Kwarafshan

Kwarafshan! 
Menene kwarafshan?
Kwarafshan shine lokacin da wannan yarinyar take bawa iyayenta kudi saboda suyi gum da bakinsu su zuba mata ido ta kula kowane kowane banza.

Kwarafshan shine wannan saurayin da zaije yayita yiwa budurwa karyar kudi kawai don cinwa wata manufa tasa ta banza.

Kwarafshan shine lokaci da kace "eh" sukace "a'a". Suka biyaka kudi don kace " a'a", kuma ka karba kabi hanyarsu ta banza.

Kwarafshan shine lokacin da shugaban kasar nan ya bada sunan wani a matsayin minista, su kuma yan majalisa suka nemi wanda aka bada sunan nasa daya basu kudi indai yana so su tabbatar dashi... Shikuma saboda son abin duniya ya basu kudin shima ya zama mutumin banza.

Kwarafshan shine lokacin da wannan Dan sanda ya karbi kudi a hannun mai laifi kuma ya sakeshi.

Kwarafshan shine lokacin da dalibai suka biya wannan malamin kudi don jarrabawarsu tayi kyau.

Kwarafshan shine lokacin da aka baka kudi ranar zabe kuma ka zabi mutumin da bai chanchanta ba.

Kwarafshan shine lokacin da aka baka wata amana ta al'umma amma saika cinye ka shirga karyar anyi gobara, ko ruwa ya cinye, ko wata dabba ta lamushe.

Kwarafshan shine lokacin da yan kwangila suke biyanka kudi don abasu kwangila suyi cuwa-cuwa baka da bakin magana.

Kwarafshan shine lokacin da kake da ikon hana kwarafshan amma ka bari anayi baka hana ba.

Kwarafshan shine lokacin daka fake da addini kaci kudin mutane.

Meka sani dangane da kwarafshan?

Naseeb Auwal

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.