WAIWAYE ADON TAFIYA (21 - 25)
WAIWAYE ADON TAFIYA 21
Tatacciyar sirar ma'aiki...
Kamar yadda muka ambata cewa mutanen madina sunata tururuwa da don su tari Annabin rahama (S.A.W) haka suka kasance tsawon kwanaki. Mun riga munji cewa mafi yawan mutanen madina sun musulunta tun kafin zuwan ma'aiki (S.A.W).
Cikinsu harda wata uwa wadda ta musulunta kuma ta lakkanawa danta musulunchi, ana kiran wannan mata da Gumaisaa'u ko Rumaisaa'u. A wannan fita da ake tarar Annabi harda wannan dan nata dan shekara goma. Haka zai bi tawagar yara (kamar yadda ake fita tawaga-tawaga manya da yara...), wasu kuwa su rinka hawa dogayen gurare don dai su fara gano Annabin rahama...
Kowace rana wannan yaro dan gidan Rumaisa haka yake fita amma haka zai dawo tare da yan uwansa yara yana mai mutukar bakin cikin rashin ganin abinda yake son gani wato Annabin rahama (S.A.W). Idanuwansa suna zubda hawayen rashin dacewa da ganin abin kaunarsa haka zai juyo zuwa gida...
Shi kuwa can Annabin rahama ya yada zango a Quba, Ranar litinin kenan a watan Rabi'ul Auwal. Inda ya zauna akalla kusan kwana goma, ya zauna tare da Bani Amru bn Auf...
Al'amarin wannan uwa kuwa wato Rumaisa'u haka ita da daukacin mutanen madina suka rinka daukin isowar Annabi, kasancewarta uwa ta gari, itace mai kwantarwa da wannan dan nata hankali a duk sanda ya dawo ciki kokawa akan rashin ganin Ma'aiki (S.A.W)...
Anas Ibn Malik shine sunan wannan d'a nata mai albarka.
Wata rana Anas na zaune, yanata tunani da bakin cikin rashin ganin manzon tsira (S.A.W) sai kawai kamar daga sama yaji mai shela yana shelanta cewa ga Annabin rahama yana tafe zuwa madina.
Cikin hanzari Anas da mutanen madina sukayi tururuwa ana rige-rige wajen ganin Annabin rahama (S.A.W).
Mata wayanda suke cikin gida da kananun yara sosai wayanda basa fita nesa da gida kuwa suka rinka hawa bene ko gini mai tsayi suna kallon Annabin rahama cikin taron mutane suna tambaya "wannene a ciki?"
Wasunsu har suna tsammanin sahabi Abubakar shine Annabin domin alamun shekaru sunfi bayyana a gareshi, har saida sukaga yana sanya tufafinsa yana yiwa Annabi inuwa dashi saboda rana sannan suka gane wannan shine Annabin. Wasu kuwa dama sun sanshi a makkah, wasu kuma basu sanshi ba, amma suna ganinsa suke banbanceshi domin siffofinsa mafiya kyawu da tsarki sun fita dabam.
Mutanen madina suka rinka farin ciki, sashensu ya rinka bi kwararo kwararo yana shelanta cewa yau ga rahama ga talikai ya sauka a madina...
A tarihin larabawa, rumawa, farisawa, girkawa da duniya baki dayanta, ba'a taba ganin irin wannan rana ba. Kuma ba za'a taba ganinta ba har a tashi duniya.
Anas cikin murna yake domin yau yaga abinda ya dade yana buri, a zuciyarsa kuwa ji yake inama ace zai kasance tare da wannan Annabi har karshen rayuwarsa... Saidai kash yasan bashi da wannan damar kuma bashi da wannan alfarmar don haka sai tausayin kansa da kansa ya kama shi...
Annabi ya sauka a gidan Abu Ayyubal Ansari. Mutane suka rinka zuwar masa da kyaututtuka da abubuwa kala-kala don nuna soyayyarsu a gareshi.
Ana haka saiga Rumaisa'u mahaifiyar Anas ta zo, ta gaishe da Annabi. A tare da ita akwai danta Anas Bn Malik gashin kansa yana dukan kafadunsa.
Rumaisa'u tace: Babu wani mutum namiji ko mace a mutanen madina, face ya baka wani abu na kyauta... Ni kuma ban samu wani abu da zan maka kyauta da shi ba sai wannan dan nawa, ka rikeshi, yayi maka hidimar duk abinda kake so...
Allahu Akbar.
Annabi cikin raha da fara'a ya juyo ya kalli Anas, ya shafa kansa da hannayensa masu tsarki, daga wannan rana Anas ya zama mai hidimtawa ma'aikin Allah, har zuwa komawarsa ga ubangijinsa.
Ya samu addu'o'i da yawa daga wajen Annabi, saboda irin soyayyar da Annabi yake masa yana kiransa da Unais, ko kuma yace masa "D'ana" yana mai jinginashi izuwa gareshi.
Tabbas Rumaisa'u ta taimakawa musulunchi domin wannan dan nata ya hidimta sosai, kuma yana daga cikin mafiya riyawar sahabbai.
Allah sarki akwai wata magana da yake kafin ya rasu. Yake cewa “Ni ina burin inga Annabi ranar alkiyama, sai ince dashi: Ya ma'aikin Allah, ga wannan dan karamin mai yi maka hidimar Unais.”
Shin wayannan mutane sun cancanci yabo da addu'a ko kuwa sun cancanci kage, sharri da kuma fasikantarwa?
Ya Allah mu masu son sahabbai ne, muna rokonka daka tashe mu tare da su a ranar gobe kiyama.
Zamu dan yada zango anan.
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy
WAIWAYE ADON TAFIYA (22)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)...
Annabi (S.A.W) ya zauna tsawon lokaci a gidan Abu Ayyubal Ansari.
Abu Ayyubal Ansari yayi farin ciki kasancewar Annabi a gidans ya sauka, domin lokacin da Annabi ya shiga madina babu wani gida da yake wucewa face sunyi da linzamin taguwarsa suna masa magiyar ya zauna a tattare dasu amma sai ma'aiki ya basu umarnin su kyale wannan taguwa hakika ita abar umarta ce... A karshe dai gidan Abu Ayyuba shine ya zama inda Annabi zai zauna. Kafin kuma inda taguwar ta zauna ya zamana an gine shi ya zama mazauni da kuma masallacin Ma'aiki (S.A.W).
Abu Ayyuba ya zabarwa Annabi sama a gidansa wato bene yace Annabi ya zauna anan, amma Annabi saiya ki, saboda dan gida shine ya dace sa sama. Amma saboda karamchi na Abu Ayyuba sai yaki yarda ya zauna a saman.
Kasan lokacin da akace mai karamchi zai karrama mafi karamchi, to tabbas mafi karamchin zaiyi duk mai yiyuwa yaga cewa bai toye hakkin mai karramawar ba. Don haka Annabi bai yarda ya karbi saman ba, da dai yaga Abu Ayyuba ya dage sai Annabi yace masa yayi hakuri, abinda yasa yafi son kasan shine saboda masu tururuwar zuwa wajensa...
Wannan kuwa ba sai na gaya mana yadda mutane suke tururuwar zuwa ganin Annabi ba.
Shi kuwa Abu Ayyuba, ji yake kamar yayiwa Allah laifi, don me zai hau bene alhalin Annabi yana kasa? Don me zai taka inda karkashinsa anan Annabi yake?
Abu Ayyuba baya cin abinci, idan suka girka Annabi ne farkon wanda zaici, sannan su kuma suci abinda ya rage, harma rige-rigen cin gurbin da Annabi ya taba suke.
Akwai lokacin da aka samu akasi ruwa ya zubi akan saman inda Abu Ayyuba yake, nan take hankalinsa ya tashi domin baya son ruwan ya ratsa ya zuba jikin Annabi. Haka suka dauko katifarsu ta kwanciya suka rinka tsane rruwan dashi...
Allahu Akbar.
Tabbas babu wani sarki, babu wani mahaluki abin halitta daya samu daidai da kwatankwacin irin gatan da Annabi ya samu daga sahabbansa.
Ana haka a madina kawai sai zazzabi ya rufarwa masulmai da sukai hijira, yau wannan babu lafiya gobe wancan. Amma Allah ya kiyaye Annabi baiyi ba. Abin ya damu Annabi mutuka. Domin yana mutukar son sahabbansa, ya rasa meke masa dadi, don haka saiya roki Allah sauki ga mutanensa, ita kuwa madina ya nema mata albarka, ai kuwa sai Allah ya amsa rokonsa.
A cikin shekara ta farko da yin hijira aka kammala gina masallachin Annabi.
Annabi ya hada yan'uwantaka ta musulunchi tsakanin Muhajirai masu hijira da Ansarawa mutanen madina. Wanda idan mukace zamu zayyano irin soyayya da taimako da take tsakaninsu to da tabbas sai mun tsawaita bayani kuma da sai zukata sun jijjika idanuwa sun zubda hawaye musamman idan muka duba da yadda musulmai suke a wannan zamani... Inama ace rayuwa na da tsayi... Amma da yardar Allah indai akwai tsawon rai muna nan tafe da bayanai akan rayuwar sahabbai daidaiku da kuma a jimlace.
A cikin wannan shekara dai Annabi ya rubuta ko muce ya kulla alaqa da makwabtansa na gefe-gefe da cikin madina musamman yahudawa.
A cikin wannan shekara dai Annabi ya tare da masoyiyarsa kuma uwarmu Nana Aisha. Wadda a karkashin sama (dandaryar kasa) ba'a riski wata mata mai ilminta ba a duniyar musulunchi. Mai daraja, tarbiyya da falala. Allah ka tashe mu da ita ranar Alkiyama. Itace fa wannan wadda daga saman bakwai Allah ya wanketa, kuma itace dai wadda daga saman bakwai mala'iika jibril ya sakko duniya don kawai ya isar mata da gaisuwar Allah. Ba don gudun tsawaitawa ba, aida mun yada zango anan munji tarihin wannan baiwar Allah.
A cikin wannan shekara ne dai aka shar'anta kiran sallah. Akwai wasu ruwayoyin da suke cewa an shar'antashi a makka ko a isra'i amma dukkaninsu basu inganta ba. (Siratun Nabawiyya 63).
Yahudawa kuwa wayanda sune suka rinka yiwa mutanen madina bushara da zuwan Annabi sai bakin ciki da Hassada ta hana su yin imani. Don me shugaban Annabawa bai fito daga cikinsu?
Sai kadan daga cikinsu ne suka musulunta kamar Abdullahi Ibn Salaam. Shima a wannan shekara ta farko y musulunta.
Mutanen madina suna jin dadi, amma kuma ruwa yana musu wahala, domin kuwa rijiyar da ake diban ruwan ta kafirai ce. Kuma musulmai sai sun biya kudi suke diban ruwa. Da wahala tai wahala sai Annabi yayi shela cewa wanene zai siya wannan rijiya a saka masa da Aljanna. Sai wannan namijin kyakkyawan Sahabin nan mai auren yayan Annabi guda biyu lokaci dabam dabam wato Sahabi Usman ya siyeta. Kuma ya mallakawa musulmai ita. Annabi yayi masa bushara da Aljanna.
Nayi rantsuwa da Allah, numfashi guda da Sahabi Usman (R.A) yayi tare da manzon tsira, yafi rayuwar masu tuhumarsa da zaginsa kakaf albarka. Tun daga na farkonsu da na karshensu.
A dai wannan shekara aka sauya sallar azahar da la'asar daga raka'a bibbiyu zuwa raka'a hudu.
A cikin shekara ta farko ne kuma aka halatta jihadi. Sabanin kafin hijira.
Zamu yada zango anan
Sai kuma a rubutu na gaba da yardar Allah!
WAIWAYE ADON TAFIYA (23)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)
Karamchi, wata dabi'a ce muhimmiya a dabi'u wayanda musulunchi ya bukaci mu dabi'antu dasu.
Tuna lokacin da za'ayi hijira, abin hawan da Annabi ya hau na sayyadina Abubakar ne, kuma kyauta ya yardar dashi ga Annabi, amma sai Annabi yaki yarda sai da ya siyi wannan abin hawan saboda neman cikakken ladan hijira da kuma karamchi irin nasa. Ashe kenan Annabi har da shi ake rige-rige wajen aikata alheri tare da cewa yayiwa kowa fintinkau... Don me bazai yi kokarin fin kowa ayyukan alheri ba alhalin shine mafi soyuwar bayi a wajen Allah kamar yadda kuma shine wanda yafi son Allah akan yadda dukkanin bayi suke son Allah?
A halittu kakaf babu mai son Allah irin son da Annabin Rahama yake masa. (S.A.W)
Filin da aka tanada wanda za'a gina gidan Annabi da masallacinsa, filin wasu bayin Allah ne, amma sai suka ba da wannan filin kyauta ga Annabin rahama. Amma sai Annabi yaki karba, sai dai ya siya. Ai kuwa haka akai don siyar filin yayi.
(Muhammad Rasulullah 183)
Sahabbai suka bukaci zasu gina wannan gida, amma shugaban masu karamchi sai yaki barinsu suyi aikin nan su kadai, haka ya shiga cikinsu ake aikin dashi, wani abinma idan ya gagaresu shine yake zuwa sanya hannu a ciki. Kasan karfin nasa ba irin nasu bane. Kuma sai kasancewar ana aikin dashi ya zamar musu wani sabon nishadi. Don me bazasu yi nishadi ba alhalin suna wuni tare ds mafi soyuwar mutane a wajensu?
Ana aikin zuciyar Annabi cike da godiya ga Allah daya taimakeshi da wayannan mutane wayanda sun zabeshi akan iyayensu, yayansu da matansu. Annabi ya furta wasu baitika yana yaba musu tare da nema masu gafara. Hakan kuwa ba karamin faranta musu rai yayi ba, sai suma suka amsa suna masu karawa Annabi kwarin gwiwa. Ana aikin karfi amma duk wanda ka kalla zaka ganshi cikin nishadi mara misaltuwa.
Muhajirun wayanda sukayo hijira daga makkah da mutanen madina Ansar suka dukufa suna wannan aiki babu gajiyawa saidai yan adamtaka ta dan Adam.
Wannan irin karamchi na Ma'aikin Allah shine abinda sahabbai suka koyo tun daga Makkah. Domin lokacin da sukai hijira mutumin madina zai kira mutumin makkah mai hijira, zaice masa inada katuwar gona a guri kaza zan rabata gida biyu in baka rabi, a kasuwa inada rumfa kaza, zan rabata gida biyu da kayan cikinta zan baka rabi, ga matana biyu ka duba kaga wadda tafi kwanta maka, zan saketa ka aureta...
Amma sai mutumin makkah wanda yabar komai nasa a can yayo hijira babu ko sisin kobo yace "Na gode da wannan karamchi, amma ka rike kayanka. Nuna min hanyar kasuwa."
Allahu Akbar. Tabbas wannan soyayya don Allah aka ginata.
Idan har haka yana faruwa tsakaninsu akan suna karkashin tutar Annabi Muhammad (S.A.W) yaya kake tunanin zasu mu'amalanchi shi Annabin rahamar?
Soyayyar da take tsakaninsu tafi soyayyar da take tsakanin shakikai. Ina kuma ace soyayyar ta hadu ga ta jini gata musulunchi? Idan ka gane hakan to saika gane irin son da Ahlul baiti sukewa Annabin rahama.
Bari mu dan kauce kadan don dauko wani misali don fito da soyayyar junan nasu a fili gaban mai karatu...
Bara'u Bn Malik yayan Anas dan Malik ne, wanda muka ambaci mahaifiyarsa ta damka shi a hannun Annabi don yiwa Annabi hidima.
Shi Bara'u tsigi-tsila ne, wato baida kiba, amma kuma jarumtarsa abar mamaki ce, domin komai yawan kafirai a filin daga yana iya dirar musu kuma yayi galaba a kansu.
Bayan komawar Annabi ga mahaliccinsa akwai wani yaki da akai, da wani babban birnin kafirai da ake kira Tustar karkashin daular Farisa. Akai gumurzu iya gumurzu da kafirai sukaga za'a ci karfinsu sai suka koma cikin biranansu, suka rinka harbo wasu kugiyoyi na wuta, idan kugiyar ta caki mutum saita daukeshi ta cillashi wajensu kodai a mace ko kuma a raye. Karafunan kugiyar kuwa sunyi jajur saboda azabar wutar dake jikinsu...
Ana cikin wannan yanayi na tashin hankali sai wata kugiya ta cakumo Anas bn malik tayi sama dashi. Cikin tsananin zafin nama Bara'u Bn Malik yayi tsalle sama yana keta iska ya damko wannan kugiyar yana kici-kicin din cireta daga jikin dan'uwansa Anas Bn Malik. Saboda dimuwa da soyayya ya manta da zafin wutar, alhalin gashi tana kona masa fatarsa, namansa da jinin jikinsa.
Wayancan kafirai suka rinka kokarin sarrafa wannan na'ura don ta kawo musu abinda ta sakalo amma sai abu ya gagara, yadda kasan suna kokarin jan katon dutse, kai kuwa ina zasu iya ja, alhalin sadaukin musulunchi ne ya riketa. Ba karfinsa bane, tsananin karfin soyayya ne da kuma karfin musulunchi wanda ya cakudu da tarbiyya muhammadiyya wadda ita kuma take tabbatar da jarumtakar zuciya da karfin zuciya... Haka Bara'u yayita kokarin cire wannan kugiyar, ai kuwa bai barta ba saida ya fitar da dan'uwansa. Amma fa babu sauran tsoka da ta rage a hannunsa sai dai kashi kawai, domin tsokar ta kone kurmus.
A wannan yaki kuma shi Bara'un yayi shahada.
Ya kake ganin irin wannan soyayyar?
To soyayyar musulunchi da ke tsakanin sahabbai dai dai take da wannan ko kuma kace gaba take da wannan ma...
Inama dai ace akwai wadataccen lokaci a wannan rayuwa tabbas da zanso inyi rubutu akan rayuwar daidaikun sahabbai masu cike da izna da darussa.
Allah ya bamu tsawon rai mai amfani, idan kuma komawarmu gareshi tafi zame mana alheri. To Allah ya karbi rayukanmu yana mai yarda da mu da kuma karramamu a fadarsa. Ameen
Rahama ga talikai suna ne, siffa ce, kuma take ne na Annabi muhammad (S.A.W). Don haka kafin zuwan sa Madina akwai adawa tsakanin wasu kabilu, amma zuwansa sai Allah ya hada kawunansu. Adawar ta yaye, rashin gaskiya ya janye, ta'addanci ya yanke...
A mutanen madina akwai wayanda suke da girma da mukamai, don haka zuwan Annabi bai musu dadi ba, domin dukkanin girma an dauka an bashi. Cikinsu, kamar Abdullahi bn Ubayyu bn Salul yana daf da zama sarkin Madina sai hijirar Annabi (S.A.W) ta afku wanda hakan ya rusa masa shirinsa, don haka saiya kullaci Annabi da sahabbai. Amma tunda madina karbabbiya ce a wajen musulmai sai yabar mummunan kudirinsa na kiyayya a zuciyarsa. Harma wani lokacin yakan tashi a masallacin Annabi yayi jawabai masu nuna tsantsar imani.
Allah sarki Annabi da Sahabbai, sun rabu da makiyan fili sun kuma fado cikin tarkon makiyan boye. Na filin ma kuma suna daga gefe bawai mantawa sukai da sha'anin musulmai ba.
Yahudawa mutane ne masu wayo, don haka da su kaga yadda Annabin rahama ya samu karbuwa, sai bakin ciki ya lullubesu, kamar yadda hassada ta hanasu yin imani da shi. Harma suka rinka fito da kiyayyarsu a fili.
Can a makkah kuwa, duk dukiyar da sahabbai suka bari kafirai sun dirar mata, indai ba wai ta wanda yake da karfin nasaba a cikinsu da tsayayyun yan'uwa ba.
Yahudawa suna tsaka da nuna adawarsu ga Annabi sai kawai sukaji labarin musuluntar Abdullahi Bn Salaam, wanda shi kuma babban malaminsu ne. Abin ya mutukar dugunzuma su, sai suka sake jin wasu masanan a cikinsu sun kara musulunta. Take fa kiyayyar su da Manzon tsira ta kara yawaita. Abu kamar wasa sai sukaga adadin masu musuluntar ya doshi arba'in a cikinsu.
Sai kuma suka shiga yin kage da sharri. Harma da sukaje makkah kafiran makkah suka tambayesu me zasu ce dangane da Addinin Annabi Muhammad (S.A.W), sai sukace ai bautar gumakan da kuke ma tafi addininsa. Suka boye ilmin da ke cikin Attaura kawai don hassada da kiyayya.
Dr. Israel Walphenson a cikin littafinsa Yahud fi bala-il-Arab p.142 ya nuna cewa wannan amsa da yahudawa suka bayar ba musulmi kadai ba, duk wanda ya yarda da Allah tayi masa ciwo...
Zamu yada zango anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.
WAIWAYE ADON TAFIYA (24)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W).
Idan aka ajiye turaren wuta a cikin daki ba zaka ji kamshinsa ba saika matsa kusa dashi, wani turaren wutar ma saika kaishi daf da hancinka sannan zakaji kamshinsa. Mata zasu fimu gane wannan misali. Amma idan aka kunna masa wuta, to tabbas zai mamaye ko ina a ilahirin dakin komai fadin dakin kuwa... To wannan shine misalin rayuwa, sauda dama mutum baya daukaka sai masu hassadarsa da adawa dashi sun fara muzguna masa da kuma yi masa kage. Da sun fara sai kaga maimakon mutum ya samu ci baya sai ci gaba ya biyo baya. Wannan muna maganar wanda ke kan gaskiya ne.
Don haka takurar kuraishawa da kuma kafiran Makkah babu abinda take karawa Annabi sai shuhura. Ko zaka iya gane cewa lokacin da yake makkah da suke gayawa baki cewa kada su saurareshi meke faruwa?
Idan baka gano ba bari na haska mana wata hikima boyayyiya, hikimar kuwa itace; duk sanda suka tsoratar da wani bako akan Annabin rahama to sai tunanin Annabin rahamar ya shiga zuciyarsa. Wanda wasu sahabban dalilin wannan tsoratarwa da akai musu yasa suka musulunta. Ko kuma muce ta zamo silar musuluntarsu.
★ ______ ★
Har a wannan lokaci Annabi da Sahabbai suna fuskantar Jerusalem ne idan sun tashi ibada, wanda a can Masjidul Aqsa yake. Tare da cewa Annabi Muhammad yafi son Ka'aba kamar yadda wasu daga cikin sahabbai suma suke son ka'aba fiye da wannan alkibla da suke fuskanta. Sai dai su sahabbai al'amarinsu shine “Mun ji. Mun bi”. Basa sabawa Allah da Manzonsa.
Bayan shekara daya da wata hudu da Hijira sai aka sauya wannan alkibla zuwa fuskantar Ka'aba. Annabi da sahabbai sunyi farin ciki. Alkiblarsu ta bambanta data Yahudawa.
Su kuwa yahudawa sai suka kara tabbatar da cewa tofa Allah ya kamata su san nayi, domin suna nan zaune zasu rasa abokantakar dake tsakaninsu da sauran larabawa. Domin sunsan tabbas wannan addini na gaskiya zai mamaye yankin larabawan. Don haka sai suka fara shirin murkushe addinin tun kafin yayi karfin da zai gagaresu. Don haka sai cutarwarsu da muzgunawarsu ta fito fili...
Akwai wata kissa da ake rawaitowa cewa akwai wanda a cikin yahudawan har shara suke zuwa su zubar a gidan Annabi muhammad, amma sai Annabi yazo ya kwashe yaje ya zubar... Wannan kissar bata da inganchi. Domin madina mun sani mutanenta mafiya yawa sunyi imani da Annabi Muhammad, don haka koshi Annabi Muhammad bai dauki mataki ba, mu tuna akwai sahabbai masu zafi irinsu Hamza, Umar, Aliyu, Bara'u da sauransu wayanda ba zasu laminta ba, hakanan masu sanyin ma irinsu Abubakar da Usman imaninsu ba zai bari su bar wani dakiki ya rinka zuba shara a gidan Annabi ba, alhalin sunada iko... An masa kwatankwacin haka a makkah ko ma abinda yafi haka amma a wannan lokaci basu da karfi shiyasa. Allah ne mafi sani.
Musulun addinine mai izza wanda bai yarda da wulakanta mabiyansa ba. Don me musulunchi zai yarda da wulakanchi alhalin cikin sunayen mai addinin harda Al'azizu? Akwai bambanchi tsakanin kawar da kai da kuma kaskanchi. Kamar yadda akwai bambanchi tsakanin tsoro da kuma hakuri.
To musulmi yana da kawar da kai da kuma hakuri. Amma bashi da tsoro da kaskanchi.
Shiyasa wani khalifa daga khalifofin musulunchi aka zo masa da labarin cewa ga wata baiwa can musulma a wata kasa wani sarki zai wulakantata. Wannan khalifa yasa aka tura masa da sako cewa kada ya sake ya wulakanta musulmar baiwar nan, idan kuwa yaki to yana sanar dashi cewa zai taso runduna zuwaga wannan sarkin, rundunarda farkonta yana can yana yakar sarkin karshenta kuma yana tafe daga birnin musulmai... Ya fadi hakan don nuna yawan rundunar.
Kamar yadda muka sani an umarchi musulmai da cewa su kame hannayensu akan masu cutar da su kuma su bautawa Allah, don haka basa fada da kowa duk da irin wannan takura da muzgunawa da suke fuskanta. Bayan anyi umarni da yin jihadi ne sai Annabi ya tashi wasu sahabbai tsiraru su takwas duk daga cikin masu hijira. Karkashin jagoranchin Abdullahi Bn Jahsh hakan kuwa cikin watan Rajab ne shekara biyu bayan Hijira. Saiya bashi letter yace dashi kada ya buda har sai yayi tafiyar kwana biyu. Sannan yabi abinda yake cikin takardar, sannan kada ya takurawa wani daga cikin dakarun cewa saiyayi masa biyayya. Wanda bazai iya ba, ya dawo.
Haka akai kuwa, suka tafi cikin zafin rana ga sahara, har saida sukai tafiyar kwana biyu sannan Abdullahi Bn Jahsh ya dauko takardar nan ya bude sai yaga Annabi yana umartarsu da zuwa wani waje tsakanin Makkah da Da'if. su kafa tantinsu su kuma yada zango a wajen, su rinka kawo rahoto akan kuraishawa. Sannan Abdullahi Bn Jahsh ya karantawa abokan tafiyarsa abinda ke cikin takardar sannan ya gaya musu cewar Annabi yace kada a takurawa wani a cikinsu. Da jin haka sai dukkaninsu suka ce sun ji kuma sun bi umarnin Annabi. Don haka sai suka tafi inda aka umarcesu din.
Suka zauna suna karantar zirga zirga ai kuwa saiga wata tawagar kuraishawa sunzo wucewa, cikinsu harda Amru bn Alhadramiy. Da wannan tawagar kuraishawa suka gansu, sai suka tsorata don haka sai suka fara shirin sauya hanya. Amma sai suka hango Ukasha sahabi daga yan aiken da Annabi ya tura, yasha kwalkwal kan nan sai sheki yake. Sai su kace au ashe masu aikin hajji ne. Don haka sai suka fasa chanja hanyar suka taho. Hakan y afku a ranar karshe ta watan Rajab.
Waqid bn Abdullah Attamimi shine mutum na farko daya fara harba mashi a musulmai, mashin ya tafi yana keta iska ya nufi inda tawagar kuraishawa take, ai kuwa nan take wannan mashi ya samu Amru bnl Hadrami kuma nan take ya mutu. Abdullahi Bn Jahsh suka kama mutum biyu a matsayin fursuna. Suka kama hanyar komawa madina da su. Bayan nan kuma sun debi ganima daga dukiyar kuraishawa. Domin suma da sukai hijira ai dukiyarsu wawusarta kuraishawan sukai.
Abdullahi bn Jahsh suka rinka murna suka taho wajen Annabi Muhammad da suka zo yaga abinda suka aikata kuma yaji, sai Annabi yace musu “Ni ban umarceku da kuyi yaki a wata mai alfarma ba, kuma ban umarceku da ku kwace musu dukiyarsu ko ku kama fursunoni ba.”
Kuma Annabi yaki yarda ya karbi komai daga abinda suka zo dashi.
Yan aiken duk suka tsargu suka rinka jin haushin kansu, me yasa basu tsaya a iyakar umarnin Annabi ba. Don haka suka nemi gafarar Allah sannan suka rinka bin sahabbai suna neman su sanya baki ko Annabi zai yafe musu laifin da sukai na sabawa umarninsa...
Su kuwa kafiran kuraishawa sai suka samu bakin magana, dama mai neman kashi ne aka jefeshi da kashin awaki. Suka rinka yadawa cewa Annabi Muhammad ya halatta yaki a cikin wata mai alfarma.
Allah da kansa ya basu amsa a suratul Bakara ayata 183 - 185. Inda Allah ya nuna kwarai hakan laifi ne, saidai laifukan da su kafiran makkah suke shirka, kafirci, fitar da mutane daga gari mai alfarma da sauransu yafi muni a wajen Allah.
(Muhammad Rasulullah 194-197)
(Zad Alma'ad (english) vol 1 p. 341)
Zamu huta anan, sai kuma a rubutu na gaba.
WAIWAYE ADON TAFIYA 25
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)
Kada muyi nisa da yawa, yana da kyau mu ambatawa masu karatu cewa a shekara ta biyun nan dai aka wajabta azumi da kuma shar'anta zakkar fidda kai, sannan a wannan shekarai dai aka fara sallar idi karama, saidai kafin ita akwai wani muhimmin al'amari daya faru wanda zamu ambaceshi da yardar Allah.
Kafin aiken da Annabi yayiwa su Abdullahi bn jahash akwai yakin daya fita da kansa. Wato yakin Abuwa'i ko kuma yakin Waddan. Ya fita don tarar ayarin kuraishawa, amma ba'a gamu ba. Saboda kafirai sun wuce da gaggawa.
Bayan wannan akwai aiken da Annabi ya yiyyi amma shima ba'a haduwa sai akaita sabani. Don haka ne a lokacin da Annabi yayi niyyar zai tura su Abdullahi Bn Jahash sai ya boye abin wanda hatta su yan aiken ba'a basu damar budawa ba sai sunyi tafiya mai nisa. A karkashin wannan saimu gane cewa Annabi bawai rayuwa yake da ka ba. Yana rayuwa ne yana daukar darussa da kuma karantar wajen da yake rayuwa a ciki da kuma mutanen da yake rayuwa dasu. Tunda sabanin da ake na haduwa da kafirai akwai yiyuwar suna samun labarin fitar Ma'aiki (S.A.W) ko kuma aikensa. Musamman idan muka duba cewa Yahudawa da munafukai suna kewaye da Annabi a madina, don haka duk abinda suka gani zasu iya kaiwa kafirai rahoto... To da yiyuwar bayan tsoro da rashin aminchi da yasa kafirai suke wuce madina da gaggawa akwai munafuncin da ake kai musu akan abinda Annabi ya shirya akansu. Saidai wannan hasashe nane, ban kuma riski wanda yayi irinsa ba a littafan dana leka na wajena. sai dai kamar a yakin badar da wasu yakunan zaka iske akwai ruwayoyi da suka nuna munafukai sun fitar da wani sirri... Nan dinma na bayyana cewa babu maganar a littafan da nake dasu ne don bayyana amanar ilmi. Domin shi rubutu idan akace na addini ne to dole sai an samarwa komai madogara...
Abin lura na gaba shine an fara shar'anta zakkar fid da kai gabanin zakka ta farilla wadda tana cikin rukunan musulunchi.
Hakanan a cikin musulmai na farko farko da suka musulunta a madina akwai wani tsoho mai suna Kulthum Bn Hidm (Siratun Nabawiyya).
Haka nan akwai Usman ibn Maz'un (Nurul Yakin)
Duk da sahabbai sun bar Makkah, amma kafiran Makkah sunata turo musu da sakonni cewa zasu zo har makkah din suyi maganinsu.
Sahabbai suka zama babu sukuni, basa bacci da daddare sai suzo suyita gadin gidan Annabi, idan wasu basa nan zaka tarar da wasu. Basa jin wani bakon motsi ko kara face sun fito suna duba lafiyar Annabin rahama. Wani lokacin idan akaji wata kara suka fito donsu duba lafiyar manzon Allah (S.A.W) sai su tarar shima ya fito don duba lafiyarsu... Duba wata soyayya don Allah, kowannensu ji yake shine mafi cancanta daya kula da dan'uwansa. Basu daina zuwa tsaron gidan Annabi ba har saida Allah ya sakko da aya wadda take nuna tabbas Allah ya kiyayeshi daga sharrin mutane.
.والله يعصمك من الناس..
Bayan saukarta Annabi ya fito garesu yana farin ciki saboda baya son abinda zai takurawa sahabbansa, ya biya musu ayar sannan yace dasu kowa ya tafi suma su rinka hutawa. Hadisin na nan cikin Sunan Tirmidhi daga Nana Aisha.
Ka tuna irin yadda wannan jibgegen Sahabin Safina yake, baya bacci da daddare saidai yayita kewaye gidan Annabi. Shi da kansa yake cewa idan na tsaya a gaban gidan sai inji kamar abokan gaba ta baya zasu fito, hakanan idan na tsaya a baya sai inji kamar ta gaba za'a bullo, don haka sai inyita zarya...
Ana cikin wannan yanayi kawai sai labari ya iske manzon Allah cewa akwai wata tawagar kafiran kuraishawa data tafi kasuwanchi, harma sun dauko hanyar dawowa daga Syria. Kuma suna karkashin jagoranchin Abu sufyan. Wanda yana daya daga cikin wayanda sukafi muzgunawa game da matsa lamba ga musulmai a Makkah.
Munji irin yadda kafirai suke da burin zuwa har makkah suyi fata-fata da sahabbai da Annabi musamman dama sun tasamma kashe Annabi, amma saiya tsere musu.
Muna kuma sane da cewa kafiran nan sune dai wayanda suka kwace mata, ya'ya' da dukiyoyin sahabbai bayan tirsasa musu dayin hijira da sukai...
Muna kuma sane da cewa sune dai wayanda suka hana raunanan sahabbai yin hijira don kawai sunada karfin iko a kansu.
Bamu manta ba dai da cutarwa da sukewa Allah na hadashi da abokan tarayya, da kuma cutarwa da sukewa Annabi da sahabbai.
Kar dai mai karatu ya gafala da cewa; dalilin cin zalin musulmai da sukai har yanzu rainin da sukaiwa musulmai yana nan cikin zukatansu. Duk da dai musulman sun samu karfi ba kamar da ba, amma dai rainin nan yana nan har yanzu cikin zukatan mushrikai, shi kuwa musulmi mai izza ne. Shiyasa kuskure ne kana musulmi kaje wani guri wanda akwai wayanda ba musulmi ba ka kaskantar da kanka kota wacce hanya. Mutukar ba akwai wani dalili mai kwari ba.
Duk na kawo wayannan bayanaine saboda mu san cewa hukuncin da Annabi yayi daidai ne. Tare da cewa nasan masu karatu babu wanda zaiga kamar hukuncin da Annabi ya dauka ba dai dai bane. Saidai ka tuno cewa akwai wasu wayanda suke sukar addinin musulunchi da cewa addinin ta'addanci ne... Mun kawo hakan don kada shubuharsu ta rudu mai karatu. Wanda akwai bayani da zamuyi na rushe dukkan shubuhohinsu ko a kusa ko a nesa.
★
Annabi Muhammad (S.A.W) da yaji labarin wannan ayari na kafirai dauke da dukiya mai yawa, sai yayiwa sahabbai umarni da su kasance cikin shiri don tarar wannan ayari na kafiran Makkah. Kamar yadda aka saba, sai labari caraf ya jewa Abu Sufyan don haka ya tura yan aiken gaggawa makkah yana sanar dasu abinda ke faruwa. Su kuwa da jin haka sai suka fito kwansu da kwarkwatarsu don kare dukiyoyinsu da kuma fatattaka musulmai don kece raini. Don haka babu wani namiji mai jini a jika da suka barshi ba tare da sun fito da shi ba. Suka hada gagarumar runduna.
Shi kuwa Annabi ba da shirin yaki ya fito ba.
Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.
Comments
Post a Comment