Tasirin fina-finai da littafai a rayuwarmu.

*Tasirin fina-finai da littafai a rayuwar mu*.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.

Abinda kake tunani, da abinda kwakwalwarka take hange da kuma tsarin rayuwarka duk suna chanjawa sanadiyyar abubuwa da dama da suke faruwa.

Mafi girman abinda yake sauya tunani kai tsaye ko kuma ta bayan fage shine kallon fina-finai da kuma karanta littafai....

Lokacin daka lizimchi karanta littafai masu kyau da manufa to tabbas zaka tsinci rayuwarka tana zama mai kyau da samun ingantacciyar manufa. Don haka ne zaka samu babu littafin dayake shiryarwa irin wanda aka saukar daga sama.

Hakanan yadda kake karanta littafai marasa kyau, marasa manufa ko masu wani mummunan sako a kunshe a ciki a hankali zai sauyaka zuwa wannan yanayin.

Don haka ne zaka samu mata masu kallon fina-finai da karanta littafai marasa kan gado basa wadatuwa da abinda mijinsu zai musu domin tuni zuciyarsu tayi gaba akwai tunanin irin mijin da take, don haka maimakon ta gode akan wani abin saikaga ta raina. Ita yadda taji ance mijin novel yanayi haka take so nata yayi. Ta manta wancan kirkirarre ne wannan kuma gaske ne.

Hakanan namiji mai kallon fina-finai da littafai barkatai marasa kan gado zaka sameshi baya ganin duk wata soyayya da kulawa da matarsa zata nuna masa domin tuni yaga koya karanta wata budurwar novel wadda ta kware a kirkirarriyar soyayyar daya karanta... Shima ya manta da cewa wancan kirkirarre ne wannan kuma gaske ne.

Hakanan inka duba zaka samu da yawan masu karance-karancen da kallace-kallacen sunada wasu dabi'u barkatai marasa kan gado.

Littafai da fina-finai kamar nau'ikan abinci ne, lokacin da kaci mai kyau hakika tunaninka zai ginu kuma kwakwalwarka da sanin rayuwarka zai bunkasa. Amma lokacin da kake dibar kowace shara kamar yadda hajjo ganon Aliyu kamal ta littafinsa HAUSA GIRL tayi to tabbas zaka raunata hankalinka tare da dakusar da kwakwalwarka.

A kula da littafan da za'a karanta da kuma fina-finan da za'a rinka kalla.

21th March 2018

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.