JAYAYYA DA ALFAHARI BA SHI NE ILMI BA

```MU KULA!``` 

Yawan surutu, yawan jayayya, yawan aibata malamai, ƙwaƙulo kura-kuran malamai, yawan hayaniya, yawan zuwa da wani abu wanda ya saɓawa wanda ake kai da kuma uwa uba tutiya da tinƙaho ba su ne alamun ilmi ba.

Da a ce yawan jayayya da binciken aibin mutane shi ne ilmi da sahabbai sun fi kowa jayayya... Amma sai muka samu su ne mafi iya rufa asirin mutane da kuma kawar da kai daga jayayya.

Ƙasa ba ta taɓa ɗaukar wani mutum mai kawar da kai da yiwa mutane uzuri sama da Annabi (S.A.W) ba. Kuma mun sani shi ne mafi cikar ilmi na addini da rayuwa.

Don haka sai mu gane cewa addini ba hayaniya ko hauragiya ba ne, addini nutsuwa ne, sanin yakamata da kuma tarbiyya. Wannan kuwa shi mu ke kira ilmi.

Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.