WAIWAYE ADON TAFIYA 11 - 15

WAIWAYE ADON TAFIYA 11
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Duk da barazana da tsoratarwa da sukewa Annabi amma babu abinda hakan ya kara masa sai himma da kuma kara zage damtse wajen kira, don haka suka takurawa Abi Dalib akan sai ya damka musu Annabi ko kuma ya basu dama su cimma sa, amma hakan bata samu ba... 

Ka duba ka gani, kafiraine, amma kuma suna girmama na gaba dasu kuma suna jin nauyin cin zarafin mai shekaru a cikinsu, ba irin matasa da muke dasu yanzu ba, wanda wani sai kaji bama gama-garin mutane yake zagi ko cin mutunchi ba, malaman addini da shuwagabanni zakaga yana zagi kuma ko a jikinsa, kaga sannan jahilcinsa yafi jahilcin jahilan jahiliyya...

Daga karshe da suka rasa yadda zasuyi, sai suka yanke shawarar cewa kowane dangi yaje yayi maganin wayanda sukai imani a cikinsu...

Khabbab ibn Aratti saboda ya musulunta riga ake cire masa, a baza garwashi a kasa a kwantar dashi akai sannan a kirawo kato ya taka kirjinsa ya danne shi... Amma hakan bai saka yabar musulunchi ba, saboda soyayya da imani... 
Ammar bn Yaseer, a gabansa aka kashe mahaifiyarsa ba don komai ba sai don kawai taki yarda ta kafircewa masoyi Annabi Muhammad (S.A.W) baya ga azabtarwa da tasha tare da mijinta da danta (Yaaseer). Annabi ya kasance yana wucesu lokacin da ake musu azaba, yaya kake tunani zuciya mai tausayi irinta Annabi zata ji, idan taga ana azabtar da wayannan mutane? 
Cikin dauriya irinta ma'aikin Allah, haka yake basu hakuri, yana kuma yi musu bushara da Aljanna. Zuciyarsa kuwa tana cike da tausayi...

Usman ibn Affan kuwa daureshi danginsa sukai, sukace ba zasu kwance shi ba har sai yabar addinin musulunchi ya dawo addinin iyaye da kakanni. Shi kuwa kai yace musu babu abinda zai chanja... 

Irin wayannan mutane sune wasu azzalumai basu da tukuicin da zasuyi musu sai zagi. Allah ka kara mana so da ganin martabar sahabban masoyi (S.A.W) Ameen.

Bilal kuwa, cikin zafin rana irin na sahara ubangidansa (Umayya bn Khalaf) zai fitar dashi, a kwantar dashi a sahara mai tsananin zafi, a dora masa katon dutse a danne shi dashi. A bashi zabi, kodai ya bar addini ko kuma yayita zama a haka. Shi kuwa jaddadawa yake Allah daya ne, Allah daya ne. Ya fita daga hayyacinsa amma abinda harshensa zaita fada kenan. Da hakan ta faru akan idon Abubakar (R.A) ai kuwa take ya shiga ya fita ya yanta Bilal (R.A).

Idan mukace zamu fadi irin muzgunawa da azabtarwa da akaita yiwa sahabbai rubutun zai tsawaita mutuka. Duka wannan abu da yake farawa kada ka manta an haramta bawa musulmai abinci ko abin sha. 

Da larabawa sukaga duk da haka Annabin rahama bai sassauta wajen kira ba, kuma suna ganin yadda suke azabtar da masu imanin amma kamar kara musu imani ake... Sai suka fara taba Annabin tsira, daga izgilanchi suka samu cigaba zuwa cutarwa ta fili...

Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

WAIWAYE ADON TAFIYA 12
Tatacciyar sirar ma'aiki (S.A.W)...

Cutarwa bata tsaya kan sahabbai ba, koda yake dama hankali bazai dauka ba, ace ana gallazawa mabiyansa amma shi an kyaleshi, duk da cewa yana da kwarjini amma hakan baya hana su tabashi ko su ci masa fuska, baya ga izgilanchi da suke masa... Sauda dama akwai wani abu dana ankara dashi a cikin tarihin Annabi (S.A.W) da dama daga masu muzguna masa, wasu lokutan yabonsa suke sai a gwalesu sannan a aibatasu a nuna musu cewa suna goyon bayansa, su kuma wannan abin abin kunyane ace sun bar addinin iyaye da kakanni, don haka don su nuna basu bar addinin ba saisu shatawa ma'aiki (S.A.W) wani rashin mutuncin....

Mu tuna larabawa akan kabilanchi da kare martabar iyayensu sukanyi yaki akan abu dan kankani wanda bai kai ya kawo ba. 

Mu kuma tunawa irin yadda suka dauki ababen bautarsu da daraja, basa yarda su rabu dasu, idan mutum zaiyi tafiya a zamaninsu yakan dauki gunkinsa ya tafi dashi, ko kuma ya dauki duwatsu guda hudu, uku daga ciki zai rinka dora tukunyarsa yana girki na hudun kuma shine abin bautarsa... Nan ba wajen tsawaita bayani bane akan wannan. Idan Allah ya bamu tsawon rai, akwai rubutun mu mai nuna alakar wayewar mutanen yamma da maguzancin jahiliyya.

Daga masu cutar da Masoyi (S.A.W) akwai Abu Jahal, wanda akwai lokacin da Annabi yana sallah, ya dauko wani katoton dutse ya nufo Annabin rahama dashi gadan-gadan da nufin idan Annabi yayi sujjada zai masa rotse, da yaga Annabi yayi sujjada ai kuwa saiya kara himma don aiwatar da mummunan nufinsa, labarabawa suna gefe suna kallon abinda yake faruwa suna jira suga me zai faru... Kamar daga sama sai kawai yaga wata halitta abar tsoro ta nufo shi, babu shiri yayi wurgi da wannan bajimin dutsen a firgice yaja da baya har saida ya nesanta daga ma'aiki (S.A.W).
(Nurul Yaqeen 18)

Hakanan akwai lokacin da yaga Annabi yana sallah, bayan ya idar, sai yazo cikin nuna isa da dagawa yace da Annabi "Ban hanaka wannan abin ba?" Duk hakuri irin na ma'aiki amma a wannan karon saida ya mayar masa da martani, shi kuwa cikin tutiya yayi fariya da nuna cewa shi mai jama'a ne, wannan karon kuwa ba Annabi ne ya bashi amsa ba. Allah ne da kansa ya masa masa a suratul Alaq ayata 15 - 19. Inda Allah yace masa ya kirawo gayyar mutanen da yake tutiya da su, mu kuma (Allah) zamu kira zabaniyawa, sannan a karshe Allah ya umarci Annabi da kada yayi masa bbiyayya bisa hanashi sallah da yakeyi, aka kuma karawa Annabi kwarin gwiwar cewa yaci gaba da sallah yana neman kusanchi zuwa ga Allah.

Ba zaka gane kiyayyarsa da sallah da manzon Allah ba, saika karanta abinda Imam Bukhari ya rawaito daga ibn Abbas cewa manzon tsira yana sallah, sai Abu lahabin ya tambaya shin wanene zai iya dauko wata shara a wani waje (Dan tayi na rakumi a bola) ya dora akan Annabi idan yayi sujjada. Wani da ake kira da ukbatu yace zai iya, ai kuwa akan idon duniya ya dauko wannan kazanta ya dora akan Annabi lokacin da ma'aiki yake sujjada. Suka rinka kyalkyala dariyar keta, Annabi kuwa ya ki dagowa daga sujjadar. Har saida fadimatu yarsa tazo cikin gaggawa ta dauke wannan kazanta daga kan Annabi (S.A.W), sannan ta gaggayawa kafiran bakaken maganganu yayinda shi kuma ma'aiki ya kai kararsu zuwa ga Allah. Ibn mas'ud yace, ai kuwa ranar yakin badar sai gasu duk sun hallaka.

Ukbatu din nan dai, akwai lokacin daya taba yin shahada, saboda Annabi yace bazaici abincinsa ba, lokacin ya gayyaci manyan kuraishawa gidansa walima, don haka saiya furta shahadar. Bayan lokaci sai suka hadu da wani, ya tambayeshi akan shahadar, saiya bada uzuri yace yana jin kunya ne ace mutum kamar muhammadu mai karamchi yazo gidansa amma baici abinci ba, sai wannan mutum yace ba zamu yarda da kai ba har saika kama shi ka mareshi ka dake shi ka shake masa wuya... Ai kuwa saida ya aikata duka wayannan abubuwa. Sayyadi Abubakar shine wanda yazo ya shiga tsakani yana fadin shin zaku kashe mutum don kawai yace Allah ne uubangiji na?

Takai-takawo idan sahabbai suka biyo hanya sai a rinka yi musu izgili ana cewa dasu ga masu mulkin duniya nan zasu wuce. Ana gaya musu haka saboda dai dai da suturunsu ba masu kyau bane.

Abubakar (R.A) kuwa akwai lokacin da ya samu dandazon manyan larabawa ya fara kiransu zuwa musulunchi ai kuwa sai suka rufeshi da duka. Utba bn Rabi'a yasanya takalmansa ya rinka dukan fuskar Sahabi mai daraja, fuskar tayi kaca-kaca har saida ya zamana ba'a banbance inane ido inane hanci saboda kumburar da fuskar tayi. Da kyar Bamu Taim suka daukeshi suka tafi dashi gidansa.
(Ibn Kasir)

Manya da yara suka koma yin izgili ga ma'aiki, kai hatta bayi marasa yanci suna cutar dashi... Idan mukace zamu lissafo da dama rubutun zai tsawaita.

Da takura tai yawa sai kawai Annabi ya tafi gida yaje ya lulluba, ka duba, duk hakuri irin na fiyayyen halitta amma ya zabi ya kebance daga mutane saboda takura, muzgunawa da kuma izgilin da ake masa. 

Bayan ya lullubane sai kawai Allah ya kirashi “Yaa kai wanda ya lulluba, ka tashi kayi gargadi.” 
Da jin wannan kira sai ma'aiki ya tashi don ci gaba da kira izuwa tafarkin mahalicci.

Zamu dakata anan
Sai kuma mun hadu a rubutu na gaba.


WAIWAYE ADON TAFIYA (13)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Haka Ma'aiki ya ci gaba da kiran mutane zuwa ga addinin musulunchi, duk da kuwa cutarwa da ake masa, da kuma cutarwa da akewa mabiyansu, wasunsu saboda azaba suka rasa rayuwarsu. Wasu azabar ta zama dalilin rasa mahaifansu, mafi yawansu kuwa sai aka samar musu da tabo wanda ya zauna a jikinsu har zuwa karshen rayuwarsu...

Da wahala tayi wahala sai Khabbab Ibn Aratti yaje ya samu manzon Allah yace “Ya ma'aikin Allah shin ba zaka yi mana addu'a ba, shin ba zaka nema mana dauki daga wajen Allah ba?”. Take fuskar ma'aiki tayi jajur saboda fushi, sannan ya bawa Khabbab labarin irin azabar da masu imani kafin su suka sha...

Hakan kuwa babu abinda ya karawa Khabbab (R.A) sai imani... Sahabbai masu abin mamaki, tabbas Allah da kansa ya zabarwa Annabi sahabbai... 

Wata rana kamar kullum Abu jahal yaci mutunchin Annabi ya zazzageshi, ya aibata shi da mafi munin kalmomi, a wannan lokaci akwai kawun Annabi (S.A.W) wanda yana daya daga cikin mafi jarumtar mazaje, don haka da yaji labarai sai abin ya fusata shi, ai kuwa take ya nufi inda Abu Jahal yake, yana zuwa kuwa bai tsaya wata-wata ba, saiya dakeshi sannan ya dora da cewa “Don me zaka rinka zagin Muhammadu Alhalin ina cikin addininsa? Daga nan ya zarce ga Annabi ya bayyana imaninsa, tabbas musulmai sunyi farin ciki da musuluntarsa, yayinda kafurai suka tsananta bakin ciki.

Da kuraishawa suka ga cewa lallai fa wannan azabtarwa da sukewa musulmai babu abinda zata haifar, domin sunyi iyakar yinsu amma musulman karuwa suke kuma yakininsu yana daduwa, sai suka sauya shawara, sukace ya kamata su samu Annabi suji me yake so, zasuyi masa amma dai su bukatarsu ya daina kafirta iyayensu, ya kuma daina zagin ababen bautarsu. Haka suka wakilta wani a cikinsu Utba ibn Rabii'a yaje ya samu Annabi, bayan shimfida da yayi ta magana saiya dora da cewa “Ya kai dan dan'uwana idan dukiya kake so, zamu tara maka dukiyoyinmu har sai kafi kowa a cikinmu dukiya, idan matsayi kake so zamu daukaka a cikinmu kuma ba za'a gabatar da wani abuba sai da umarninka, idan kuwa mulki kake so, zamu mayar da kai sarkinmu, idan kuwa Aljanu ne suke damunka kuma baka da damar da zaka nemi magani, to zamu hada duka dukiyar da take garemu domin muyi maka magani...
Annabi yace dashi “Ya Aba Waleed ka gama?”
Yace “Kwarai da gaske.”
Ma'aiki (S.A.W) yace “Dan saurare ni...”
Sai Annabi ya biya masa ayoyin farko na suratul Fussilat zuwa ayata 14.
Utba ya bada hankalinsa tabbar Qur'ani ya ratsa shi tabbas bai taba jin wani abin saurareba irin wannan...
Daya koma wajen kafiran kuraishawa sai suka tambayeshi ya kukai, jama'a ana son jin tsegumi a samu sabon abin tsokanar ma'aiki dashi. Sai utba yace dasu “Na rantse da Allah naji wata magana, ban taba jin irinsa ba, Na rantse da Allah, ba waka bace, ba kuma sihiri bane....” yaci gaba dayi musu jawabi yana mai nuna musu cewa su kyale wannan Mutum ya cigaba da abinda yake, ya kuma yabi abinda ya saurara ya kuma nuna musu cewa idan da'awar Annabi tayi tasiri to hakika ribarsu ce... 
Da jin haka sai sukace lallai Muhammad ya asirceshi.

Daga nan sai suka sauya shawara, don dai sunga wannan kira da Annabi yake kullum sai samun cigaba, azabtarwarsu basa amfanar da komai... Sai suka bukaci cewa Annabi Muhammad yazo su hada kai su bautawa Allah tare, amma da sharadi shima zai rinka taya su bautar gumakansu... Nan ma dai sai Allab ya saukar da suratul kaafirun (Qulya ayyuhal kafirun...)
Daga nan sai suka sake dabara, sukace sunji yaje yayi addininsa amma ya cire duk inda ake aibata iyayensu da bautar gumaka, shima nan sai Allah ya saukar da ayar nan ta cikin suratul Yunus "Kace musu bai kasance agareni in chanja shi (Qur'ani) don ganin dama na ba, ni dai kawai ina bin abinda akai min wahayinsa ne."

Da kafirai su kaga tabbas bukatunsa bazasu biya ba, sai sukace abinda ya dace suyi yanzu shine su kure Annabi, don haka sai suka nemi yazo musu da aya. Ayar kuwa itace suna so ya tsaga musu wata gida biyu. Ai kuwa take sai mu'ujiza ta afku watan ya tsage, Ma'aiki yace musu to ku shaida, amma inaa sai sukace ai wannan sihiri ne.

Akace tabarmar kunya da hauka ake nadeta, da suka ga wannan ayar da suka bukata ta tabbata sai suka rinka bijiro da bukatu kala kala don dai su kure ma'aiki. Kamar suce bbaza suyi imani ba saiya rikito musu da sama, ko kuma a sauko musu da littafi jimla guda lokaci daya, ko kuma a samar musu da wata aljanna nan take, ko kuma nan take sunaso suga Annabi ya samarwa da kansa gida kasaitacce... Dama wasun haka duba suratul isra'i 90 zuwa 93. 

Wannan karon sai Allah ya basu amsa da cewa “Kace musu tsarki ya tabbata ga Allah, tabbas ni ban kasance ba face mutum kuma dan aike. (Dan aiken Allah)”
Domin Allah yasan koda an zo musu da wayannan ayoyi bijirewa zasuyi, ita kuwa sunnar Allah idan yazo da ayoyi masu girma kuma aka kafirce to tabbas kifar da al'ummar kafirai yake...

Zamu yada zango anan.


WAIWAYE ADON TAFIYA (14)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)

Kada a manta wannan gwarzon namijin da mu kace ya musulunta, harma mu kace sahabbai sunyi murna mutuka da musuluntarsa kamar yadda kafirai su kayi bakin ciki da barin addininsu da yayi. Wannan ba kowa bane face Sayyadina Hamza (R.A).

Kada kuma dai a manta har ila yau kafirai suna ganawa musulmai azabobi kala-kala, wanda wannan tasa idan har sahabi Abubakar ya riski ana azabtar da bawa akan yace Allah shine abin bautarsa shi kadai, to yanayin iyakar kokarinsa yaga ya sayi wannan bawa sannan ya 'yanta shi. Kamar yadda misali ya gabata akan bilal (R.A). 

Mu kara yin taku biyu zuwa baya kadan mu sake duba irin abinda larabawa suke bukatar a basu a matsayin hujja ko kuma aya. Wanda wannan zai kara bamu hujja akan cewa Allah yana sane da bai basu wasu abubuwan da suke bukata ba.

Duba ayar suratul Anfal da suke cewa "Indai wannan shine gaskiya daga gurin ka, to ka saukar mana da duwatsu (jefowa) daga sama ko kazo mana da azaba mai radadi." 
Maimakon su nemi shiriya sai su nemi azaba, kaga kenan babu alamar yin imani a tattare dasu.

Da takura, muzgunawa, gallazawa da azabtarwa tayiwa musulmi yawa, Annabi Muhammad saiya kasa jurewa don haka saiya umarchi sahabbansa da suyi hijira, suka tambaya zuwa ina? Sai yayi musu nuni izuwa Habasha, ya kuma gaya musu dalilinsa, cewa Habasha Ahlul kitaab ne, sannan sarkinsu Najashi yana da adalchi kuma guri ne na aminchi.

Wayanda sukai hijira sun hada da maza goma mata biyar. 

Mafi girman biyayya ga Allah shine Annabi Muhammad (S.A.W) don haka wannan hijira saida Allah ya bashi umarni sannan ya umarchi sahabbai da suyi. Duba suratul Zumar aya ta 10.

Kafirai suka bi bayan wayannan tsirarun mutane da sukai hijira, suna masu burin su kamo su su mayar dasu gida don gana musu sabon narko na azaba, wai mai neman kuka aka jefa da kashin awaki...

Sahabbai suka himmatu wajen ganin sun tserawa kafiran kuraishawa. Cikin sahabban akwai Usman ibn Affan tare da matarsa Rukayya yar gidan manzon Allah (S.A.W), da Abu salama da ummu salama, Mus'ab bn Umair, Usman bn Maz'un da wasunsu. Kuma a abinda Ibn Hisham ya rubuta shine Annabi ya wakilta Usman bn Maz'un a matsayin shugabansu. 
Nurul Yakeen (50)

Haka wayannan masu hijira suka rinka tafiya cikin gaggawa da tsoro da kuma fargabar kada abokanan bugawarsu suzo su kamasu. Babban tashin hankalinsu shine gabansu akwai kogi wanda idan har suka samu jinkiri na rashin jirgin ruwa to tabbas sunansu kamammu...

Suka karaso bakin tekun ai kuwa sai Allah ya duba zuciyoyinsu masu haske, suna zuwa suka tarar da jirgi suka biya suka nufi Habasha. Da mushrikai suka karaso basu samesu ba, sai suka juya makkah. Shi kuwa Annani mutanen da suke tare dashi sun ragu. 

Musulmai suka zauna a Habasha cikin kwanciyar hankali.
(Nabiyyur Rahma 49)

Sun gudu don tsira da addininsu, don yada addininsu da kuma neman waje mai aminchi ga musulmai. Karka manta mahaifarsa suka bari, da yan'uwansu don tsira da imaninsu. Amma wani zaici ya koshi ko alwala bai gama iyawaba zakaji tsakaninsa dasu sai habaici... Allah ya datar damu.

A irin wannan lokacine sahabi Umar bn Khaddab ya musulunta, kafin nan kuwa an sanshi da tsanani akan musulmai, shine na karshe a musulunta cikin Halifofin Annabi masu shiryarwa amma idan ka duba irin abubuwan da ya aiwatar saikayi tsammanin shine na farkonsu. Idan Allah ya bamu tsawon rai, akwai rubutu da zamuyi akan wannan bayan Allah. Insha Allah.
Wannan abubuwa sun faru a shekara ta biyar bayan fara kira.

Zamu dan yada zango anan.


WAIWAYE ADON TAFIYA (15)
Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Abdullahi bn Mas'ud yake cewa “Bamu gushe muna masu izza ba tunda umar ya musulunta.”
Dama kuma kafin nan Annabi Muhammad da kansa yayi addu'ar cewa Allah ya daukaka musulunchi da Umar ko muce ta sanadiyyar Umar. 

Ko lokacin daya musulunta shi bayyanawa yayi. haka nan bauta da akeyi a boye shine ya fara sawa a bayyanata. Kafirai sunyi bakin ciki mutuka.

A wannan shekara ta biyar bayan fara kira cikin watan ramadan sai Annabi ya iske manyan kuraishawa zaune a bakin ka'ada, mafi yawansu basa jin Qur'ani domin manyansu sun umarcesu da kada su sake su rinka saurara... Ayata ashirin da shida a fussilat tana kara fito da maganar tasu fili. 

Annabi sai yayi amfani da wannan damar sai kawai ya daga sauti ya fara karanta suratun Najmi, duk akai shiru ana saurararsa aka rasa wanda zai inkari, karatu mafi dadi daga sauti mafi kyawu, don haka wannan karatu ya ratsasu, ilahirin wajen yayi tsit ana sauraron masoyi (S.A.W)... Lokacin da yazo karshen surar (kuyi sujjada ga Allah ku bauta masa). Sai yayi sujjada, ai kuwa sai kafirai duk suka fadi suma suna masu sujjadar, cikinsu babu wanda ya iya jurewa saida yayi sujjadar... (Bukhari)

Kasan duniya da chanja labari, don haka wannan labari sai gashi har a Habasha, akaje aka gayawa sahabbai da sukaje Habasha cewa su dawo ai kafiran kuraishawa duka sun musulunta, cikin murna suka tattaro kayansu suka taho gida (Makkah), saidai tun kafin su shiga makkah suka gane akwai gyara a labarin daya riskesu. don haka sai wasunsu suka koma Habasha, wasunsu kuma suka shiga makka a boye ko kuma ta hanyar neman taimakon wani daga cikin kafiran. 

Mezai faru?
Sai azaba ta ninninku ga musulmai, babu shiri Annabi ya sake umartar sahabbai da suyi hijra zuwa ga Habasha a karo na biyu.
A wannan karon mazaje tamanin da biyu ne sukai hijira zuwa Habasha, idan aka hada harda Ammar adadinsu zai koma tamanin da uku domin shi Ammar anyi sabani akan hijirarsa. Mata kuwa guda sha takwas ne, wasu malaman tarihin kuma suna cewa sha tara.

Wannan hijira tafi wahala, tsanani da azabtarwa fiye da hijarar farko, hakanan sunfi fuskantar tsangwama da takura da 'keta daga kafirai fiye da wadda ta gabata.

Annabi ya shugabantar musu da Ja'afar ibn Abi Abi Dalib. A hanyarsu ne mucijiya ta sari Khalid Bn Hizam, kuma hakan ya zama ajalinsa.

Zamu yada zango anan.

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.