ILMI KAFIN AURE.

Ilmi shine ginshikin ko jigon da yake jagorantar rayuwar mutane zuwa ga inda ya dace a lokacin da ya dace. Da ilmi ne al'umma take samun cigaba, hakanan da shine abokan adawa suke cin galaba akan kishiyarsu, da kuma shine din dai al'umma take samun kariya daga sharrin abokan adawarta. Ilmi nada mutuqar muhimmanci......

Idan muka juyo da idanuwanmu zuwa ga  rayuwar mu a cikin gidajenmu, zamu ga cewa ilmi na taka muhimmiyar rawa wajen nuna mana yadda zamu tafiyar da rayuwarmu data abokan zamanmu.....

Mu dauki rayuwar aure wadda a yanzu tana daga cikin manyan matsaloli anan kasar hausa, duba da yadda mace-macen aure yake kara yawaita da kuma rashin zaman lafiya. Wanda idan kayi nazari kayi bincike a karshe zaka tarar da cewa 90% na matsalolin ana samu ne saboda karancin ilmi, ragowar 10% dinma idan ka tsawaita yawatawa da tunaninka tofa zaka tabbatar da cewa rashin ilmin dai ba wani abuba.

Kafin aure akwai abubuwa da dama daya kamata mutum ya sani dangane dashi auren, amma hakan bata yiwuwa domin da anyi maganar aure abinda yake zuwa kan mutane shine; ciyarwa, shayarwa, tufatarwa da kuma biyawa kai buqatu da hayayyafa.... Eh to wannan yana ciki, amma kuma an manta da abubuwa da dama da suke a karkashin wayannan.

Ciyarwa: Bawai yana nufin ciyarda mata kawai ta koshi bane, a'a. Ciyarwa yana nufin ciyarda ita da abinda ya dace wanda kuma zai gina mata jiki gwargwadon samunka. Kamar yadda zaka gina naka jikin itama haka zaka gina mata nata jikin, idan kuma kai kanka baka cin abinda zai gina maka jiki to ita hakkinka ne ka bata abinda zai gina mata jikin.
Mafi Alkairinku shine wanda yafi kyautatawa iyalansa.

Shayarwa: Shima yana nufin shayar da ita da abu mai kyau kamar yadda ciyarwar take.

Tufatarwa: Shima yana nufin tufatar da ita da tufafi wanda musulunchi ya amince da shi, sannan tufafi bamai nuna kaskanchi ba, kamar yadda kake son ka ganka da kaya masu kyau to itama haka zaka samar mata masu kyau, idan kuma kai baka damu da gyaran jikinka da sanya tufafi masu kyau ba, tofa ita hakkinta ne Allah ya dora maka don haka saika sauke nauyi.

Biyawa kai bukata: Ma'ana saduwa ta aure shima wannan akwai bambamci tsakanin mutum da dabba, kafin saduwa anso a aiwatar da wasanni da abubuwan da zasu bada gudummuwa.
Kada ku jewa matanku kamar yadda dabbobi suke zuwarwa matansu.

Hayayyafa: Mutane da dama sun san darajar tara yaya barkatai amma kuma fa basa damuwa da kula da tarbiyyarsu, wanda hakan laifi ne domin yana kusa da kisan yaya saboda tsoron talauchi, kamar yadda na bayyana haka a wani rubutuna.
Dukkanninku masu kiwo ne kuma da sannu za a tambayeku akan abinda aka baku kiwon.

Bayan wayannan abubuwa da aka lissafa a sama, ya kamata ace mutum yasan yadda zai mu'amalanchi matarsa, lokacin da tayi masa laifi, da lokacin da shi yayi laifi, da lokacin da take cikin fushi ko halin bakin ciki.... Da dai sauransu.

Wannan shine amfanin tattaunawa da ake kafin aure, anan ne ake gane halaye da dabi'un juna ake kuma shiryawa zaman da za'ai wanda ake fatan mutuwace zata raba tsakani.

Rubutawa.
Naseeb Auwal
Abu umar Alkanawy

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUTUM DA HANKALI

EYE OPENER... (SIWES)

LIKITAN ZUCIYA...