WAIWAYE ADON TAFIYA. (6 - 10)

WAIWAYE ADON TAFIYA 6
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Masoyi (S.A.W) tun daga yarintarsa ya taso da dabi'u mafi kyawu, dubi yadda muka bada labari  yadda kwanakin jahiliyya suke, amma sai Allah ya bawa Annabi muhammad kariya daga dukkanin wasu halaye ababen kyamata. 

Da ace a yarintar Annabi an sameshi da wani laifi, kamar karya, rashin girmama na gaba, tsananin son mulki da sauran halaye to da abokan adawarsa sun tada jijiyoyin wuya akan abinda aka sameshi dashi mara kyau. Amma sai Allah ya tsarkakeshi tsarkakewa.

Mafi girman abinda larabawa suka himmatu akai a wayannan kwanaki akwai caca, shan giya da kuma bautar gumaka, amma Annabi bai taba yin koda daya daga cikin wannan ba. Domin ya haramtawa kansa shan giya, caca, bautar gumaka ko kuma cin abin yankan da aka yankashi ga gunki. Tun a yarintarsa ya tsani gumaka kamar yadda ya tsani waka da alfasha...
(Nurul Yaqeen 23) 

Har saida mutane suke kiransa da sunaye na girmamawa da karramawa, cikin wayannan sunaye akwai Al'amin. Suna kiransa da wannan suna saboda dabi'unsa na daga tausayi, hakuri, godiya, yabawa, adalchi, kyautayi, gudun duniya, gudun abin hannun mutane, dogaro da kai, afuwa, kawar da kai, jarumta da kuma uwa uba kunya.
(Ibn Hisham vol. 1, 183)
(Muhammad Rasulullah 98)
(Nurul Yaqeen 22)

Tun kafin zuwan Ma'aiki (S.A.W) anyi bushara da zuwansa a littafai kamar Attaura ta Musa da injila ta Isah (A.S). Idan jayayya ta gifta tsakanin mutanen madina da yahudawa, sai yahudawa su rinka gaya musu cewa; ai lokacin zuwan Annabin karshe ya kusa, Annabin da zamu hade kai dashi mu yakeku kamar yadda aka hallakar da Adawa (Aãd)... Suna fadar hakan domin sun karanta kuma sunsan da zuwansa a littafansu, amma lokacin da Annabin yazo sai hassada ta hana da yawansu yin imani su kuma da dama daga mutanen Madina sukai imani... 
(Nurul Yaqeen 28)

A lokacin da Annabi yakai shekara 14 ko 15, sai akai wani yaki tsakanin Quraishawa da kabilar Qais, an kira yakin da suna Harbul-Fijar. A wannan yaki Annabi ya kasance yana daukar masun da Qais suka jefo, ya damkawa yan'uwansa kuraishawa. Duk da karancin shekarunsa amma haka ya aiwatar da wannan bajintar (S.A.W).

Hakanan Annabi yana kiwo a wannan lokaci, dama kuma sunnar Annabawa ne, kowane Annabi sai yayi kiwo. Domin samun gogewa wajen jagoranchi, da kuma kula. Domin kamar yadda makiyayi idonsa yake kan kowace dabba a cikin dabbobin da yake kiwo haka kowane Annabi idonsa yana kan kowanne lungu da sako na al'ummarsa.
(Saheeh Bukhari)
(Ibn Hisham)
(Muhammad Rasulullah 99)

Kamar yadda muka sani, larabawa abinda zai sakasu yakar junansu baida yawa, domin sukanyi shekara da shekaru suna yaki akan rakumi a wannan lokaci. To sai wani babban abu ya taso na gyaran ka'aba, dukkanin larabawa suka himmayu wajen wannan aiki, wasu suka himmatu wajen aikin karfi, wasu kuwa abinci suke samarwa, yayinda wasu suke kawo ruwa... Kowace kabila tana jin wannan aikin ita tafi cancanta dashi domin Dakin Allah ake gyarawa, kuma dukkaninsu sukan bugi kirji suce su bayinsa ne... Hayaniya ta yawaita, fushi ya mamaye zukatan kowace kabila, mutanen da suke yakar juna akan dabba balle kuma yanzu da ake magana akan dakin Allah... Don haka mafi girman yaki gab yake da barkewa... Dalilin hayaniyar kuma shine akan wacce kabilace zata dora dutsen Hajarul-Aswad a bigirensa... Wani mai hikima a karshe yace duk wanda ya fara shigowa ta waje kaza to shi zai musu hukunchi ai kuwa dukkaninsu suka yarda da hakan, ai kuwa sai Annabin rahama ya shigo. Da shigowarsa sai kowace kabila ta cika farin ciki musamman sunsan Annabi shine mafi adalchinsu, sannan Annabi yanada wani hali wanda saboda mutuncinsa kowane mutum yanajin cewa Annabi yafi sonsa akan kowa... Don haka kowane mutum a cikin wayannan kabilu murna yake saboda wannan dalilan guda biyu. 
1. Sun yarda Annabi shine mafi adalchin su.
2. Kowanne yana jin shi mai alfarma ne a wajen Annabi domin yafi sonsa akan sauran.
(Abu Umar Alkanawy)

Shi kuwa Annabi da aka bijiro masa da maganar sai ya shimfida mayafinsa a kasa yace kowace kabila ta wakilta wakilinta ya kama gefen wannan mayafi nasa mai albarka, su dagoshi sama, ai kuwa cikin nishadi aka hadu aka daga wannan dutse sama shi kuma Annabi ya ciccibeshi ya azashi a inda ya dace...

Maimakon yaki ya afku tsakaninsu, sai Manzon tsira ya samar musu da hukuncin da zai sanya walwala, rahama da soyayyar junansu a tsakaninsu.

Tabbas Annabi rahama ne ga talikai.

Zamu huta anan kafin muci gaba!
Shin wannan Annabi (S.A.W) yayi kama da wanda ya kawo ta'addanchi?
Shin wannan soyayya dake tsakaninsa da mutanensa zata wanzu har karshen rayuwarsa?
Zamu ji a rubuce-rubucenmu na gaba!

WAIWAYE ADON TAFIYA (7)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Hilful fudul yana daya daga cikin tarurrukan da suka samu albarkar halartar masoyi (S.A.W). 

Wannan taro an yishi a gidan Abdullahi Bn Jda'aan attaimiy. Wata guda bayan afkuwar yakin harbul-fijar wanda muka ambata a rubutun daya gabata. 

Dalilin hilful fudul kuwa shine wani mutum yazo daga zabid, wani sashe na kasar Yemen. Ya siyar da kayansa ga daya daga cikin shuwagabannin kuraishawa, mai suna Al'as Ibn Wa'il. Sai Al'as ya hana wannan dan kasuwa bako daga yemen kudin kayansa, wannan bako ya nemi taimakon larabawa amma sai sukaki sauraronsa, suka hantareshi... Bayan daddaga maganar da yayi da bayyanata a fili, sai manyan kuraishawa suka zauna akan wannan matsala a gidan Abdullahi ibn jad'an. A karshe suka fitar da tsarin cewa zasu tabbatar da adalchi... Sannan duk wani mara karfi da aka zalunta za'a mayar masa da kayansa (Ba cuta babu cutarwa), sannan suka tirsasa Al'as ibn Wa'il ya mayarwa da wannan mutumin yemen kayansa. Annabi ya halarchi zaman nan dukda karancin shekarunsa a wannan lokaci, kuma ya taka muhimmiyar tsaiwa a taron. 
(Fiqhus Sirah 72)
(Muhammad Rasulullah)

Kamar yadda muka sani shekaru kamar shafuka suke, to haka kwanakin Annabi sukaita tafiya, koda yaushe nagartarsa tana kara fitowa fili, kyawun halitta, farin jini, kwarjini, da iya zama da mutanensa suna kara haskawa duniya cewa tabbas wannan akwai abubuwan mamaki a tattare dashi. Shi ba mala'ika ba amma babu wani lokaci na wasa a tsarin rayuwarsa, ko sau daya ba'a taba samunsa da wasa ko wani hali na rashin daraja ba. 

Mun sani, muna sane, muna kuma kan hanyar sanin cewa Annabta tana jiran wannan Annabi mai girma, alhalin shi a kankin kansa a wannan karon baisan meke tunkaroshi ba, don haka ne Allah yake bada labari a cikin suratul shura ayata 52..

_Kuma kamar hakane muka saukar maka da ruhi daga al'amarinmu (wahayi/Qur'ani), baka kasance kasan menene littafi ba ko kuma menene imani..._

Da kuma fadinsa madaukakin sarki...
وما كنت ترجوا أن يلقى إليك الكتاب
Ayar tana nuna cewa Annabi bai taba burin inama dai ace za'a sakko masa da wani littafi ba (kafin Annabta).   

Kamar yadda muke rayuwa yanzu zaka iske wani tun yana karami yana burin ya samu matsayi ya zama likita, injiniya ko wanin haka. Toshi Annabi babu wannan tunanin game da Annabta a tare dashi. Kawai dai yasan cewa shi bawa ne zababbe daga bayin Allah. Shiyasa lokacin da aka fara saukar masa da wahayi ya shiga damuwa har wani lokacin yake zuwa ya bukaci a lullubeshi... (Zamu zo nan gaba kadan)

Ita Annabta bawai aikin mutum ne yake kawota ba, Allah tun asalin halitta ya rigada ya zabi inda zai ajiye Annabta. Don haka yake cewa Allah yasan inda zai sanya sakonsa (Annabta). Su kuwa sauran darajoji kamar walittaka da sauransu aikin mutum shine yake kaishi wannan mukamin.

Abu na gaba, Allah ya halicci wannan Annabi zababbe abin so bai iya karatu ko rubutu ba.

Anan akwai wata mu'ujiza mai girma, kayi tunani ta yaya mutumin da a yarintarsa bai taba nuna sha'awar mulki ko da'awar Annabta ba lokaci guda bayan cikarsa shekara arba'in zai fara?
Ta yaya wanda bai iya karatu da rubutu ba zaizo da littafin da har a ilmin wannan zamanin yanada ta cewa?
Ta yaya bai iya karatu da rubutu ba zaizo da tsarinda idan aka bishi duniya zata zauna lafiya, kuma an gwada an gani?

Da wasu tambayoyin da yawa ma kuwa.
A karkashin wannan saika gane cewa lallai Allah shine ya aiko Annabi Muhammad (S.A.W)
Tabbas Babu kamarsa kuma babu na kusa dashi.

Mezai faru idan aka fara saukar masa da wahayi?
Yadda yakeda tarin masoya anya zai samu matsala idan ya kirawo su?
Shin meyasa ya kirasu kai tsaye zuwa ga addini bai fara kiransu da wani abin da zaifi ja musu hankali ba?

Zamuji a rubutunmu na gaba da yardar Allah.

WAIWAYE ADON TAFIYA 8

Lokacin da masoyi (S.A.W) ya cika shekara arba'in, duniya cike take da duhu. Zalunchi ya mamaye ko'ina, bawai iyakar shuwagabanni kadai ne suke zalunchi ba, hatta yan kasuwa zaka iske suna zaluntar abokan cinikayyarsu. Manya suna zaluntar na kasa, yayinda masu kudi maimakon su taimaki talaka saidai su zalunceshi ko su tattare abinda ya mallaka. Kuna a cikin gari wani sarki mai iko ko wasu ayarin dakaru zasu iya zuwa su fatattake ku, su kwashe abubuwan da za'amora su kuma bankawa garinku wuta babu tausayi babu imani.

A cikin al'ummar da ake ganin sunada saukin zalunchi ne zaka iske sunada al'adar uba zaije ya binne yarsa da ranta, don kawai yana tsoron talauchi... Me yakai wannan jahilcin jahilci a jahiliyya? Amma a hakan akwai wasu sassa na duniya da wannan zaluncin nafila ne a lokacin jahiliyya. 

A bangaren shirka, bidi'a da sauran tarurruka na addinai marasa tushe abin zai baka mamaki, tare da daure maka kai idan kaji irin jinanen da ake zubarwa tun daga kan tsuntsaye, dabbobi masu kafa hudu, yayinda wasu addinan har mutum suna yankawa ga abin bautarsu don samuwar wata biyan bukata...

Kasancewar Annabi zai taso a irin wannan yanayi sai Allah madaukakin sarki ya sanya masa son kebantuwa daga mutane, inda a wannan lokacin zai tattare kayansa ya hada guzuri yaje can bayan gari, bazai dawo ba har sai wannan guzuri ya kare. Ita kuma matarsa Nana Khadija saita juri hakan bata hanashi ba, hasalima tana bashi gudummuwa tare da karfafa masa gwiwa. Kamar yadda tarihi ya nuna itama tun jahiliyya Allah ya kiyayeta daga sharrin jahiliyya don haka kamila ce kuma nutsatstsiya...

Idan Annabi yana tafiya a bayan gari, ya kanji duwatsu suna masa sallama. 
(Sahih Muslim)
(Sirah Ibn Hisham)

A wannan lokaci Annabi ya kasance baya wani mafarki, face sai mafarkin ya tabbata. 
(Nurul Yakeen 28)

Ranar 17 ga watan Ramadan, wanda yake cikin shekarar 610 A.D, Annabi yana farke ba'a bacci ba, sai kawai yaga mala'ika jibril ya bayyana gareshi, shi kuwa lokacin yana cikin kogon Hiraa, ba tare da wani yunkuri ba, jibril yace "Yi karatu", Annabi yace "Ban iya karatu ba." Sai mala'ikan ya matseshi, matsa mai tsanani, ya kake tunanin matsar mala'ika? 
Mala'ikan ya sake sakin Annabi yace "Yi karatu." Amsar farko Annabi ya kara bashi. Shi kuma ya kara damkar Annabi damka irinta farko... Saida sukai haka sau uku. Kowace damka sai Annabi ya fita daga hayyacinsa. 

(Annabin da yasha wannan wahalar har shine zai hanaka askin banza kaqi hanuwa?  Annabin daya sha wannan wahalar har shine zai hanaki shan kayan maye kiqi hanuwa?)

Sai Mala'ikan ya biyawa Annabi wayanan ayoyi a matsayin wahayi "Kayi karatu da sunan ubangijinka wanda yayi halitta ★ Ya halicci mutum daga gudan jini ★ Kayi karatu da ubangijinka mafi karramawa ★ Wanda ya sanar (ilmantar) ta hanyar alkalami ★ Ya sanar da mutum abinda bai sani ba ★

Sai kuma Annabi ya nemi wannan halitta mai tsananin tsoratarwa ya rasa, don haka saiya tattare kayamsa ya tafi gida a tsorace, domin yau yaga abinda bai taba ganiba, koda kuwa a mafarki, kai baima taba jin koda labarin irin wannan abuba...

Lokacin daya koma gida da matarsa, uwar gida nana Khadija, sai hankalinta ya tashi domin ta ganshi cikin firgici, abinda bata taba ganiba kenan... 
Domin daya shiga ma, cewa yayi ta lullubeshi. 

Bayan ya samu nutsuwa saiya bata labarin abinda ya faru, ta gaya masa maganganu masu dadi, ta nusar dashi cewa shi mutum ne mai kyawawan dabi'u don haka Allah bazai kunyatashi ko tozarta shi ba, ta kuma kara masa da cewa babu kokwanto cewa Allah ya zabeshi ne don ya shiryar da mutane...

Daga suka dunguma suka tafi wajen waraqatu ibn naufal dan amminta, shi kuwa yayi addinin nasara (kirista)  a jahiliyya. Da Annabi ya bashi labarin abinda ya gani, sai Waraqatu yace "Lallai wannan shine mala'ikan da aka saukarwa da Annabi Musa, inama dai ace inada karfi lokacin da mutanenka zasu koreka daga garinka..."

Kamar daga sama Annabi yaji maganar, mamaki ya mamaye zuciyarsa, ya tuno irin soyayyar da suke nuna masa, ya tuno irin yadda suka aminta dashi, ya tuno yadda basa barin wani ya ci masa mutunchi... "Shin zasu fitar dani daga garina...?" Annabi yayi tambayar cikin tsananin mamaki. 
Warakatu yace "Ai babu wani mutum da yazo ko zaizo da irin abinda kazo dashi face anyi adawa dashi an cutar dashi... Inama dai ace ina raye lokacin da zan taimakeka da dukkanin karfi na."

Daga wannan lokaci sai wahayi ya yankewa Annabi (S.A.W) ya rinka tunani kala-kala ya kuma kagu wahayin yazo amma shiru... Wasu malaman sukace saida akai kwana arba'in ba'a saukar da wahayi gareshi ba...

To fa kaka-kara-kaka...


WAIWAYE ADON TAFIYA (9)
Tatacciyar sirar ma'aiki (S.A.W).

Bayan dawowar wahayi, daga cikin wayanda suka fara imani da ma'aiki (S.A.W) akwai Nana Khadija (R.A). Ita kuwa dama matarsa ce, kuma tafi kowa sanin wanene shi, kuma tasan cewa babu son zuciya a zuciyarsa. Sai Aliyu (R.A) wanda a wannan lokacin yaro ne, kuma ya taso a hannun mafi iya koya tarbiyya (S.A.W). Zaid Ibn Harisa shima ya musulunta a farko-farko, shikuma yantaccen bawan Annabi ne, wanda iyayensa sun taba zuwa suka nemi zasu tafi dashi, amma da aka bashi zabin shin zai yarda yabi iyayensa ko kuwa zai zauna tare da Annabi... Ka duba irin shakuwar da take tsakanin iyaye da yayansu amma a hakan zaidu ya zabi zama tare da Annabi saboda soyayya, shakuwa da kulawa da yake samu a wajen Annabin rahama (S.A.W). shekara da shekaru yana karkashin Annabi, amma Annabi bai taba yi masa mummunan kalma, hantara, zagi ko kallon banza ba. Bare kuma akaiga ambaton duka.

Daga wayannan mutane a imani sai Sayyadina Abubukar (Abdullahi) Ibn Abi kuhafa (Usman) (R.A). Shi kuma abokin Annabi ne tun kafin Annabta, kuma dan kasuwa ne mai daraja lamba daya. Ana girmamashi ana karramashi a cikin mutane domin shi din mai karamchi da karramawa ne. Lokacin da Annabi ya kirashi zuwa musulunchi take ya amsa... Don me bazai amsa ba alhalin yafi kowa kusanchi da Annabi ta fuskar abokai kuma tsawon rayuwarsu tare bai taba jin Annabi (S.A.W) yayi karya ko tatsuniya ba. Don haka da musuluntarsa saiya fara kiran abokansa yan kasuwa a boye. Wanda a lokaci guda ya kawo Usman ibn Affan, Zubair Ibn Awwam, Abdirrahman Ibn Auf, Sa'ad Ibn Abi Wakkas da kuma Dalhatu ibn Ubaidullah (R.A). Wani abin burgewa shine dashi da wayannan mutane daya kawo suka karbi musulunchi suna daya daga cikin mutanen da Annabin rahama ya lissafasu a cikin mutane goma da akaiwa bushara da Aljanna tun anan duniya. 
Mai zagi da cin mutuncin Sayyadina Abubakar saika mutu saboda bakin ciki.

Idan muka lura Annabi baya kiran wani mutum sai wanda ya yarda da cewa idan ya kirashi zai amsa kiransa.

Kada mu manta har yanzu a boye ake kiran mutane zuwa ga addinin musulunchi. Tsawon shekara uku, wanda bayan wayanda muka fada a sama an samu wasu sunyi imani kimanin mutum talatin ko fiye da haka da kadan cikinsu akwai Abu Ubaida, Arqam ibn Abil'arqam wanda gidansa shine inda ake haduwa, Usman ibn Maz'un, Ubaida ibn Harisa ibn Abdulmuddalib, Sa'ad Ibn Zayd, Khabbab Ibn Aratti, Abdullahi Ibn Mas'ud, Ammar Ibn Yasir da wasunsu.
(Nurul Yaqeen)
(Muhammad Rasulullah)
(Golden Rays of Prophethood)
(Sirah ibn Hisham)

Daga nan saifa mutane suka fara zuwa da kansu suna karbar addinin musulunchi. Ai kuwa sai magana ta fara yawo a tsakanin mutane cewa Annabi muhammad ya fara koyarda wani sabon addini.

Daga nan bayan cikar wahayi shekars uku da fara sauka sai aka umarchi Annabi daya fito fili ya kira mutane zuwa Addini.

WAIWAYE ADON TAFIYA (10)
Tatacciyar sirar ma'aiki (S.A.W)...

Bayan wannan umarni da akaiwa Annabi, saiya dabbaka wannan umarni domin shi baya bata lokaci wajen bin umarnin Allah, baya tunanin irin cutarwa da zai fuskanta ba kuma ya tsoron zargin mai zargi akan abinda zai kirasu izuwa gareshi...

Abinda ya farayi shine tattara danginsa, ya hau kan dutsen safa, ya fuskancesu, daga nan ya kirayi sunan yan kowane gida, don jawo hankalinsu, dukkaninsu suka nutsu suna masu sauraron abinda zaice musu, domin suna sonsa suna alfahari dashi kuma dukkaninsu a shirye suke da taimaka masa idan taimako yake nema, idan mulki yake nema a shirye suke su bashi matsayi mai girma...
Bayan Annabin Rahama mai hikima (S.A.W) ya kirawo sunayensu sai yace dasu “Yanzu da zance muku ga wata rundunar mazaje akan dawakai sunzo su yakeku zaku yarda...?” Cikin hadin baki dukkaninsu suka amsa masa. Harma suna gaya masa cewa ai basu taba samunsa da karya ba, dadai yabo wanda ke nuni da gaskiyarsa kuma amanarsa...
Sai Ma'aiki yayi farin ciki domin dama abinda yake son tabbatarwa kenan, kenan idan har sun yarda baya yiwa mutane karya kuma baya cin amanar mutane to tabbas cin amanar Allah ko yiwa Allah karya sune mafi munin nau'ikan karya da cin amana... Don haka saiya samu nutsuwa domin mutanen dazai kira sunsan Allah, kuma sunsan girmansa, don haka bazata taba yiwuwa mafi gaskiyar cikinsu ya rasa wanda zaiyiwa karya ba sai Allah mahalicci.

Annabi ya sake cewa dasu, tofa lallai shi manzo ne izuwa garesu mai gargadi izuwa garesu tun kafin azaba mai radadi ta saukar musu...

Kaji hikimar Ma'aiki, saida ya sanya da bakinsu suka yarda cewa shi ba makaryaci bane, ba kuma maciyin amana bane sannan ya isar musu da sakon, kaga kenan koda sun karyatashi to tabbas sunsan sun karyata gaskiya ne, sannan koda basu furta cewa sunyi imani ba to tunani zaiyita kaikawo a zukatansu...

Aka rasa wanda zai karyata Annabin Rahama a cikinsu, can sai Abu lahab yayi magana ta batanci ga Annabi, amma maimakon ya karyata Annabin shima sai cewa yayi “Don wannan ka tara mu anan?”

Daga wannan lokaci sai Manzo ya zamana yana kiran mutane a bayyane akan hanya, ko a gida ko a wajen zama, duk da haka basa cutar dashi domin shinr mafi daraja da kuma girma a cikinsu, kuma shine wanda suka amincewa lamba daya. 

Saidai izgilanchi da suke masa su rinka nunashi suna cewa wannan dan gidan Abi khabshata ne, yana riya cewa wai ana masa magana daga sama... shi wannan Abi khabshata din shine mijin Halimatu Sa'adiyya. Suna jingana Annabi dashi don kaskantar da Annabi... (S.A.W).

Lokacin da Annabin tsira ya fara aibata gumakan da suke bautawa, yana ambatarsa da cewa basa amfanarwa kamar yadda basa cutarwa, tofa sai suka harzuka don haka suka fara shiri da shirye shirye na cutar da ma'aikin Allah.

Suka rinka hantara da muzgunawa Annabi, amma Abu Dalib a haka ya sake jan Annabi jikinsa yana mai kyautata masa mutukar kyautatawa da kuma bashi kariya. Shi kuwa ma'aiki (S.A.W) takurar da muzgunawar bata hanashi kiran mutane zuwa musulunchi ba. Kamar yadda babu abinda zai hana mahaifin gwarzo Aliyu (R.A) bada kariya ga Annabi.

Quraishawa suka shiga tattaunawa a tsakaninsu akan hanyar da zasu bi su hana Annabi wannan kira da yake, a karshe sukaje wajen Abu Dalib suka kai karar ma'aiki (S.A.W) wanda dama kafin wannan lokaci sun masa magana amma saiyayi musu irinta manya wato yayi watsi da maganar. Sukace bazasu lamunta ba, a rinka aibata iyayensu, ana jahiltar dasu ana kuma zagin ababen bautarsu... Suka kuma kausasa harshe sukace da Abi Dalib, kodai ya hana Annabi wannan da'awa da yake ko kuma su hada da shi da Annabin su yakesu... Harsai daya daga cikinsu yayi nasara. 

Tsohon dattijon ya shiga tunanin mafita, daga karshe ya kira ma'aiki yace dashi “Yakai dan dan'uwana, mutanenka sunzo gareni sun tsoratar dani mutukar kaci gaba da kira izuwa ga addininka, ka tseratar da rayuwata da taka, kada ka dauko min abinda bazan iya dashi ba...”
Manzon tsira dayaji haka sai yayi tsammanin cewa kawunsa Abu Dalibi ya gaji da bashi kariya, saboda haka babu sauran wata kariya ko kulawa da zai bashi. Annabin rahama (S.A.W) yace “Yakai kawuna, Na rantse da Allah, idan zasu saka rana a hannun dama na, wata kuma a hagu na, su kuma nemi in ajiye wannan aikin (Da'awa) to bazan daina ba har sai Allah ya tabbatar da nasarata ko kuma in mutu ina mai kiran (zuwaga Allah)... Hawaye suka fara zubowa daga idanun masoyi (S.A.W), hawayen suna kwaranya ya tashi zai fice. Saboda tsananin soyayyar da Abu Dalib ke yiwa Annabi saiya kasa jurewa yaga idanun Annabi suna zubar da hawaye, duk da cewa rayuwarsa zata iya salwanta idan yaci gaba da bawa masoyinsa kuma dan dan'uwansa kariya, yana wannan yanayin yaga Annabi yana gab da ficewa ai kuwa saiya kwallawa Annabi kira yace "dawo yakai dan dan'uwana, kaje inda kake so, kuma ka fadi abinda kake so fada. Nayi rantsuwa da Allah bazan taba sallamaka ga abokan adawarka ba." 

Allahu Akbar, shin akwai soyayyar da tafi wannan?
zamu yada zango anan, sai kuma a rubutu na gaba. Tare da ni
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.