tsakanin sa da abincinsa, kenan yafi amfani da sauti abin da ake cewa sound waves, idan ma abincin mai rai ne jemage zai iya gane idan yayi tafiya da sauri cikin lokaci kaza zai iya riskar abincin nasa kuma a cikin lissafin zai haɗa da lissafin tafiyar abincin nasa tunda shima ba a tsaye yake waje guda ba. To kaga hakaito rayuwarka a matsayinka na mutum da rayuwar jemage abu ne da zai maka wahalar fahimta. Ɗalibai iri na da suke karantar ilmin dabbobi zasu riski bayanai da yawa makamantan wannan a littafin 'Are we smart enough to know how smart animal are?' rubutawar Frand De Waal ko kuma shahararren littafin nan na 'Thinking Animal'.

A wajen gizo gizo mai jego zata cinye mijinta, idan ƴaƴanta suka girma suma su cinyeta kuma hakan dai dai ne a wajensu sabo da haka tsarin rayuwarsu ya nuna.

Dalilin kawo wannan misali shi ne; kamar yadda hankalin dabbobi ya bambamta sabo da bambamcin tsarin rayuwarsu to haka hankalin mutane ya bambamta saboda bambamcin wajen zama da kuma irin abubuwan da suke kewaye da su.

Wasu mutanen a wajensu mata sune ya kamata su fita su nemo abinci kuma hakan a wajensu dai dai ne, suna ganin namiji ya fita neman abinci wani abu ne bambarakwai.

Wasu a wajensu maza ke yin kitso, idan suka ga mace da kitso sai suga hakan ya saɓawa hankali da al'ada.

Wasu a wajensu tafiya da daddare shi ne mafi kyawu kuma mafi dacewa da hankali yayinda wasu suke ganin tafiya da rana ko da sanyin safiya shi ne abin da ya dace da hankali.

Wasu ƙabilun suna auratayyar zumunci a tsakaninsu yayin da wasu suke ganin hakan ya saɓawa hankali harma wasu suke haramta hakan.

To idan muka gane cewa hankali yana rarrabuwa sabo da sauyin wajen zama to sai mu gane cewa ashe hankali wani abu ne da yake iya sauyawa daga nau'i kaza zuwa nau'i kaza. 

Abin da kuwa yake sauyawa bai dace ya zamo jagora wajen addini ba domin shi addinin baya sauyawa daga nau'i kaza zuwa nau'i kaza.

To wanne hankali ne ingantacce kenan tunda mun ji yana sassauyawa?

Hankali ingantacce shi ne wanda yake tafiya kafaɗa da kafaɗa da shari'a. 

Da ace hankali kaɗai zai iya jagorantar mutane zuwa addini ingantacce to da Allah baya buƙatar ya turo manzanni mutane da kanzu zasu gane cewa ga yanda ya kamata muyi bauta.

Amma sai Allah ya aiko da manzanni don su samarwa da mutane abin da zai saita tunaninsu kuma su bi hanya guda ɗaya wadda zata tseratar da su daga halaka.

Saboda haka sai muce shi hankali ingantacce shi ne wanda aka san Allah da shi, da siffofinSa maɗaukaka, da littafanSa masu girma, kuma da shi ne ake barin son zuciya abi abin da shari'a tazo da shi, kuma da shi ne ake gane girman Allah yayin da akai nazari akan halittar sammai da taurarin cikin ta da sauran halittu mabambamta masu ban mamaki da tsananin girma, kuma da ingantaccen hankali ne idan aka dubi ƙasa da abin da take fitarwa na daga tsirrai da ma'adanai sai a sake girmama sha'anin Allah...

Sahabi Aliyu Ibn Abi Ɗalib yana cewa "Wasu mutane sun rigaya a cikin Aljanna mai girma ba wai don sun fi sauran mutane yawan sallah ko azumi ko hajji ko umara ba, sai dai su sun hankalta dangane da Allah da halittunSa masu izina, sai zuciyoyinsu suka girgiza, rayukansu suka samu nutsuwa, suka ƙasƙantar da gaɓoɓinsu zuwa ga Allah, sai sukaiwa mutane fintinkau wajen kyawun wajen zama, da ɗaukakar daraja a wajen mutane a duniya da kuma ɗaukakar daraja a wajen Allah a lahira." 
Ibn Abid dunya ya fitar da shi a (Ashraaf 3).

Wannan tasa Nana Aisha (R.A) itama take cewa "Lallai wanda Allah ya bawa hankali ya rabauta."
(Zammul hawa na ibn Jauziy 8)

Shahararren masanin Qur'anin nan cikin sahabbai wato Ibn Abbas (R.A) yana cewa "An haifawa Kisraa yaro, sai aka kira wani malamai aka ajiye yaron a gabansa, sai aka ce da shi "Menene mafi alherin abin da za a bawa wannan yaron?"
Sai yace "A haife shi da hankali."
Sai aka ce "Idan ba wannan ba fa?"
Sai yace "kyakykyawar ɗabi'a da zai rayu da ita cikin mutane."
Sai aka ce "Idan ba wannan ba fa?"
Sai yace "Tsawa da zata ƙone shi." 
(Zammul hawa sh. 8)

Duka waƴannan maganganu na sahabbai zamu ga suna nuni akan girma da kimar hankali, kuma muna sane da cewa hankali ba hankali ba ne mutuƙar bai tafi kafaɗa da kafaɗa da shari'a ba.

Misali (7)
Malaman kimiyya da dama sun zurfafa bincike akan halittun Allah, kuma sun riski abubuwa da dama da suke gaskata abin da ke cikin Qur'ani, kamar tsagewar wata, motsin rana, hasken rana da yake haska wata, alaƙar tsawa da walƙiya, halittar mutum a cikin mahaifiyarsa da wasu abubuwan da yawa...

Amma hakan bai sanya sun karɓi musulunci ba, sai ma sake bauɗewa da wasunsu sukai sabo da hankalin baya tare da shari'a. Wasu har suna riya cewa duniya ita ta samar da kanta da kanta, wasu kuma sai suce ai wani ƙarfi ne kawai ya samar da ita...

Allah ka nuna mana gaskiya gaskiya ce ka bamu ikon binta.

Zamu dakata anan sai kuma a rubutu na gaba.


MUTANE DA HANKALI
05
Kamar yadda bayanai suka gabata zamu iya gane abubuwa da yawa daga ciki.

★ Hankalin da baya iya bambamce abin da yafi zama maslaha a jerin abubuwa ba za a kira shi cikakken hankali ba 

★ Hankali abu ne da yake iya sauyawa sabo da wasu dalilai da kuma yanayi na lokaci, guri da irin tafarkin da mutum ya taso a kai.

★ Idan hankali yana sauyawa to cewar za a gabatar da shari'a akan hankali wauta ce, don me za a gabatar da abin da yake sassauyawa tsakanin mutane da yankunansu da al'adunsu da kuma abin da yake saukakke daga sama?

Wannan sune mafi girman bayanan da suke ƙunshe a rubutun, akwai ƙananun fa'idodi wanda ba sai mun maimaita su ba don gudun tsawaitawa.

A ƙarshe hanya ɗaya da zata sadar da mutum zuwa ga Allah itace hanyar neman ingantaccen ilmin addini tare da gabatar da hukuncin Allah akan tunanin dukkanin wani abin halitta koda kuwa waliyyi ne mai karama da yake tafiya akan iska yake wasa da wuta ko ɗan boko masanin saƙo da ƙurya na kimiyya da rayuwar mutane.

Wannan shi ne abin da ya sawwaƙa daga wannan gajeran rubutu.
Sai kuma an kuma jin mu a wani baƙon rubutun.
Allah ya shiryar damu ya kuma albarkaci rayuwarmu. 
Ameen

Abu Umar Alkanawy

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.