WAIWAYE ADON TAFIYA (26 - 30)
WAIWAYE ADON TAFIYA (26)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)
Yanayin yanda sahabbai suka ga Annabi ya basu umarni, da kuma yadda suka ga bai damu da cewa da yawansu su fita ba sai sukayi tsammanin ba yaki za'a gwabza ba. Don haka adadin musulman yayi karanchi sosai. Domin kuwa wayanda suke da dabbobi amma a nesa Annabi bai basu umarni suje su dauko ba, hasalima da sukai niyyar su dauko dakatar dasu yayi bai kuma tsaya jiransu ba yayi gaba tare da sauran sahabbai.
A karshe Annabi ya fita da sahabbai adadin Dari uku da goma sha uku (313). Cikinsu mutum dari biyu da arba'in da yan kai duka mutanen madina ne, wato Ansarawa, ragowar kuwa mutanen Makkah ne ma'abota hijira wato muhajirai.
(Nurul Yakeen 89)
Kasancewar Abu sufyan masanin hanya, bayan ya turawa kafiran Makkah abinda ke gab da faruwa na tare ayarinsu da za'ai, saiya sauya hanya, kuma cikin sa'a sai ya kewaye wa su Annabi. Ganin ya tsira saiya tura da sako zuwa ga kafiran Makkah yana umartarsu dasu koma tunda babu abinda ya same ayarin dama kariya ce yake neman to kuma gashi ya kaucewa shirin su Annabi Muhammad (S.A.W). Amma sai Kuraishawa suka ki yarda su koma, sukace yadda suka fito da karfi babu abinda zai maidasu gida. Karfinsu zai kara fitowa fili idan ka kwatantashi da karfin rundunar sahabbai. Suka rinka murna domin su tunaninsu lokacin fatattaka sahabbai ne yayi...
Lokacin da labarin irin shirin da kafirai sukai ya zowa Annabi (S.A.W) sai hankalinsa ya tashi bawai yana tunanin rayuwarsa bane, abinda yake tunani shine masoyansa Sahabbai da kuma makomar da'awar musulunchi. Saidai kuma tare da hakan yasan Allah (S.W.A) yana sane kuma zai kawo mafita.
Tare da cewa Annabi Muhammad (S.A.W) yafi sahabbai kakaf kaifin basiri, ilmi da kuma fahimtar addini amma a tare ds hakan sai ya juyo da al'amarin garesu yana mai neman shawara. Mutum na farko Abubakar (R.A) shine ya fara jawabi, bayan ya gama Sahabi Umar (R.A) shima yayi nasan jawabin duka su biyun sukai magana mai kyau. Allah ya kara yarda a garesu. Mikdad ibn Amru shima ya tashi yayi magana yana mai nuna goyon bayansa. Shima Annabi yayi masa addu'a.
Amma a hakan Annabi bai yanke hukunchi ba, ko kasan saboda me? Saboda mutanen madina basuyi magana ba, su kuma sunyi shiru ne saboda girmama Muhajirai domin suna ganin cewa tawagar da take da Abubakar da Umar da sauran manyan sahabbai ita yafi kamata tayi magana. Shi kuma Annabi yaji maganar mutanen mutanen Makkah masu hijira don haka yanzu Ansarawa yake da burin ji.
Annabi saiya nemi a bashi shawara bayan neman farko da yayi, anan sai Sa'ad Bn Mu'azu ya gane abinda ke nufi don haka saiyayi magana mai sosa zuciya mai nuna tsananin goyon bayansu ga ma'aikin Allah (S.A.W). Annabi yaji dadin maganar kuma ta burgeshi game da nishadantar dashi. Kuma daga nan ne fa aka san cewa yaki aka fito. Amma maimakon juma'a su noke sai abu ya faskara domin ba zasu iya barin masoyinsu ba.
Karkashin wannan zamu gane wani darasi; Akwai wasu abubuwa da Allah da kansa cikin littafinSa mai tsarki ya nemi Annabin rahama ya rinka yi dangane da hakkin sahabbai.
. فاعف عنهم واستغفر لهم، و شاورهم في الأمر
1. Yi musu afuwa idan sukai masa laifi. An umarceshi da haka domin su sahabbai ba ma'asumai bane kamar shi.
2. Ya nema musu gafara idan sunyi laifi, da kuma cikin ibadunsa. Idan shi sukaiwa laifin ma yayi afuwa to ya hada da nema musu gafara a wajen Allah.
3. Ya rinka shawara dasu idan al'amari ya taso masa na yau da kullum.
Ayar nanan cikin Ali imran 159 da bayani a jimlace.
Yan'uwa ya kake tunanin nagartar mutanen da Allah da kansa ne ya umarchi mafi girman halitta da ya rinka neman shawararsu? Anya akwai hankali ga mutumin da yake sukar mutunen da Allah yayiwa irin wannan karramawar.
Hakanan umarnin ya sauka akan Annabi ne, amma hukuncin ya game dukkanin al'umma.
1. Yiwa sahabbai afuwa shine kawar da kai daga laifukan da suka aiwatar tare da kamewa bisa rigingimu da sabani daya shiga tsakaninsu.
2. Nema musu gafara shine nema musu gafara a wajen Allah (S.W.A) kamar yadda wata ayar ta zo da haka 6aro-6aro.
3. Yin shawara da su shine komawa zuwa ga fahimtarsu akan ayoyin Qur'ani da Hadisan ma'aiki (S.A.W).
Wannan hasashe nane kawai, kuma ina ganin daidaine domin babu kuskure a ciki. Idan akwai tsawon rai da nisan kwana da yardar Allah zamuyi karin haske akan wannan batu.
Munji adadin rundunar musulmai dari uku da sha uku ne, rakuman hawa guda saba'in sai kuma dawakai biyu ko uku. Mutum uku ake hadawa akan dabba guda. Idan wannan ya gaji sai wannan ya hau.
Annabi Muhammad da kansa su uku ne akan rakumi guda. Da shi (S.A.W) da gwarzon namiji Aliyu (R.A) da kuma Marsad ibn Abi Marsad.
Aliyu da Marsad suka bukaci Annabi ya hau abin hawan su zasuyi tattaki, su sun yarda zasu jurewa zafin rana da wahalar tafiyar. amma sai Annabi yaki yarda harma ya nuna musu cewa su biyun basu fishi karfin jiki donyin tattaki ba, kuma kamar yadda suke kwadayin lada shima haka yake kwadayin lada don haka yadda zasu samu ladan tafiya a kasa shima yana son samun wannan ladan. Hadisin na nan cikin Musnad da Ibn Hibban.
Ashe da Annabi ake rige-rigen yin ayyukan lada.
Ina mai cewa shi Annabi kawai yake so, soyayyar Annabi kawai ya rike ba ruwansa da aiki don baya son lada? To wannan raddi ne gareka.
Babban abinda zakayi ka burge Annabi idan har da gaske kana sonsa to shine kayi aiki tukuru don neman lada da yardar Allah. Annabi zaiyi alfahari da masoya masu aiki ne ba masoya masu labewa ba.
Karfin Rundunar Musulmai da ta kafirai bazai hadu ba, domin su kafirai kusan su dubu suka fito, tare da rakuma dari bakawai da dawakai dari.
Kowace runduna na tafe kusancinta da abokiyar gwabzawarta yana karuwa.
Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.
WAIWAYE ADON TAFIYA 27
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)
Bayan rundunar musulmai sun bar Madina suna tafe bisa dandaryar kasa, wasunsu akan abin hawa yayinda da yawansu ke tafe a kasa bisa duga-dugansu. Kowane abin hawa yanada ayyanannun mutane akansa, idan wannan ya gaji da tafiya sai na kai ya sakko kasa shi mai gajiyar sai ya hau, haka shima idan ya samu hutu sai cikon na ukunsu ya karba. Wani abin burgewa shine shi wanda yake kai Allah-Allah yake ya sauko don wanda ke kasa ya huta, shi kuma na kasan yana iyakar iyawarsa wajen ganin ya boye gajiyarsa don kada nakan abin hawan yaga alamar ya gaji ya sakko... Wasu mutanen tsaf zasu iya goyon uku akan dabbar da suke tarayya akanta. Saidai baza suyi hakan ba, domin musulunchi addini ne wanda yayi umarni da kyautatawa dabbobi da kuma kula da hakki da lafiyar dabbobi sawa'un na kiwo ne ko kuma na hawa ne.
Tawagar sahabbai na tafe dukkaninsu cikin sadaukar da zuciyoyinsu zuwa ga Manzon Tsira (S.A.W).
Cikin wannan runduna ta sahabbai harda wani yaro dan shekara goma sha shida. Wanda yake ta boye kansa kada Annabi Muhammad ya hangoshi, domin yasan mutukar Annabin rahama ya ganshi tofa tabbas zai mayar da shi madina ne saboda karanchin shekarunsa. Yana cikin rakabewar ne caraf yaji an rikeshi. Wannan yaro da ake kira Umair bn Abi Wakkas, saiya tsorata, bisa ga mamakinsa sai yaga ashe yayansa Sa'ad Bn Abi Wakkas ne ya damke shi. Sa'ad ya tambayeshi ko lafiya yaketa labe-labe cikin mutane, sai Umair ya zayyanewa yayansa abinda yake tunani idan Annabi ya ganshi, shi kuma abinda yasa yake son wannan yaki shine, yana son Allah ya azurtashi da shahada...
Haka wannan yaro Umair ya wanzu cikin wannan runduna, ai kuwa sai sukai ido hudu da Annabin rahama. Ai kuwa take Annabi ya kirashi ya gaya masa maganganu masu kwantar da hankali daga nan ya umarceshi daya koma gida... Nanfa Umair ya fara sharara kuka... Ya fashe da kuka yana tuno zafi da radadin rabuwa da manzon Allah, ya rinka tuno irin fargabar da zai shiga idan akace yana madina Annabi kuma yana nan...
Da Annabi yaga yadda wannan yaro ya damu, sai kawai ya bashi umarnin yayi zamansa. Ya kyaleshi.
Bayan sun kusanta ga inda za'a gwabza gumurzun, sai suka zauna a masaukansu suna masu jiran wayewar gari. Suna jiran dayan nasarori biyu. Kodai a kashesu suyi shahada, ko kuma su su kashe su samu lada kuma addinin Allah ya daukaka. Don haka su a ganinsu babu faduwa anan.
Washe garin ranar rundunonin biyu kowace ta fito don karawa da abokiyar gwaminta. Jere suke reras bisa sahun yaki.
Duba da zahiri, babu hadi domin kafirai sun ninninka yawan musulmai, haka nan idan ka duba karfin ababen hawa namma zaka iske cewa gaba ake da musulmai nesa ba kusa ba, bare kuma azo maganar makamai, don a cikin sahabbai akwai masu karyayyun takubbai wasu kuma abinda suke dashi bai kai haka ba.
Annabin rahama kuwa daga hannunsa sama yayi yana kai kukansa zuwa ga Allah, hawaye na kwaranya daga idanunsa guda biyu, Sayyadina Abubakar dake tare dashi ya sunkuya kasa, ya dakko mayafin manzon tsira wanda ya fadi kasa saboda yadda Annabi ke daga hannunsa sama yana mai neman taimakon ubangijinsa. Sahabi dan Sahabi da Sahabiya Abubakar (R.A) ya rarrashi Annabi yana mai kara masa kwarin gwiwa kamar yadda shima Annabi yya karfafa masa gwiwa a wannan lokacin da suka shifa cikin kogo yayin hijira. Hakika Abubakar ya razana ganin kafirai na gab da cim musu, amma sai Annabin rahama yace dashi "Kada kaji tsoro, hakika Allah yana tare da mu."...
Wannan itace abota tagari, wannan itace abota wadda ake so. Wadda idan sashe ya samu rauni ko karaya daya sashen zai karfafeshi.
Daga nan Annabi ya fuskanchi sahabbai, yayi musu maganganu masu ratsa zuciya da kuma kwadaitar dasu da rahamar Allah. Maganganu ne masu mutukar girma da ratsa zuciya irin maganganun nan masu mutukar ratsa zuciya su mayar da mafi lalacin mutanen mafi jarumtarsu.
Daga kafirai kawai saiga wasu mutum uku sunyi fitar burtu suka wanzu a tsakiyar filin daga cikin nuna isa da kasaita, suka kuma nemi fito na fito da wasu daga cikin sahabbai. Wayannan kafirai kuwa Utba ibn Rabīa ne da dan'uwansa da dansa Shayba da walīd.
Kafin muhajirai suyi wani yunkuri tuni wasu daga Ansarawa mutum uku sun fito don yin fito na fito da wayannan zaratan kafirai, amma sai wayannan kafirai suka ce sunfi son mutane daga tsatsonsu.
Kafin wani ya fita tuni Annabi ya kira sunayen mutane uku. Ubaida bn Harisu, Hamza bn Abdulmuddalib da Aliyu Bn Abi Dalib.
Kai kana jin wayanda Annabi ya kira kasan Annabi yasan mazajen fama. Ai kuwa take suka hallara. Ubaida kasancewarsa mafi girman shekaru saiya tari dan uwansa a yawan shekaru wato Utba, Hamza kuma da Shayba, Aliyu kuwa saiya tari walīd.
Kura ta turnuke ilahirin bigiren da suke. Kafin wani kyakkyawan lokaci Aliyu ya gama da Walīd, Hamza ma kuma ya kawar da Shayba. Yayinsa Ubaida da Utba suketa gwabzawa sun jiwa junansu raunuka. Ganin haka yasa Aliyu da Hamza suka kawo dauki suka hallaka Utba. Shi kuwa Ubaida sai aka daukeshi aka kaishi wajen manzon Allah, Annabi ya dorashi akan cinyarsa. Tabbas ya zubar da jini da yawa. Annabi ya lakana masa kalmar shahada, yayi sannan yace yaso ace Abu Dalib yana nan don ya tabbatar da cewa baitukan da
Ganin haka sai kafirai suka dugunzuma. Sukayo dauki kan musulmai da zummar suyi musu kwaf daya ta hanyar yi musu sukuwar sallah.
Annabi ya kara karfafar sahabbai game da gaya musu cewa tabbas duk wanda yayi yaki saboda Allah aka kasheshi to hakika zai shiga Aljanna. Umair ibn Humam yana jin haka sai ya sake tambayar Annabi. Annabi ya maimaita masa cewa kwarai wanda yayi shahada sakamakonsa Aljanna. Ai kuwa sai Umair ya fito da wasu dabinai yana ci wayanda suke jikinsa, daga bisani yayi wurgi dasu yace bazai tsaya bata lokaci ba ga Aljanna yana gani kiri-kiri ai kuwa saiya zabura ya afkawa kafirai da sara da suka suna maida martani har a karshe suka kasheshi.
(Nurul yakeen 94)
(Zad al ma'ad)
Runduna biyu ta hadu, karar haduwar karafa ta karade ilahirin filin badar. Wata gagarumar kura ta sake karade filin ashe mala'iku ne suka sauka don taya muminai yaki. Cikin lokaci kankani sai gashi anyi buju buju da kafirai, suka juya suna neman matsera, yawansu ya zama na banza. Musulmai suka bisu suna kamawa da kashe na kashewa. A mushrikai an kashe wayanda adadinsu ya kai mutum saba'in ko kusa da haka. Cikinsu akwai Utbatu da Shaiba da walīd wayanda tun a farkon yakin aka shafe babinsu. Hakanan Abu ubaida shima ya kashe mahaifinsa bayan mahaifin nasa ya kawo masa farmaki Allah ya tseratar dashi. Hakanan cikinsu akwai Umayya bn Khalaf da dansa Aliyu, Cikin wayanda suka kasheshi da dan nasa akwai Ammar bn Yasir da kuma Bilal don ramuwa akan abinda ya aiwatar musu na azabtarwa a makkah. Cikin wayanda aka kashe harda Hanzalata dan Abu sufyan, da Abu Jahal... Da wasu da dama.
Hakanan wayanda aka kama a matsayin fursuna wato wayanda aka kamasu suka zama a hannun musulmai suma mutum saba'in ne.
Cikin wayanda sukai shahada a wannan yaki na Badr harda Umair bn Abi Wakkas, wannan matashin yaron da Annabi ya umarceshi daya koma madina shi kuma ya nace lallai shahada yake nema.
Ayi mana hakuri zamu dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba da yardar Allah.
WAIWAYE ADON TAFIYA (28)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W).
Rukayya (R.A) yar gidan Annabi bata da lafiya kuma mijinta Usman Bn Affan shi Annabi ya bawa umarnin ya zauna tare da ita don kula da ita. Usman ya zauna amma zuciyarsa cike da damuwa gami da tunanin abinda ka iya zuwa ya dawo. Na farko dai yana cikin tashin hankali mara misaltuwa domin matar da yafi so a duniya kuma yar gidan wanda yafi so gata nan kwance babu lafiya. Na biyu kuma mahaifinta wanda yafi so gashi can ya bijirar da ransa zuwa gakafirai. Usman (R.A) yana cikin tashin hankali mutuka, ya rasa inda zaisa ransa, tunani kala-kala yana ta kai kawo a cikin zukatansa, yana kuma bijirowa da Allah bukatunsa. Yana ta kai kuka wajen Allah akan Allah ya bawa AnnabinSa nasara akan kafirai... Yana cikin wannan yanayi matarsa rai yayi halinsa. Hawayen bakin ciki ya kwaranyo daga idanuwansa ya wanke fuskarsa, duniyar tayi masa nauyi tamkar a mafarki yake jinsa, ji yake kamar ya kirata ta amsa. Shikenan ta tafi ta barshi. Yana cikin wannan yanayi sai tunanin Annabi muhammad yazo masa. Nan fa hankalinsa ya kara dugunzuma ya rasa ina zaisa kansa, shin yanzu a wanne hali Ma'aiki yake ciki. Zuciyarsa ta rinka saka masa tunani kala-kala. Haka yayi ta maza sukaje suka binne yar Annabi Muhammad (S.A.W). A hanyarsu ta dawowa suka hadu da masu bushara suke sanar dasu cewa Annabi muhammad yayi nasara. Cikin sahabbai 313 goma da yan kai ne kawai sukayi shahada.
Bayan Annabi ya dawo aka raba ganima cikin wayanda aka bawa harda wasu da akai musu uzuri basu je ba kamar dai shi Usman da sauran sahabbai wayanda kodai an basu tsaro ko kuma an aikesu wani guri bincike.
Daga nan Annabi ya nemi shawarar yaya zaiyi da fursunoni. Take Sahabi Umar yace a karkashesu. Wasu sahabbai da dama suka yarda da abinda yace. Sai Abubakar yace kada a kashe su, a sanya fansa akansu. Kowa daga kafirai yazo ya fanshi dan'uwansa. Hakan akai kuwa.
Cikin wayanda aka kama akwai Abul As ibn Rabi'i, mijin Zainab yar gidan Annabi. Shi kuwa mutum ne, idan nace mutum ina nufin mai mutumtaka. Domin kuwa akwai wani halacci da yayi mana wanda ba zamu manta da shi ba... Lokacin da wutar adawa ta kunnu tsakanin Annabi da Kafirai, sai suka takurawa Abul-As cewar sai ya saki yar Annabi (S.A.W) ba don komai ba, sai don suna so su wulakanta Annabi. Amma sai wannan mutum yaki yarda. Saidai alfahari ma da yayi cewa abin alfahari ne ace yana auren yar Muhammad (S.A.W). Don haka da labari ya jewa matarsa zainab cewa ga mijinta an kamashi, saita rasa me zatayi fansarsa dashi. Ai kuwa sai dabara tazo mata. Take ta lalubo wasu kayanta masu kyau, wayanda mahaifiyarta marigayiya Nana Khadija ta bata don fitar amarchi lokacin da akai bikinta. Ai kuwa ta bada wannan rigar tace aje a bada ita a karbo mata mijinta. Aikuwa akaje da wannan riga.
Annabi yana zaune sai kawai ganin dan aiken yayi ya bijirowa da sahabbai wannan riga daga yar'sa Zainab zatayi fansar mijinta da shi. Take tausayinta ya kama Annabi, tabbas yasan basu da kudi, kuma a lokaci guda ta tuno masa da masoyiyarsa khadija. Mutum biyu kacal zasu gane irin yanayin halin da Annabi ya shiga wannan lokaci. Mai auren daya rasa matarsa mafi soyuwa a gareshi, wadda soyayyar da ke tsakaninsu babu ratsi a ciki. Ko Kuma mai ya'ya. Don haka take jin kai da tausayi suka mamaye Annabin rahama. Ya tuno irin soyayya da kulawa da mahaifiyar wannan yar tasa ta bashi. Ya kuma tuno irin shakuwar da take tsakaninsu. Zuciyarsa ta mamaya da tausayinta.
"Idan kuna ganin zaku sakar mata wanda aka kama mata, kuma ku mayar mata da kayanta (dukiyarta) to ku aikata"
Annabi ya furta hakan zuwa ga sahabbansa.
Yan' albarka, babu wanda yayi musu a cikinsu, cikin girmamawa da soyayya da rige-rige wajen daukar shawarar Annabi suka sakar mata mijinta da kuma mayar mata da kayanta. Amma bisa sharadin bayan ya koma makkah zai barta tayo hijira. Haka akai kuwa Annabi ya tura wasu sahabbai su taho da ita.
Ka duba darajar aure, yar Annabi guda tana auren kafiri amma Annabi bai tirsasa an raba auren ba kasancewar akwai soyayya a ciki. Kuma bayan ta dawo da mijin nata ya musulunta, take Annabi ya mayar da ita gidan mijin nata ba tare da anyi sabon aure ba.
Ko ka tuna Abu jahal da irin yadda ya cutar da Annabi?
To a wannan yakin na Badar ya rasa rayuwarsa, wanda shine ya rinka ziga mutane cewar su fito kwansu da kwarkwatarsu, ashe kiransu yake su fito suga kaskantarwa da Allah zai masa. Domin kuwa yara kananu ne suka kasheshi yayan wani mutum wani da ake kira Afra.
Lokacin da kafirai suka koma makkah sai koke koke ya cika ko'ina a makkah da dama daga cikinsu suka rinka cin alwashi sai sun dauki fansa akan Annabi Muhammad (S.A.W), cikinsu harda Abu Sufyan.
Amma sai suka boye qudirinsu saboda suna sane da yan'uwansu da suks hannun Annabi a matsayin fursunonin yaki.
Al'amarin wayanda Annabi yasa aka kama kuwa haka yan'uwansu sukaita zuwa suna fansarsu. Wanda kuma ya iya rubutu da karatu sai a hada masa yara goma cikin musulmai ya koyar dasu. Da wannan koyarwar da zai musu sai ya fanshi kansa. Daga cikin wayanda suka koyi karatu da rubutu a wannan lokaci harda Zaid ibn Sabit.
Wasu kuwa saboda Annabi yaga talakawane sai kawai ya sake su, wasunsu da dama bayan sun koma makka sai suka musulunta saboda ganin irin karramawar da akai musu. Suna kamammu masu laifi amma musulmai basa cin abinci har sai sun tabbatar kamammunsu sun koshi. To ina abin mamaki anan, addinin da ko mage ba'a yarda ka tsareta ba tare da abinci ba... Shin akwai wani addini ko wata kungiya da takai musulunchi mutunta yan'adamtaka da kuma hakkin dabbobi?
Wasu kuwa sun shirya munafunchi a boye, amma idan suka zo fansar yan uwansu sai su tarar Annabi yana basu labarin abinda suke kullawa. Don haka saisu tsinke da lamarinsa saisu musulunta.
Wasu sun shirya idan sunzo zasu faki ido su kasheshi (S.A.W). amma rashin damar yin hakan tasa suka hakura. Amma bisa ga mamakinsu saisu tarar Annabi ya basu labarin irin kullin da suka taho dashi.
A cikin kamammu akwai Abbas baffan Annabi kuma shima talaka ne, sannan tirsasashi akai ya fito wannan yaki, amma saboda adalchi irin na Annabi bai sakeshi ba, saida ya fanshi kansa. Harma yake gayawa Annabi cewa shifa bashi da kudi. Sai Annabi yace masa amma ai akwai kudin daka bawa wance ajiya... Sai mamaki ya kamashi. Domin daga shi sai ita suka san wannan maganar.
Kamar kullum dai ayi mana afuwa zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy
WAIWAYE ADON TAFIYA (29)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)
Nasarar da aka samu akan kafiran Makkah ta mutukar dugunzuma su, kamar yadda ta fusatasu suka rinka cin alwashin sai sun dauki fansa akan wannan nasarar da akai akansu.
Wasu kamar Abu Sufyan, shi rantsewa yayi yace bazai kara taba ruwa ba (wanka), harsai ya dauki fansa. Haka kuwa akayi, don babu jimawa da yin badar ya tara mahaya mutum dari biyu suka nufo madina a sukwane da gaggawa don kada ma aji labarin tahowarsu. Sallam ibn Mishkam shugaban yahudawan Banun Nadir shine ya saukesu, ya basu abinci da abin sha, sannan ya basu bayanai akan madina. Abu Sufyan ya kashe mutane biyu sannan ya arce. Annabi da sahabbai suka bi bayansu amma inaa basu sadu da su ba.
Haka yahudawan Banu Qainuk'a suma suka sabawa alkawarin da ke tsakaninsu da Manzon tsira. Tare da cewa dole ta saka a karshe sun mika wuya. Sannan aka tirsasawa suka bar madina tare da cewa anada bukatar karfinsu domin sunada mayaka sama da dari bakwai ga kuma gwanintarsu da kwarewarsu wajen kera makamai. Saidai menene amfanin kwarewa ko karfin soja ga wanda ke manufantar Annabi da Sahabbai?
Kasancewar Abu Sufyan yazo har Madina ya kashe mutum biyu, hakan saiya karawa kafirai karfin gwiwa suka rinka tanadi suna son zuwa daukar fansar yan'uwansu.
Bayan yakin Badr da kadan wani muhimmin abu ya faru. Wato aure daga aurarraki mafiya daraja a doron kasa. Abubakar da Umar (R.A) da kansu sukaje suka samu Aliyu kowannensu yana mai bashi shawarar ya nemi auren 'yar gidan Annabi Fadimatuz-Zahra'u.
Dan'uwa wayannan su ake kira abokai nagari. Kamar yadda hadisai suke gaya mana yadda ya kamata musulmi da musulmi su zama, to haka tarihin Annabi da Sahabbai cike yake da nuna mana misalai.
A wata riwayar wadda na riska kwanannan akwai wata baiwar Allah da itama tayita bawa Aliyu bn Abi dalib shawarar neman Nana fadima.
Da Sayyadina Aliyu yaga shawara ta yawaita, sai yaje wajen Annabi ya nemi auren Nana Fadima, sai Annabi ya bukaci ya kawo sadaki, inda ya dauki bargonsa ya tafi dashi wajen amininsa Usman Bn Affan, yace masa yana so ya siya zai biya sadaki da kudin. Sahabi kuma ma'abocin karamchi da alkunya Usman ya sayi bargon nan da daraja, da Aliyu zai tafi, sai Usman ya hada masa da kudin da kuma bargon, yace ya bar masa shi.
Cikin murna Aliyu (R.A) ya rasa da wanne sakamako zai sakawa wannan amini nasa, sai yayi masa addu'ar alheri. Daga bisani kuma ya tashi ya tafi izuwa ga Annabi ya kaiwa Annabi wannan kudi a matsayin sadaki da kuma abinda zasuyi siyayyar abinda ya zama dole dashi. Ya kuma gayawa Annabi abinda ya faru tsakaninsa da Usman.
Farin ciki ya mamaye zuciyar Annabi, domin babban burinsa shine yaga kan sahabbansa a hade. Annabi bai iya boye farin cikinsa ba, saida ya fito da shi fili yayiwa sahabi Usman Addu'ar alheri.
Riwayar kissar auren tana nan a cikin wani rubutunmu daya gaba ta amma ba wannan (waiwaye adon tafiya) ba.
Bayan yakin badr dai Annabi ya bada umarnin kashe wani shugaba (Ka'ab Ibn Ashraf) daga yahudawa wanda yake yin iyakar kokarinsa don ganin ya jefa Annabi cikin matsala, hakanan koda yaushe cikin wakoki yake na cin mutunchin matan sahabbai da batanchi ga Annabin rahama.
Can al'amarin kafiran makkah kuwa, duk wanda aka kashewa dan'uwa a Badr sun hadu wajen Abu Sufyan. Wannan dukiyar da Abu sufyan ya tseratar da ita kuwa dukanta aka juyata aka siyi makaman yaki da sauran tanadi. Suka tashi runduna cikin shiri wanda ya zarce na badr domin wannan karon su dubu uku ne, sannan cikakkun mayaka ne kwararru.
Matansu suka fito tare dasu don basu kwarin gwiwa. Suka zo daf da madina suka kafa sansani.
Abinda Annabi kuwa ya tsara shine ya zauna a cikin madina, ya barsu su kadai, ba tare da yakarsu ba, mutukar ba kokarin shigowa madina sukai ba. Abdullahi Ibn Ubayyu da kansa ya yarda da wannan abu da Annabi ya tsara.
Su kuwa sahabbai musamman wayanda basuje Badar ba, sai suka rinka neman Annabi ya basu umarnin su fita don samun falala ko shahada.
Bayan wani lokaci jim kadan da wayancan sukaita matsawa Annabi akan suna so suma su samu wannan falala don haka a fita a tari kafirai, sai Annabi ya shiga gida yayi shirin yaki, sai suka gane cewa tabbas sunyi kuskure, don haka sai suka cewa Annabi ya zartar da abinda yake dai dai. Domin suna ganin kamar takura masa sukai. Sai Annabi yace musu bai dace da Annabi ba, yayi shirin yaki ya kuma kiyin yakin ba. Ko kamar yadda yace...
Kaji jarumta irinta irinta Annabi. Annabi ya fita da mayaka mutum dubu guda. Yayainda kafirai suke mutum dubu uku, ga kuma matansu a tattare dasu.
Akan hanya Abdullahi Bn Ubayyu ya janye kaso daya bisa uku na rudunar yace musu Annabi yaki bin shawarata (ta zama cikin madina) don haka sai rundunar Annabi ta zama mutum dari bakwai da yan kai.
Annabi bayan ya fita saiyaje daf da dutsen uhudu shida sahabbansa. Wanda ke arewa da madina. Ya sanya dutsen a bayansu. Sannan yayiwa sahabbai kashedi cewa kada suyi yaki har sai ya umarcesu. Aka damka tuta ga Mus'ab Ibn Umair.
Annabi ya tsattsarawa sahabbai komai kuma ya umarci kowa ya zauna a bigiren da aka sakashi komai rintsi.
Kamar dai yakin dawa wuce haka wannan ma an samu yara guda biyu masu shekaru sha biyar, amma sai Annabi ya umarcesu da komawa gida, sai baban daya Rafī yace ai dansa mayakine na gaske, don haka Annabi ya kyaleshi, da jin haka sai wancan yaron shima yace ai ko kokawa za'ai zai iya kayarda Rafī. Nan take aka basu fili kuwa, sai Samura ya kayar da Rafī, don haka duka su biyun sai aka barsu don bada tasu gudummuwar.
Daga nan kowane sashe yayi dauki kan sashe. Matan kuraishawa suka fara wakoki don karawa mutanensu kwarin gwiwa. Da kuma zuga su don daukar fansa.
Kafirai sun zo da wata zuciya mai cike da son daukar fansa. Yayinda sahabbai suka fito da wata zuciya ta son yin shahada.
Ko yaya gamuwar zata kasance?
Zamu yada zango anan.
Sai kuma a rubutu na gaba idan Allah ya bamu iko.
WAIWAYE ADON TAFIYA (30)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...
Kamar yadda masu iya magana sukace waiwaye adon tafiya, to bari mu waiwaya kadan kafin mu ci gaba da rubutun domin mun tsallake abubuwa da yawa, tare da cewa dama mun ambata cewa wannan tarihin namu takaitacce ne, amma akwai muhimman abubuwa da takaitawar bai kamata ta sanya a rinka ajiye su ba.
★ A goma ga watan Zulhijja na shekarata biyu bayan hijira aka fara sallar yanka. A itane Annabi ya yanka manyan raguna kyawawa guda biyu.
★ A wannan watan kuma a cikin wannan shekarar Usman ibn Maz'un ya rasu a riwaya mafi inganchi. Kuma aka binneshi a Baqi'a. Shine mutum na farko daya mutu aka binneshi anan cikin masu hijira.
★ A watan Rabi'ul Ula na shekara ta uku ne Usman Bn Affan (R.A) ya auri Ummu kulthum yar gidan masoyi (S.A.W) bayan rasuwar yar'uwarta Rukayya. Itama ta biyun Allah bai kaddara masa haihuwa da ita ba.
★ A watan Sha'aban na shekara ta ukun dai Annabi ya auri Nana Hafsa ma'abociyar ibada da kamala yar gidan bawan Allah Umar bn Khaddab. Bayan rasuwar salihin mijinta Kunais bn Huzafa.
★ A watan Ramadan na shekarar dai Annabi ya auri Zainab bnt Khuzaima bayan wata biyu ko uku da auren saitayi tafiya. Ma'ana ta koma ga mahaliccinta.
★ A tsakiyar watan Shawwal na shekarar dai wato ta uku bayan hijira yakin Uhudu ya afku wanda shine muke tsaka da kawo shi.
Idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a inda rundunonin biyu suka bazamo ga junansu kowacce runduna tana shaukin haduwa da yar uwarta. Su kafirai sun kudiri daukar fansar abinda akai musu a badar kamar yadda musulmai kuma suke kwadayin shahada don komawa ga rahuwar da babu damuwa balle bakin ciki a ciki.
Rundunar ta hadu aka wanzu ana kai sara da suka, karar haduwar makamai ta yawaita sautin jifan masu da wucewar kibbau ya rinka kaikawo.
A can gefe kuma ga mahaya doki daga kafirai suna neman su kewayowa musulmai ta baya, amma maharban da Annabi ya ajiye akan dutse yace kada su motsa sun hanasu sakat.
Kafirai da dama sun shirya kashe Hamza saboda fitattun cikinsu daya kashe a yakin Badr, don haka sai suka rinka bijiro masa amma babu wanda ke iya wanzuwa a gabansa face Hamza (R.A) ya turashi garin da ba'a dawowa.
A can gefe kuwa Wahshi bawan Jubair bn Mud'im yana ankare da sahabi Hamza, shi Jubair Hamza ne ya kashe masa kawunsa Tu'ayma. Don haka ya sanya wahshi ya daukar masa fansa. Don haka Wahshi saiya rinka kokarin saita Hamza da mashinsa don jefe shi.
Gwarzon sadauki Hamza yana yaki don daukaka kalmar Allah sai kawai Wahshi ya jefo masa wannan mashi... Mutane anata faman kai sara da suka da mangara haka wannan mashin ya taho yana keta iska da matsanancin gudu da kuma karfi... bai tsaya a ko'ina ba sai a gangar jikin Sayyadi Hamza ya soke shi a kasan cikinsa, har saida wannan mashi ya bulla ta bayansa.
Sautin matan mushrikai da suketa wake-wake ya cika wajen, yayinda shi kuma Annabi duk lokacin da yaji baitinsu saiya kai kukansa zuwa ga Allah.
Kamar yadda Allah yayiwa musulmai alkawarin nasara nan take sai nasara ta samu. Domin duk marika tutar kafirai saida aka kashe su. Kafirai suka juya suna neman tserewa musulmai da suke filin daga suka bisu suna kama su gami da kwasar ganima.
Su kuwa wayannan maharba da sukaga kafirai sun tsere, sai sukayi tsammanin yaki yazo karshe kuma suka sakko domin suma a tattara ganima da su. Wanda Annabi ya wakilta a matsayin shugabansu saiya tsoratar da su, yana mai tunatar dasu abinda Annabi ya Umarcesu da shi. Amma sai suka bijire suka sauka.
Daga can bangaren kafirai kuwa Khalid Bn Walid tare da zunzurutun mayaka mahaya dawakai dama abinda suke jira kenan, wato saukowar wayannan maharba. Don haka da sukaga maharban kan dutsen suna sakkowa sai su kuma suka zagayo ta baya a sukwane suna sara da sukar sahabbai take guri ya hargitse sahabbai suka rude ya zamana har sashensu ya rinka dukan sashe. Aka saka musulmi a tsakiya. Tabbas sunga tashin hankali.
Jama'a wayannan fa sahabbai kenan, duk imaninsu, duk soyayyar da Annabi... Amma da suka saba masa sai Allah ya jarrabesu ta hanyar sallada musu abokan ganarsu akansu. Ashe abinda ke faruwa ga musulmj yanzu na kaskanchi da zubar da jininsu yanada alaka da bijirewa umarnin Annabi da muke kenan?
Yi nazari mana.
Sahun sahabbai ya cakude, suka sauka daga tsarin da Annabi ya basu a yakin gaba daya. Saki zubar da ganimar da suka diba, suka saki bayin da suka kama, suka koma neman tsira da rayuwarsu.
Aka kashe Mus'ab Bn Umair wanda shine ke dauke da tutar musulmai.
Duk da wannan tashin hankali, musulmai suna iyakar kokarinsu wajen kare kansu da kuma fuskantar kafirai da wata zuciya mara tsoron mutuwa.
Suna cikin wannan yanayi na halin dimuwa sai kuma wani babban tashin hankalin ya danno wanda yafi na baya, sukaji mai kira yana kira cewa an kashe manzon Allah. Nan take hankalin sahabbai ya sake tashi wasu suka fita daga hayyacinsu. Wasu kuwa haka suka tsaya suna yakin suna cewa ko an kashe ma'aiki zasuyi yakin saboda musulunchi, wasunsu kuwa wayanda suke wajen Annabi dama sun san karyace kawai.
Sahabbai da dama babban tashin hankalinsu shine rashin sanin a ina Annabi yake. Su kuwa kafirai sai ya zamana inda Annabi yake tare da jama'ar sahabbai nan suke kai farmaki. Suka jefo wani katon dutse, dutsen ya daki fuskar ma'aiki da matsanancin karfi. Annabi ya fada rami, Aliyu ibn Abi Dalib ya rike hannun Annabi gagam yayinda Dalhatu Bn Ubaidullah ya dagoshi har saida ya tsaya da duga-dugansa. Hakorin Annabi na gaba ya karye, lebensa ya fashe yana zubar da jini. Ya saka hannu yana share jinin dake zubowa daga fuskarsa yana cewa “Tayaya mutanen da sukaiwa Annabinsu rotse zasu rabauta.”
Sai aya ta sauka da take cewa babu ruwan Annabi da wannan al'amari, ko Allah ya azabtar da su kowa yafe musu...
Abu Ubaida a kokarinsa na cire wani karfe daga fuskar Annabi da yasa bakinsa saida hakoransa biyu suka fita.
Abu dujana da yaga yadda kafirai ke ruwan kibbau da jifa da masu da duwatsh ga Annabi sai kawai yazo ya kare Annabi ai kuwa haka bayansa yayi kaca kaca da harbi da raunuka. Sannan yayi shahada.
Sa'ad Bn Abi Wakkas kuwa, yana tare da Annabi. Annabi yana miko basa kibiya yana harbawa Annabi yana fansar da mahaifinsa da mahaifiyarsa gareshi.
Qatada bn Nu'uman kuwa wani duka da akai masa a fuska saida idonsa ya fice, amma Annabi daya mayar masa da idon nan take sai ya koma lafiyayye.
Kafirai suka kara matsa lamba don ganin sun kashe Annabi amma sahabbai suka rinka bada rayuwarsu fansa ga tasa rayuwar.
Dalhatu Bn Ubaidullah hannunsa ya rinka sakawa yana kare Annabi daga harbi ko jifa, har saida hannayensa gaba daya sukai rauni.
Annabi yayi yunkurin hawa dutse amma sai abu ya faskara, saboda ciwoka da yaji, da kuma jini daya zubar. Dalhatu dai shine ya taimaka ya ciccibashi zuwa ga kan dutsen. Wanda anan Annabi yayi sallarsa. Itama sallar sai a zaune yayi.
Anas bn Nadru kawun Anas bn Malik (R.A) ya wanzu yana kashe kafirai. Wani daga cikin sahabbai ya gaya masa hatsarin wajen da yake, amma sai yace shi yana jiyo kamshin Aljannan ne a wannan wajen. Ai kuwa anan ya rasa rayuwarsa. Gawar tasa ma ba'a iya ganeta ba, domin sara ne kusan saba'in, sai wata yar uwarsa ce ta ganeshi da dan yatsansa.
Ziyad bn Aslam su biyar duka Ansarawa haka suka tsare suka hana kafirai isa wajen Annabi ta fuskarsu, haka aka rinka kashesu daya bayan daya. Shima ziyad din a karshe faduwa yayi sakamakon muggan raunuka. Annabi yayi umarni da a kawo masa Ziyad, ya dorashi akan cinyarsa. Ai kuwa akan cinyar Annabi rai yayi halinsa.
Sa'ad Bn Rabī shima da sara sama da guda saba'in a jikinsa amma kafin ya mutu saida ya barwa sahabbai wasiyya cewa su kula da Annabi da lafiyarsa, tabbas basu da wata hujja a wajen Allah idan aka cutar da Annabi alhalin suna numfashi. Yana gama barin wasiyyar ya cika da imani.
Tabbas musulmai sunga tashin hankali mara misaltuwa, basu kuma dawo hayyacinsu ba har saida suka samu yakinin cewa Annabi yana raye. Nan fa farin ciki ya mamayesu har saida suka manta damuwar da suke ciki a filin daga.
Ubayyu Bn Khalaf a wannan yaki ya bijiro don kashe Annabi, Annabi ya bawa sahabbai umarnin a barshi ya karaso, ai kuwa ya bazamo akan dokinsa Annabi yana tsaye. Kwaf daya Annabi yayi masa ya turashi garin da su Abu Jahal suka tafi ranar Badr.
Abu Sufyan kuwa da wutar yaki ta tsaya saiya kirawo musulmi yace dasu shin a cikinku akwai Muhammad? Sai Annabi ya hanasu su bashi amsa.
Abu Sufyan ya sake tambaya shin a cikinku akwai Ibn Abi Quhafa (Abubakar)?
Shiru musulmai basu amsa masa ba.
Sai ya sake kiransu, shin cikinku akwai Umar Ibn Khaddab?
Namma dai kowa yayi shiru don bin Umarnin Annabi Muhammad (S.A.W).
Abu Sufyan sai yayi tunanin sun mutu don haka saiya fadi kalma ta alfahari da nuna isa. A wannan karon sai Umar Bn Khaddab ya kasa jurewa yace "Kai makiyin Allah, wayanda ka kira suna raye...” sannan Umar ya maida masa da bakar magana.
Sai Abu Sufyan yacewa musulmi zaku tarar da kisan wulakanci a cikin mamatanku da aka kashe, bani ne nayi umarni da ita ba, kuma don anyi hakan banji haushi ba.
Daga nan ya kambama ubangijinsu Hubal. Umar ya gwaleshi yace Shine mafi girma da daukaka.
Duk abinda ya fada sai Umar ya bashi amsa.
Me yasa Abu Sufyan ya tambayi Abubakar da Umar (R.A)?
Saboda hatta kafirai a wannan lokaci sun san wayannan suna waziran Annabi, sune mafi girman sahabbansa babu wani wanda ya darasu a daraja.
Ciwukan da Annabi yaji kuwa, Sahabi Aliyu ne da Nana fadima suka wanke masa su, da Nana fadima taga jini yaki tsayawa sai ta kona tabarmar kaba, aka saka tokar a wajen take kuwa jinin ya tsaya. Kaji likita yar gidan likita.
Munyi kokarin takaita yakin uhudu takaitawa mutuka.
An kashe sahabbai kusan saba'in da doriya. Kuma tabbas Annabi yayi bakin ciki mara misaltuwa, musamman ya rasa mafi soyuwar mutane a gareshi a wannan yakin. Sannan Abi sufyan ya bukaci shekara mai kamawa zai dawo filin da akai Badar don sake gwabzawa da Annabi da Sahabbai. Kuma Annabi ya amsa masa.
Sahabbai kuwa da suka bijirewa umarnin Annabi a wannan yaki saboda shubuha ko sharrin shaidan Allah da kansa yace ya yafe musu cikin suratu Ãli Imran aya ta 152.
Allah yayi musu afuwa, tare da cewa akwai wasu mutanen banza da suke ganin cewa abinda Allah yayi ba dai dai bane. Suna kokarin su nuna cewa sunfi Allah sanin yakamata...
Mukam muna neman tsarin Allah daga wannan dabi'a. Muna kuma rokon Allah daya sanya mu cikin wayanda zasu rinka nemawa kansu gafara da kuma wayanda suka gabacemu na daga sahabbai da wayanda suka biyo bayansu da kyautatawa.
Mafi girman darasin da yake a cikin wannan yaki shine sanin illar sabawa umarnin Annabi Muhammad (S.A.W).
Sahabbai wasu halittu ne na musamman wayanda Allah yake amfani dasu don buga mana misali da kuma bamu mafita a cikin al'amuranmu. Saboda su, da kuma cudanyar da sukai da Annabi da kuma irin gudunmuwar da suka bayar, shi yasa zaka iske babu wani abu face addinin musulunchi ya koya mana yadda zamuyi.
Hakanan babu wata dabi'a da kake da ita face a cikin sahabbai sai ka samu mai rin wannan dabi'ar wanda idan kaso zai zamo maka tamkar madubin dubawa. Idan mun samu dama farfasa bayanan a rubutun dana ambata cewar idan akwai tsawon kwana zanyi shi akan yake-yaken Annabi Muhammad (S.A.W).
Zamu dakata anan. Sai kuma a rubutu na gaba.
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.
Comments
Post a Comment