KASATA NIGERIA

Shekaru lambobi ne kawai, aikin da akai a cikinsu shi yake mayar da shekarun su zama ababen sha'awa ko ababen kyamata... 
Ko kana iya tuno wata shekara da wani abin burgewa ko sha'awa ya faru? 
Idan ka tuno me kake ji?

Hakanan ko kana iya tuno wani lokaci da kayi wani abin kunya, abin kyamata ko haushi?
Idan ka tuno me kake ji?

Wannan kadai ya isa ya tabbatar maka da cewa shekaru, watanni da kwanaki lambobi ne kawai, kuma aikin da aka aiwatar cikin wayannan lambobi shine abin dubawa ba yawan lambobin ba.

Wani lokacin zai iya zama abin kunya ace ga tarin shekaru amma babu wani abin amfani a cikinsu, abin kunyar yana karuwa idan akace bayan shekarun akwai damammaki na amfanar shekarun amma ba'ai amfani da wayannan damammakin ba.


Kasata Nigeria!
Alfarma ta sanya ma'aikatan da zasu cicciba kasar zuwa ga tudun tsira mafi yawansu nakasassu ne, domin ba nagarta ake dubawa ba, alfarma ake dubawa.

Cin hanci da rashawa sun saka ayyukan alheri sunki aiwatuwa a wannan kasar, yayinda komai munin aikin sharri da yan kudi yan kadan za'a aiwatar dashi cikin ruwan sanyi.

Jahilci ya auri talauci don haka sai suketa haifar ta'addanchi, mugunta, keta, barna, fyade da sauran ayyukan kazanta.

Rashin wadatar zuci da rashin tausayi sai suka auri juna suketa haifar da zalunchi, danniya, murdiya da sauran ayyukan zalunchi.

Rashin tsafta ya kyallaro ido ya hango halin ko in kula da muke dashi a fannin kula da lafiyarmu don haka sai sukai aure, inda nan take sukaita haifar cututtuka, gurbatacciyar iska, ruwa, gurbataccen muhalli da sauran abubuwa masu kawo barazana ga lafiya.

Kasar tun tana karamarta wasu sukai kokari suka raineta, kafin takai ga girma sukai mata fyade mafi muni, bayan ta girma suka damka ta a hannun manyan yayanta, wayanda su kuma sukaita kokari gwargwadon nasu ikon tare da cewa sun gaza ta wata fuskar... Amma maimakom na bayansu su gyara sai suka rufe ido sukai watsi da kasar suka dira kan kadarorinta...

Nigeria Kasata!
Muna sonki, wasu abubuwa da suke faruwa a cikinki yasa wasu suke jin kamar basa sonki, suke jin cewa suna cikinki ne saboda kaddara... Ko banza mu dai muna sonki kuma zamu bada lokutanmu don amfanuwarki, zamu zubda basirarmu don samuwar cigabanki, zamu bada sadaukar da jin dadinmu don samuwar naki jin dadin, zamu shayar da jinanenmu gareki mu bada su fansa ba don tutarmu taci gaba da kadawa ba kawai, harma don a cigaba da ganin girman tutar a sassan duniya baki daya.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.