Posts

WAIWAYE ADON TAFIYA. (6 - 10)

WAIWAYE ADON TAFIYA 6 Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)... Masoyi (S.A.W) tun daga yarintarsa ya taso da dabi'u mafi kyawu, dubi yadda muka bada labari  yadda kwanakin jahiliyya suke, amma sai Allah ya bawa Annabi muhammad kariya daga dukkanin wasu halaye ababen kyamata.  Da ace a yarintar Annabi an sameshi da wani laifi, kamar karya, rashin girmama na gaba, tsananin son mulki da sauran halaye to da abokan adawarsa sun tada jijiyoyin wuya akan abinda aka sameshi dashi mara kyau. Amma sai Allah ya tsarkakeshi tsarkakewa. Mafi girman abinda larabawa suka himmatu akai a wayannan kwanaki akwai caca, shan giya da kuma bautar gumaka, amma Annabi bai taba yin koda daya daga cikin wannan ba. Domin ya haramtawa kansa shan giya, caca, bautar gumaka ko kuma cin abin yankan da aka yankashi ga gunki. Tun a yarintarsa ya tsani gumaka kamar yadda ya tsani waka da alfasha... (Nurul Yaqeen 23)  Har saida mutane suke kiransa da sunaye na girmamawa da karramawa, cikin wayannan sunaye akwai A...

KASATA NIGERIA

Image
Shekaru lambobi ne kawai, aikin da akai a cikinsu shi yake mayar da shekarun su zama ababen sha'awa ko ababen kyamata...  Ko kana iya tuno wata shekara da wani abin burgewa ko sha'awa ya faru?  Idan ka tuno me kake ji? Hakanan ko kana iya tuno wani lokaci da kayi wani abin kunya, abin kyamata ko haushi? Idan ka tuno me kake ji? Wannan kadai ya isa ya tabbatar maka da cewa shekaru, watanni da kwanaki lambobi ne kawai, kuma aikin da aka aiwatar cikin wayannan lambobi shine abin dubawa ba yawan lambobin ba. Wani lokacin zai iya zama abin kunya ace ga tarin shekaru amma babu wani abin amfani a cikinsu, abin kunyar yana karuwa idan akace bayan shekarun akwai damammaki na amfanar shekarun amma ba'ai amfani da wayannan damammakin ba. Kasata Nigeria! Alfarma ta sanya ma'aikatan da zasu cicciba kasar zuwa ga tudun tsira mafi yawansu nakasassu ne, domin ba nagarta ake dubawa ba, alfarma ake dubawa. Cin hanci da rashawa sun saka ayyukan alheri sunki aiwatuwa a wannan k...

DAMISAR TAKARDA...

Image
Da Sunan Allah mai rahama mai jin kai. Mafi girman abinda yake kara daraja da kimar mutum a rayuwa shine ilmi, gwargwadon darajar abinda mutum ya ilmantu akansa gwargwadon kimarsa da darajarsa. Don haka ne zaka iske mafi darajar mutane sune Annabawa, domin sunfi kowa ilmi, kuma ilminsu shine mafi darajar ilmummuka. Tabbas ilmi yana da darajar da duk wahalar da akasha akan nemansa ko kuma duk dukiyar da aka salwantar dominsa ba'ayi asara ba. Saina tuno kissoshin da muka karanta da kuma wayanda muka ji labari na irin dawainiya da wahalhalun da magabatan wannan al'umma suka sha a wajen neman ilmi, wannan ya hada da tafiye-tafiye da wahalhalu mabambanta. Kissoshi masu taba zukata, masu cike da almara, ababen tausayi da kuma dimbin darussa. Kissoshin suka sakani cikin wani yanayi na tsananin mamaki, saidai mamakin yana kaucewa idan na tuno da girma da darajar abinda suke nema wato ilmi. Idan muka kewayo wannan zamanin, wanda muke rayuwa a ciki. Za muga tabbas akwai gagar...

KNOWLEDGE AND ITS NEGATIVE EFFECT...

Image
Nowadays, sources of knowledge such as books, videos, audio, and apps are readily available, including Islamic knowledge. However, the availability of such knowledge can have both positive and negative effects. Islamic knowledge, or Sharia, is valuable and applicable in any situation, regardless of how good or bad the circumstances or people are. But in the olden days, people had to make tireless efforts to acquire knowledge, unlike the lazy instant gratification generation of today. These days, an uneducated person can simply download or buy weighty books without any guidance or instruction. However, simply reading voluminous books doesn't equate to knowledge. Without proper guidance and education, readers may develop negative perspectives on various issues, leading to terrorism or a lack of regard for Islamic principles. As such, it's crucial to seek knowledge from pious scholars and listen to respected sheikhs who are admired for their breadth of knowledge and th...

MAFI SOYUWAR MUTANE A WAJEN ALLAH!

*MAFI SOYUWAR MUTANE A WAJEN ALLAH*. Hadisi daga Ibn Umar (R.A), Masoyi (S.A.W) yana cewa _“Mafi soyuwar mutane a wajen Allah shine wanda yafi amfanar da mutane”_. *Silsilat-Assahiha* na Albaniy 906 Abu Umar Alkanawy yace  “Idan har mafi soyuwar halittu a wajen Allah sune mutane, to tabbas mafi soyuwar mutane a wajen Allah sune masu taimakon mutane. Ko ba'a fito fili an gaya maka ba zaka gane idan kayi la'akari da wasu abubuwa kamar haka. ★ Allah yana ninka sakayyar alheri cikin ayyukan da suke na taimakon bayinsa. Misali, wanda yayewa wani bakin ciki Allah zai yaye masa nasa bakin cikin anan duniya da lahira. Wanda yaji qan wayanda suke kasa, wanda yake sama zaiji kansa. Wanda ya ciyar da wani shima Allah zai ciyar dashi tare da shigar dashi Aljanna. Wanda ya bawa wani dama ya rinqa tatsar nonon dabbarsa don yasha (koda akuyace) Allah zai shigar dashi Aljanna. Wanda ya dauke dutse daga kan hanya ko wani abu mai cutarwa, Allah zai shigar dashi Aljanna. ★ Allah ya jingina sababi...

JAYAYYA DA ALFAHARI BA SHI NE ILMI BA

```MU KULA!```  Yawan surutu, yawan jayayya, yawan aibata malamai, ƙwaƙulo kura-kuran malamai, yawan hayaniya, yawan zuwa da wani abu wanda ya saɓawa wanda ake kai da kuma uwa uba tutiya da tinƙaho ba su ne alamun ilmi ba. Da a ce yawan jayayya da binciken aibin mutane shi ne ilmi da sahabbai sun fi kowa jayayya... Amma sai muka samu su ne mafi iya rufa asirin mutane da kuma kawar da kai daga jayayya. Ƙasa ba ta taɓa ɗaukar wani mutum mai kawar da kai da yiwa mutane uzuri sama da Annabi (S.A.W) ba. Kuma mun sani shi ne mafi cikar ilmi na addini da rayuwa. Don haka sai mu gane cewa addini ba hayaniya ko hauragiya ba ne, addini nutsuwa ne, sanin yakamata da kuma tarbiyya. Wannan kuwa shi mu ke kira ilmi. Abu Umar Alkanawy.

Next Generation!

Next Generation! .....Overloaded traveling car moving on the road loaded with huge amount of goods..... Not as usual, today its only three children are running after the ramshackle overloaded old car. They are shouting while running saying a word "Kiyaye!". An old driver who manage to share his seat with an additional passenger managed and threw three pieces of sweets to the three children. As they are doing frequently..... To my astonishment, children started fighting, strongers want to take either all three sweets or two, and the latter, the weakest one trying to make every effort to survive with one......... Think about it my people. These are our next generation. We really need to do our utmost to save the next generation..... What is your suggestion? Let us share ideas! Naseeb Auwal Abu umar Alkanawy!