MANYAN GOBE.... CI GABA KO CI BAYA?

..... Akwalar motar ta sukwano akan lalatacciyar fasashshiyar kwalta mai ramuka a dama da hauni wayanda yanayin damuna yasa suke cike da gurbataccen ruwa wanda ya jirkita sakamakon cakuduwa da ruwan toshashshiyar kwatar da shara ta toshe gami da tare hanyar da ruwa ya dace yabi.....

Motar, an mata lodi da kaya wayanda sunfi karfinta.... Kujerun baya an ciresu an cakudasu da kayan da akai lodinsu, mazauninsu shima an makare shi da wasu kayayyakin, kan motar kuwa gani zakai kamar gashin wata mata mai wadatar gashi yayinda ta tsefeshi ta barshi a tsaitsaye...

Wasu gungun yara da suke aikace-aikace a gefen titin wasu suna wanke yalo, dabino, goba wasu kuma mangwaro, suna ganin wannan motar ta sukwano da yawansu suka bar aikin da suke suka tsaye a gefen kwaltar suna fadin "Kiyaye..."  

Direban motar wanda yake takure matuka saboda su biyune a kujerar tasa ya murtuke fuska gami da yiwa yaran muzurai.... 

"Kiyaye..." Wasu yaran suka kuma firtawa suna biye da motar da gudu kamar zasu kwaci wani abu.
Wani yaro da alamu ya gaji da bin motar sai kawai yaci birki, yayinda wani yaro ya kara kwallawa yace "kiyaye..." Gajiyayyen yaron yace "in ya bayar..."

Wane da yake kan kujerar mai zaman banza wanda shima a takure yake saboda su biyu ne yayi namijin yunkuri ya zaro alewa gudu uku daga aljihunsa, domin a wannan lokacin yara uku ne biye dasu ragowar duk sun saduda sun koma wajen aikinsu....

Alawowin suka taho suna keta iska suna jujjuyawa ledar da aka rufesu tana kyalkyali a cikin matashin hasken rana, alawowin suka dira a dandaryar kasa......

Bisa ga mamakina maimakon wayannan yaran su nutsu kowa ya dauki guda daya amma sai kokawa ta barke a tsakaninsu kowa yana burin shifa saiya samu abinda yafi na dan uwansa koda kuwa dan uwansa zai rasa.

Me kake tunani akan wayannan yara da muke tunanin sune manyan gobe kuma masu iko a wannan kasar?

Rubutawa
Naseeb Alkanawy
7th August 2020

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.