DAMISAR TAKARDA...

Da Sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Mafi girman abinda yake kara daraja da kimar mutum a rayuwa shine ilmi, gwargwadon darajar abinda mutum ya ilmantu akansa gwargwadon kimarsa da darajarsa. Don haka ne zaka iske mafi darajar mutane sune Annabawa, domin sunfi kowa ilmi, kuma ilminsu shine mafi darajar ilmummuka.

Tabbas ilmi yana da darajar da duk wahalar da akasha akan nemansa ko kuma duk dukiyar da aka salwantar dominsa ba'ayi asara ba.
Saina tuno kissoshin da muka karanta da kuma wayanda muka ji labari na irin dawainiya da wahalhalun da magabatan wannan al'umma suka sha a wajen neman ilmi, wannan ya hada da tafiye-tafiye da wahalhalu mabambanta. Kissoshi masu taba zukata, masu cike da almara, ababen tausayi da kuma dimbin darussa. Kissoshin suka sakani cikin wani yanayi na tsananin mamaki, saidai mamakin yana kaucewa idan na tuno da girma da darajar abinda suke nema wato ilmi.

Idan muka kewayo wannan zamanin, wanda muke rayuwa a ciki. Za muga tabbas akwai gagarumin cigaba wanda kimiyya da fasaha ta kawo a bangarorin rayuwarmu da dama. Cikin abubuwan da aka samu cigaba na gaba-gaba akwai hanyoyin samun ilmi da kuma shi ilmin kansa.

Ilmin da a wancan zamanin sai kayi tafiya ka keta kungurmin daji, yanzu kana kwance akan gadonka zaka sameshi ba tare daka fita daga cikin dakinka ba. Ta hanyar sauke littafi (download) a na'urarka ko hoto mai motsi (Video), Sauti (Audio) ko kuma hotuna sandararru (Images). Wani abin mamaki abinda za'a misalta maka shi a zamanin da, yanzu kanada damar da zaka bincikoshi harma ka samu ilmi mai tarin yawa akansa. Saidai kash, duk da wannan gãta da muke da shi a wannan zamani mai cike da ababen mamaki, saidai kash babu albarka ko ince albarkar tayi karanchi idan ka kamantata da albarkar da ilmin magabatan ke dauke da ita. 


DAMISAR TAKARDA
Matsalolin da yawaitar hanyoyin samun ilmi suka haifar.
Masu iya magana sukace komai idan yayi yawa matsala ne. Dauki misalin ruwa wanda Allah ya ambaci cewa kowane abu mai rayuwa, rayuwarsa tana bukatar ruwa, amma shi kansa idan yayi yawa matsala ne.
Ilmi yayi yawa ba matsala bane, asali ma shi ilmi baya yawa. Sai dai hanyoyin samunsa idan suka yawa kuma ake samunsa cikin mafi saukakawar sauki to tabbas hakan na iya zuwa da matsaloli. Wannan shine mafi girman matsalar da muke fuskanta a bangaren addini. Zaka iske mutum yana tutiyar shi masanin addini ne, alhalin bai san kananun abubuwa (basic) wayanda sune jigon addinin ba. Ko kasan saboda me bai sansu ba? Saboda bai yi karatu wajen malamai ba. Kawai ya riski wasu littafai ne da aka fassarasu ko aka rubutasu da yaren da yake fuskanta, shine ya dauka yake dubawa tare da jin cewa shima yanada ta cewa a bangaren mas'aloli na addini. Ya manta duk wayancan guraben daya tsallake, ya manta kananun abubuwan da bai sani ba. Na daga hukuncin rafkanwar sallah, hukunce-hukunce azumi, jinin haila, hajji, zamantakewa da ladubbai... Duka ya manta da wayannan sai kaji yana tada jijiyar wuya akan wata katuwar mas'ala wadda da zaiyi karatu irin wanda yake tsawon shekara goma babu abinda zai fuskanta akanta. Saboda tsaurin ido sai kaga wannan wai yanada tsaurin idon da zaiyi jayayya da malamin daya shekara ashirin, arba'in ko talatin yana neman ilmi daga wannan soro zuwa wancan soro. Ya manta karatun addini ba karatun jarida bane.  

Ko karatun kimiyya (Science) idan mutum bai san kananun abubuwa ba babu yanda za'ai ya fuskanchi manyan abubuwa.

MISALI
Mutum yaci karo da katon littafi akan human cell, sai yaji wani malamin masani akan cell biology yana magana akan plant cell, sai wannan dalibi daya karanta jibgegen littafi akan human cell ya tashi yaci mutuncin malamin yace cell a jikin human yake ba'a jikin plant ba. Harma ya kira malamin da jahili saboda shi a nasa karatun da yayi iyakar human cell kawai ya karanta kuma yake jin ya gama da cell duka. 
Irin wannan itace matsalar da muke fuskanta a ilmin addini. Mutum bai san komai ba yazo yana kore abinda yake gaskiya yana kuma kushe maganganu ko ayyukan malamai.

Ga wani misalin mafi fitowa fili.
Mutane ne gudu hudu aka rufe musu idanu, sai aka ajiye musu giwa akace suje su tabata saisu fadi menene.
Mutum na farko saiya kama hancin giwa, saiya dawo yace ai wata abace kamar igiya.
Mutum na biyu da yaje ya kai hannu sai caraf ya riko kunnuwanta, shima daya koma sai yace ai abin nan da aka ajiye musu wani abune kamar abin fifita.
Mutum na uku da yaje yakai hannu saiya kama kahon giwar, don haka saiya koma yace ai abin nan wani abune kamar kaho.
Na hudun kuma dayaje sai hannunsa ya fada kan gangar jikin giwar, iyakar inda hannunsa zai kai yaji duk itace. Sai ya koma yace ai wannan abin wani abune kamar bango ko katon dutse.
Da fadar haka sai rigima ta kaure tsakaninsu kowa yana ganin abinda ya fada shine dai dai, domin kowannensu yayi amfani da abinda ya tabo ne a zahiri. 
Menene ya janyo hakan? An rufe musu ido shiyasa, da ace idanunsu a bude suke babu wanda zaiyi jayayya da wani, domin kowanne yasan dan uwansa wani sashi na giwar kawai ya ambata. A wannan misalin na biyu, malami na kwarai shine ido, yayinda dalibi bashi da malami to tabbas makaho ne shi a duniyar ilmi.
Shin me kake tunanin zai faru idan masu karatun saka kai suka zama malaman wannan al'umma?


Akwai mamaki mutuka, kaga karamin dalibi ya hakikance yana sukar bajimin malami akan wata mas'ala. Kuma idan ka bibiya sai kaga kodai abu iri daya suke nufi da shi da malamin, ko kuma shi dalibin gabaki daya baima fuskanci mas'alar ba. Shiyasa nake cewa Wanda yafi kowa karatu da ilmi a cikin malamai, yafi kamewa daga cin mutumcin malamai yan'uwansa kan wani sabani.


Wani a irin dalibanmu na yanzu, har Allah-Allah yake idan yana karatu yaci karo da wani abu wanda mutane basu san da shi ba, don ya aiwatar dashi ya nuna musu shi mai ilmi ne, wanda sukai masa inkari kuwa sun jawowa kansu jahilchi daga jahilchinsa. 

Duka wannan shike haifar da wasu yara wayanda ke tutiyar su din masana ilmin addini ne, amma ko kusa su din basu da komai na daga ilmin Damisar takarda ce kawai.
Wayannan mutane basa ganin darajar addinin, yadda suka sameshi da ilminsa a banza, haka suke daukarsa shirmen banza. 
Wasu kuwa saboda basu fahimci addinin ba, saboda babu malami mai nuna musu hanya sai suka zurfafa zurfafawa, har suka wuce gona da iri wajen tsanantawa a addini, a karshe saika iskesu cikin jerin yan ta'adda, kuma toshewar basira har tasa su bari kafirai su rinka amfani dasu wajen cutar da musulmi da kuma yi musu kisan gilla.   

DAN'UWA, 
Idan zaka nemi ilmi ka nema don Allah, da kuma taimakon bayin Allah.
Kabi hanyar magabata na kwarai wajen neman ilmin.
Ka rike malamai na Allah, sannan duk wata mas'ala daka riska ka bijirar da ita zuwa garesu. 
Ka rinka girmama malamai, Allah zai albarkaci abinda ka samu daga garesu.


Allah nake roko daya datar damu, ya shiga lamuranmu ya kuma bamu ilmi mai amfani.

Assalaam Alaikum warahmatullah.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.
 

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.