IDAN 'BERA DA SATA...

Da sunan Allah mai jin kai. 

Duk lokacin da akace tarbiyya to ana maganar rayuwa ne baki daya, domin tarbiyya ke kawo kwanciyar hankali, zaman lafiya, albarka da abubuwa da dama na morewa zaman duniya.

Mutane nawa ne suke da dukiya amma babu kwanciyar hankali ba kuma sa jin dadin dukiyar domin rashin aminchi da fargaba sun dabaibayesu? 
Idan ka fahimchi wannan saika gane me muke nufi da morewa zaman duniya. 

Idan muka karkato da tunaninmu zuwa ga rayuwar yara masu tasowa tabbas duk mai kula hankalinsa zai tashi. Bari mu kasa yaran gida uku don bayanin yafi fitowa fili.

Kashi na farko, sune yaran da suke da gata kuma iyayensu suke kokari wajen basu kyakkyawan ilmi na zamani. Zaka iske irin wayannan yara suna tasowa da tsananin tsabagen rashin tarbiyya da wani tunani na babu wanda ya isa ya ja dasu ko kuma kaga suna jin cewa babu wanda ya isa ya taka su.... To ai sunada kudi sunsan indai a wannan kasar ne indai kanada kudi to sai yanda kayi da hukuma. Irin wayannan yara zaka iske basa girmama na gaba dasu ko kadan. Kamar yadda basa jin kunyar zuwa kowace kafar sadarwa suyi rashin kunyar da kake so. Duk a takamarsu ta cewa su din rarrafen carfet ne, kuma suna karin kumollo da wainar kwai da shayi mai kauri...

Wasu daga iyayen wayannan yara suna mutukar jin mamaki wai shin daga ina yayansu suke koyo irin wayannan dabi'u da fitintinu duk da cewa sun killacesu daga yaran talakawa wayanda suke ganin sune akan gaba wajen lalacewa... Saidai kash wayannan iyaye sun manta cewa da kudinsu suka siyowa yaransu wayannan halaye na Allah wadai.

Irin fina-finai da yaran suke kalla yau da gobe sune suke tasiri a rayuwarsu, kuma duk wani salo na wata mummunar dabi'a da suka gani tsaf zai zauna daram a cikin kwakwalwarsu, idan zaman kawai yayi da sauki. Sai dai kash ba iyakar zaman yake ba, harma kokarin dabbakawa suke. 

Ko munki ko mun so finai finai suna koyawa yaranmu dabi'u da dama. Shiyasa su turawan da suke ababen kwaikwayo a wajenmu zaka iske ba kowane irin film suka yarda yaro ya kalla ba, kai su mafi yawan lokaci ma fina finansu suna yinsu don yan kallo wayanda suka haura shekara 18 domin su a wajensu wannan shekarar mutum yana cimmata to dai dai yake da kowa.

Mu kuwa nan muna kwaikwayon turawanne kawai, kuma abin haushin ma bama dai dai muke kwaikwayon ba. Shin gidaje nawa ka sani da suke tantance wayanne fina finai ya kamata yaransu su kalla?

Yaran da suka taso suka samu tarbiyya daga wajen indiyan Bollywood da jaruman Indiyan Hausa da Jarumai dabam dabam na kasashen waje dama na gida sune zaka iske suna maganganu na rashin tarbiyya a Twitter, Facebook da sauran kafafen sadarwa. 

Wasu daga irin wayannan yaran akan dauko malami ya koyar dasu karatun addini, ko ayi kokarin kaisu islamiyya. Saidai kash, abinda ake kowa musu a islamiyyar anan gidan nasu ake fara nuna musu shirmen banza ne.

Taje makaranta ance mata ta rinka saka hijabi, ta dawo gida za'aje unguwa ta dauko hijabi ance mata "Sannu ustaziya, kinga don Allah ki saka mayafi, ke ko zafi ba kya ji..."
Taje makaranta ance mata babu kyau aske gira ko sauya halittar Allah. An tashi biki a gidansu taki tayi wannan abu don bin abinda addini ya koyar, amma sai kaji ance da ita "Sannu matar, liman... To wance tayi saukar Qur'ani amma ita kanta tana yin kaza din"...
To a karshe dole yaro zai daina ganin girman wanda yake koyar dashi addinin da kuma girman addinin ma gaba daya.

Shiyasa sai kaji ka kawowa mutum maganar addini amma saiyayi maka wata kwabar da abin zai daure maka kai.

Kashi na biyu, wayannan sune yayan talakawa wayanda suka taso cikin wahalar rayuwa. An haifesu an yasar dasu ga al'umma babu ruwan iyayen da karatunsu ko cikakkiyar lafiyarsu. Yaro daya fara wayo a fara matsa masa da hantararsa ana cewa yana ganin sa'anninsa suna kaza da kaza suna nemo kudi amma shi yana zaman banza. Yaro dan shekara goma ko da yankai waishi akewa fada akan ya fara neman kudi... Ton haka daga nan yaro saiya fara gwangwan da tsince tsince, ana haka saiya fara fitar sassafe don kerewa abokansa daga nan sai a fara daukar abubuwa har masu amfani... A kwana a tashi sai kaga yaro ya zama barawo. Tun yana yaro ya fara sabawa da kashe kudi don haka duk sanda babu kudin nan to duk mai yiwuwa zata yiwu. 

Da dama irin wayannan su suke fara shaye shaye daganan sai a shiga harkar fizge da kwace.

A inda nake rayuwa akwai irin wayannan yara birjik, hakanan a cikin makaranta Jami'ar Bayero na riski wasu yara da suke satar idon security su shigo don yin tsince-tsincen kayan robobi, kwatsam saina gansu a wani waje suna kokarin dibar abubuwa wayanda su kansu sunsan masu amfani ne. Kafin inyi kokarin yi musu magana sun ankare sun arce.


KASHI NA UKU.
Suna yaran da suke yan tsaka-tsaki wayanda sun taso cikin rufin asiri. Suma zaka iya iskesu mafi kusa da yaran farko yayan masu kudi ko kuma mafi kusa da yara na biyu yayan talakawa.

Abinda rubutun yake kokarin nunawa a takaice shine. Mafi yawan mutane muna jahiltar lalacewar yara. Wani yana kudurce cewa yaro baya lalacewa sai ka kama hannunsa ka nuna masa hanyar lalacewa...
Wannan ba haka bane, tabbas akwai abubuwan da ainihinsu ba aibu bane amma idan ka saki yaronka ka kauda ido daga kansa don yayisu to tabbas kamar ka dorashi a hanyar lalacewar ne. Idan har yaro zai rinka wadaka da kudi kai kuma babu abinda ya dameka tunda yana rage maka wani nauyi don haka ba zaka tambayeshi a ina ya samo ba to tabbas kayi babban kuskure.

Neman kudi ba haramun bane a wajen yaro, amma ya kamata a san irin neman kudi ko sana'ar da za'a koyawa yaro, a kuma lura da wajen wanda za'a turashi ya koyi sana'ar. Idan ma ta aikin karfi ce asan wacce iri ce tare da wa yake sannan a ina yake aiwatarwa?

Tabbas yara amana ne a wajen iyayensu, kamar yadda muka sani wannan amanar ta hadar da ci, sha, tufatarwa da uwa uba tarbiyya. Duka wannan nauyi yana kan iyaye kuma bazai taba sauka ba har sai yaro yakai wani minzali na mallakar hankalin kansa.

Allah ka bamu ikon sauke nauyin daka dora mana. 
Ameen thumma Ameen


Zamu dakata anan.

Naseeb Auwal 
Abu Umar Alkanawy!

Comments

  1. Gaskiya ne Wannan bayani. Allah ya bamu Ikon baiwa Ya'yanmu tarbiyya ta Gari Kodan kada mu tsinci Kanmu a wuta. Domin Allah yace: "mu tserar da Kanmu da iyalanmu daga shiga wuta" Suratu Tahrim.

    Allah ya saka da Alkhairi ya gyara halinmu Dana Yaranmu.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.