Babban Sako.

BABBAN SAKO.

Musulmai da dama a cikin kaso 99% na Qur'ani suna amfana ne da iyakar 1%.  Wayannan ina maganar musulmai masu karantashi ne bawai masu ajiye shi sai jefi-jefi ba.
Da dama suna karanta Qur'anine don samun lada kawai sun manta da cewa.

Yana maganin bakin ciki.
Yana kawar da damuwa ga mai damuwa.
Yana yalwata arziki.
Yana haska zuciya.
Yana karfafa fahimta.
Yana sanya kwarin zuciya da tabbatuwa.
Yana kawo _firaasa_.
Yana zama sababi na amsa buqatu.
Yana bada kariya daga cututtukan cikin jiki, kama daga kan na sassan jiki har zuwa na wasu organs na jiki.
Yana bada kariya daga cutukan da suke a zuciya irinsu hassada, kyashi, kishi mara amfani da sauransu.
Yana saka hangen nesa.
Yana kawar da son duniya.
Yana saka karfin gani da karfin sauran sassa kamar hakora, ji, da sauransu.
Kai mutum kamar ni bai isa ya fadi kashi 3% daga 100% na amfanin Qur'ani ba.

A takaice zan iya cewa Qur'ani kamar ruwa ne, wasu suna amfani dashi wajen sha ne kawai.
Wasu kuwa suna amfani da ruwa wajen sha, wanka da tsaftace tufafi ne kawai.
Wasu kuma suna amfani dashi wajen sha, wanka, tsaftace tufafi, noma, kiwo da wasu ayyukan.

Don haka kada ka kuntata aikin Qur'an a waje guda kawai. Ka fadada shi don samuwar cigaban ka.

Naseeb
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.