RIGA-KAFI
RIGA KAFI
Don shawara ko neman karin bayani sai a neme mu a kafar whatsapp a lambar
08096699926, ko a turo da sakon email ta Nasibauwal@gmail.com.
Gabatarwa
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da amincin Allah su tabbata ga
manzon tsira Annabin rahama wanda aka aikoshi rahama ga talikai.
Bayan haka, wannan wani takaitaccen rubutu ne wanda zan iya kiransa da amsa ko
kuma shawara zuwa ga wasu masu tambaya ko neman shawara. Sau tari nakanyi rubutu
irin wannan a kafar sadarwa duk don sauke wajibin da yake kaina na umarni da
kyakykyawa da kuma hani ga mummuna, amma wannan karon saina zabi rubutashi a
matsayin littafi don amfanuwar yan'uwa da kuma killaceshi ko wani ko wata zai
buqaceshi nan gaba.
Allah nake roko daya sanya littafin ya zamo mai albarka kuma mai shiryarwa izuwa abinda Allah ya yarda dashi.
Abinda yake cikin littafin na dai-dai daga Allah ne, wanda kuma yake na kuskure,
to daga nine. Allah nake roko daya karbi wannan aiki don son ManzonSa Muhammad (S.A.W).
Yaya ake gane saurayi mai tsoron Allah?
Ta yaya zan zabi miji na garo?
Ina da masoya kala-kala, wacce hanya zan bi in zabi wanda yafi zama nagari?
Ina cikin halin dimuwa don Allah a gaya min yaya ake gane saurayin banza dana
kirki?
Wayannan sune wasu daga cikin tambayoyin da yan'uwa suka jefo min wanda kuma
dukkaninsu ina bayyana musu cewa zan bada amsa bada dadewa ba. Duk da dai nakan
bada wasu amsoshin jikin jerin gwanon rubutu da nake ta hanyar sanya wani a
cikin labari yayi irin tambayar kuma wani a cikin labarin ya bashi amsa dai-dai gwargwado.
Don saukaka aikin abinda zamu aiwatar shine zamu raba littafin zuwa gida uku.
1. Abin lura daga cikin Kur'ani mai girma.
2. Abin lura daga hadisai ingantattu.
3. Abin lura daga tunani ingantacce.
Babi na farko.
Babu wani littafi a duniya kamar wanda Allah ya saukar don haka babu wani darasi
da za a rasa a ciki. Don haka a ciki zamu fara tsakuro wasu daga cikin bayanai.
A farin farko dai sanin falalar Alkur'ani abune da baya bukatar a maimaitashi
domin mai ido yasan muhimmancin hasken rana, saidai kawai a kara masa ilmi akai.
Don haka kai tsaye zamu tafi gurin abinda muke ganin shine ya tattaramu anan.
Da farko dai a matsayinki na mace musamman ma mai kamun kai, duk namijin da yazo
wajenki zaiyi kokarin nuna miki shi mutumin kirki ne. Domin kuwa da kai tsaye
idan yace miki shi mayaudari ne, ko mazinaci, ko mai shan kayan maye bai zama
lallai ki saurareshi ba. Asalima cewa zakiyi watakila shi din bashi da hankali.
Don haka maganar bincike da gane inda halayensa suka dosa naki ne.
Saboda haka idan saurayi yazo da zummar yaudara kai tsaye kinga kenan ya shiga
sahun munafukai.
Aya ta tabbata a kur'ani Allah yana cewa
إذا جاءك منفقون قالوا نشهد إنك لرسول الله، والله يعلم إنك لرسوله والله يشهد إن
.المنفقين لكذبون
"Idan munafukai sukazo maka suka ce; Mu mun shaida cewa kai manzon Allah ne",
Kuma shi Allah yasan cewa kai manzonSa ne, kuma Allah ya shaida cewa su
munafukai makaryata ne"
A karkashin wannan sai aka nuna mana munafukai a kan idon Annabi suna nuna cewar
su masu imani ne, alhalin ba haka bane.
To irin hakane kema samari da suke zuwa wajenki, kowa zai miki da'awar na kirki
ne, saidai ke ki tsaya ki tantance ki gani shin abinda yake fada gaskiya ne ko
kuwa kawai arar kayan mutanen kirkin yayi ya yafa. Zaki iya gano hakan ta
abubuwa da dama nasa tun daga kan yadda yake jera kalamansa, da kuma yanayin
askinsa, wankansa da kuma yadda yake kallon rayuwa. Ko yaya mutum yakai ga boye
wayannan abubuwa tabbas ana tare wata ran zai nuna su.
Sau tari sukan riki rantse-rantsensu su zamar musu
Kariya ko garkuwar yaudarar mace, nikam abinma yana bani mamaki wani lokacinma ya bani dariya, idan
naga budurwa ta yarda da saurayi kawai saboda yayi mata rantsuwa, alhalin kuwa
bai cike matakan zama nagari ba.... Wani lokacin sai inyi tunanin cewa kota manta abinda munafukai suke aikatawa ne?
اتخذو أيمانهم جنة فصدو عن سبيل الله
Kinga anan zaki ga cewa suma munafukai a lokacin Annabi suna amfani da
rantsuwarsu ne don a aminta dasu daga bisani kuma su sabi Allah.
Shima saurayin banza haka yake, zaiyita yi miki abubuwan da zakiji cewa tabbas
wannan yana sonki tsakani da Allah kuma zai baki kulawa alhalin shi ba wannan ne
burinsa ba, wani burinsa shine ya tara yammata da yawa don kawai a cikin
abokansa a san cewa shi gwanina wajen sace zuciyar yammata, kuma idan baki sani
ba duk abinda ya wakana tsakaninki da shi kai tsaye fa yana bawa abokansa labari
baya ga karin gishiri da zaiyi wanda wannan karin gishirin zai bata miki suna.
Wata zatace to wai wacce alamace da wayannan?
To ga wasu daga alamominsu wayanda kur'ani ya fada.
1. Zaki same su suna raina addini da masu addini.
وإذا قيل لهم آمنوا كما آمن الناس قالوا أنؤمن كما آمن السفهاء ألا إنهم هم السفهاء
ولكن لا يعلمون
"Idan akace dasu (munafukai) kuyi imani kamar yadda mutane sukayi, sai suce shin
zamuyi imani kamar yadda wawaye sukeyi? Ku saurara su sune wawaye sai dai su
basu sani ba"
Kinga anan ayar zaki gane cewa ashe halin munafukai ne yiwa masu addini kallon
wawaye ko wayanda basu waye ba. Idan kuma kema kina wannan kallon to saiki
tuhumi imaninki.
2. Son kafirai.
Daga alamun da zaki gane saurayi wanda ba na Allah ba shine ki sameshi yana so
da daukaka kafirai fiye da musulmai.
Shiyasa aka ambace su da cewa suna rikar kafirai masoya koma bayan musulmi ko maimakon muminai
الذين يتخذون الكافرين أولياء من دون المؤمنين .
Kafin hakan kuma Allah cewa yayi:
"Kayiwa munafukai bushara cewar a garesu akwai azaba mai radadi" su wanene
munafukan da ake magana?
Sai Allah da kansa ya bamu amsa da cewa "sune wayanda suke rikar kafirai a
matsayin masoya koma bayan muminai"
To don haka idan kikaga cewa saurayinki yafi girmama kafirai akan musulmi saiki
sake tunani domin hakan alamace ta munafunci.
3. Umarni da mummunan aiki da kuma hani ga kyakykyawan aiki.
Duk lokacin da kika samu saurayinki yana umartarki da mummunan aiki kamar aikata
sabon Allah, sabawa iyaye da sauransu to shima wannan ba abokin zama bane, domin
babu alkhairi a cikin tarayyar da babu taimakon juna don tsira saidai kokarin
hallakar da juna.
Allah daya ambaci munafukai saiya ambacesu da cewa:
"Suna umarni da mummunan aiki suna kuma hani ga kyakykyawan aiki"
Kowane dan Adam yana da nasa kura-kuran don haka za'a iya samun matsala, amma
idan hakan ya zamo yana faruwa akai-akai to hakan yana nuna halinsa ne hakan.
Kamar yadda wani bature ya ambata cewa "We are what we are repeatedly do".
4. Karya.
Idan kika sameshi da yawan karya da ambaton abinda bai faru ba to hakan yana
nuna cewa ba abokin tarayya nagari bane, domin yanada wani nau'i na munafunchi.
Allah ya siffanta munafukai da karya inda yake cewa
والله يشهد إن المنفقون لكذبين
Kuma Allah ya shaida cewa su munafukai makaryata ne.
Wannan shike nuna cewa karya ma alama ce tasu a yare irin Alkur'ani.
Don haka idan kikaga ya fiya gaya miki ko aikata miki karya saiki guje shi,
domin da wannan karyar ne ake rudar yammata da yawa.
Kada ki manta zai iya hana cikinsa ci ya koshi tsawon watanni don kawai yayi
miki karya guda daya kawai.
5. Karancin ilmi.
Musamman karancin ilmin addini, domin kuwa ilmin addini shine hasken dake haska
zukata, kuma shine sanadarin da yake tsarkake zuciya.
Allah ya ambaci munafukai da cewa:
ولكن المنفقين لا يفقهون
"Saidai su munafukai basa fahimta ilmi)"
Anyi amfani da kalmar fiqhu, ita kuma tana nufin ilmi.
Saidai anan mutane da yawa suna kuskuran fahimta. Domin a tunaninsu mai ilmi
shine mai tarin littafai, wannan ba haka bane. Ainihin mai ilmi shine wanda yake
da ilmi a aikace.
To menene ilmin inba aiki da shi ba.
Saboda haka mutum koya haddace littafai da dama mutuqar baya aiki dasu to wannan
ba mai ilmi bane kawaidai kamar yayi dako ne, yanzun in dan dako ya dauko kaya
zaikai wani waje ai hakan baya sanyawa ace kayan nasa ne.
6. Kasala yayin ibada.
Na'am wannan babbar hanya ce da zaki tantance, domin kuwa ita ibada babu mai
jurewa yinta sai mutum nagari mai tsoron Allah, koda mutum mutumin banza ne mutukar ya bada himma wajen ibadah to da sannu zai gyaru.
Allah yana siffanta munafukai da cewa
. إذا قاموا إلى الصلاة قامو كسالى، يراءون الناس ولا يذكرون الله إلا قليل ....الخ
"Idan suka tashi zasuyi sallah, suna tashi da kasala, kuma sunayin riya ne, basa
ambaton Allah sai dan kadan"
Anan saika gane cewa idan kaga mutumin banza yana ibada watakila yana yine don
gudun zargin mutane ko kuma don riya. Hakanan zaki sameshi da karancin ambaton
Allah, domin kuwa babu mai jurewa ambaton Allah sai wanda zuciyarsa take cike da
alheri. Shin wanne zaki zaba. Wanda zuciyarsa take cike da alheri ko kuma wanda
zuciyarsa take cike da sharri?
Saboda gudun tsawaitawa zamu dakata anan mu tsallaka babi na biyu.
Babi na biyu
Kamar yadda mukaji kadan daga cikin abubuwan da suka zo daga kur'ani dangane da
halayen masu fuska biyu wanda mukai amfani da hakan don ganin cewa wannan shine
hanya ta musamman kuma mafi sauki wajen gane masoyan gaskiya dana karya.
Masoyin gaskiya idan yazo burinsa shine samun dacewa da kuma cigaban ki keda shi
a duniya da lahira.
Shi kuwa na karya yana zuwa da wani burine a zuciyarsa. Amma saboda yasan idan
har ke tagari ce idan ya nuna miki dabi'unsa zaki guje shi, to don haka saiyazo
miki da fuska biyu, a zahiri musa a zuci kuma fir'auna.
Kamar yadda muka rarraba wayancan ayoyi a babin daya gabata don saukaka aiki, to
haka anan ma zamu rarraba tsirarun hadisan da muka dauko don saukaka rubutun da
kuma gudun tsawaitawa.
Munyi maganar karya, wanda anan zamu sake kawota, domin itace ta kunshe gaba
daya jawaban namu.
Da karyar ne za'a iya aron halin wani, ko ayi wani jawabi mara kan gado, ko
dadin baki wanda da shine mace mai karamar kwakwalwa zataji ta nutse take.
Tayaya zan gane mai karya?
Ya isheki hanyar ganewa idan yana yawan surutu barkatai mara kan gado. Hadisi ya daga shugaba (S.A.W)..
كفى بالمرء كذبا أن يحدث بكل ما سمع
"Ya ishi mutum ya zama maqaryaci idan yace zai bada labarin duk abinda yaji".
Akwai hadisi daya fadi wasu alamun munafukai, a ciki akace "Idan yayi zance sai
yayi karya, idan yayi alkawari saiya saba, idan aka amince masa sai yayi
ha'inci" sahihaini
A wata ruwayar aka kara da cewa "Idan akayi husuma (hatsaniya) dashi sai yayi
fajirchi"
Dama wasu riwayoyin makamantan wannan.
Saurarin da zaizo wajen ki yayita sharara miki zance da karya ba mutumin kirki
bane, sauda yawa wayanda suke da wannan dabi'ar sunfi zama mayaudara.
Akan kuma samu mai surutu amma maganganun nasa masu fa'ida, to anan a matsayinki
na mai hankali saiki tantance ki gani shin ina zatukansa suka fuskanta.
Duk abinda mutum yake cewa sanine baiyi ba, amma labarinsa yake bayarwa.
Karya alkawari kuwa shine abinda ma yake kawo mayaudara wajenki da marasa tsoron
Allah. Domin kuwa ba auren ne a gabansu ba, idan ma an samu anyi auren tofa
alkawarin da aka dauka na baki kulawa, da nuna miki tsantsar soyayya, tun tafiya
batai nisa ba zakiga sun fara karya alkawarin.
Zai tayi miki abubuwa har zuwa lokacin da zaki aminta dashi, da kuma kin bada
imani da shi din sai ya yaudare ki. Mafi saukin yaudara shine wanda zai janye ya
barki da cutar soyayya. Amma wani azzalumin saiya yi miki tabon da bazaki manta
da shiba har karshen rayuwa. Wani lalata rayuwarki zaiyi. Wani kuma tarbiyyarki zai lalata ya koya miki wasu abubuwan na batance wayanda rabuwa dasu da wahala.
Don haka duk wanda kikaga alamar yana kokarin sanyaki wata hanya to gwara ki
barshi tun kafin son da kike masa yayi karfin da zai sanyaki ki sabawa Allah.
Idan muka duba abubuwan da muka fada dukkaninsu suna aikine hannu-da-hannu da
karya.
Kamar yadda Shaikhul Islam Ibn taymiyyah yace "Karya wani rukuni ne daga rukunan
kafurchi"
To hakanan zan iya cewa "Karya jigoce daga jigogin yaudara".
Tayaya zaki bada rayuwarki ga wanda bai iya inganta tasa rayuwarba, kuma a haka kina burin ki samu cigaba tare da gina taki rayuwa?
Ita rijiyar da babu ruwa ko an zira guga bazai debo komai ba.
Allah ya datar damu.
Babi na Uku
A bisa tsari na rayuwa hankali yana riskar abubuwa da dama. Domin Allah daya
tashi halittar dan Adam yayi shi da hankali da yake ganewa da tantancewa
tsakanin abu mai kyau da mara kyau.
Saidai kamar yadda shaikhul islam ibn taymiyyah ya kamanta cewa shi hankali
kamar ido ne, ilmin addini kuma kamar haske ne da yake haskawa idon don ganin
abubuwa....
Misali yanzu idan mai ido ya shiga daki mai tsananin duhu babu abinda zai iya
gani. Amma idan aka samu wani haske na rana ko wata ko fitila ya ha�ska masa sai yaga komai da idon.. haka mai hankali mara ilmin addini bazai iya ganin abinda ya dace ba sauda dama, koda yayi abu yana ganin dacewarsa amma a zahirin gaskiya ya kaucewa hanyar dacewa. Ina ka baro masu aiki da hankali da a karshe wasunsu suka ce da alama Allah ya mutu? Shin wannan hankalin nasu za a kirashi da ingantacce?
Ko kuwa masu cewa babu wata rayuwa bayan mutuwa, kawai dai ana chanjawa ne daga mutum zuwa ma'adinai?.
Idan ka kula saikaga cewa lallai hankalin daya samu hasken kur'ani da hadisi da
shiryarwar addini shine yake iya gane abinda ya dace...
Mafi girman hanyar samun abokin zama nagari shine mutum ya dage da addu'a tare da dabi'antuwa da dabi'a ta gari din.
Kamar yadda muka sani Allah ya nuna mana cewa mazaje na gari, na mata nagari ne,
mazajen banza na matan banza ne.
Duk da dai ana samun jarrabawa ta inda kai zaka zamo nagarin sai Allah ya
jarrabeka da mace wadda bata gari ba... Wannan kuma wani babi ne na dabam.
Amma mutukar kana addu'ar samun nagari, tofa ita macen da kakeso ka samu ko
saurayin da kike son samu nagarin shima addu'a yake Allah ya bashi tagarin.
Kinga kenan indai baki zama tagari ba, to baza'a hadu ba.
Kamar kina son samo wani abune a gabas, amma sai kika juya yamma maimakon ki nufi gabas kinga haduwarku da wahala.
Indai har addu'ar salihai abar karba ce, to lokacin da kike neman miji nagari, saiki gaggauta zama tagari domin yana can yana rokon Allah ya bashi tagari......
Kada kuma ki manta da cewa akwai istikhara da Annabi ya koyar. In baki iya ba saiki nemi malamai su koya miki.
Sannan a yanayin mu'amala da zamantakewarki da saurayi kiyi kokari ki karanci
abubuwa da dama daga gareshi. Kuma kiyi kokari kosan halayenshi saiki auna
kigani shin zamanku tare zaiyiwu.
Misali idan ke kina da matsanancin kishi, shi kuma yana da kule-kulen mata. To
saiki auna kiga zaman zaiyiwu?
Idan baya son alaqarki da maza baki daya, kuma shi dan kasuwa ne, ke kuma
likitace ce ko malama sai ki duba kiga zaman zaiyiwu...
Shiyasa akwai abubuwa da dama daya kamata kafin aure miji ya sani dangane dake
da aikinki.
Misali idan dan kasuwane ke kuma kina aiki a asibiti ko jami'a to saiki gaya
masa ga yanayin aikinki, wata ran wani namijin zai iya kiranki a waya ko wanin
haka...
Basai bayan anyi aure yaga anata kiranki barkatai ba, tabbas ba kowane namiji
bane zai juri hakan musamman wanda baisan condition din ba.
Duka-duka wannan shine gajeran bayani da shawarar da zan baku yan uwa mata
matasa.
Ina rokon Allah daya amfanemu da abinda muka tattauna.
Ameen
Naseeb
Abu umar Alkanawy
Nasibauwal@gmail.com
Allah ya saka da alheri! Wannan rubutu ya cancanci a rubuta shi da tawwadar zinare akan takardu na zubardaju da yaqutu
ReplyDelete