Posts

AUREN DOLE.

Wannan takaitaccen fadakarwa ce akan auren dole, hukuncinsa a addini da kuma shawarwari.... Mun tattara bayanan ne don amfanuwar Malamai, Dalibai, Iyaye, matasa da wasunsu. Aikin da mukai na dai-dai daga Allah ne, wanda mukayi na kuskure kuma dama mu yan Adam ne, muna rokon Allah daya gafarta mana. Ya kuma sanya littafin ya zama mai amfamarwa ne ga daukacin yan'uwa musulmi. Tare da mu Dan uwanku. Naseeb Abu Umar Alkanawiy. Da yar'uwarku. Shifaa khamis Adam. AUREN DOLE 0⃣1⃣ Tabbas soyayya jigo ce mai girma a zamantakewar auratayya. Shiyasa Allah da kansa yake cewa... "Yana daga cikin ayoyinSa ne, ya halitta muku matan aure daga rayukanku, domin ku nutsu zuwa gareta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani." Rum:21 Hakanan Annabin rahama yake fada cewa "Banga abinda yafi dacewa da masoya biyu ba sama da suyi aure". Anan zamu gane cewa soyayya jigo ce a cikin aure kuma da itane aure ...

Babban Sako.

BABBAN SAKO. Musulmai da dama a cikin kaso 99% na Qur'ani suna amfana ne da iyakar 1%.  Wayannan ina maganar musulmai masu karantashi ne bawai masu ajiye shi sai jefi-jefi ba. Da dama suna karanta Qur'anine don samun lada kawai sun manta da cewa. Yana maganin bakin ciki. Yana kawar da damuwa ga mai damuwa. Yana yalwata arziki. Yana haska zuciya. Yana karfafa fahimta. Yana sanya kwarin zuciya da tabbatuwa. Yana kawo _firaasa_. Yana zama sababi na amsa buqatu. Yana bada kariya daga cututtukan cikin jiki, kama daga kan na sassan jiki har zuwa na wasu organs na jiki. Yana bada kariya daga cutukan da suke a zuciya irinsu hassada, kyashi, kishi mara amfani da sauransu. Yana saka hangen nesa. Yana kawar da son duniya. Yana saka karfin gani da karfin sauran sassa kamar hakora, ji, da sauransu. Kai mutum kamar ni bai isa ya fadi kashi 3% daga 100% na amfanin Qur'ani ba. A takaice zan iya cewa Qur'ani kamar ruwa ne, wasu suna amfani dashi wajen sha ne kawai. Wa...

Tasirin fina-finai da littafai a rayuwarmu.

*Tasirin fina-finai da littafai a rayuwar mu*. Naseeb Auwal Abu Umar Alkanawy. Abinda kake tunani, da abinda kwakwalwarka take hange da kuma tsarin rayuwarka duk suna chanjawa sanadiyyar abubuwa da dama da suke faruwa. Mafi girman abinda yake sauya tunani kai tsaye ko kuma ta bayan fage shine kallon fina-finai da kuma karanta littafai.... Lokacin daka lizimchi karanta littafai masu kyau da manufa to tabbas zaka tsinci rayuwarka tana zama mai kyau da samun ingantacciyar manufa. Don haka ne zaka samu babu littafin dayake shiryarwa irin wanda aka saukar daga sama. Hakanan yadda kake karanta littafai marasa kyau, marasa manufa ko masu wani mummunan sako a kunshe a ciki a hankali zai sauyaka zuwa wannan yanayin. Don haka ne zaka samu mata masu kallon fina-finai da karanta littafai marasa kan gado basa wadatuwa da abinda mijinsu zai musu domin tuni zuciyarsu tayi gaba akwai tunanin irin mijin da take, don haka maimakon ta gode akan wani abin saikaga ta raina. Ita yadda taji ance mijin...

RIGA-KAFI

RIGA KAFI Don shawara ko neman karin bayani sai a neme mu a kafar whatsapp a lambar 08096699926, ko a turo da sakon email ta Nasibauwal@gmail.com. Gabatarwa Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon tsira Annabin rahama wanda aka aikoshi rahama ga talikai. Bayan haka, wannan wani takaitaccen rubutu ne wanda zan iya kiransa da amsa ko kuma shawara zuwa ga wasu masu tambaya ko neman shawara. Sau tari nakanyi rubutu irin wannan a kafar sadarwa duk don sauke wajibin da yake kaina na umarni da kyakykyawa da kuma hani ga mummuna, amma wannan karon saina zabi rubutashi a matsayin littafi don amfanuwar yan'uwa da kuma killaceshi ko wani ko wata zai buqaceshi nan gaba. Allah nake roko daya sanya littafin ya zamo mai albarka kuma mai shiryarwa izuwa abinda Allah ya yarda dashi. Abinda yake cikin littafin na dai-dai daga Allah ne, wanda kuma yake na kuskure, to daga...

ILMI KAFIN AURE.

Image
Ilmi shine ginshikin ko jigon da yake jagorantar rayuwar mutane zuwa ga inda ya dace a lokacin da ya dace. Da ilmi ne al'umma take samun cigaba, hakanan da shine abokan adawa suke cin galaba akan kishiyarsu, da kuma shine din dai al'umma take samun kariya daga sharrin abokan adawarta. Ilmi nada mutuqar muhimmanci...... Idan muka juyo da idanuwanmu zuwa ga  rayuwar mu a cikin gidajenmu, zamu ga cewa ilmi na taka muhimmiyar rawa wajen nuna mana yadda zamu tafiyar da rayuwarmu data abokan zamanmu..... Mu dauki rayuwar aure wadda a yanzu tana daga cikin manyan matsaloli anan kasar hausa, duba da yadda mace-macen aure yake kara yawaita da kuma rashin zaman lafiya. Wanda idan kayi nazari kayi bincike a karshe zaka tarar da cewa 90% na matsalolin ana samu ne saboda karancin ilmi, ragowar 10% dinma idan ka tsawaita yawatawa da tunaninka tofa zaka tabbatar da cewa rashin ilmin dai ba wani abuba. Kafin aure akwai abubuwa da dama daya kamata mutum ya sani dangane dashi auren, amma haka...

INA HANKALIN YA TAFI?

Idan aka samu bambamcin shekaru masu tazara, tabbas za'a samu bambamcin fahimta da kuma yanayin yadda kowa tsakanin babba da karami suke kallon rayuwa...... Ka tuna lokacin da kake hakikancewa abu kaza da kaza daidaine, yayinda iyayenka da sauran magabata suke nuna maka cewa ba dai-dai bane..... In kuwa hakane ina hankalin maza da yawa yake tafiya lokacin da suka auro yarinyar da aqalla tazarar shekarunsu yakai 8 ko goma sha..... Kuma suke tunanin samun tunanin ta irin nasu? Da zarar tayi wani abu wanda ke dauke da yarinta kuma sai kaga an fara samun matsaloli a haka sai kaga matsala tana ta barkewa. A lokacin da kake tare da yaro, kaima saika koma yaro wani lokacin ba don komai ba sai don ku zauna lafiya kuma ku samu fahimtar juna..... Ka dubi rayuwar Annabi (S.A.W) da Nana Aisha... Shin daya aureta hana ta komai na yarinta yayi ko kuwa? Sign Abu Umar Alkanawy.

MU FARKA YAN NIGERIA

Bugun zuciyar yana tafiya da sauri tamkar karar kofaton ingarman doki lokacin dayake sharara gudu a dandaryar kasa, yayinda ruwa ya taso daga cikin ido ya cike saman idon wanda hakan ya bada damar ganin komai dishi-dishi.... Kafin daga bisani ruwan ya rikede ya zama hawaye sakamakon satatowa da zaiyi ya wanke wadataccen filin fuskar...... A zahiri kenan, a badini kuwa bakin ciki cike yake da zuciya wanda sanin ciwon kai da kishin al'umma su suka haifar da wannan bakin ciki.... Ba imani, ba kudi, ba ilmi, ba tarbiyya, ba shugabanchi, ba tausayi, ba jinkai, ba...ba...ba........ Abin da yawa, bawai babu su bane gaba daya, akwai su amma sunyi karanchi... Wanda wani sashen ma babu wasu gaba daya. Ta yaya al'ummar da jahilanta suke mulkarta zataci gaba? Ta yaya al'ummar da manyanta basa tausayawa kanana, kuma kananan basa girmama na gaba zataci gaba? Tayaya rashin tsaro, rashin tsari, rashin tarbiyya, rashin imani, rashin ilmi zasu cakuda basu haifar da abinda yake barazana ...