TARKON SHAIDAN

Tarkon Shaidan 1

SHIMFIDA
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.
Tsira da aminci su tabbata ga shugaba jagaba (S.A.W), da ɗalibansa kuma abokanan rayuwarsa (Sahabbai) da kuma mafiya tsarkin iyali a doron ƙasa (Ahlul baiti).

Bayan haka. 
Lokacin da ubangiji (S.W.A) ya halicci Annabi Adam tare da Nana Hauwa'u kuma ya sanyasu a cikin Aljanna, da Shaiɗan yaso ɓatar da su, bai zo musu kai tsaye da sunan mai ɓatarwa ba, hasalima ce musu yayi "Haƙiƙa ni a gareku mai yin nasiha ne..." baya ga rantsuwa da ya yi musu ya kuma ƙawata umarninsa da  wasu abubuwa da suke so duk don ya ɓatar da su...
Kuma ya samu nasara.

Mu tuna lokacin Annabi Nuhu da mutanensa, tabbas Shaiɗan bai ɓatar da su ba sai da ya yi amfani da tarkonsa ta hanyar nuna musu cewa lallai su akan gaskiya suke kuma shi wanda aka turo ɗin bashi da girman da za a turoshi zuwa garesu.

Duba Annabi Yunus, shi ma Shaiɗan bai hanashi yaɗa da'awarsa ba, amma sai ya ɗana masa tarkon fushi, inda ya fusata mutuƙa lokacin da mutanensa suka bijire kuma suka ƙi imani da shi, harma ya tafi ya barsu...

A taƙaice babu wani mutum da ya ɓata daga hanyar gaskiya face akwai wani tarko da Shaiɗan ya ɗana masa, kodai ya lulluɓe masa gaskiyar ta yanda zai kasa ganeta mafi kyawun ganewa... Ko kuma ya gane gaskiyar kuma ya fahimceta amma karɓarta zai kawo karshen wani jin daɗi ko matsayi don haka sai mutum ya bijirewa gaskiyar...

Hatta masu aikata zunubai, zaka iske Shaiɗan wani tarko ya kafa musu kuma caraf ya kamasu ta yanda kodai ya ƙawata musu zunubin ta fuskar da za su ganshi ba zunubi ba, ko kuma su rainashi, ko kuwa ma sun san zunubin ne amma sai ya sanya musu tunani na cewa suna da lokuta masu tsayi da za su tuba...

Dama wasun wayannan da yawa cikin jerin abubuwan da zamu tattauna a wannan takaitaccen rubutu.

Zamu ambato tarkunan Shaiɗan tare da faɗar irin hanyoyinsa wajen ɗana su, da kuma yanda wasu suka afka ciki kamar yanda wasu suka tsira...

Allah nake roƙo da ya bani ikon rubuta abin da yake dai dai.
Ya kuma yafe abin da yake na kuskure. Ya kuma sanya rubutun ya zama domin Shi akai, ya kuma sanya ya zama mai amfanarwa. 
Ameen thumma Ameen

Tarkon Shaidan 2

MATAKAI DA SHAIƊAN YAKE DAUKA DON HALLAKAR DA ƊAN ADAM.    
Babban cikas da Shaiɗan zai fuskanta shi ne a haifi bawa ya zama musulmi, domin tun daga nan yake jin cewa dole sai yayi da gaske sannan zai iya raba mutum da farin ciki gami da jin daɗi mai ɗaurewa.

Abin lura dangane da Shaiɗan shi ne; duk kusancin bawa zuwa gare shi hakan baya sanya adawar da yakewa bawa ta gushe. Domin kuwa wannan adawar tana nan tsakaninsa da bayi koda kuwa sune mafi kusanci a wajensa har zuwa ranar sakamako.

Don haka abu na farko da Shaiɗan zai yi don kifar da musulmi shi ne buɗe masa kofofin shirka ta yanda mutum zai tsinci kansa cikin shirka da Allah. Ita shirka ba wai sai kaje kayiwa wanin Allah sujjada ba ne kawai kayita, ko kuma idan kace kai ba Allah ne ya halicceka ba...

Hanyoyin faɗawa shirka suna da yawa daga ciki akwai; bin bokaye, neman taimakon wanin Allah a abin da babu mai iko sai Allah, yin yanka ga wanin Allah, ko amfani da wasu ɗalasumai don neman tsari, tsafi da sauran dangoginsa, neman sa'a... Da sauransu, Idan da tsawon rai zamu saki rubutun mu akan aqeeda idan Allah ya nufa.
A taƙaice duk wani nau'in bauta idan aka yiwa wani wanda ba Allah ba hakan na iya zama shirka. Hakan shi ne ya sanya roƙon mamata ko rayayyu a janabin da babu mai wannan ikon sai Allah hakan ya zamo shirka. Sai dai don ka roƙi wani abin duniya misali kuɗi da maroƙa suke roƙa ko agaji da talakawa suke nema wajen masu karfi wannan baya cikin jerin shirka.

Ɗan'uwa yana kasuwanci yana samun arziki fiye da ɗan'uwansa, sai Shaiɗan ya zo yayi ta ziga ɗayansu, yayita hakaito masa abubuwa a ƙarshe ba zai bar shi ba har sai ya sanyashi yaje wajen boka, kaga daganan ya ruguza masa imaninsa, ya kuma sanyashi a harkar shirka.

A irin ɓatarwar da Shaiɗan ya yiwa mutane akwai ɓatarwarsa ga magabata a zamaninnikan da suka shuɗe, inda idan wani salihin bawa ya mutu suke zana surarsa ko su sassakashi don tunawa da shi, lokaci yana tafiya har takai ga ana zuwa ana roƙon waƴannan gumakan salihan magabatan wanda hakan bauta ne. 

Kamar hakane a wannan zamanin zaka iske Shaiɗan yana ƙawatawa mutane akan wasu malamai, inda zasu kama ƙafa da su, suna neman ceto a wajensu, ko arziki, ko gafarar zunubai da wanin haka. 

To kuwa tabbas idan Shaiɗan ya samu wannan ribar a wajen bawa ya gama samun riba domin ita shirka tana ragargaza ayyuka ta bata su gaba ɗaya.

Kamar yadda Allah ya ambata a ayoyi masu yawa. Hakanan wanda ya cakuɗa aikinsa da shirka to shi ma Allah zai bar shi da abin da yayi shirkar da shi ko dominsa. Hadisai ingantattu sun inganta akan wannan.

A dai nau'ikan shirka da Shaiɗan yake yaudarar mutane yake afkar da su cikinta shi ne shirkar Riya (yin abu ba don Allah ba).  
Ta inda mutum zai yita wani nau'in bauta don kawai ya burge mutane.
Ya gina masallatai babu lada.
Yayi salla babu lada.
Yayi jihadi babu lada.
Yayi azumi babu lada.
Ya karantar babu lada.
Yayi rubutun babu lada.
Yaje aikin hajji babu lada.

Duk saboda ba don Allah yayi ba, bai tsarkake niyyar yin aikin zuwa ga Allah ba. 

TARKON SHAIDAN 03
Babban dalilin da yasa idan shaidan ya riski mutum da imani yake biyo masa ta hanyar ɗorashi a turbar shirka shi ne sanin cewa Allah yana gafarta dukkanin laifukan da suke tsakaninsa da bawansa amma banda shirka. Kamar yadda wannan ayar take nunawa.
إن الله لا يغفر أن يشرك به و يغفر ما دون ذلك لمن يشاء.

To idan haka ne tabbas Shaiɗan zai yi murna ya sanya mutum ya aikata laifin da yasan mutukar mutum ya mutu yanayi to babu gafara ko rahama tsakaninsa da Allah. Muna neman tsarin Allah da faɗawa cikin wannan tarkon.

Idan Shaiɗan yaga ya kasa jefa mutum cikin tarkonsa na farko, to sai ya sakko zuwa martaba ta biyu. Wato matakin *BIDI'A*.

Meyasa yake son bidi'a fiye da manyan zunubai (kaba'ir)?
Abinda yasa shi ne, idan mutum yana aikata manyan zunubai irinsu zina, shaye-shaye da sauransu to tabbas mutum yasan laifi yake aikatawa, kuma zai rinka tuba muddin yana da rabo. Amma idan mutum aka ce bidi'a yake, to shifa bai ma yarda ba bauta yake ba, domin shi ƙudurcewar da yake shi ne kyautatawa yake wajen Allah.

Bidi'a shi ne dukkanin wani abu wanda aka ƙirƙiro kuma aka shigar da shi addini da sunan cewa bauta ne, ko kuma ƙari akan abin da addini yazo da shi.

Shaiɗan idan ya fuskanchi mutum mai son addini ne, to sai yayita ƙoƙarin kawo masa abubuwa ta fuskar addinin wayanda ba tabbatattu ba, ko ince wayanda ba su da asali daga Qur'ani ko Hadisi.
Ta wannan fuskar Shaiɗan ya ɓatar da mutane da adadinsu bazai misaltu ba, cikinsu har da malamai.

Tun a lokacin sahabbai aka samu wani mai ƙara zikiran bayan sallah akan 33 da akace, da Allah ya soshi da rahama sai yayi mafarki cikin mafarkin aka nusar da shi cewa aikinsa ba karɓaɓɓe ba ne.

Don haka idan mutum yana so ya kubuta daga sharrin shaidan a wannan tarkon sai ya ajiye a ransa cewa sharudan karbar aiki guda biyu ne. 
1. Ikhlasi, wato yin abu don Allah.
2. Mutaba'a, wato kwaikwayon yanda Annabi ya aikata aikin.
Dukkanin aikin da babu wannan a ciki to wannan aikin ba karbabbe bane a wajen Allah.

Asalin abin da ke sanya mutum ya afka cikin wannan tarko shine kokarin neman kusanci ko bauta ga Allah bata hanyar da Annabi (S.A.W) ya koyar ba. Ita kuwa darajar Annabi a wajen Allah takai matakin da duk wani aiki indai bashi ya koyar ko yace ayi ba to Allah bazai karba ba.
Hadisai da ayoyi a wannN babin sunada mutukar yawa.

Tare da cewa akwai sabanin fahimta a wannan bigiren sosai ta inda zaka iske wasu suna daukar wani abu a matsayin ibada yayinda wasu suke daukarsa a matsayin bidi'a. Makasudin dai anan ba shine karanto sabani ba, maqasudin shine ambaton tarkon shaidan din kawai.

Koma dai menene, mai hankali zai gane cewa...
Mafi alherin bauta ko hanyar kyautatawa Allah da itace wadda ta samo asali daga masoyinmu manzon (S.A.W).
Idan akwai tsawon rai, insha Allah zamu fadada bayani a wannan fagen a wani rubutun dabam.
Wani mawaki yake cewa
_Bidi'a a addini ta labe_
  _Banda kere-kere na yan china_

TARKON SHAIDAN 4
Yayinda shaidan yaga cewa an tsallake tarkon farko na shirka da dangoginta, an kuma kaucewa bidi'a da karikicenta to saiya bijirowa mutum ta hanyar manyan zunubai, domin katangar da take tsakanin musulmi mai imani da aljanna sune manyan zunubai. Mutukar mutum ya kaurace musu tofa hakika ya dace kuma ana kyautata zaton ya wuce kamar yadda ayoyi da hadisai da dama sukai nuni akan hakan. 

Saidai wani zai iya cewa to ai akwai hadisai da suka nuna cewa cikin masu aikata manyan zunubai akwai wayanda zasu shiga aljanna ba tare da sun shiga wuta ba, kamar yadda wasu zasu shiga wutar daga bisani bayan an wankesu su dawo aljanna. 

Sai muce dashi, kwarai kuwa, sai dai babu mai tabbacin cewa yana cikin wayanda zasu aikata laifi yaje lahira ace dashi ya wuce an yafe masa. Mutum mai hankali kuwa idan har yasan yanda wuta take to bazai taba son ko tunanin a sakashi a ciki ba. Ta hanyar da har zai iya biyewa shaidan yayi manyan zunuban da zasu sabbaba masa bita wutar kafin yaje aljanna.

Babban dalilin da yasa shaidan yake bijiro da manyan laifuka shine, yanda suke kekasar da zuciyar mai aikatasu, da kuma yadda suke kautar da ita daga fuskanta ko karbar alheri, kamar yadda suke sanya hasken imani ya disashe. To tabbas muddin zuciya ta kekashe, hasken imani ya gushe ta kuma daina karbar alheri to wannan dandanon imani da akeji da nutsuwa yayin bauta zai kauce sannan kuma ganin girman Allah da manzonsa zai kau daga wannan zuciyar don haka saiya zamana mai zuciyar ya zama baya karbar alheri amma a bangaren sharri sune a kan gaba. Muna neman tsarin Allah da wannan.

Shaidan babbar hanyar da yake bi wajen tura mutane wannan hanyar mai hatsarin gaske shine bijiro musu da tunanin cewa ai Allah mai gafara ne mai kuma jin kai. Da haka saiya rinka turasu yana kawo musu wannan tunanin su kuma suna biyewa suna aikatawa. Tun suna ganin girman laifukan harsu daina ganin girman laifukan. 

A hikima irinta Allah saiya musanya muminai da abubuwa mafi kyau.
Idan shaidan yana jan bayi zuwa zina to sai Allah ya halatta musu auratayya.
Idan shaidan yana jan bayi zuwa ga shan kayan maye sai Allah ya halatta ababen sha masu dadi da kara lafiya.
Idan shaidan yana sanya bawa yayi karya sai Allah ya dorawa gaskiya nutsuwa da kima...

Kai bazaka taba ganin wani aikin sharri da shaidan yazo dashi ba face ka samu Allah ya bada wanda yafi wannan sau malala gashin dubbobin duniya.
Kuma babu wani abu da Allah zai haramta face kaga yana cike da cutarwa.

Dama shi Shaidan makiyi ne, babban burinsa yaja bayi zuwa ga abinda yake cutarwa ga lafiyarsu, da karayar arzikinsu da kuma uwa uba tabewa a lahirarsu.


TARKON SHAIDAN 5
Shirka, Bidi'a, Manyan zunubai, sune abubuwan da muka ambata a rubutukan da suka gabata akan hanyoyin da Shaidan Iblis yake bi don hallakar da Dan'adam.

Hanya ta gaba itace bijirowa da dan'adam da kananun zunubai. Wayanda basu kai wayancan manyan girma ba.

Babban dalilinsa kuwa shine mutukar za'a juri yin kananun zunubai to tabbas za'a wayi gari a tsinci kai tsundum cikin manyan zunubai. Sannan kuma kananun zunuban kansu idan suka taru sukan zama manyan kamar yadda ma'anar hadisai da yawa yazo akan hakan.

Kuma tabbas kamar yadda manyan zunubai suke lalata zuciya haka kananun ma suna lalatawa baya ga nakasa lafiya da suke. Shi kuwa Shaidan idan muka kula dashi lafiyar ma wadda zata taimaka wajen bautawa Allah kokari yake ya kawar da ita... 
Shin wanne hanyoyi Allah madaukaki yake bi wajen rusa aikin Shaidan da kuma warware kaidinsa ga bayi? Wannan shine abinda zamu tattauna a karshen wannan rubutu idan Allah ya bamu iko.

A sunna ta rayuwa idan mutum ya juri aikata wani laifi to tabbas zaka iske kullum laifin kara gaba yake. 

Kafin mu bada misalai irin na tuggun Shaidan don hanyoyin su kara fitowa fili mu tafi matakin da yake bi na gaba...

Wato Idan yaga bai samu damar saka bawa kananun zunubaiba to saiya bijirowa mutum ta abubuwan da suke *mubahaat*, abubuwan da za'a iya yinsu kuma babu zunubi don anyisu. Anan wajen yana samun riba guda biyu. Kodai ya batawa mutum lokaci, ko kuma yayi amfani da mubahaat din wajen kai mutum zuwa zunubi.

Babban misali a bayyana shine yanda mutane suka kwallafa rayuwarsu akan wayar hannu. Zaka iske dole a samu dayan biyu. Kodai a bata lokaci wajen hira (chat) mara amfani ko kuma a aikata wani zunubi karami ko babba.

Sau nawa za'ai gulmar wani a waya ta hanyar rubutu ko sauti?
Sau nawa wayar take sakawa a rasa sallar jam'i cikakkiya? 
Wannan dan kankanin misali kenan.

Kaga anan idan muka duba zamuga Shaidan koda baka aikata zunubi ba da wayarka tofa tilas ya samu riba domin tabbas ya bata maka lokaci. Bare kuma yanzu zai wahala ka iske wanda baya gulma baima san yanayi ba a harkar network, idan bayayi to yana kallon abubuwan da basu dace ba, kada ma akai ga maganar fina finai irin na batsa, hatta kallon matan daba muharramai ba laifi ne, kuma masu rubutu ba zasu fasa rubutawa ba.
Allah ya tsare mana imaninmu.

Ga wani misali na karshe a wannan gabar kafin mu tsallaka gaba.

Macece take chat da namiji da bata sanshi ba, a karshe suka saba da ita da sunan yana sonta.
_matakin mubahaat_

Da shakuwa tayi shakuwa ta koma soyayya saiya bukaci hotunanta, ita kuma tun tana tura na kirki harya hure mata kunne ta fara tura masa masu dauke da shigar da bai dace ba.
_Matakin kananun zunubai_

Yayi mata alkawarin zai aureta, ita kuma ta yarda donta aminta dashi. Saiya fara tambayarta hotuna masu nuna tsiraici... Tun tana musantawa har ya shawo kanta ita kuma taga cewa tunda shi zata aura kuma duk a cikin soyayya ne saita tuttura masa... A karshe ya gudu ya barta. Bayan wani lokaci sai wani yazo da gaske zai aureta. Sai wancan dan'iskan ya dawo mata yace kodai ta bashi kanta ko kuma ya turawa wanda zata aura wayannan hotunan nata...
_Matakin manyan zunubai_

Mu kula da wannan da kyau. Kaga a farko shaidan ya biyo mata daga kananun matakai harya zuwa manyan matakai... Kuma a karshe bai barta ba saida ya cutar da ita domin dama shi shaidan ba masoyi bane makiyi ne. 

Ayi hakuri mun dan tsawaita tare da cewa a hakan munyi kokarin takaitawa. Gabarce tana da abubuwan fada da yawa. 

Don jin ragowar matakan, da yadda shaidan yake amfani dasu. Da kuma yanda yake idan mutum ya tsallakesu duka sai a sauraremu a rubututtukan gaba da yardar Allah.

TARKON SHAIDAN 6
A lokacin da Shaidan yaga ya biyo maka ta matakan da muka ambata kuma yaga dukka tsallake wanda dama idan mun kula burinsa a wayanan matakai ya ginu ne akan lalata zuciyar bawa da kawar da kaunar Allah da son addinin Allah a cikinta to sai ya sauya salo.

Wannan salon yafiyinsa ga mutanen da suke son Allah da manzonsa kuma suke da kokari matuka wajen aikata alheri.

Wannan wacce irin hanyace?
Wannan hanya itace *Barin yin abinda yafi falala ko wanda yafi kamata zuwa ga wanda bai kaishi falala ba*.

Don bayyana hakan ga misali, akwai mutanen da zaka iske koda yaushe suna cikin karanta littafan addini kodai na wake-waken yabo ga fiyayyen halitta ko tarihi ko wanin haka amma kuma basu da lokacin karanta Qur'ani alhalin karatun Qur'anin yafi wannan abinda suke karantawa.

Anan ribar Shaidan shine ya rage musu lada da kuma kusancin da zasu samu zuwa ga Allah.

A irin hakane zaka iske an kira sallah amma saikaga mutum ya kirkiro wani aiki wanda ainihin aikin aiki ne mai kyau, amma ta dalilin yin wannan aikin sai kaga mutum ya rasa cikakken jam'i ko jam'in ma gaba daya.

Ko kaga mutum ga wani guri da ake bukatar taimako nagaske wanda da zai taimaka a wannan wajen dubban mutane zasu amfana ko kuma tasirin taimakon ya sanya Allah ya gafartawa mutum, amma sai shaidan ya kautar da hankalin mutum wajen kawata masa wani abu wanda bai kai wannan ba. 
Ko mutumin da bai sauke wajibin dake kansa ba y tafi yana aikata abinda yake mustahabbi ko sunna. Misalai dai anan sunada yawa.

Abin lura anan shine; Shaidan bazai taba samun wuta hanya da zai hallakar da bawa ko ya sanyashi yayi hasara ba har sai yabi wannan hanyar.

Idan mutum ya tsira daga nan to matakin gaba da yake mafi hatsari shine Shaidan zai kokari wajen sanyawa mutum cuta wadda kodai kasala yayin ibadah ko wanin haka. Sai kuma rubdugu da zaisa mabiyansa daga mutane da Aljanu zasu yiwa mutum.

A irin wannan mataki ne Shaidan zai iya bayyana ga mutum ko kuma ya bayyanarwa da mutum wani abu wanda indai ba wanda Allah ya kubutar ba sai kaga mutum ya zurme a wannan hanyar.

akwai matakin da mutum zai kai da Shaidan zai iya bude masa hanyoyin alheri guda saba'in ba don komai ba sai don kawai ya jefashi ga hanyar sharri guda daya.

Don gudun tsawaitawa zamu dakata anan. Tare da kawo misalai da kuma irin yanda shaidan yake bi wajen dulmiyar da malamai na kowane bangare a rubutunmu na gaba.


TARKON SHAIDAN (7)
Tabbas bayin Allah nagari a kowane lokaci shaidan bashi da wani buri akansu face ganin ya jefasu cikin wahala da kuma fadawa cikin tarkonsa. 

Don ma Allah yana mayarwa da shaidan makircinsa ta hanyar wani abu wanda yake kara tabbatar mana da cewa Allah gwanine kuma mai hikima. 

Misali guda daya da zan bayar, idan mumini yana rashin lafiya, to Allah zaisa a rubuta masa ladan ibadun da yake lokacin da yake da lafiya bayan gafarar zunubai da wannan cutar zata zamar masa. To anan sai shaidan yayi biyu babu domin ya sanyawa mumini wata cuta koya shafeshi da wata cuta amma maimakon yaga wannan muminin ya samu nakasu sai yaga an kankare masa laifukansa harma da alakoron ladan ibadun da yake lokacin da yake da lafiya... Shikuwa shaidan wannan ne baya so.

Saboda gudun tsawaitawa bari mu dauki irin wasu tarkuna da shaidan ya kafawa masana da malamai don sake nunawa al'umma irin hatsarin da shaidan ke da shi.

Dangane da lamarin ilmin  Qur'ani sai Shaidan ya shigowa da wasu malamai bayanai na tawili inda suke tunanin wasu abunuwan da suke a cikin Qur'ani suna bukatar tawili, tawilin kuma mara kyau (masana tafsiri sunsan banbaci tsakanin tawilin dake nufin tafsiri da kuma wanda ke nufin sauya ma'anar abu).
Wasu kuma ya tura su hanyar batar fassara Qur'ani don biyewa son zuciyarsu. 
Misali mutum ya kirkiro wani abu ko kuma yazo da wata fahimta, sai daga baya kuma ya tafi Qur'ani yana neman abinda zai karfafi wannan fahimta tasa. Ya manta cewa *shi Qur'ani binsa akeyi bawai shine yake bi ba*.

Wasu kuma sai suki zuwa wajen malamai masana don sanin ma'anar Qur'ani don haka saisu karanta shi suyi masa wata fahimtar. 
Misali akwai ayar da take bada labarin cewa banu isra'ila an taba umartarsu dasu kashe kawunansu a matsayin abinda zaisa ubangijinsu ya gafarta musu. Shima daya karanta sai yaje yahau kan katon dutse ya fado yana mai biya wannan ayar... Saboda tunaninsa har yanzu idan kayi laifi ka kashe kanka to Allah zai yafe maka...
Misalai akan haka masu yawa ne.

Wasu kuma sai shaidan ya sanyasu suke amfani da ayoyin Qur'anin don aiwatar da siddabaru, har wasunsu suke ganin ai tunda da Qur'ani suke amfani... Sun manta irin yadda suke jirkita rubutun Qur'anin kodai suyishi ta baya, ko kuma kuma su cakuda ayoyinsa ko kuma su rubutashi da najasa ko ajiyeshi a wajen najasa da wanin haka.
Idan mukace zamu ambaci abinda ke wakana a cikin lamura kuwa irinsu musabaka da yanda wasu musamman a zamanin nan suke rera Qur'anin to tabbas abubuwan fadar zasuyi yawa.

Wasu kuma daga mutane na wannan zamanin sai shaidan ya zuwar musu da wani tunani ta inda suke kudirta cewa abinda yafi dacewa shine a daina amfani da fassarar magabata a Qur'ani a rinka fassara wadda tayi dai dai da zamani.

Wanda ke karanta abubuwan da suke kai kawo tsakanin malamai, yan boko akida da yan dadi arna zaifi gane inda maganar ta dosa.

Inama ranakun sunada sarari da tabbas zanso alkamina yayi rubutu na ilmi akan littafin Allah da irin abubuwan da yake fuskanta a rayuwarmu ta yau.

Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu ikon binta.

Zamu dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba.

TARKON SHAIDAN (8)
Shaidan baya barin wata kafa face yayi amfani da ita don rufta mutum da batar dashi don haka kamar yadda ya batar da wasu ta hanyar sanya musu son zuciya a janibin littafin Allah to haka nan a bangaren hadisan ma'aiki ma ya kafa manyan tarkuna da babu mai kauce musu sai wanda Allah ya tseratar. A takaice zamu kawo wasu tarkunan nasa a gurguje.

Akwai wayanda Shaidan ya sanya musu tunanin cewa babu wani littafi wanda ake dogara dashi sai Qur'ani don haka su Qur'anin kadai suka yarda dashi babu ruwansu da hadisai... Sun manta hadisai sune abubuwan da suke bayanin Qur'anin domin kamar yadda Qur'ani yake wahayi haka shima hadisi yake wahayi... Domin Annabin da yayi maganar "baya furta son ransa duk abinda ya fada koya aiwatar to wahayi ne daga Allah". Wanda yayi wannan maganar a saukake sai kace masa ya kawo maka inda adadin raka'o'in salloli yazo a Qur'ani, ko kuma zikiran da ake a sallah cikin ruku'u da sujjada da sauransu.

Wasu kuma sai sukace duk hadisin da yayi magana akan wani al'amari na gaibu wanda babu shi a Qur'ani to basu yarda da shi ba. Don haka suke karyata azabar kabari, zuwan dujal, saukowar Annabi isah, shafar aljanu da sauransu.
Suma wayannan babu makawa sun bata bata mabayyani.

Wasu kuma sai Shaidan ya laqanta musu amfani da hadisai marasa inganchi ko kuma wayanda kwatakwata basu da madogara a littafan musulunchi, wasunsu ansan wayanda suka kirkirosu, kamar hadisan falaloli da zakaji ance wanda yayi abu kaza za'a bashi ladan Annabawa kaza da wasu masu irin wannan ma'anar wanda mai ido a ilmi yana ji yasan ba hadisi bane. Wasu hadisan ma ba'a san daga ina suke ba saidai ayita jin yawonsu a bakin gamagarin mutane.

Wasu kuma sai Shaidan ya bijiro musu da rashin fahimtar ma'anar hadisan saboda rashin karatu gaban malamai don haka sai su bata kuma su batar. wasunsu ma har hakan ya kaisu ga aibata magabata na kwarai.

Anan nake shawartar dalibai dasu lazimchi ilmin hadisi domin anan ne mutum zai gane littafai ingantattu na hadisi da wasunsu.

Ta fuskar malaman fiqhu kuwa sai shaidan yazo musu da wata siga ta kawar da kansu ga hadisi da Qur'ani, a gefe guda kuma sun maqalqalewa ra'ayin daya daga cikin malaman mazhaba ko wani cikin magabata. Maimakon su maqalewa maganar fiyayyen halitta sai suka maqalewa maganar malami cikin malamai. Wasunsu harma suna riya cewa abinda yazo cikin hadisai da Quran yayi karancin da dole sai anyi tawilin (sauya ma'anar) wasu abubuwa... Ko ga abinda ake gani kiri-kiri cikin hadisi sai suce ba haka ake nufi ba, wani abin dabam ake nufi. Wanda ya karanta littafai kamar Kitaabul Imaan na Ibn Taimiyya zai tsinci bayanai masu kyau akan wannan.

Malaman larabchi kuwa suma sai shaidan ya kwararo musu ta hanyoyi mabambanta domin wasunsu har suna tsammanin akwai gyare-gyare a cikin Qur'ani.

Abin lura!
Na takaita wayannan bayanan ne takaitawa saboda akwai inda nake so in sukwana.

Zan fadada bayanine akan wasu bangarori uku wanda kowanne zamu fadi irin yadda shaidan yaci galaba a kansu.
1. Masu da'awar Sunnah
2. Masu da'awar Sufanci
3. Masu da'awar Wayewa.

Kowanne cikin wayannan bangarori zaka iske akwai hanyoyin da shaidan yake bi don batar dasu tare da cewa a cikin kowacce cikin ambatattun akwai wayanda suka tsira daga wannan kaidi na shaidan saidai mun sani babu mai tsira dari bisa dari.

Tarkon Shaidan (9)
MASU DA'AWAR SUNNAH.
Daga ciki akwai wayanda shaidan ya saka musu gubar rashin ladabi wajen maganar data shafi Allah da Manzonsa (S.A.W). Kamar fadar sunan Ma'aiki (S.A.W) ba tare da girmamawa ba ko saita sauti.

Wasu kuma sai Shaidan ya shayar dasu gubar rashin ganin girman na gaba dasu daga malamai da iyaye. Ta inda zaka iske babu ladabi da tarbiyya cikin yanayin da suke yiwa magabatansu raddi komai girman hidimar da mutum yayiwa addini kuwa. 

Wasu kuma rashin kyautata mu'amala tsakaninsu da mutane, kai kace zabar wayanda zasu kula suke yi. Su kuwa musulmai yan'uwan junane.

Wasu kuma sai shaidan ya shayar dasu gubar kafirta juna a bisa wani sabani wanda bai kai ya kawo ba. Wani abinda zai daure maka kai wani sabanin ma dukansu abu guda suke nufi amma banbancin lafazi da kuma kin fahimtar juna yasa kaga anata tayarda jijiyar wuyar.
Misali mas'alar sanin gaibu ga Annabi Muhammad (S.A.W). Shi wannan yana cewa Annabi bai san gaibuba, saboda babu wanda yasan gaibu sai Allah. Shi kuma wancan yana cewa Annabi yasan gaibu saboda Allah ya sanar dashi.
To anan idan kayi kallo bida idon basira zakaga abinda duka su biyun suka yarda dashi shine. Allah ya san gaibu, a cikin gaibunsa ya sanar da Annabi. 
Kaga kenan kusan abu guda suke nufi. Wanda idan ka hadeshi zai zama *Annabi yasan gaibun da Allah ya sanar da shi*. Kenan wanda Allah bai sanar dashi ba bai sani ba!

To rashin fahimtar me kowane sashe yake kai shi yake kawo mafi girman rabuwar kai.

A fuskar Addini shaidan yana amfani da abubuwa guda biyu wajen batar da mutane.
1. Kodai ya sanyasu su wuce gona da iri
2. Ko kuma suyi sako-sako.

To maganar gaskiya, masu da'awar sunnah da dama (ba duka ba) zaka iske suna sako sako da abinda yake bangaren girmamawa, kamar yadda suke da tsauri a bangaren aqida. Wanda tsauri a bangaren aqidar shiya janyo wannan sako-sakon da suke dashi a wannan bangaren.
Wanda idan muka koma bangaren magabata, duk da tsaurinsu a bangaren aqida amma hakan bai sanyasu sun zubar da girmamawa ga na gabansu ba.

Akwai wani dana taba halartar karatunsa, tun a yarinta kusan shekaru shida baya, tun a yanayin yadda yake ambaton sunan Annabi kamar sunan sauran mutane zuciyata ta kasa samun nutsuwa. ban sake komawa ba.

Wayanda suka tsiran daga wayannan abubuwan daba fada suma basu gama kufcewa ba. 



Allah muke roko daya karemu daga fadawa tarkon Shaidan.
Ameen

TARKON SHAIDAN (10)
MASU DA'AWAR SUFANCI.
Wayannan wasu mutanena da suka sadaukar da rayuwarsu wajen bautawa Allah harma suka bar duk wani abin jin dadin rayuwa suka kauracewa mutane... Wannan sufayen farko kenan...

Kwana a tashi sai shaidan ya rinka shigo musu da abubuwa kala kala don sauke su daga kan turbar da suke so. Kamar yadda zamu fado wasu a takaice.

Tunda yasan burinsu shine bauta ga Allah to sai ya shigo musu da wasu nau'ika na bauta wayanda Allah bai shar'anta ba domin bautat tasu ta zama aikin banza.

Wasunsu saiya sanyasu suka haramtawa kansu da dama daga abubuwan da Allah ya haramta ba don wani dalili ba sai don kawai tunanin hakan karuwar kusancine zuwa ga Allah... Wasunsu suka kauracewa aure, wasu suka kauracewa saka kaya masu kyau, wasunsu suka kauracewa cin abinci mai dadi... 

Wata hanya daya farar musu da ita itace kishi, kamar yadda mata suke kishi to haka zaka iske wannan shehun yana kishi da wancan shehun wanda hakan yana haifarda matsaloli bama ga iyakar shehunan ba har izuwa ga mabiyansu.

Wasu lokutan Shaidan yana iya fitowa wani malami ko mabiyin sufanci a wata siffa mai rikitarwa, ko a siffar wani mamaci daga cikin malamansu don kawai ya batar dashi. Kai wani lokacin ma a mafarki yake zuwar musu ya kawo musu rudani. Don haka zakaji wasunsu suna fadar maganganu kai saika dauka babu lissafi ko karya ce kawai suke fada nan kuwa shaidanine suka hadu dashi kamar mai cewa shehu wane yazo ya daukeshi a fuka-fuki, ko Allah ya halatta masa abinda yake na haramun.

Hakanan shaidan idan ya kula babban burin mutum shine samuwar karaama irin karamar waliyyai to anan ma zaiyita bijiro masa da abubuwa da sukai kama da karamar kamar tafiya a saman ruwa, tashi sama akan dadduma da wanin haka.

Daya daga cikin manyan malaman musulunchi an taba zuwa an bashi labarin cewa akwai wasu wayanda suke hawa dadduma suke yawo a iska suna sanar da mutane cewa su waliyyan Allah ne.
Sai wannan malami yace duk sanda suka fito ayi masa magana. Aikuwa sun fito suna shawagi akan iska harde bida daddumarsu, sai aka gaya masa, yana fitowa sai suka fado kasa. Aka tambayeshi ya akai hakan ta faru?
Sai yace ai shaidan ne yake daukarsu a wannan daddumar, Annabi kuwa yace indai aka biya ayatul kursiyyu a waje to duk shaidanun wajen suna guduwa shine na biyata...

Akwai bambamchi tsakanin karaamar waliyyan Allah da kuma abinda shaidanu suke aiwatarwa. Idan da tsawon rai inada wani tsohon rubutu wanda na fadada bayanai sosai akan wannan gabar.

Daga cikinsu kuma akwai wayanda ya shagaltar dasu daga abinda yake daga wajen Annabi suka sake shi suka kama wanda yazo daga wajen wani bawan Allah tare da kudurce cewa wannan wanda suke rike din yafi na Annabi falala.

Wasunsu kuma sai ya zurmasu cikin wasu aqidu na majusawa da kirista kamar masu kudurta komai Allah ne ko wahdatul wujud da wanin haka. 

Abin fadar a wannan gabar yanada yawa.

TARKON SHAIDAN (11)
Masu da'awar wayewa...
Su kuma wayannan sai Shaidan ya cire musu ganin girman addinin a zukatansu harma suke wasu tunane tunane marasa tushe.

Wasunsu suna karyata duk abinda ilmin kimiyya bai tabbatar da shi ba, sun makance da ganin irin kimiyyar da take cikin Qur'ani. Su a wajensu ma'auni na farko shine tunanin mutanen yamma don haka abinda yake na musulunchi da yazo dai-dai da fahimtar turawan yamma zasu karbe shi hannu bibbiyu abinda yaci karo da fahimtarsu kuma saisu wofantar dashi.

Daga cikinsu akwai masu musanta labarai na gaibu da Annabin rahama ya bada labari kamar zuwan dujal, Ya'ajuj da Ma'ajuj, azabar kabari da wanin haka.

Daga cikinsu masu musanta mu'ujizozin Annabi (S.A.W) kona sauran Annabawa da suka zo cikin hadisai.

Daga cikinsu akwai masu ganin shari'ar musulunchi kauyanchi ne kuma zamaninta ya wuce don haka dole a sauya ta ta yanda zatai dai dai da zamani. Ko kasan zamanin a wajensu me suke nufi? Wayewar turawan yamma. Sun manta da cewa ko nan Africa tun kafin zuwan Mungo Park da kusan shekaru dari biyar munada wayewarmu da karatunmu... Saidai kash kawunansu basa daukar komai sai abinda turawan yamma suka haska musu.

Wasunsu suna jin kunyar nuna musuluncinsu saboda kada ace musu kauyawa ko ace basu waye ba. Tare da cewa sunsan musulunchin shine dai-dai kuma a turbar gaskiya yake saidai neman yardar turawa yasa sun rufe ido.

Wasunsu kuma har a cikin zukatansu sun yarda abinda turawan suke shine dai dai don haka sai suke kokarin modernizing din musulunchi...

Wasunsu kuma sai kai tsaye suka bar addinin suka koma tafiyar nan ta atheism sun manta hatta malaman kimiyyar sun sallama sun yarda da samuwar Allah... Kuma sun yarda da cewa shike halitta da jujjuya al'amura.

Idan akwai tsawon rai insha Allah zamu yi kokarin yin rubutu koda takaitacce ne akan ababen mamaki dangane da musulunchi da kimiyyi.

Allah muke roko daya shiryar damu zuwa tafarki madaidaichi.

Sai kuma a rubutu na gaba kuma na karshe wanda zamuji mafi girman makaman da bawa zai rike don tserewa tarkon Shaidan.


TARKON SHAIDAN (12)
Mafi girman makaman da dan'adam zai yaki shaidan dasu suna da yawa amma mafi cikarsu shine ambaton Allah.

★ Yawaita ambaton Allah yana wanke zuciya kuma yana sanya rabon shaidan a zuciyar bawa ya zama dan kadan.

★ Yarda da cewa Manzon tsira Muhammad (S.A.W) yafi kowa a wajen Allah don haka dukkanin shiriyi, bauta da sauran al'amuran rayuwa da sukazo daga gareshi sune mafi girman abubuwan da zasu kusanta mutum da Allah.

★ Sanin cewa duk lokacin da mutum ya bari shaidan yayi galaba a kansa to hakika shaidan din zaiyi amfani da wannan galabar da yayi don sake yin wata galabar domin babban burinsa shine yaga ya kautar da dan'adam daga hanya.

★ Bayan shaidan ya sanya mutum ya fandare ko yayi zunubi a boye to tabbas zaiyita kokari wajen tonawa wannan mutum asiri domin kuwa kiyayyar dake tsakanin shaidan da bayi bamai gushewa bace.

★ Rashin yin kowace bauta sai wadda ta samo asali daga Annabin rahama (S.A.W).

Anan muka kawo karshen wannan shiri mai albarka. Allah muke roko  daya amfanemu da abinda muka karanta.

Abinda yake na dai dai daga Allah ne, wanda kuma yake ma kuskure to daga nine kuma daga shaidan ne Iblis karkatacce. Allah muke roko da yayi mana katangar karfe daga gare shi.

Subhanakallahumma rabbana wabi hamdika, nash-hadu anla ilaha illa anta, nastagfiruka wa natubu ilaika.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy
21/01/1443 A.H
30/08/2021 M

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.