ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

👉🏼Lokacin da akace musulmi ana nufin wani mutum wanda ya mika wuyansa ga Allah, ya hakura da son zuciyarsa, kuma ya zabi yayi rayuwa yadda musulunchi ya tsara masa.

👉🏼Idan akace Musulunchi, to wani addinine wanda bai bar komai ba saida yayi magana akansa, tun daga kan bautar Allah har zuwa shiga bandaki, cin abinci, kallon madubi, taje kai da kuma yanayin tsarin kwalliya.

👉🏼In kuwa hakane musulmi yana da kyau ya zama musulmi, kuma yana da kyau ya zama mai bin koyarwa addinin musulunchin.

Bana mantawa da wani umarni da ubangiji ya bayar cewa _A shiga musulunchi gaba daya, kada abi hanyoyin shaidan_. Wato dukkanin tsarin rayuwa ya zama yadda Allah ya tsara bisa koyarwar sunnar masoyi (S.A.W) ba tare da an karkace anbi hanyar shaidanu ba.

👉🏼A watan azumi ana kokari mutuka wajen bauta, da kuma komawa ga Allah, saidai kuma azumi yana wucewa sai wasu abubuwan sun kunno kai wayanda suke nuna cewa mutane lambo sukai da azumin.

Mai zato ma sai yayi zaton Allah wanda ake bautawa a watan ramadan ba shine wanda ake bautawa a shawwal da sauran watanni ba.

Insha Allah zamu tattauna akan mas'alolin taku bayan taku.

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU 0⃣1⃣

Wata taje England tayi karatu, data dawo sai aka tambayeta *What is your name?* saita fara zazzaro ido saboda bata san me zata ce ba, don dai kawai taje karatun ne amma fa bata koyo komai ba....
Wani zaiji mamaki, amma ba abin mamaki bane, domin wannan shine misalin wanda watan azumi ya kama akai azumi dashi, wataqila ma dashi akai tsayuwar dare, amma bayan wucewar azumin sai ya bishi da ayyulan barna.... Bai fa'idantu da makasudin azumin ba....

Babu shakka kowa yasan cewa watan azumi watane na ibada, kamar yadda sauran watannin suke. Kai a takaice wata hikima ta Allah ne daya sanya wannan wata watan azumi ga musulman duniya baki daya.

Misali ko abin hawa ko gidan da kake zauna a ciki, ko kuma dakin da kake zama kake kwana a ciki, yana da bukatar lokaci zuwa lokaci ka rinka gyara shi, idan abin hawa ne kakaishi a duba lafiyarsa, idan gidane ka gyara inda ya lalace, idan zuba yakeyi kasake rufin gidan ko ayi masa faci, da dai sauran ayyuka.

To shima watan azumi haka yake, domin Allah daya shar'antashi a karshe saiyace ...watakila kwa samu tsoron Allah......

Kamar yadda Allah ya shar'anta ibada a azumin ramadan kuma ya rattaba dokokin azumin, hakanan shine ya shar'anta idi a watan shawwal kuma bai barshi kara-zube ba har saida ya shar'anta abubuwan da ya dace ayi a kwanankin idin.

Babu wani abu na haram da Allah yake halattawa kawai don zuwan sallar idi. Tayaya zai halatta kazanta, sa'bo, alfasha da shirme alhalin shi mai tsarki ne, mai girma, mai kuma izza?

Allah mai tsarki ne, baya karba sai mai tsarki.

Shi imani abinda ya tabbata ne a zuciya, kuma ayyuka suka gaskata shi.

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU 0⃣2⃣

_Dukkaninku makiwata ne, kuma kowannenku za'a tambayeshi abinda ya kiwata_, Mai gida za'a tambayeka akan yadda ka tafi da rayuwar matanka da yayanka, hakanan mata za'a tambayeta akan yayan data haifa, kai a matsayinka na babba mai kanne kaima za'a tambayeka dangane da kiwon kannenka.

Saidai kash wasu mutanen basu da dabara ka duba kaga yadda wasu suke kiwon awaki a waje mai kyau mai tsafta, amma kuma maimakon su basu abinci mai gina jiki, saisu rinka basu abinci mai guba, mai cutarwa, mai bawa barawo saurin damar sacesu ko awon gaba dasu koma yi musu lalata.
Kun fahimchi me nake nufi?

Zaka iske uwa da uba sune kan gaba wajen koyawa yaransu shigar banza tun yarinya tana karama har zuwa girmanta, ko ina taqawar da aka samu a azumin? Ko kuwa dai dakon yunwa da kishirwa kawai akai?
Allah ya kyauta!

Shi yaro yana tasowa ne da dabi'a wadda aka ginashi akai, kamar yadda tun suna yara kuka sakasu a makarantar boko don kunaso su taso su zama yan boko, to haka tun suna yaran za'a rinka yi musu shiga ta musulunchi don su girma su zama musulmai cikakku.

Tabbas wajibine kowane uba, uwa da yayye su kula da tarbiyyar na kasansu.

Sai kaga an karawa yarinya gashi, an saka mata matsatstsun kaya waida sunan ai ita karama ce, kai saika rantse kace iyayen ba sune masu jin radio wadda kullum sai kaji anyi maganar fyade ba, ko kuma kayi zaton iyayen ba sune masu wuni a kafar facebook ko WhatsApp ba, suna jin duk abinda ke wakana amma tsabar zaluntar kansu da yayansu saisu tirsasawa yayansu su cutar dasu.

Sau nawa yarinya zatayi kwalliya tayi shiga mara kyau, amma maimakon a hanata a gidansu sai kaji ance *Oh, su wance an zama budurwa*, ko kuma kaji ance *kaii rangadi wannan yarinya za'ai tashen kyau*.
Allah ya kiyaye mana zuri'a.

Sai anzo ana bada tarihin jahiliyya suyita ganin ba'a kyautaba lokacin da ake binne ya'ya' mata... Alhalin yanzu su abinda suke yafi binne yaya matan illah.....

Wani zaice menene dalilin fadar hakan?

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU 0⃣3⃣

Lokacinda kake da dabba sai kake kokarin rabuwa da ita saika yankata, ko kuma ka kaita zuwa ga abokan adawarta suka yagalgalata sukai mata kaca-kaca ba tare datayi maka laifin komai ba... To tabbas baka kyauta ba.

Saidai kasheta kai tsaye yafi karancin laifi akan wahal da ita da kuma mikata wajen abokan adawarta, domin yin hakan yana nuna tsantsar rashin tausayi.

Wannan shine misalin iyayen zamanin jahiliyya dana yanzu.

Iyayen zamanin jahiliyya suna yanke rayuwar yayansu lokaci guda, su kuwa iyayen wannan lokaci sukan bi doguwar hanya don lalata rayuwar yayansu, sai kaga sun dabi'anceta ta hanyar da idan ta girma zata rasa kunya, kamun kai, mutumchi da sanin yakamata.

Kamar yadda muke fada yayanmu bawai iyakar hakkin ci-da-shansu ne kawai a kanmu ba, bari ma dai hakkin tarbiyya yana daga cikin manyan hakkoki.

Don haka muke jan hankalin iyaye dasu rinka sanin irin kayan da yayansu zasu rinka sakawa, susan wanne irin film zasu rinka kalla, susan wanne tashoshi zasu kalla, susan wanne irin abokai suke kulawa tun suna yara... Sannan susan wanne irin wasa suke.

Ko kasa abin har yakai yara da kansu suna child-abuse din kansu, wannan kuwa an gani  ba sau daya ba, ba sau biyu ba.

Kuma duk laifukan suna komawa gareku iyaye.

(Akwai rubutu da zamuyi akan tarbiyyar yara nan bada jimawa ba insha Allah.)

Gareku Yammata Adon gari.
Nikam da in zama adon gari gwara na zama adon addini. Ko banza dai da in burge wani katon kawai, gwara na burge Allah da manzonsa, don haka shigar da suka yardar mini inyita ita zanyi ran sallah, a cewar wata matashiyar budurwa.

Kafin mu fadada bayani mata ga tambaya.
1. Shin ta dalilin yawan masu karya doka a cikinku, Allah zai sauya shari'ar musulunchi ne?

2. Shin saboda yawan masu shigar banza Allah zai sauya sakon da Annabinsa ya kawo ne?

3. Shin wanne yafi dacewa ki burge, Annabin rahama ko kuma gardin kan hanya?

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU 0⃣4⃣

يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك و نساء المؤمنين يدنين عليهنّ من جلابيبهنّ ذلك أدنى أن يعرفنا فلا يؤذين وكان الله غفورا رحيما...

Allah subhanahu wata'ala da kansa tsarki ya tabbata a gareshi yake umartar Annabi da cewa ya umarci matansa, yayansa da matayen muminai dasu suturce jikinsu da sutura irin wadda musulunchi ya yarda da ita.

Wannan ayar da takwarorinta na suratun nur sun bayyana karara cewa haramun ne mace ta bayyana wani ado na jikinta a waje ko a gurin wanda ba muharrami ba sai abinda aka togace ko kuma wani dalili ya bada damar togacewar.

Kuma kakaf malaman duniya babu wanda yace ai wannan ayar bata aiki ranakun sallah, ko kuma wannan ayar da lokacin sanyi take aiki, bari ma dai abinda yafi shine afi kiyayewa a ranakun sallah saboda aukuwar fitina a wannan lokaci yafi samun gurin zama.

Sauda dama ina mutukar jin mamakin ganin yadda da yawan iyaye, kawaye da kuma gama-garin mutane suke goyon bayan barna da alfasha da ake a ranakun sallah.

إن الذين يحبون أن تشيع الفاحشة في الذين آمنوا لهم عذاب أليم في الدنيا والآخرة و الله يعلم و أنتم لا تعلمون....
Tofa kaji ubangijin sammai da kassai ya bayyana cewa  masu son yaduwar alfasha akwai azaba mai radadi a garesu a duniya da lahira.

Azaba mai radadi a duniya yana nufin rashin nutsuwar zuciya, rashin kwanciyar hankali, rashin jin dadi da kuma haduwa da fitintunu.

Alal misali ka duba kaga abubuwan da bayyana tsiraichi yake haifarwa, zaka iske fitintinu ne da yawa wayanda Allah ne kawai yasan iyakarsu.

Alhamdulillah Ilmi ya yawaita idan akace shigar da musulunchi ta yarda da ita kowa yasan irin wadda ake nufi. Hakanan idan akace turaren daya kamata musulmi su saka kowa yasan abinda ake nufi, kuma wannene na maza wannene na mata.

Allah yayiwa wani daga magabata rahama wanda yake cewa "MADALLA DA KWALLIYAR MAZA KAMSHI WANDA BASHI DA KALA, MADALLA DA KWALLIYAR MATA KALA WADDA BATA DA KAMSHI."

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU 0⃣5⃣

و إنك لعلى خلق عظيم.....

Da aka tambayi Nana Aisha dangane da halayen Annabi (S.A.W), batai kasa a gwiwa ba saidata kwatantashi da Qur'ani.
Babu misali wanda yakai wannan, wanda yasan menene Qur'ani, kuma maganar wanene bazai musanta hakan ba.

An turo Annabi don ya cike kyawawan halaye, kuma ya nunawa mutane kyawawan dabi'u, sa'annan ya kore musu munanan dabi'u.

Don haka zaka iske Annabi yana da kunya, kuma shari'ar dayazo da ita mai kunya ce, yayinda kuma zaka ga baya goyon bayan rashin kunya hasalima dai yayi hannun riga da marasa kunya, dashi da masoyansa da shari'ar da yazo da ita........

Lokacin da karancin suturce jiki ya yawaita, sanya kayan da suka dace ya qaranta, kunya ta tashi sama, yayinda rashin kunya ya sakko kasa ya baibaye halittu sai wasu suke kasa bambance ma shin wacce shiga ce take nuna tsiraichi.... Sun manta tun tuni ake gaya musu a islamiyya.....

Ku sani ya yan'uwa musulmi, hakika suturce al'aura a ranakun sallah wajibi ne, kamar yadda yake a sauran ranakun... Duba suratun nur aya ta 31.

A cikin ayar Zaki iske Allah ya hana bayyana ado sai wanda ya bayyana, wannan kuwa ana nufin wanda babu makawa saiya bayyana kamar tufafi tunda dai bazaki saka tsummokara ki rinka yawo dasu ba.

Saidai akwai bambanci anan Allah cewa yayi
إلا ما ظهر منها
Sai abinda ya bayyana daga adon.
Ba cewa yayi
إلا ما أظهرن منها ba....
Wato baice sai abinda su matan suka bayyana daga adon ba.

Ko kunsan Annabi ya tsinewa mace mai nuna tsiraicinta?
Ko kunsan wadda duk ta sake tsinuwar Annabi ta hau kanta inba Allah ne ya sota da rahama ta tuba ba shikenan ta tafi...... Sai labari.

Shin kina ganin cewa babu komai bari da gangan kiyi abinda kema tsinuwar Annabin zata hau kanki, idan yaso daga baya kya tuba? Bakya tunanin zaki mutu kafin ki tuban?
Ko kina da tabbacin za'a karbi tuban?

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU0⃣6⃣

Kasancewar zaiyi wahala ka samu wanda baisan yadda musulunchi yake son mata da maza suyi shigarsu ba, zamu tsagaita da bayanin yanayin yadda ake son shigar ta kasance, domin wanda kaga yayi shigar da bata dace ba a kasar hausa to kai tsaye zakaci _ya sani ya take_, irin wayannan kuma sune wayanda aka riski maganar Annabawan farko akansu cewa *Idan baka jin kunya, to ka aikata abinda kake so*...

Bayan bangaren sutura zamu duba abubuwa da dama da ake na zubar da kima, mutunchi da raini ga abinda addini yazo dashi, na daga karya dokokin Allah a ranakun sallah.

Ranakun ci da sha da ambaton Allah da hutun jiki, saisu koma ranakun shaye-shaye, raye-raye da wahalar da jiki ta hanyar sabawa Allah.

Saika iske abinda ake son aikatawar a ranakun sallah yayi gabas su kuma sunyi yamma.... Kai abinda yayi gabas da wanda yayi yamma ma zasu iya haduwa tunda duniyar Allah mulmulata yayi... Saidai kace shari'a tayi sama su sunyi kasa.....

Zaka iske kato ya dauki katuwa sun tafi kallon gardawa, ko ka iske shashasha ya dauki ballagaza sun tafi kallon dabbobi... Da wanin haka...

Kato da katuwa kaga sun zage sunata tiqar rawa wai da sunan murnar sallah. Ko a ina ake murnar a haka?

Tsantsar tsabagen tsagwaron tsabar tsaurin ido da rashin kunya shine zai sanya mace ta fito bainar jama'a tana rawa.

Don wake-wake da kade-kade tsakaninsu su-i-su mata wannan anyi rangwame. Tare da sharadai da aka gindaya akai.

Ba wajen fadada bayani bane nan, abin lura anan shine rashin ingancin hakan, ga mai son bayani saiya duba littafin _Istiqaama_ na ibn taymiyya, ko littafin dalibinsa ibn qayyim _igathatul lahfan_.

Yanzu da zaka kai motarka gareji ayi kwana 29 ko 30 anayi mata aiki kuma ka fitar da makudan kudade ta inda kake bada sama da abinda masu gyaran suke bukata don motarka ta gyaru... Bayan an dawo maka da ita kana kunnuta saika iske matsalolinta sunanan, harma da wasu matsalolin wayanda babu su asali.
Shin motarka ta gyaru ko kuwa asarar kudi kawai kayi?

Misalin masu azumi kenan da suke barin azuminsu a ranakun sallah.

Allah ya shiryar damu, ya albarkaci rayuwarmu.

Nan zamu kawo karshen rubutun.

Tare da ni
Naseeb Abu Umar Alkanawy.
Tare da malama
Shifaa khamis Adam.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.