MUMMUNAR RAYUWA

Mummunar rayuwa itace rayuwar da ake yinta cikin rashin samun abincin da zai gina jiki, da ruwan dazai kori kishirwa, da muhallin da mutum zai rufawa kansa asiri, da ilmin da zai tafiyar da rayuwarsa dashi....

Mafi munin rayuwa kuma itace rayuwar da akayita ba tare da ciyar da zuciya abincin imani ba, ba tare da suturce zuciyar da jiki daga sharri ba, ba tare da koyi da magabata ba, ba tare da sani da karantar zamanin da mutum yake rayuwa a cikinsa ba.

Tabbas muna cikin rayuwa mafi muni, muna cikin duhun da bama iya hangen abinda ke gabanmu, ga fitilu a hannunmu amma mun kasa kunnasu domin ana kunnasu ne da zuciya, mu kuwa zukatan namu sunyi nauyi, ko mun kunna tofa chajin imanin da yake cikin zukatanmu baida wani haske na azo a gani dazai haska mana abinda zai wadatar damu. Zukatan sunyi tsatsar da wankesu da fitar da tsatsar abune da zai dauki lokaci mai tsayi abune gagararre saida a gurin Allah madaukakin sarki.

Babban tashin hankalin shine muna cikin kungurmin daji mai cike da ramuka masu zurfi, ga tsoffin rijiyoyi wayanda ba'a shinge su ba, ga muggan mayunwatan namun daji wayanda rashin kuzarin da yake jikinmu yasa munaji muna gani suke far mana koda yaushe ba tare da mun iya kare kanmu ba......... ta gabanmu zasu wuce ba zamu iya kamasu ba, a gabanmu zasu farwa makocinmu su hallakashi amma ba zamu iya kwatarsa ko taimakonsa ba, saidai bayan tafiyarsu muyita koke-koke muna jingina laifin ga wasu tsirarun mutane.........

Tabbas a irin wannan yanayi muke, ko kuma ince mafi muni...... Tabbas mafi muni domin wannan wani yanki kawai na tsakura a cikin jerin gwanon abubuwan da suke faruwa a garemu yau da kullum.

Yan'uwa, mu tuna fa, abubuwan da suke faruwa yau da gobe sune suke haduwa su haifi abinda zai faru jibi da gata, abincin da kake ci yauda gobe shine yake zama makomar lafiyarka ta jibi da gata.

To tabbas abinda matasanmu suke kalla, da abubuwanda suke karantawa sune suke haduwa a zukatansu, suyi 'kwaikwaye su 'kyankyashe duk a cikin zukatansu.......

Ko muna tunanin abinda yaranmu suke kalla su kurawa ido yana zama a kwakwalwarsu ne iyakar lokacin da ake kalla zuwa lokacin da za'a kashe abin kallon?
A'a, wannan abin yana rubuce a kwakwalwarsu, kuma sunanan zasu kamanta shi saidai wani dalili ya hanasu..... Kodai saboda bayyanar hasken imani ko kuma saboda rashin samun damar aikatawar.

Yara kananu yan shekara 16-20 sunayin barnar da manya yan shekara talatin basu yiba a shekarun baya, sun zama yan kwaya, sun zama yan bariki, sun zama yan sara-suka, sun zama yan fisge, sun zama barayin zaune, kai wasunsu sun zama masu garkuwa da mutante, wasunsu sun zama yan bindiga dadi.

Wayannan yara zaka samesu basa ganin mutunchi da girman kowa. Ita kuwa sallah dama basa jin kunyar anayinta suna zaune suna baza hanci, suna tutiyar sunfi karfin su dora goshinsu a kasa don su bautawa mahalicci, su din ai manyan yara ne........ To wanda baiga girman Allah ba anya zaiga mutuncin wani kuwa?

Wani zai iya basu kariya yace basa wannan tunanin, amma ni dana sansu nasan me suke nufi bazan basu wannan kariyar ba.

A naka hangen menene mafita?
A naki hangen mecece mafita?


Naseeb Auwal
Abu umar Alkanawy

Comments

  1. Mafita itace komawa zuwa ga Addinin Allah da kuma tsarin tarbiyya wadda Iyayenmu da Kakanninmu suka rayu dasu duk da karancin iliminsu. Amma Kyawawan dabi'unsu yasa suka zauna lafia musamman Kunya da kamun kai.

    Allah ya shiryemu baki daya.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.