WAIWAYE ADON TAFIYA 46 - 50
WAIWAYE ADON TAFIYA (46 - 50)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)
Annabi bai bar Da'if ba har saida yayi musu addu'ar shiriya.
A wannan shekara ta takwas bayan Hijira aka haifawa Annabi santalelen yaro, Mariya ce ta haifeshi. Anas (R.A) wanda rainon Annabi ne yana bada labari cewa bayan an haifi Ibrahim (R.A), Annabi Muhammad ya fito ga sahabbai yake sanar dasu cewa, da daddare an haifa masa yaro kuma ya sanyawa yaron sunan Babansa Ibrahim (A.S).
Matan madina suka rinka tururuwa cewa suna son su shayar da wannan dan albarkar yaro suna masu neman albarka saboda mahaifiyar yaron tana da karanchin abinda zata shayar dashi. A karshe Annabi ya damka Ibrahim a hannun Ummu Saif.
Wannan sahabin wanda ya samu tarbiyya a gidan manzon Allah wato Anas Bn Malik yake kara cewa bai taba ganin mutum mai so da jinkan iyalansa ba kamar manzon Allah, domin ya kasance yana yawaita shiga inda Ibrahim din yake ya daukeshi ya kuma sumbaceshi.
A shekara ta tara sai shugabanni suka rinka bijirowa suna karbar musulunchi a wajen Annabi, saida shuwagabanni kusan sittin suka zo suka karbi musulunchi.
A shekarata taran dai Sarki Najjashi ya rasu, Annabi ya yabe shi kuma yayi masa Sallah.
A shekara ta taran dai aka tashi wata rundunar don fuskantar mafi girman daula a duniya, wato daular Rum. Wannan yaki na daban ne, domin kuwa ba'a daukewa kowa ba. Domin wayanda za'a fuskanta din gwanaye ne wajen yaki, masana ne wajen artabu, gwaraza ne wajen gumurzu. Babu wanda akaiwa uzuri sai masu lalura don haka Annabi ya tashi da runduna mai yawa wanda yawanta yakai mutum dubu talatin. Ga shi tafiyar, tafiyace mai nisan gaske. Ga tsananin zafin rana, ga karanchin ruwa. Annabi yayi umarnin da'a kawo agaji da kuma tallafi don tafiya wannan yaki.
Aliyu ibn Abi dalib yayi tanadin wannan fita amma sai Annabin rahama ya umarceshi daya zauna ya kula da gida (madina) tunda an tafi an bar mata da kananun yara. Sahabi Aliyu yaji takaici don wannan fita mai muhimmanchi amma an hanashi fita, sai yacewa manzon tsira "Shin yanzu tafiya za'ai a barni cikin yara da mata?"
Sai Annabi yace da shi "Shin baka son ka zama a gareni kamar matsayin haruna ga musa?"
Da wannan sai Annabi ya rufe masa baki.
Abdurrahman bn Auf ya kawo dirhami dubu dari takwas ya bayar fisabilillah. Annabi yayi murna ya karba.
Sai ga Usman bn Affan yazo da wata hamshakiyar dukiya da ba'a taba jin labarin irinta ba. Annabi ya cika da farin ciki yayi masa bushara da cewa duk abinda zai aikata bayan wannan rana ba zai cutar da shi ba. Amma hakan bai sanya Usman ya rage ibada ko sakankance ba, hasalima sai kara himma da yayi don godiya ga Allah.
Ko kasan an rawaito kowace rana yana sauke Qur'ani... Shin mai aibatashi yana iya karanta izu biyu a rana ko kuwa yana karanta Qur'anin dai dai?
Umar Bn Khaddab kuwa duk abinda ya mallaka ya raba biyu ya kawoshi ga manzon Allah, ya bar rabin a gida. Annabi yaga yawan abinda Umar yazo dashi. Ya tambayeshi meka bari a gidanka, Umar yace na bar musu kwatankwacin wannan (R.A)...
Abubakar kuwa, sai gashi da dukiyarsa duka zuwa ga Annabin tsira. Annabi ya ajiye masa tambaya cewa shin meka barwa iyalanka? Abubakar yace na bar musu Allah da manzonsa.
Haka sahabbai sukaita kawo abubuwa kowa gwargwadon iyawarsa.
Munafukai kuwa sai suka rinka izgilanchi, idan mutum ya kawo kadan sai su ce ya raina Allah da manzonsa. Idan kuma ya kawo da yawa sai su ce riya yake yi don a gani.
A halin wannan tafiya ne wani uzuri ya riski Annabi inda ya jinkirta sallah, da sahabbai suka jirashi suka ga shiru, sai suka sanya Abdurrahman bn Auf ya shiga gaba ya jasu. Bayan ya idar ne, sai suka ga Annabi ya mike yana ciko raka'a guda daya... Take tsoro ya kamasu, ya gashi anja Annabi sallah. Bayan ya idar saiya karfafesu cewar abinda sukai dai dai ne. Wanda yayi nazari akan wannan zai gane muhimmancin sallah da kiyaye lokacinta.
Bayan wahalar da aka sha ana tafiya a karshe dai an riski tabuka, inda Annabi ya yada zango, saidai kash bai riski kowa ba. Babu wani abu mai rai a wannan waje.
Da Annabi yaga haka, saiya tura da sakonnin kira zuwa musulunchi ga garuruwa mabambanta. Ya kuma tashi gwarzo Khalid ya turashi tare da mutum dari hudu da yan kai zuwa ga wasu mutane inda a karshe suka mika wuya cewa zasu biya jizya.
Babban sarkin Rum ma ba'a kyaleshi ba, haka Annabi ya tura masa da sako. Inda ya maido da amsa cikin lumana cewa "Ba zasu karbi addinin ba, ba kuma zasu bada jizya ba, hakanan kuma ba zasu yaki Annabin rahama ba."
Annabi kuwa saiya wadatu da wannan amsa. Dama kuma shi baya zartar da abu da son rai. Shi kawai mai bibiyar abinda aka umarceshi ne.
Bayan Annabi yayi kwana ashirin a tabuka amma babu arna babu dalilinsu, sai kawai ya tashi ya nufi madina. Haka aka kara ratsa wannan hanyar karkashin rana mai tsananin zafi.
Mutanen madina suka fito sunata murnar dawowar Annabi muhammad.
Zamu dakata anan
Sai kuma a rubutu na gaba.
Tare da ni
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy!
WAIWAYE ADON TAFIYA (47)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...
Bayan dawowar Annabin rahama madina daga wannan gagarumar fita da akai ta tabuka, sai aka farlanta zakkah, a shekara ta 9 bayan hijira kenan. Wannan zakkah kuwa tana cike da hikimomi kala dabam dabam. A ciki akwai kyautata alaka tsakanin masu kudi da talakawa, da kuma inganta tattalin arzikin kasa, da kuma yaki da talauchi...
A wannan shekara ta tara dai Annabin rahama ya tura sahabi Abubakar (R.A) zuwa makkah don aiwatar da aikin hajji tare da sahabbai dari. Inda sukaje suka aiwatar, kuma daga wannan lokaci aka kawo karshen bautar gumaka a ka'aba, maguzanchi da kuma yin dawafi tsirara.
Shekara mai kewayowa kuwa, sai Annabi yaji cewa tabbas yanada bukatar fita hajji da kansa. Domin ya sadu da musulmai masu zuwa daga sassan duniya mabambanta, sannan kuma ya isar da mafi girman sako wato sakon Allah. Don haka zakaji wasu suna kiran wannan hajji da hajjin bankwana, wasu kuma suce hajjin isar da sako, yayinda wasu suke cewa hajjin cikawa. Tabbas wannan hajji ta gagari suna guda daya saboda muhimmancinta da girmanta.
Masoyi (S.A.W) haka yayi aikin hajjinsa wanda sahabbai suka rawaito mana komai a ciki, wasu ruwayoyin ma sai kaji kamar kai mai karantawar a gabanka akai aikin hajjin.
Tabbas a tarihi babu wani mutum daya samu kulawa kuma tarihinsa ya samu tsaro sama da Annabi Muhammad (S.A.W) hakan kuwa ya samo asali ne bisa ga jajircewar sahabbai da wayanda suka biyo bayansu da kyautatawa. Shiyasa masu dabara idan suna son sukar Annabi basa sukarsa kai tsaye, saidai su soki sahabbansa saboda mutukar suka lalata kimar sahabbai a idon musulmai to rushe abinda Annabi yazo dashi abune mai sauki. Shiyasa ka kula da wani abu guda. Duka abinda suke suna son su sanya dayan abubuwan nan a zuciyar musulmai. Kodai su sanya shakku akan mutuntakar sahabbai, ko kuma su sanya shakku akan girma da darajar Annabi.
Idan akwai tsawon rai zamu yi bayani akan hakan insha Allah.
A wata safiyar ranar Alhamis cikin aikin hajjin Annabi ya fita zuwa minna yayi sallar azahar da la'asar a can, washe garin ranar kuma saiya nufi Arfa.
Yayi huduba mai ratsa jiki, yayi bayani mai cike da hikimomi tun daga kan magana akan jahiliyya da aikoshi, da hakkokin mata da kuma kabilanchi...
Tabbas mata suna da daraja a wannan addini mai girma.
Bayan Annabi ya gama jawabinsa, saiya daga murya yana mai kallon sahabbai wayanda suke sauraronsa ko cikakken motsi basa yi saboda tarbiyya... Annabi yaji dadi sosai da zabin da Allah yayi masa na mafificiyar Al'umma da kuma mafifitan sahabbai, tabbas Annabi yasan cewa babu wani Annabi da yake da sahabbai irin nasa. Shin ko akwai wani Annabi mai sahabi irin umar a sahabbansa ko kuwa Ali Haidar gwarzon maza?
Annabi ya tambayesu shin ya isar da sako? Suka amsa da cewa tabbas ya isar...
Annabi ya daga hannunsa sama yace Ya Allah ka shaida... Ya kuma basu umarnin su isar da sakonsa ga sassan duniya. Wannan shine dalilin da ya sanya mafi yawan sahabbai da suka rayu bayan Annabi basu mutu a makkah ko madina ba.
Allahu Akbar.
Bayan wannan huduba sai Annabi ya tsaya a jikin taguwarsa, ga daga hannunsa sama yana gayawa Allah cewa tabbas ya isar da wannan sako, yana kuma nemawa kansa gafara... Yana kuka yayinda hannayensa suke sama, yana jinjina girman Allah da kuma neman gafarar Allah idan akwai inda yayi kuskure...
Allah yana ji kuma yana ganin masoyinsa yana zubar da hawaye don haka Allah madaukakin Sarki take ya saukar da wahayi akan cewa tabbas ya cika addini...
Duba wata soyayya don Allah, Allah baya son ganin manzonsa cikin wannan yanayi, yana kuma son faranta masa, don haka abinda yake rokon akai sai aka saukar masa da aya sukutum ana bayyana masa cewa tabbas an cikashe addinin. Wanene ya cika addinin inba dan aiken daya zo dashi ba?
Tun a wannan lokaci sai wasu daga cikin sahabbai suka sha jinin jikinsu, domin sunsan babban abinda Annabi yazo yi duniya shine isar da sakon musulunchi to kuwa tunda ya isar kuma Allah da kansa yayi masa shaidar isarwar menene ya rage. Don haka sai hankalin wayannan sahabbai ya dugunzuma. Wasu kuwa basu gane ba don haka sai sukaita murna cewar addini ya cika.
Zamu dakata anan sai kuma a rubutu na gaba.
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy!
WAIWAYE ADON TAFIYA (48).
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...
Tabbas addini ya cika da gaske, idan mahalicci ya fadi abu to tabbas babu jayayya. Kuma wata irin cika da musulunchi yayi shine babu abinda bai koyawa mabiyansa ba, domin kuwa komai na rayuwa da mu'amala an koyar shi yasa addinin yake tafiya da kowane zamani da kuma kowane irin mazauni... Wannan kadai ya isa ya tabbatarwa da mutum cewa tabbas wannan addini daga Allah yake... Idan akwai tsawon kwana zamuyi rubutu akan abubuwan da addini ya fada tun lokacin Annabi wayanda a kimiyyance hankali bazai tunanin an sansu lokacin rayuwar Annabi ba, amma sai gashi kimiyyar zamani ta tabbatar da abin. Tabbas Allah gwani ne kuma gagara misali.
Bayan cika addinin da Allah yayi sai kuma ya zabarwa Annabi wasu mutane na musamman don su zama mataimakansa, kuma kada mu manta sune wayannan da a cikinsu kuma a kansu aka saukar da cewa "Kune mafi alherin al'umma a cikin al'ummomin mutane, kuna umarni da kyakykyawa kuma kuna hani da mummuna..."
A cikin wayannan sahabbai saboda Allah mai hikima ne, bai tattare komai ya tarawa mutum daya ba a cikinsu, sai ya rarrabasu, wasu sukai fintinkau a Qur'ani irinsu Ubayyu ibn Ka'ab, wasu sukai fintinkau a tafsiri irinsu Ibn Abbas da Ibn Mas'ud, wasu kuwa idan kana maganar sanin gidan Annabi ne to su za'a komawa irinsu Nana Aisha, wasunsu kuwa idan kana maganar gurare ko ayyuka da Annabi ya aiwatar to kai tsaye jeka ka samesu irinsu Abdullahi Bn Umar, wasunsu kuma sai Allah ya basu mutukar kaifin kwakwalwar rike maganganun Annabi da sanar dasu irinsu Abu Huraira... Wasu kuma aka basu wasu abubuwan wayanda suke na musamman misali idan kana batun iya hukunchi da iya magana to hakika zaka iske Aliyu Bn Abi dalib shine kan gaba, idan kuma kana batun karfin firasa (hangen nesa da Allah ke sakawa mumini), Ilhama da karaama ne to tabbas daka tunkari Umar bn Khaddab zaka tabbatar kakarka ta yanke sake... Inama dai ace rayuwar nada tsawo, inama dai ace hannu bazai gajiya ba, inama dai ace uzurin rayuwa baiyi yawa ba... Da tabbas ababen rubutu akai sunada yawa.
Sahabban nan sune Allah yayi amfani dasu wajen tabbatar da fadinsa cewa "Hakika mu muka saukar da zikiri (Qur'ani) kuma hakika mune zamu kiyaye shi..."
Kada in kauce hanya daga kan sirar, bari mu dora daga inda alkalinmu ya kakare...
Dukkanin ramadan Annabin rahama da mala'ika jibril sukanyi saukar Qur'ani tare, amma a wannan ramadan da Annabi ya azumta na karshe sai suka karance shi sau biyu. Anan ta kara tabbata cewa lallai Annabin rahama yana gaf da barin duniya.
Harma Annabi da kansa yana bawa sahabbai labarin cewa lallai lokacin komawarsa ga Allah ya kusa, amma da yake ance cikin ma'anar wani hadisi "Hakika mai jin labari ba kamar mai gani da ido bane, domin lokacin da aka gayawa musu kaucewar banu isra'ila yaji babu dadi amma daya ganewa idonsa saida yayi jifa allunan Attaura saboda fusata..." Tare da cewa lokacin da Allah ya sanar dashi yasan tabbas gaskene sun kauce din kuma dan maraki suke bautawa amma daya dawo ya tarar da idanuwansa sai fushinsa ya karu. To haka suma sahabbai sun riski isharori da yawa, amma bakin cikinsu bazai kai kamar ace gashi yau an wayi gari Annabi ya koma ga mahaliccinsa ba.
Cikin irin maganganun daya rinka yi akwai "Bawai ina tsoron talauchi a gareku bane a bayana, saidai ina tsoratar muku duniya (arziki da wadaka da dukiya)"
Da kuma fadinsa shi zai riga su tafiya kuma zai musu shaida, wajen haduwarsa dasu shine ruwan alkausara.
Watan safar yana kamawa sai Annabi ya kama rashin lafiya, kafin nan kuwa yaje wata makabarta yayi addu'a ga mamatanta, washe gari sai zazzabi mai zafi ya rufe shi. Har yake sanar da Nana Aisha cewa kansa yana ciwo.
Lokacin da ciwon ya tsananta sai yasa aka kirawo masa matansa, a lokacin yana dakin Maimuna, ya nemi su bashi izinin yin jinya a dakin Nana Aisha. Ai kuwa sai suka amsa.
Ka tuna juriya irinta Annabin rahama amma sai ya kasa tafiya, sai da Fadlu Ibn Abbas da Aliyu Bn Abi Dalib suka rirrikoshi daya a dama dayan a hagu sannan ya iya lallabowa cikin jan kafa ya karaso dakin Nana Aisha. Dama mun sani su Annabawa zafin zazzabinsu ninkin namu ne. (Bukhari)
Mai karatu zai iya tuna inda mukace yahudawan Khaibar sun bawa Annabi guba a nama kuma yaci. To a wannan rashin lafiya sai yake sanar da Nana Aisha cewa tabbas yana jin tasowar wannan gubar da yahudawa suka bashi a Khaibar...
Zamu yada zango anan
Sai kuma gobe in Allah ya kaimu.
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy
WAIWAYE ADON TAFIYA (49)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...
A kwana a tashi saida Annabi yayi kwana goma sha uku bashi da lafiya, duk da zafin ciwo amma shi yake jan sallah, bai umarci wani da jan sallah ba saida zazzabi yayi karfin da fitar ma tana gagararsa kamar yadda muka ambata a baya.
A wannan rashin lafiya yayiwa al'ummarsa kashe ji cewar kada su riki kabarinsu a matsayin wani wajen bauta ko wajen idi. Kamar yadda bai bar abin haka ba har saida ya roki Allah yana mai cewa Allah kada ka mayar da kabarina wajen bauta (kamar wani gunji da za'a rinka bautawa). Wannan addu'a kuwa gashi har yau tana tasiri domin kabarin Annabi abin kiyayewa ne kuma ba'a maishe shi wajen bauta ba kamar yadda ake a kaburburan da dama daga cikin waliyyai ba.
Ranar lahadi, sai zazzabi ya kara tsananta ga Annabin rahama, su usama kuwa da aka hada rundunarsa don zuwa Rum tuni labari ya riskesu sunyo kwana. Kamar yadda da yawan sahabbai zukatansu suka kasa jurewa suka zo suka tare basu da karfin jikin da walwalar da zasu iya aiki ko kasuwanci.
Wanda ke biye damu ba sai mun misalta masa irin shakuwar da take tsakanin Annabi da sahabbai ba. Shi Annabi a wannan lokaci duk yanda zaiyi don sahabbai suji dadi a ransu haka yakeyi domin baya son ganinsu cikin wannan yanayi. Don haka juriya yake yana wasu abubuwan don kawai su dan ji dama-dama a ransu. Ko kasan ba irin zazzabin mutum daya Annabi yake ba? Shi ana ninninka masa ne, don haka zafi da radadin zai ninninku, kamar yadda ladan da zai samu kuma zai ninninku.
Da kusantowar daren litinin kuwa sai Ma'aiki ya danji sauki, to kuma yasan halin da sahabbai suke ciki, don haka saiya kokarta yazo gaban mayafin dake tsakaninsa dasu daga cikin gidansa, ya yaye sitirar dake tsakaninsu... Sai gasu jere sahu sahu suna sallah a bayan Sahabi Abubakar.
Annabi ya kalli masoyansa, tabbas ko yabar duniya akwai jajirtattun mutane daya bawa raino wayanda tabbas zai bar duniya yana mai yarda dasu kamar yadda ubangijinsu ma ya yarda dasu... Shin wanne zaiyi da zai faranta ran sahabbai?
Annabi yayi murmushi a garesu yana mai mutukar nuna farin ciki.
Babban sahabin nan Anas yake cewa "Da muka ga Annabi saida muka kusa bata sallarmu saboda murna..."
Ganin Annabi ya samu sauki sai sahabbai sukaita murna harma wasunsu da gari yayi haske suka tafi harkokinsa cikin kuzari.
Da hantsi sai jikin Annabi ya dawo, zazzabi ya sake lullubeshi, Nana Fadima tana kuka tana maganganu masu nuna bakin ciki, sai Annabi ya gaya mata cewa babu bakin ciki ga mahaifinki bayan yau.
Annabi na tsakanin cinyar Nana Aisha da kirjinta, yana sanya hannusa cikin ruwa yana shafawa a fuskarsa saboda zafin zazzabi. Yana kuma ambata musu irin dacin mutuwa...
Hankalinsu duka ya tashi babu mai sauran farin ciki a cikinsu, su suna duba yanayin da mafi soyuwar mutane a gurinsu yake, suna tunanin rayuwa idan babushi ya zata kasance?
Shi kuma yana tunaninsu yana kuma tunanin al'ummarsa da zasu zo a bayansa... Wayanda basu sadu da shi ba...
Bayan wani lokaci sai sukaga ya daga hannunsa sama yana mai cewa "izuwa guri maidaukaki" sai kawai sukaga ya sauke hannun. Ashe raine yayi halinsa!
"Wani kamshi da ban taba jin irinsa ba shine ya mamaye inda muke" inji Nana Aisha. Ita a wannan lokaci ma bata son ya rasu ba. Ta zata zazzabin ne ya kuma lullubeshi.
Labarin komawar Annabi ga mahaliccinsa ya bazu ai kuwa sai sahabbai suka rude, da yawansu suka karyata domin zuciyarsu ba zata iya daukar wannan rashi da sukai ba.
Sahabi Umar ya zare takobi zuciyarsa na tafarfasa, shi a nasa tunanin kawai Annabi ya tafi izuwa ga mahaliccinsa ne kuma zai dawo kamar yadda Annabi Musa yaje ya dawo... Ya tara sahabbai yana musu jawabi game da nanata musu cewa wanda ya kara cewa Annabi ya rasu to saiya sare kan mutum...
Ana wannan yanayi Sahabi Abubakar ya dawo, kai tsaye ya wuce dakin Nana Aisha zuciyarsa cike da fargaba, yana shiga dakin ya durkusa ya dubi fuskar Annabi, idanuwa na kwallah... Manzon rahama ya tafi. Dan aiken Allah babu, gatan marayu ya bar duniya, garkuwar halittu ya koma ga mahaliccinsa... "Kayi kyau a rayuwarkar kuma kayi kyau a mutuwarka ya ma'aikin Allah..." Ya rufe fuskar manzon Allah (S.A.W).
Daga nan ya fita izuwa ga sahabbai, ya tarar umar yanata jawabi akan cewa Annabi bai mutu ba...
Sahabi Abubakar ya kirayi Umar, amma Umar bai saurareshi ba. Ta ina zai saurareshi alhalin hankalin ya gushe saboda tsananin tashin hankali?
Don haka sai kawai ya fara jawabinsa ga sahabbai ai kuwa sai duk suka bar Umar (R.A) suka dawo gareshi.
"... Wanda yake bautawa Annabi Muhammad, to hakika Annabi Muhammad ya mutu, wanda kuma yake bautawa Allah, to hakika Allah rayayye ne baya mutuwa..." Sahabi Abubakar ya fada, sannan ya karanta musu ayar da take nuni akan lallai Annabi Muhammad zai bar duniya.
Da yawan sahabbai sai sukaji wannan ayar kamar lokacin aka saukar da ita, domin sun manceta saboda rudewa da rudani. Take sahabbai suka fashe da kuka suna koke-koke...
Wannan soyayya da take tsakani babu misalinta, babu wani shugaba da mabiyansa sukai masa koda tsagi irin na wannan soyayyar ta Annabi da Sahabbai da Ahlul baiti...
Fadar halin da sahabbai suka shiga abune daya wuce alkalami ya rubutashi, ya wuce zuciya ta hasasoshi, domin kamar yadda zuciya ba zata taba iya hasashen yanda kyawawan halayen Annabi suke ba, to haka ba zata taba iya hasaso wannan ba zugi, radadi da kuma halin rashin ba.
Annabi ya koma ga mahaliccinsa a 12 ga watan rabi'ul Auwal shekarar ta 11 bayan hijira. Yana da shekara 63.
An binne Annabi a inda ya rasu kamar yadda yake a sunnar Annabawa, inda suka rasu anan ake binnesu.
Sahabbai sun tsayar da Sahabi Abubakar a matsayin khalifan manzon Allah (S.A.W).
Bayan dawowarsu daga binneshi, Nana Fadima (R.A) ta kalli Anas cikin yanayi na kuka tace "Yanzu zuciyarku ta iya jurewa har kuka iya binne manzon Allah (S.A.W)?"
Anan muka kawo karshen wannan tarihi mai albarka.
Tare da ni
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.
WAIWAYE ADON TAFIYA (50)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...
Babu tarihin daya samu kulawa sama da tarihin ma'aikin Allah (S.A.W). Babu wani mai kidaya da zaice ga adadin littafan da aka rubuta akan wannan fiyayyen halitta.
Wanda ya karanta wannan littafi kai tsaye zai iya takaice dabi'un Ma'aikin Allah (S.A.W) kamar yadda wasu malaman sunyi littafai da dama akan halaye da dabi'unsa. Ga mai bukata zai iya nema ga sunan bila adadin.
Tarihin Annabi Muhammad bawai don jin dadi kawai ake karanta shi, ba kuma don aji tausayi a zubar da hawaye ba, kamar yadda ba don aji kokarin magabata ba kawai. Shi tarihi ana karanta shi don samun abin koyi, don sanin ainihin daga ina ake kuma ina za'aje.
Tabbas rashin sanin tarihi kamar mutum ne ya rasa tunani baki daya. Bambancin da yake tsakanin tsakanin masanin tarihi da wanda bai sani ba kamar banbancin wanda keda ido ne da makaho, mai ido yana ji yana gani bazai barka ka jashi zuwa ga hallaka ba, amma makaho tsaf zaka rikeshi ka jefashi rami.
Musamman yanzu da muke rayuwa cikin wasu mutane wayanda burinsu shine su cakuda tarihin abu mai kyau su cuda shi da mara kyau...
Ga ababen koyi masu kyau, amma matasa da yaranmu sun baude, shi akan ya koyi dabi'un manzo ya gwammace ya koyi dabi'un wani arne... Domin an kusanto masa da arnen fiye da yadda aka kusanto da ma'aiki (S.A.W). Yafi samun update akan arnen fiye da yanda yake jin hadisai ko tarihin Manzon Allah, hakanan yafi jin dadin ganin bayanai akan arnan fiye da yanda yake jin dadin bayanai akan fiyayyen halitta.
Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka sanyani na rubuta wannan takaitaccen rubutu.
Kuma hakika nayi kokari mutuka wajen takaita shi don kada yayi tsayi, tare da fito da wasu darussa na rayuwa a ciki babu ma dai irin darasi na mu'amala tsakanin Annabi da sahabbai...
Na kawar da kai daga ambaton wasu abubuwa da dama don gudun tsawaitawa. Ina fado abubuwan da suke muhimmai ne kawai. Akwai abubuwa da yawa da basu inganta ba, wasu ina kokarin fadarsu tare da bayanin rashin ingancin inayin hakane idan nasan abin ya zama sananne a wajen mutane.
Littafan da nafi dubawa a wannan rubutu sune
1. Muhammad Rasulullah na S. Abul Hasan Ali (English)
2. Nabiyyur Rahma na Dr Sani Umar R/lemo (Arabic)
3. Nurul Yaqeen na Muhammad Khudry
4. Silsilat Al adira minas siratin nabawiyya na Shaikh Musa ibn Rashid al'azimiy. (Arabic)
5. Raheeq maktoum (Arabic)
6. Zaadul Ma'ad na Ibn Qayyim
Wayannan sune kusan kowane rubutu ina kokarin duba su, wani zubin kuma ina takaita daga littafi guda idan naga ya bada komai a wadace.
Sai kuma gama garin littafai da wasu lokatan bukata tana biyowa ta kansu kamar Tafsirai ko hadisai.
A karshe idan akwai tsawon rai Insha Allah. Zan tattara rubutun ta fuska mafi amfanarwa don amfanin daliban ilmi masu bincike.
Zaka iya turawa yan uwa don su amfana da rubutun kwarai da gaske.
Kuma don shawara ko neman karin bayani ko gyara za'a iya tuntubarmu a nasibauwal@gmail.com
Allah nake roko daya tsarkake zuciyata kuma ya karbi wannan aiki ya kuma sanya albarka a cikinsa ya kuma sanyashi ya zamo mai amfanarwa ga wanda ya karanta.
Abinda yake na daidai a cikin littafin daga Allah ne, wanda kuma yake na kuskure to tabbas daga nine domin dan adam ajizi ne. Kuma ina neman afuwar Allah bisa kurakurai.
Alhamdulillah!
Bawa mabuqaci zuwa ga Ubangijinsa
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy!
Comments
Post a Comment