WAIWAYE ADON TAFIYA 16 - 20

WAIWAYE ADON TAFIYA 16
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)

Munji cewa Sahabi Umar ibn Khaddab (R.A) ya musulunta, kuma muka ambaci cewa Annabin tsira da Aminchi ne yayi addu'ar cewa Allah ya karfafi addinin musulunchi da Umar...

Wannan shine abinda ya tabbata a ruwayoyi wayanda na riska, saidai guda daya wadda Nana Aishatu uwar muminai take cewa abinda ya tabbata shine Annabi yace “Allah ka daukaka umar da addinin musulunchi...” dalilinta kuwa shine, tace “Shi musulunchi wani baya iya daukaka shi, saidai shi ya daukaka mutum.” Wannan fahimtarta ce. 
Allah ne mafi sani.


Kafirai da sukaga musulunchi yanata daukaka kuma sukaga duk matakin daya kamata su dauka sun dauka amma abu yaki ci yaki cinyewa sai suka sauya shawara. 

Suka nemi a basu Annabi, a sallama musu shi, su kasheshi, zasu musanya shi da wani daga cikinsu, sannan zasu biya dukiya mai tarin yawa...
Abu Dalib da yaji bukatarsu sai yace amma gaskiya wannan abu nasu ya bashi mamaki, wannan wanne irin shirme ne, ya basu dansa su kashe, su kuma su bashi nasu dan ya rayashi, ya ciyar da shi ya kuma tufatar dashi?

Wannan amsa ta Abu Dalib ta fusatasu matuka, don haka sai suka koma suka sake zama, a karshe suka fitar da wata takarda ta zalunchi cewa zasu yanke alaqa da Banu Hashim da Banu Abdulmuddalib, zasu daina saida musu ko a siya a wajensu, sannan za'a daina shiga al'amuransu na yau da kullum. Wannan kuwa hukuncin ya hade musulmansu da kafiransu. Saidai banda Abi lahab, domin shi ba'a sanyashi cikin wannan dokar ba domin shi yana fito da tsana da kiyayyar ga Ma'aiki a fili.  
Saida ya zamana Annabi da sauran yan'uwansa basa samun abinci, ya zamana Banu Hashim da Banu Muddalib suna cin ganyen bishiya saboda yunwa...
(Siratun Nabiyyi, Shaikh Musa Ibn Rashid Al'azimiy Sh.17)

A wannan rintsi matar Abbas dan gidan Abdulmuddalib (R.A) tana da juna biyu, amma hakan bai sanya sun rangwanta mata ba, wannan wahala da akesha harda ita, amma sai tayi hakuri, ai kuwa sai Allah yayi mata sakayya mai girma inda ana cikin wannan matsi, takura da wahala ta haifi santalelen jariri, aka rada masa suna Abdallah... Ko kasan wanene? 
Shine Abdullahi Ibn Abbas, wanda kaf musulman duniya sun yarda a sanin tafsiri shine madakata. 
Allahu Akbar

Al'amarin kafirai kuwa, labari ya riskesu cewar Hijirar da sahabbai sukai zuwa Habasha sun samu nasara, domin suna can cikin kwanciyar hankali. Don haka sai kafirai suka tara dukiya suka tashi wayayyu biyu daga cikinsu; Amru Bn Ass da Abdullah Bn Rabii'a, suka turasu da dukiya a matsayin kyauta ga sarkin Habasha Najashi.

Bayan an musu iso sun shiga gareshi, sai suka gabatar da kansu gami da gaya masa cewa akwai yan'uwansu na jini da suka gudo kasarsa, sunzo da wani sabon addini wanda ba irin nasu ba, kuma ba irin na Najashi din ba. Don haka shuwagabanninsu wayanda wayannan masu hijirar yayansu ne da kannensu suka turo su don ya damka musu su, su mayar dasu zuwa ga danginsu....

Da jin wannan bayani sai fadawan Najashi suka goyi baya suka ce tabbas abinda ya kamata ayi kenan, amma shi Najashi sai ya bukaci yaji ta bakin bangaren masu hijira. Don haka suma sai aka bijiro dasu aka bukaci suyi bayani.
Ja'afar wanda shine shugaba shine ya fara jawabi, ya faro tun daga kan duhun da suke ciki a jahiliyya har zuwa lokacin da hasken musulunchi yazo musu, da kuma irin kyawawan dabi'un da yake koyar dasu. 

Najashi, saiya bukaci yaji wani abu daga cikin sakon da Manzon Allah yazo dashi. Aikuwa sai Sahabi Ja'afar ya fara rero masa suratul maryam. Najashi yayita kuka har saida gemunsa ya jike sharkaf da hawaye. Sannan yace “Tabbas wannan (Qur'ani)  da sakon Isah (A.S) daga waje guda suke.” kuma yaki sallamasu ga su Amru.

Ai kuwa sai gwiwar su Amru tayi sanyi, amma washe garin ranar sai gashi ya dawo fadar Najashi yana kokarin aibata musulmai a idon Najashin. Amru bn Ass, wannan duk kafin ya musulunta ne, saiya gayawa Najashi cewa musulmai suna fadar wata babbar magana akan Annabi Isah dan Maryama.
Nan ma dai sai Najashi yasa aka kirawo su, sunata murnar samun aminchi kawai sai sukaji kira. Take hankalinsu ya tashi, amma sai suka amsa kiran. 
Najashi ya tambayesu me zasu ce game da isah dan maryam? Sai suka bada amsa da cewa Bawan Allah ne kuma manzonsa ne, dan Maryama wadda namiji bai taba shafarta ba....
Da Najashi yaji haka sai yace tabbas kuje ku amintattu ne a wajena. Sannan yasa aka mayarwa da kafirai kyautarsu ya aibatata yace yana neman tsari daga rashawa.

Cikin mutuwar jiki da borin kunya su Amru suka juyo zuwa makkah.

Har ila yau, kada mu manta ana can anata azabtar da Annabi da yan'uwansa musulminsu da kafiransu, an hana kowa zuwa wajensu, babu ci, babu sha babu kulawa.

A wannan lokaci Sahabi Abu Bakar ya fito don yin hijira zuwa Habasha amma sai wani shugaba ya hanashi, yace masa ya koma makkah ya bautawa Allah, zai kasance karkashin kulawarsa. Wannan shugaba ya nemawa Abubakar (R.A) alfarma a wajen kafirai, ai kuwa suka amsa sukace amma da sharadi zai rinka bautar ne a iyakar cikin gidansa.

Haka kuwa akayi, haka yake sallah da karatun Qur'ani kullum cikin kuka, to yaya ba zaiyi kuka ba alhalin an rabashi da masoyinsa?
Idan yana kukan cikin gidansa yana karatu sai mutane suzo su kewaye shi. 

A karshe kafirai suka kai kararsa gurin wannan shugaba akan cewa Abubakar fa yana bayyana karatu. Shi kuwa wannan shugaba yazo ya bawa Abubakar zabi, kodai ya daina karatu a fili yaci gaba da kare shi, ko kuma yaci gaba amma zai dauke hannunsa daga gareshi. Sai Abubkar ya zabi yaci gaba da karatun, yace kiyayewar Allah yake nema. 

Ai kuwa wannan shugaba ya janye kulawar da yake bashi, don haka yanzu kowa zai iya zuwa yayi masa rashin mutunchi son ransa.

Zamu dakata anan
Sai kuma a fitowa ta gaba!


WAIWAYE ADON TAFIYA 17
Tatacciyar sirar ma'aiki (S.A.W)...

A kaci gaba da muzgunawa Annabi Muhammad da sauran makusantansa, aka yanke alakarsa data sahabbansa, kamar yadda mu kaji har ganyen bishiya suke ci saboda yunwa da rashin abinci...

Wannan abu da yake faruwa tabbas yana damun wasu daga cikin larabawa da suke da alaka da Annabi (S.A.W).

Hisham Bn Amru shine ya fara zuwarwa Zuhair Bn Abu Umayya da maganar yace masa "Shin yanzu zaka yarda kaci abinci ka koshi amma yan uwanka suna can cikin yunwa?", sai Zuhair yace shima abin yana damunsa amma bashi da wani mataimaki da zai goya masa baya idan yayi wannan maganar, sai Hisham yace dashi "Gani nan, ni zan goyi bayanka."
Sai Zuhair Almakzumiy yace su biyu sunyi kadan suje su nemi na uku. Sai suka tafi zuwa ga Mud'im Bn Adiyyu suka ce masa shin zuciyarka tana nutsuwa kaci abinci ka koshi amma yan'uwanka su kwana da yunwa? Sai yace dasu shima abin yana ransa amma bashi da wani mataimaki idan ya bijiro da wannan maganar, sai su kace da shi yana da yan uwa biyu akan wannan maganar kuma ga su nan a tare dashi. Sai yace dasu to su nemi mutum na hudu... In takaice muku labari dai saida suka zama su biyar. 

Ai kuwa washe gari Zuhair yaje yayi dawafi, bayan ya kammala sai ya soki wannan mugunta da azabtarwa da akewa Banu Hashim da Banu Abdulmuddalib nan take kuwa su biyar ragowar hudun nan suka goya masa baya... Aikuwa da ganin haka sai Abu jahal wanda akan idonsa suke aibata wannan hukunci yace “Wannan shiryayyen abu ne, jiya da daddare kuka shirya shi...” 
A karshe dai suka janye wannan hukunci duk da wasu basu so janyewar ba. Ita kuwa takarda da aka rubuta wannan hukunci da akaje sai aka tarar gara ta cinyeta sai inda aka rubuta sunan Allah kawai, dama kuma tuni Annabi ya bawa Abu dalib labarin hakan kafin afkuwar wannan abu.

A karshe-karshen shekara goma bayan hijira ne Abu Dalib ya rasu bayan janye wannan takura da akai musu, Annabi yayi iyakar kokarinsa wajen lakkana masa kalmar shahada amma sai bai karba ba saboda ganin manyan kuraishawa a wajen amma ga dukkan alamu yasan cewa abinda Annabi yazo dashi gaskiya ne. Annabi yayi bakin ciki sosai, sannan ya dauki aniyar cewa zai nemawa Abu Dalib gafara amma sai Allah ya saukar da aya ya haneshi da aikata haka.

Allah sarki, ka duba irin soyayyar da yake masa, amma son da yakewa Allah ya danne kowace soyayya. Hakanan anan zamu gane cewa ita shiriya ta Allah ce.

Bayan rasuwarsa da kadan sai Nana Khadija itama ta rasu, Allahu Akbar, ita kuwa tun kafin ta rasu Allah yayi mata bushara da Aljanna. (Bukhari da Muslim) 
Mutuwarsu ta mutukar girgiza Annabin rahama, kuma yayi bakin ciki mai yawa. Kada mu manta ya rasa mai kareshi a waje da kuma mai kwantar masa da hankali a gida...

A wannan rintsi dai wasu mutane daga Najran suka zo, suka ce sunji labarin Annabi Muhammad (S.A.W) don haka suka zo don suji abinda Allah ya turoshi dashi, su kuwa wayannan mutane mabiya addini Annabi Isah ne, aikuwa bayan sun saurari Annabi sai sukai imani... Abu jahal yayi dariya ya aibatasu yace amma dai su wawaye ne shi bai taba ganin wawaye irinsu ba, amma sai sukai masa magana ta aminchi suka kuma yi masa uzurin jahilchi...

Annabi tare da sahabi Abu bakar haka suka rinka bi kwararo kwararo suna samun daidaikun mutane da kuma taro suna kira zuwa ga Allah... Sayyadina Abubakar Allah ya hore masa ilmin nasabar larabawa don haka shike jagorantar Annabi dayi masa karin haske akan kabilu da nasaba.

Annabi ya nemi auren Nana Saudatu da Nana Aisha anyi sabani akan wadda ya fara aura amma dangane da tarewa an hadu akan cewa ya fara tarewa da Nana saudatu. Dalilin da yasa Annabi ya aureta kuwa shine ita da mijinta sunyi hijira zuwa habasha, kuma sai Allah yayi masa rasuwa. Don haka kuma bata da wani majibincin lamari musulmi, kunga kuwa komawarta hannun yan'uwanta kafirai zai zama babbar barazana ga lafiyarta, amincinta da imaninta. Don haka sai Annabi ya nemi aurenta. 
Macece mai ibada mai kuma mutukar biyayya da son manzon Allah (S.A.W).

Cutarwa ga Manzon Allah (S.A.W) saita karu, zuba masa kasa, watsa masa kashin dabbobi idan yana sallah da dai sauran abubuwa marasa dadi.

A karshe Annabin rahama ya yanke shawarar zuwa Da'if don neman taimako.

Zamu yada zango anan zamu ci gaba.

WAIWAYE ADON TAFIYA 18
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)

Annabi ya zabi ya tafi Da'if don neman taimakonsu, watakila idan ya kirayesu zasu amsa masa. Kuma ya zabi Da'if ne domin itama cibiya ce kamar makkah, kuma suna da karfin iko kwatankwacin makkah, hakanan akwai sanayya tsakaninsa da wasu daga cikinsu...

Bisa saiya fara da manyansu, inda yaje yana kiransu ga addinin musulunchi, amma duk wajen wanda yace sai su hantareshi suce ya fitar musu daga gari. Daga karshe suka hadashi da yara da wawayen cikinsu, suka biyoshi suna jifansa da duwatsu suna zaginsa suna gaya masa bakaken maganganu... Sahabbai da suke tare dashi suka rinka kareshi amma inaa jifan yayi yawa haka suka biyo Annabi yana tafe suna jifansa har saida suka zubar masa da jini, takalmansa suka cika da jinin dake gangaruwa daga jikinsa, saida sukai tafiya mai nisa a wannan yanayi...

Ana tsaka da wannan abu sai mala'ika jibril ya sauko tare da wani mala'ika ya cewa ma'aiki (S.A.W) wannan mala'ika ne da aka wakiltashi ga duwatsu, idan kana so yanzu sai ayi masa umarni yayi musu ruwan duwatsu...

Sai Annabin rahama yace a kyalesu, wata kila Allah zai fitar da muminai daga cikinsu...
Allahu Akbar, kaji sarkin hakuri.

Daga nan Annabi yakai kukansa zuwa ga Allah yana mai neman agaji da tallafi.

Daga nan Annabi ya dawo makkah ya shigeta tare da taimakon daya daga cikinta mutanenta, domin idan ba haka ba tabbas ba zasu barshi ya shiga ba.

Akwai Kabilu da dama da Annabi ya kira zuwa musulunchi wayanda ba quraishawa ba, amma sai suka aibata abinda yazo da shi, cikinsu akwai masu barazanar kasheshi, cikinsu akwai masu ce masa ta yaya baya cikin kabilarsu zasu yarda dashi bayan sunsan idan ya samu karbuwa ba zasu samu wani alheri ba... Da dai amsoshi mabambanta.

Annabi ya ci gaba da kira, a fili da a boye, har lokacin aikin hajji yayi. Kamar yadda muka sani tun farko farkon fara kira kafirai suka hana baki masu zuwa aikin hajji sauraron Annabin rahama. 

A hajjin shekara ta goma da aiko Annabi (S.A.W) sai ya rinka bi yana kiran mutane, saidai kash yana kira a biye dashi kuma akwai kafirai daga yan'uwansa na jini da suke karyatashi...

Saboda haka sai Annabi ya sake dabara, inda da shi da sahabi Abubakar da wasu sahabbai suke bin dare suna zuwa masaukin ma'aikata aikin Hajji suna kiransu izuwa musulunchi. Sai hakan ya samu karbuwa domin ana samun fahimta tare da cewa wasu basa karbar addinin saidai suna gamsuwa da abinda yazo da shi.

A wannan wannan fita ne ya hadu da wasu matasa shida daga mutanen madina dukkansu yan kabilar Khazraj ne, bayan Annabi ya kirasu sai suka amsa masa. Suka karbi musulunchi. Domin dama su sun jima suna jin labarin zuwansa a wajen yahudawa, harma yahudawan suna gaya musu idan yazo su zasuyi imani dashi su yaki larabawan...

Bayan wayannan mutanen madina sun karbi musulunchi sai suka koma gida, inda anan ne suka rinka yada labarin Annabi da addini har saida ya zamana babu wani gida a madina face ana labarin manzon Allah (S.A.W).

Bayan wasu lokuta ne kuma wani babban Al'amari ya afku, Annabi yana gida bayan sallar Isha'i sai mala'ika jibrilu yazo yace dashi ya fito su tafi masallacin harami inda ka'aba take.
(Anyi sabani akan yaushe wannan al'amari ya faru, amma abinda malamai suka fi gabatarwa ko zaba shine wannan lokacin da muka zaba.)

Bayan sunje ka'aba, sai mala'ika jibril ya tsaga kirjin Annabi ya fito da zuciyarsa ya wanketa da ruwan zam-zam. Sannan ya bijiro masa da wata dabba wadda ake kira BURA'KA, ya umarci Annabi daya hau bayanta, cikin gudu kamar walkiya sai gasu a baitil maqdis, masjidul aqsa wanda yake Palestine a yanzu. 
A ciki Allah ya rayawa Annabi dukkanin Annabawa wayanda adadinsu yakai dubu dari da ashirin da hudu, cikinsu akwai manzanni guda 315 kamar yadda ibn Hibban ya rawaito a sahihinsa. 
Siratun-Nabawiyya na shaikh Musa bn Rashid Azimiy sh. 27}

Note: Akwai maganganun malamai akan adadin Annabawa da Manzanni. Maganar da tafi kwanta min shine babu wanda yasan adadinsu na gaskiya sai Allah madaukakin sarki.

Jibril ya umarci Annabi, ya shiga gaba yayiwa Annabawa limanci domin shine shugabansu.

Daga nan suka bar wannan dabba bura'ka, mala'ika jibril ya dauki Annabi suka luluka sararin samaniya.

A saman duniya ya hadu da Annabi Adam (A.S).
A sama ta biyu ya hadu da Annabi Yahaya da Isah (A.S).
A sama ta uku sai suka hadu da kyakkyawan Annabin nan Yusuf (A.S).
A sama ta hudu kuwa sai ga Annabi Idris (A.S) wanda shi dama a wannan samar aka dauki ransa.
A sama ta biyar sai ya ci karo da Annabi Haruna (A.S).
A sama ta shida suka hadu da gwarzon namijin sadauki wanda suka sha artabu da fir'auna wato Annabi Musa (A.S).
A sama ta bakwai saiya sadu da kakansa, kuma baban Annabawa badadin Allah ma'abocin ilmi da hikima Annabi Ibrahim (A.S), harma kakan nasa ya bashi tsaraba cewa ya gaishe da al'ummarsa sannan ya gaya masa wani lakani yace ya gayawa al'ummarsa, lakanin shine Subhanallah, walhamdulillah, wala'ilaha illallahu, wallahu akbar sune bishiyun (ado) na gidan aljanna.
Daga nan yaga Aljanna harma aka nuna masa gidan gawurtaccen gwarzon musuluncin nan wato sayyadina Umar (R.A). 
Yaga wuta yaga irin azabar da take cikinta da kuma mai gadinta.

Kai in takaice mana labari saida akazo wani bigire da shi kansa mala'ika jibril tsayawa yayi, ya cewa ma'aiki nan shine iyakarsa, idan kuwa yayi gangancin wuce wannan waje konewa zaiyi.

Annabi yayi gaba yaje wajen nan inda mala'iku basa zuwa balle mutane. Ya gana da Allah aka bashi ayoyin karshe na suratul baqara sannan aka bashi salloli guda hamsin.

An rawaito cewa Annabi Musa shine ya rinka umartar Annabi daya koma ya nemi ragi, har saida sallar ta koma guda biyar. 
Babu mamaki domin Annabi musa yasha bakar wahala a wajen banu isra'ila don haka yake nemawa Annabi sauki. Kaji dan'uwa na gari.

Annabi da masoyinsa jibril basu sauko a ko'ina ba sai a masjidul Aqsa, daga nan bura'ka ta kuma dauko ma'aiki har zuwa makkah. 

Duka wannan abu ya faru daga bayan sallar isha zuwa gabanin sallar asuba. 
Allahu Akbar.

Zamu dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba.


WAIWAYE ADON TAFIYA (19)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Haka musulunchi yayita yaduwa a madina, su kuwa yahudawa wayanda ta dalilinsu wasu suka san cewa tabbas akwai Annabin Karshen zamani da zaizo, sai girman kai gami da bakin ciki da kuma hassada suka hanasu suyi imani.

Wata hikima ta Allah anan itace, Annabi yaje Da'if don yana kyautata musu zato, amma sai akasin abinda yake tunani ya afku, da ace Annabi yasan gaibu, da kai tsaye zai taho madina amma sakamakon baya sanin gaibu sai wanda Allah ya sanar dashi sai ya zabi zuwa Da'if. 

Kada mu manta, al'amarin musulunchi da alkawarin shiga musulunchi da mutanen madina sukai yaje kunnen mutanen makka, don haka sai muzgunawarsu da takurarsu ga Annabi ta karu matuka, harma ya zamana sunayin hakan da gayya, tare da cewa hakan bai hana Annabi kira ba. Akwai lokacin da zai rinka bin mutane a gurarensu na kasuwa ko majalisu yana kiransu zuwa ga bautar Allah, amma saika iske daya daga cikin kafirai da suke na jikinsa ta fuskar nasaba sune biye dashi suna karyatashi.

Da abu yayi yawa, wata rana sai Annabi yayi mafarki mutanensa suna hijira zuwa madina, ai kuwa saiya bawa sahabbai labari. Idan mai karatu ya bibiyemu a rubututtukanmu na baya zai tuno mun ambata tun kafin a fara wahayi mafarkai Annabi yake, ta yanda baya mafarkin wani abu sai ya tabbata. To kasancewar an fara saukar da wahayi hakan bai katse waccan hanyar ta mafarki ba.

Don haka Annabi yayi umarni da hijira, farkon wanda ya fara hijira Abu salamata ne, sai kuma Ameer Bn Rabi'atu da matarsa Laila kamar yadda muka sani kuma wannan hijirar a boye akeyi, domin kafirai ba zasu bari ayi a bayyane ba. Hatta sahabi Umar duk shayinsa da ake amma dare yabi tare da Ayyash bn Rabia da Hisham bn Ass. Ibn Ishaq  sirarsa ya fitar da sanadi ingantacce. Amma dangane da batun cewa Umar (R.A) ya fito yayi tutiya kuma yayi hijira wannan kissar tana da rauni. 
(Siratun Nabawiyya na Shaikh Musa bn Rashid Al'aazimiy 46.)


Abu kamar wasa yau sai a wayi gari a makkah aga babu wannan, washe gari sai aga wane ma ya fita, jibi sai aji da wane da wane da matar wane da jikan wane basa gari, rana ta gaba sai kaji ana wance da wance da maigidansu suma sun sulale.

Sai abin ya fara bawa kafirai tsoro, don haka sai suka kara zuba ido suka kara tsaurarawa. Suka kuma zauna sukai shawarar yadda zasu yiwa Annabi.

Wasu suka ce a kore shi, masu wayon cikinsu su ka ce yanda yake da dadin baki nan, duk inda yaje sai sun bishi, kuma ya dawo ya gagareku.
Wasu sukace a killaceshi, masu wayo suka kuma cewa idan aka killaceshi masu imani da shi zasu zo su kwace shi, don kuwa sunga mabiyansa suna fifitashi akan iyayensu...

Ka duba fa, wannan shaidar kafiran kuraishawa kenan akan sahabbai, amma yanzu sai kaga an samu wani kato yaci ya koshi yana kokarin sukar mutane masu daraja lambar farko irinsu sahabi Abubakar da Umar.
Allah ya kiyayemu da aikin da na sani. 

Daga nan kafirai sukace kashe Annabin nan kawai za'ayi a huta. Amma sai dai a rarraba jininsa, abin nufi a tattaro samari daga kowace kabila, mutum biyu ko wanin haka, su tsaya suna jiransa a kofar gidansa, yana fitowa sai suyi masa bugun mutum guda, idan sukai haka yan'uwansa ba zasu iya daukar fansa ba. Saidai dole su hakura da Diyya. 

Sahabi Abubakar, Sahabi Aliyu da Annabi sune suka rage basuyi hijira ba, sai kuma masu mutukar rauni. Daga musulmai.


Sahabi Abubakar (R.A) yana yawan tambayar Annabi yana neman izini akan hijira, amma sai Annabi ya katse masa hanzari yace masa ya jira watakila Allah yana so ya hada shi da abokin tafiya... Shima Annabi a zuciyarsa so yake su tafi tare da Abubakar, kai tunda akai duniya bamu riski wasu aminai masu mutukar jin son junansu irin wayannan masoya biyu ba. Allah ya barmu da son na farko dana biyu dana uku dana hudu dana biyar da sauran sahabbai. 

Kwatsam wata rana sai Annabi ya tafi gidan Abubakar (R.A), Sahabi Abubakar yaga Annabi ba'a lokacin daya saba ziyartarsa ba, ya sameshi a daki tare da Nana Asma'u da Nana Aisha ya'yan Sahabi Abubakar (R.A). Abubakar (R.A) ya tambayi ma'aiki lafiya? Sai Ma'aiki ya ambata masa cewa an masa umarni da hijira, cikin gaggawa sahabi Abubakar ya tambaya shin tare zasu tafi, Annabin rahama ya jaddada masa cewa kwarai tare zasu tafi sai sahabi Abubakar ya fashe da kuka saboda farin ciki. Nana Aisha tace bata taba zaton mutum yana kuka saboda farin ciki ba sai wannan lokaci.

Abu salama kuwa da yayi hijira tun farko yana can cikin zulumi da tunanin matarsa domin yan'uwanta sun kwaceta daga gareshi sun hanata fitowa, ya tafi ya barta da dansa, ba don ya so ba sai don fin karfinsa da zaluntarsa da sukai. Kullum saita fito tayita kuka, saida ta doshi shekara a haka kafin daga baya su barta ta taho ta biyo daji ita kadai...

An yiwa Annabi umarni da hijira amma kuma kash akwai abubuwan mutane a wajensa domin babu amintacce irinsa, kowa idan baya so a samu matsala a kayansa, to fa wajen Annabi yake kawosu. 

Al'amarin maganar kashe Annabi kuwa, to tabbas sun hadu suna jiransa a kofar gidansa, suna jira ya fito, suna ta lekashi, duk sanda suka leka sai suga tabbas yananan.

Suna nan tsaye da muggan makamai ya fito ta gabansu ya wuce basu ganshi ba, wani dabam daga gefe ya bazamo yace musu ai Annabin da kuke jira ya fita. Suka leka sukaga mutum a kwance, sai sukace yana ciki, bayan dogon lokaci sai sukaga ashe Aliyu (R.A) ne, suka gama borin kunyarsu suka watse, shi kuwa Sayyadi Aliyu Annabi ne ya umarceshi daya kwanta a shimfidarsa. Kuma ya nunnuna masa kayan jama'a ya umarceshi daya mayar musu da kayansu.

Ka duba soyayya irinta sahabi Aliyu da sadaukarwa, yanda yayi bajakolin rayuwarsa don tseratar da manzon Allah, shi ya yarda idan shigowa ma za'ayi a shigo a kasheshi mutukar addinin Allah zai ci gaba da yaduwa...
Shin irin wayannan mutanen har akwai wani dalili da zaisa mu rinka bibiyar laifukansu?

Annabi da Sahabi Abu bakar suka tafi kogo Saur (Thaur) suka buya. 

Su kuwa kafirai abinda suke tsoro yana daf da faruwa don haka sai suka saka kudi masu tsoka ga wanda ya kashe ma'aiki ko kuma ya kawo musu shi. Suma kuma suka bazama neman Annabi.

Sahabi Abubakar suna cikin wannan kogo, Asama'u yar Sayyadina Abubakar ita ke kawo musu abinci...

Kamar wasa kwatsam suna cikin kogon nan saiga kafirai a bakin kogon suna laluben Annabi da Sahabi Abubakar.
Hankalin Sahabin Annabi ya tashi, bugun zuciyarsa ya karu, ya dubi Annabi cikin razani yana mai gaya masa halin da suke ciki. Amma da ke Annabi jan gwarzo ne, sai ya kwantar masa da hankali yace, kada yaji tsoro Allah yana tare dasu. 

A wannan lokaci da dayansu zai kallo wannan wajen cikin sauki zaiga su Ma'aiki, amma inaa Allah bai basu iko ba.

Ana rawaito cewa gizo-gizo yayi yanarsa hakanan tsuntsuwa tayi kwai a wajen wanda hakan yasa kafirai sukai tsammanin an dade ba'a shiga kogon ba, saidai kissar tana nan cikin musnad kuma bata da inganchi.

Abinda muka sani shine,  Allah wanda ya kautar da zukatan kafirai daga imani bayan hujjoji bayyanannu yana da ikon da zai hana su kallon wajen ko kuma hana hangen nasu riskar jikkunan mutane biyun kamar yadda suka kasa riskar Qur'ani da Hikima.

Zamu yada zango anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.


WAIWAYE ADON TAFIYA (20)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Muna bada hakurin jinkiri da muka samu saboda wasu dalilai.

Mun ji cewar sahabbai sun fara hijira, kamar yadda daga baya ya rage Annabi Muhammad (S.A.W) da Sahabban nan jajurtattu guda biyu wato Gwarzon matashi Aliyu (R.A) da kuma Dattijon arziki Abubakar (R.A). Sai kuma wasu tsirari na mutane marasa karfi wayanda basu da damar yin hijirar saboda rauni. 

Zamu iya cewa akwai kuma wayanda wasu dalilan dabam suka sanyasu basuyi hijira ba idan mukayi la'akari da masu cewa Abbas kawun Ma'aiki ya musulunta tun kafin hijira saidai ya boye musuluncin ya ci gaba da zama a cikin kafiran Kuraishawa ne, yana mai turowa Annabi bayanai akan tuggun da suke aikatawa. Saidai da dama daga cikin malamai sunce hakan baya nuna ya musulunta, yana hakan ne saboda alakarsa da Annabin rahama domin 'dane a wajensa...
Koma dai menene muna sane da cewa Abbas yana cikin wayanda aka gallazawa kafin Hijira don basu yarda a cutar da ma'aiki ba, kuma ya bayyana imaninsa ranar fatahu Makkah. Kamar yadda zamu zo wannan bigiren nan gaba. Idan Allah ya karfafemu da dama da kuma tsawon rai akwai rubutu akan Ahlul baiti wanda zamu ambato tarihinsa a ciki da irin gudummuwarsa tare da sauran Ahlul Baiti (R.A).

Hankalin kafirai ya tashi matuka domin sun san cewa tabbas akwai matsala tunda har suka bari musulmai suka sulale. Tare da cewa sunyi iyakar kokarinsu wajen ganin sun dakile musulmai daga kowane kyakkyawan motsi amma inaa hakan bata yiwu ba.

Ka duba irin hikima ta Allah, ko anan zaka san lallai Allah ya cika mai hikima. Bari mu ambaci wasu darussa kada 
★ Kiran da Annabi yayi, yafi samun matsala daga wajen yan'uwansa, da kuma kabilarsa. Hikimar hakan kuwa shine, da ace lokacin daya fara kira duka yan'uwansa sun mara masa baya. To da har yau kafirai zasu rinka kafa hujja da hakan suna cewa ai dama neman mulki larabawa suke shine suka kirkiri wannan hikimar.
★ Yankin da Annabi ya fito yanki ne da akwai masarautu a duniya manya wayanda gaba suke da yankin ta fuskar mulki da tattalin arziki da yawan jama'a. Da ace Annabi ya fito daga wayannan manyan dauloli to da har yanzu za'a yita sukar cewa wannan daula mulki take nema shine ta bashi wannan aiki don ta mamaye duniya ko kewayenta. Ta yanda kowa zai zama karkashinta. Amma sai Allah ya zaboshi daga wani yanki wanda su wayancan daulolin ma basu damu da shi ba.
★ Lokacin da Annabi ya fara kira, yanada hikima da dabarar da zai iya jawo hankalin larabawa yace musu su hade kai, domin zasu samu karfi ko mulki a duniya ko wanin haka, amma saboda sakon ne kawai a gabansa kuma yana hangen abinda ka iya faruwa bayan tsawon lokaci sai yayita kiransu akan a bautawa Allah domin shine gundarin sakon da aka aikoshi da shi. 

Mai karatu da kanka idan ka fara fito da darussa a wannan rayuwa mai albarka, na tabbata zakaji mamakin tarin darussan da zaka iske.

Kafiran Makkah suka sanya kudi mai yawa ga duk wanda ya kawo musu Annabi a mace ko a raye. Sudai burinsu kada a sake a barshi yakai madina. Saboda makudan kudin da suka saka sai nan da nan labari ya yadu a fadin ko'ina a wannan yanki.

Daga cikin wayanda suka himmatu don samun cin wannan gasa akwai Surakatu Dan Maliki, wata rana yana zaune sai wani yazo ya sameshi yace masa shifa ya hango wasu mutane biyu nesa can suna tafiya kuma yana kyautata zaton Annabi ne da Abubakar.
Farin ciki ya kama surakatu amma sai ya danne, ya kalli mai maganar sannan yace ai basu bane, wayannan daka gani wane da wane ne. Don haka mai maganar saiya tafi. Da Surakata ya tabbatar mai kawo rahoton yayi nisa sai shima ya mike ya faki ido ya kyarawa bayinsa suka hada masa doki ya hau bisa yabi bayan su Annabi. Haka yayita gudu har saida ya zamana ya fara hango su Annabi nan danan ya kara himma saida ya kusa cimmasu sai kawai ya fado daga kan dokinsa kasa kuwa ta rike dokin nasa har zuwa gwiwa. Bayan ya gama kici-kici ya fitar da dokin saiya kara zabura... Wannan karon ma kasarce dai ta kara rike dokin ta rikito dashi, akai haka har sau uku. Da kansa ya nemi sulhu sannan ya gayawa su Annabi abinda mushrikai suka shirya...

Suka ci gaba da tafiya, idan aka gansu sai a rinka tambayar Sahabi Abubakar (R.A) wanene wannan a tare da kai... Shi kuwa sai ya bada amsa da cewa mai shiryar dashi hanya ne. Su masu sauraron sai suyi tsammani  hanya dai da ake tattaki akai, shi kuwa yana nufin hanya zuwa ga ubangiji.

Annabi yafi Abubakar shekaru, amma alamomin tsufa sunfi bayyana a tare da Abubakar, hakanan shi Sahabi Abubakar sananne ne a kowane yanki na makkah da kewayenta. 

Can Madina kuwa, labari ya bazu ko ina cewa Annabi yana tafe. Don haka kullum saisu fito suna masu duba hanya tare da jiran zuwan shugaba. 

Zamu dakata anan!

Sai kuma a fitowa ta gaba.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.