MAFI SOYUWAR MUTANE A WAJEN ALLAH!

*MAFI SOYUWAR MUTANE A WAJEN ALLAH*.

Hadisi daga Ibn Umar (R.A), Masoyi (S.A.W) yana cewa _“Mafi soyuwar mutane a wajen Allah shine wanda yafi amfanar da mutane”_.
*Silsilat-Assahiha* na Albaniy 906

Abu Umar Alkanawy yace 
“Idan har mafi soyuwar halittu a wajen Allah sune mutane, to tabbas mafi soyuwar mutane a wajen Allah sune masu taimakon mutane. Ko ba'a fito fili an gaya maka ba zaka gane idan kayi la'akari da wasu abubuwa kamar haka.

★ Allah yana ninka sakayyar alheri cikin ayyukan da suke na taimakon bayinsa. Misali, wanda yayewa wani bakin ciki Allah zai yaye masa nasa bakin cikin anan duniya da lahira. Wanda yaji qan wayanda suke kasa, wanda yake sama zaiji kansa. Wanda ya ciyar da wani shima Allah zai ciyar dashi tare da shigar dashi Aljanna. Wanda ya bawa wani dama ya rinqa tatsar nonon dabbarsa don yasha (koda akuyace) Allah zai shigar dashi Aljanna. Wanda ya dauke dutse daga kan hanya ko wani abu mai cutarwa, Allah zai shigar dashi Aljanna.

★ Allah ya jingina sababin karbar addu'ar bayinsa ko aikinsu cikin taimakon bayinsa misali. Yin tawassali da wani aikin taimako ga bayi da kayi abin karba ne. Yayin rashin lafiya da ake bukatar sauki, sai Allah ya sanya sadaka tana daga cikin sabubba na samuwar lafiya. Da wasunsu.

★ Allah ya fada idan yaso mutum da alheri zaiyi shela mutane da mala'iku su soshi. Abin sani kuwa mafi soyuwar mutum a wajen mutane shine wanda mutane suke amfana dashi.

★ Saboda Allah yana son masu amfanar da mutane saiya hukunta cewa wanda yayi umarni da kyakkyawan aiki, kamar shima yayi aikin ne. Misali, wanda ya umarci mutane da yin wani kyakkyawan aiki, shima za'a rubuta masa ladan wannan aiki.

Mu lura da kyau, Annabi Muhammad shine mafi soyuwar Annabawa a wajen Allah don haka zaka iske anfi amfanuwa dashi akan sauran Annabawa, hakanan mutanen da suka amfanu dashi sunfi mutanen da suka amfanu da sauran Annabawa yawa. *Babu wani bigire da yake sanya Allah yaso bawansa, face ka iske shuguba jagaba malamin sahabbai (S.A.W) yayi fintinkau a bigiren*

A takaice ba don abin fada ya qare ba zance.... Mafi soyuwar shugaba shine wanda ya amfani talakawansa, mafi soyuwar malami shine wanda ya amfanar da mutane ta hanyar cire son zuciya da dorasu a hanyar data dace, mafi soyuwar malaman makarantun zamani shine wanda ya amfanar da dalibai bai cutar dasu ba, hakanan mafi soyuwar dan social media shine wanda yake amfanar da mutane ta fuskar gyara kuskure, tunatarwa da kuma bada shawarwari a lokacin bukatar hakan.

Alhamdulillah

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy
13/8/2020

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.