ALFAWA'ID 1

ALFAWA'ID 
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, tsira da amincin Allah su tabbata ga zaɓaɓɓe fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W). 

Wannan wasu taƙaitattun bayanai ne ko kuma tunatarwa da na tsarasu don ƙaruwarmu baki ɗaya. Allah subhanahu wata'ala ya sanyamu mu amfani da abinda zamu karanta, ya kuma yafe mana kura-kuren da suke ciki.

Kamar sauran rubuce-rubucen mu, wannan ma muna bada damar za'a iya yaɗawa yan'uwa domin shi aikin umarni da hani yana kan kowa da kowa.
Allah nake roƙo daya sanya mu cikin bayinsa tsarkaka ma'abota Aljanna maɗaukakiya. Kuma shi nake roƙo daya karɓi wannan aiki namu. Haƙika shi mai karamchi ne mai kuma afuwa.

SAƁANIN AL'UMMA
Wasu matasa biyu sunyi sabani, har ta kaisu ga tada jijiyar wuya... 
Sai wani dattijo yazo ya riskesu, ya tambaya ko akan me suke tada jijiyar wuya.

Saina farkonsu yace, ce masa nayi mutanen duniya dukansu batattu ne, shiryayye shine wanda yabi shiriyar Allah da manzonSa (S.A.W)."

Na biyun kuma sai yace "Ni kuma ce masa nayi mutanen duniya dukansu shiryayyu ne, bataccen cikinsu shine wanda yabar koyarwar Allah da manzonSa (S.A.W)."

Sai wannan dattijo yayi murmushi. Sannan yace "Duk ku biyun abu guda kuke nufi, kuna nufin shiryayye shine wanda yabi shiriyar Allah da manzonSa (S.A.W).

"Idan hakane duk duniya batattu ne sai wanda yabi shiriyar Allah, kamar yanda duk duniya shiryayyu ne sai wanda yabar shiriyar Allah.

Tsoho yaga kamar akwai alamun rashin fahimta a fuskar daya daga cikin matasan, don haka sai yaci gaba da cewa "Mutanen duniya kala biyu ne, da masu bin shiriyar Allah da masu barin shiriyar Allah, don haka idan ka dauke shiryayyun ragowar da zasu rage sune batattun, kamar yadda idan ka dauke batattun ragowar da zasu rage sune shiryayyun..."
Yana gama fadin haka sai wayannan matasa sukai murmushi suka tafa, cikin hadin baki kowannensu yace "Yanzu ka gane abinda nake nufi ko?". Suka kyalkyale da dariya tare.

Nace: 
Wannan shine irin sabanin da malaman wannan zamani suke fama dashi, wanda da yawansu rashin tsayawa su fahimci maganar juna shine yake janyo mafi girman sabani.

Allah yasa mu dace.



KARÃMAR WALIYYAN ALLAH DA SABABIN SAMUWARTA.
Umar Dan Khaddab ya rubutawa kogin Nil wasika, kuma kogin ya karbi sakon harma ya aiwatar da abinda Umar (R.A) ya bukata. Hakanan idan kana bawa Umar (R.A) labari ka jefa karya a ciki saika gama tsaf zaice maka labarinka duka gaskiya ne, saidai banda kaza da kaza, kuma saiya fado maka karyar daka saka.


Wata rana Aliyu Ibn Abi dalib (R.A) ya zauna a karkashin wata katanga, sai wani yace masa yakai sarkin muminai, wannan katangar fa gata nan zata fado... Sai Aliyu (R.A) yace "Allah ne mai tsarewa..." Ai kuwa wannan katanga bata fadi ba, sai bayan ya gama abinda yake ya tashi sannan ta fadi.

Ubaad ibn Bashar da Usaid bn Hudair sun bar wajen Ma'aiki (S.A.W) cikin wani dare mai duhu, sai kawai wani haske yayita binsu yana haska musu hanya. 

Safina (R.A) Annabi (S.A.W) ya gamu aike shi, a hanyarsa ya gamo da wani katon zaki, zakin ya tare masa hanya, Safina ya cewa wannan zakin shi dan aiken Annabi ne, wannan zakin dajin haka saida yayi masa jagora ya bashi tsaro har saida ya kaishi inda aka aikeshi.

Khalid bn Walid (R.A) yaje wata gari ya kai musu musulunchi, sai sukace ba zasu musulunta ba har sai yasha guba (poison) kuma suka kawo masa gubar. Ai kuwa yayi bismilla ya sha. Kuma babu abinda tayi masa. 

Daya daga cikin magabata masu jihadi suna kan hanyarsu sai jakinsa ya mutu, aka tafi aka barshi. Sai yayi addu'ar cewa "Ya Allah, hakika na fito ne don jihadi akan tafarkinka, kuma don neman yardarka, kuma nayi imani kai kana raya matacce, Ya Allah ka raya min jakina... Ai kuwa sai jakin nan ya tashi, kuma yabi bayan abokanansa yaje yayi yakin harma ya dawo kufa da jakin ya siyar dashi. 

Ibn Qayyim yake cewa bayan mutuwar malaminsa Ibn Taimiyya, mutane sunsha yim mafarki dashi suna masa tambaya akan wani abu daya shafi addini, kuma saiya basu amsa wadda itace dai dai. 

Wani zaice menene ya janyo haka? 
Bari muji amsoshi a takaice.
1. An rawaito cewa Allah ya cewa Annabi Musa "Yakai musa, ka zamar mini kamar yadda nake so, zan zamo maka kamar yadda kake so." Ibn Qayyim ya ambaceshi a raudatul muhibbeen.

2. Nana Aisha take cewa Annabi (S.A.W) "Ban taba ganin ubangijinka ba, face yana sauri wajen yin abinda ranka yake so..."
Bukhari da Muslim.

3. An rawaito Abu Dalib yake cewa da Manzon tsira "Ban taba ganin ubangijinka ba face yana maka abinda kake so." Sai Annabi (S.A.W) yace dashi "Ya kai Baffa na, da zaka yi masa abinda yake so, shima zai maka abinda kake so."
Baihaqi ya rawaito shi.

Nace: Kenan idan muka yiwa Allah bauta bauta yadda yake so, muka yi rayuwa yadda ya tsara mana, shima zai karramamu da abinda muke so.
Akwai littafi keɓantacce da nayi akan wannan maudu'i idan Allah ya bada iko zan fito dashi ga makaranta insha Allah.


DOLE NE MAI GIDA YA KULA DA TARBIYYAR IYALINSA DA TSARESU DAGA CUTARWA.
Allah yana bamu labari...
Sai mukace ya Adam hakika wannan (Shaidan) ma'kiyinka kai da matarka  don haka kada ya fitar da ku daga Aljanna... zuwa karshen kissar. Suratu Daha 115-123.

Nace: A karkashin wannan zamu fa'idantu da abubuwa da dama. Saidai zamu karkatar da tunaninmu waje guda domin sakon namu na yau yafi karkata ga wajen.

Allah ya bawa Annabi Adam labarin shaidan da kuma cewar tabbas abokin adawar Adam (A.S) da matarsa ne. Sai kuma Allah yaja kunnen Annabi Adam cewar kada su bari shaidan ya fitar dasu daga Aljanna... Kenan Annabi Adam shine shugaban Nana Hauwa'u. 

Kamar yadda aka umarci Annabi Adam daya kula da iyalinsa to haka kowane mai gida hakkin kula da iyalinsa yana kansa, kuma kulawar bawai iyakar ci da sha da tufatarwa ba kawai. Kulawar ta hada harda tarbiyya da kuma basu kariya daga dukkanin abinda yake na cutarwa. Domin idan muka duba da kyau, na farko an fara sanar da Annabi Adam matsayin shaidan a wajensu, sai kuma aka dorawa Annabi Adam din nauyin kada ya bari shaidan ya batar dasu.

Yaku wayanda kukai imani, ku tseratar da kawunanku da iyalanku daga wuta wadda makamashinta mutane ne da duwatsu



MUSULUNCI HANYA GUDA NE.
Musulunci na Allah ne, kuma ana koyarsa ne ta hanyoyi guda biyu kawai. Qur'ani da Hadisi, sai kuma abinda yake akan doronsu. 

Kuskure ne kace kai dan kungiya kaza ne, sannan kuma ka rinka bibiyar dalilai a cikin Qur'ani da Hadisi wayanda zasu karfafi wannan kungiyar taka. Abinda yake dai dai shine Qur'ani da Hadisi ba'a sakko dasu don tallafawa wata kungiya ba...

Tushen addinin da kuma inda ake dauko ilmi shine Qur'ani da Hadisi don haka sune abinda ya kamata su zama ma'aunin farko a wajenka. Ka koye su kasan ma'anarsu sai kayi aiki dasu. Amma muddin kace zaka rinka amfani dasu don bawa kingiyarka kariya to tabbas son zuciya zai shigo maka kana sane ko baka sane.

Allah ya jikan Imamul A'imma Ahmad Ibn Taymiyya, yana cewa bayan koro kwatankwacin irin wannan jawabi "Su maganganun malamai suna bin maganar Allah da Manzonsa (S.A.W) ne, bawai maganar Allah da Manzonsa (S.A.W) ne suke bin maganganun malaman ba".
(Istiqaama 31)

Nace:
Idan da zamuyi amfani da wannan maganar da mafi yawan sabanin da muke ya kauce. 


DARUSSA DAGA RAYUWAR NANA KHADIJA (R.A)
Kafin Nana Khadija (R.A) ta nemi Annabi akan harkar yi mata kasuwanci saida daya daga cikin magabatansa ya bashi shawarar yaje wajenta don neman ya zama cikin masu yi mata kasuwanci...

Annabi (S.A.W) bai je ba, kuma cikin wani ikon Allah sai ita da kanta ta bukaci yazo don ta ji labarinsa da amanarsa da sauran kyawawan dabi'unsa.  

Bayan yi mata kasuwanci saita kara yarda dashi harma soyayyarsa ta ginu a zuciyarta don haka ta bukaci tana son ya aureta.

Annabin rahama baiyi gaban kansa ba, sai yace mata yanada magabata don haka sai yaje yaji ta bakinsu...

Yan'uwa sanin kowane, idan sanin yakamata ne Annabi yafi magabatansa, kamar yadda ya fisu komai na cikar dan'adamtaka amma a hakan yana gabatar da su ga dukkan lamuransa... To ke wacece ko kai wanene da ba za ka nemi magabatanka a al'amuranka na yau da kullum ba?

Wannan mata Khadija (R.A) Allah ne ya zabeta don ta zama mata ga Annabin rahama. Kuma cikin bikinsu duk da a  kwanakine na jahiliyya amma ba'ai shirka ba, ba'asha giya ba, ba kuma ayi wani abu daya sabawa musulunchi ba.

Manzon Allah yana mata magana cikin girmamawa domin yana mata magana kamar yanda akewa sarakai... Ko lokacin daya fara ganin mala'ika jibril, daya dawo cewa yayi "ku lullubeni" ko "a lullubeni" bai ce mata "ki lullubeni" ko "yi maza ki lullubeni" ba. Ashe kenan anaso miji ya rinka yiwa matarsa magana cikin nuna girma ba cikin kaskantarwa ba. 

lokacin da Nana Khadija taji cewa Annabi yaga wani abin tsoro har ya tsorata sosai, maimakon tace "kai ai kuwa tafiya zanyi in barka" ko kuma ta tsorata itama tace masa "lallai wannan abin tsoro ne..." Amma inaa, sai ta nuna bata ji tsoro ba. Hakan kuwa tabbas zai kara nutsuwa ga zuciyar Annabi.
Ashe kenan anaso mace ta zamo mai kwantarwa da mijinta hankali.

Sannan don Annabi yasan abinda ya shafeshi ita ya shafa, kuma donta nuna masa cewa ta damu da damuwarsa, kuma ita mai kokari ce wajen magance matsalolinsa... Sai ta dauke shi zuwa ga wani malami... 
Ashe kenan kamar yanda miji ake so yayi kokari wajen bada kariya da iyalinsa da jajircewa a al'amuransu haka ake so gwarzuwar mace ta zama...

Kowa da kowa yasan kissar, saidai wasu suna karanta kissoshi ne ba tare da kokarin fito da darussan ciki ba.

Inama dai ace rayuwa zatai tsayi, kuma lokuta zasu yi albarka sannan dama ta yalwata. Tabbas da zanso cikin karamin sanina na zakulo mabambantan darussan cikin tarihin magabanmu. 

HALACCIN YIN SADAKA GA MAKUSANCI DA FALALARTA.
Zainab matar Abdullahi Bn Mas'ud wata rana tana masallaci sai Annabi yayiwa mata umarni da su yawaita sadaka. 
Ita kuwa Zainab, idan ta tashi yin sadaka yadda take shine tana bawa mijinta Abdullahi da kuma wasu marayu da suke karkashinta. Don haka da taji Annabi (S.A.W) yayi umarni da a yawaita sadaka sai ta cewa Abdullahi "Kaje ka tambayi Annabi (S.A.W) shin ya halatta idan na tashi yin sadaka inyita gareka kai da marayun sa suke karkashina?"
Sai Abdullahi yace, "Ke kije ki tambayeshi da kanki mana."
Sai kuwa Zainab ta tashi ta tafi gurin Annabi, saita tarar da wata mata a bakin kofar Annabi wadda take da bukata irin tata bukatar. Suna nan sai ga Bilal yazo wucewa, Sai sukai maza sukace da shi "Ka tambaya mana Annabi (S.A.W) shin ya halatta muyi sadaka ga mazajenmu da marayun da suke karkashinmu? 
Sannan sukace dashi, kada kace masa mune.
Sai Bilal (R.A) ya shiga tambayi Annabi (S.A.W). Sai Ma'aiki (S.A.W) yace "Su wanene?".
Sai Bilal yace "Su Zainab ne".
Sai Annabi (S.A.W) yace "Wacce daga cikin Zainabobin?" (Saboda suna da yawaitar zainab, hatta gidan Annabi kadai akwai Zainab guda uku.)
Bilal yace "Mayar Abdullahi."
Sai Manzo (S.A.W) yace "Na'am (ya halatta), kuma tana da lada biyu. Ladan dangantaka (Zumunci) da kuma ladan sadaka."
Bukhari (1397)
Muslim (1000)

Nace:
Ashe idan kayi sadaka ga makusancinka mabukaci zaka samu lada biyu ne, ladan zumunci da ladan sadaka.
Ashe kuma ba faduwa bane idan mace mawadaciya ta bawa mijinta kyauta ko sadaka.


MIJI BAIDA UZURI IDAN BAI TSERATAR DA MATARSA BA.
Shehu Usman dan Fodio a cikin littafansa na wathiqatul Ikhwaan yana cewa duk wanda ya bar matarsa ta fita cikin shiga da bata dace ba, ko taje wajen da ake cakudedeniya da maza take gogayya dasu to wannan mutumin fasiki ne mutukar yana da damar hanata kuma yaki hanata.

Nace: Babu wanda zai bari matarsa tayi shiga tana mai nuna sassan jikinta ta fita a haka sai wanda bashi da kishin iyalinsa. 
Yan dadi arna suna kiran hakan wayewa... _ai mijin wance wayayye ne ba ruwansa_. Shi kuma Annabi (S.A.W) yana cewa "Duk wanda baya kishin iyalinsa ba zai shiga Aljanna ba."

Ina kuma ga wanda bama matarsa ba, yarsa zaiga tayi shigar banza kuma ya barta ta fice a haka. Wata kila ma kaji yana yabawa shigar da tayi.  

Kishin ya'yanka bawai shine idan an dake su a makaranta ka kwashi kafa kaje ba, mafi girman kishi kuma mafi soyuwarsa shine kayi kishin iyalinka akan addininsu, mutuncinsu da ci gabansu.


TAUSAYI DA JIN ƘANTA GA MAHAIFINTA YA SHIRYAR DA ITA.
Na hadu da wata yar'uwa wadda na sani, sai naga yanayin shigarta ta sauya. Maimaikon sanin da nayi mata tana yin shiga wadda gama-garin yayan Hausawa sukeyi, sai naga tayi shiga mafi cikar kamala. Bance mata komai ba, da alama ta kula da cewa na lura da chanjin yanayin shiga a wajenta. Musamman muna yawan tattaunawa akan al'amuran da suka shafi musulunchi da ita. Sai tace da ni “Kwanakin a wannan littafin (Wasiqatul Ikhwaan) daka aramin na karanta wata magana, Shehu Usman Fodio (Marubucin littafin) yake cewa “Duk mutumin daya bar matarsa ta fita da tufafi masu nuna tsiraichi kuma yana da ikon hanata amma bai hanata ba, to hakika shi fasiki ne...” 

Taci gaba da cewa “Sai nayi tunanin cewa idan har miji zai iya zama fasiki akan barin matarsa ta fita da shigar da bata dace ba, to ubane yafi dacewa da wannan hukuncin. Don haka sau da dama nakan shirya zan fita, amma saboda gudun kada babana ya shiga cikin fasikai sai in fasa, musamman ina halarto yanda babana yake kokari wajen yin bauta, ni kuma haka kawai ta dalilina in jawo masa fushi da azabar Allah... gashi yanzu abin harya zama jikina...

Nace: 
Mata da yawa ko ma ince al'umma baki daya suna tunanin cewa shiga mai nuna tsiraicin wasu gurare itace wadda musulunchi ya hana, sun manta da cewa mace dukkaninta al'aurace inka dauke tafukanta da fuskarta. Kenan wuyanta, hannunta, ƙaurinta, damtsenta, bayanta, ƙeyarta da sauran gurare suma duk al'aura ne.

Allah ubangiji ka yafe mana ka kuma bamu ikon bin gaskiya.


ANNABI AKE BI BA MAZHABA BA.
Shehun mu kuma jagoran mu, mujaddadi Usman Fodio Allah ya saka masa da mafificin sakamako yana cewa cikin wani takaitaccen littafinsa mai suna Hidaayatud Ɗullaab.

“Hakika Allah maɗaukakin sarki bai wajabtawa wani a cikin littafinsa ba, haka nan Manzo (S.A.W) bai wajabtawa wani a cikin sunnarsa ba, cewa ya lazimci wata mazhaba (malikiyya, shafi'iyya, hanafiyya, hanbaliyya da sauransu) daga mazhabobin mujtahidai (manyan malamai) ba. Hakanan daga cikin magabata na kwarai malamai bamu samu wani da yake umarni da'a makalkalewa wata mazhaba guda ba.

“Da ace hakan ya faru kuwa da sun afka cikin laifi domin kaucewa amfani da kowane hadisi wanda malamin da suke bi bai amfani da shi ba.”

Nace:
Dama abin sani shine babu biyayya ga abin halitta cikin saɓon mahalicci. Kuma suma malaman mazhaba abinda suke kai shine amfani da Qur'an da Hadisi, idan ilmin abu ya ɓuya a garesu ne to sai suyi magana da ra'ayi. Kuma littafai cike suke da bayanansu akan cewa idan aka samu maganarsu data ci karo data Ma'aiki (S.A.W) to a ajiye tasu ayi amfani data Annabin Allah.

Shiyasa kuskure ne don kana ɗan malikiyya kace iyakar hadisan da imamu malik yayi amfani dasu dasu zakai aiki,  Domin ba'a turo maka Maliku ba, Annabi Muhammad (S.A.W) aka turo.

Allah kada ka jarrabemu da gabatar da ra'ayin wani daga cikin malamai akan shari'ar AnnabinKa (S.A.W).


MU HIDIMTAWA ANNABI (S.A.W)
Sau da dama nakan ƙalubalanci matasa masu bayyana cewa su masoya Annabi Muhammad (S A W) ne, musamman saboda duba da yanda basu damu da koyi da ɗabi'unsa ba ko kuma ƙoƙarin bin koyarwarsa...

Sai dai na kula da wani abu guda. Tabbas soyayyar da suke faɗa din da gaske suke, inda matsalar take shine kusancin da suke samu da lalatattun mutane da kuma sauƙin hanyar samuwa da hanyar shaidan yafi yawa. Amma da za'a matso musu da Annabin rahama da rayuwarsa kamar yanda aka matso musu da rayuwar turai, kuma a shigar da rayuwar Annabi cikin rayuwarsu kamar yadda aka shigar musu da finafinai, wasannin da sauransu, to da tabbas za'a samu chanji mai yawa.

A matsayinka na wanda kake ganin kasan abinda ya dace shin mutane nawa zaka iya lissafowa waƴanda ta dalilinka suka samu shiriya?

Ki sani cewa ke wakiliyar musulunci ce a duk inda kike, kuma Allah zai tambayeki wane irin wakilci kikaiwa musulunci, kuma wacce gudummuwa kika baiwa musulunci...

Mu ƙaddara cewa aikinmu ne duka, mu ɗora yan'uwanmu akan tafarkin Annabin rahama domin shima bai zauna ba, tashi yayi tsaye saida addinin ya kafu.

Hakika abin koyi kyakykyawa shine mafi kyawun halitta (S.A.W).

Allah ya sanya mu cikin masu shan ruwan alkausara ranar alƙiyama.
Ameen.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.