Posts

IYAYEN KO MALAMAN?

ƊALIBAN, MALAMAN KO IYAYEN? Rubutawar Naseeb Auwal (Abu Umar Alkanawy)                     Da Shifaa Khamis Adam    ★      ★       ★     ★       ★ Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin rahama, shugaban farare da baƙaƙe. Bayan haka. Taɓarɓarewar ilmin addinin musulunchi da kuma rashin ganin girmansa abune daya samo asali daga wasu abubuwa da zamu tattaunasu a wannan rubutu, kafin nan yanada kyau muyi waiwaye wanda ake cewa adon tafiya. WAIWAYE ADON TAFIYA Lokacin zuwan turawan mulkin mallaka, sun tarar da sarakuna na wancan lokaci suna kula da alarammomi da sauran dalibai masu neman ilmin addini, sa'annan masu ilmin ababen girmamawa ne da kuma girma da kima a idon mutane. Da ...

MERCY FOR THE WORLDS

Image
MERCY FOR THE WORLDS... By Naseeb Abu Umar Alkanawy “And we have sent you not but as a mercy for the worlds.” Did you know that;  Never in the history of human conflict had any conqueror shed so little blood and was crowned with such remarkable success, than a prophet Muhammad (S.A.W)? (Muhammad rasulullah p.361) The number of his battles was 27, while he is reported to have sent out 60 forays and expedition, estimated by my beloved author Ibn Qayyim in his incomparable book 'Zad-al-ma'ad'. Although no fighting had taken place in many of them. To make long note short; on all these battles only 1018  persons, Muslims as well as non-muslims, lost their lives. Qadiy Muhammad sulaiman mansurpuri gives this figure after a detailed study. (Rahmatulil Alamin). Surprisingly, within a berief period of ten years more than a million square miles  was won for ISLAM. Brig. Gulzar Ahmad in his book 'The battles of the prophet of Allah' 1975 p. 28, stated that...

SHUGABANCHI 3

Umar ya nufi waje daga cikin gidan yana rike da takardar da mahaifiyarsa ta bashi. Soron cike yake da kashin dabbobi wayanda suke kiwatawa, tare da cewa kullum sai an share soron amma hakan bai hana kasar wajen cakuduwa da fitsari gami da kashin dabbobin ba, sanadiyyar haka yasa zakaji yanayin soron wani iri. Ya sanya hannunsa ya jawo kofar gidan wadda take a sakaye, duk tayi tsatsa. Tayi wata kara gami da tirjewa, amma sai gogan naka ya sanya karfi ya fincikota, karfin jan dayayi mata ya sanya kofar ta sallama ta budu tare da cewa tana tirjewa game da kartar kasa tamkar bata son motsawar. Ya kalli layin nasu wanda yake cike da ledoji barkatai, dududu fadin layin ko keke napep bazai iya shigowa ba. Tsakiyar layin kuma wata kwata ce wadda gurbataccen ruwa ya dankare ya tsaya a cikinta, a haka yaci gaba da tafiya kansa a kasa daga bisani ya samu guri kebantacce a gefen layin inda aka ajiye wani kututture, ya zauna akai. Ya kalli dama da hauni, yaga babu kowa inka dauke tatta...

SHUGABANCHI 2

Tun bayan fitowar matashi Umar daga dakin jarrabawar yake ta sake-sake a zuciyarsa gami da tunanin makomar wannan jarrabawa tasa, amma abinda yafi damunsa shine dubu dayar da aka karba daga hannunsa. “Idan naje gida me zan cewa Baba, tunda dai da ita suka dogara a matsayin cefanen gobe.” saurayin ya fada yana mai zurfafa tunani akan mafita. Duk da wasu daga yan'uwansa masu zana jarrabawa suna ta iface-iface domin kuwa yaune ranar kammala jarrabawar, yayinda wasu masu adadin shekaru basa wannan iface-iface, wasunsu ma tuni sun bar harabar makarantar... Tabbas wayanda suke baki a wajen zana wannan jarrabawar sunfi kowa murna da hauka gami da wauta. “Gaskiya ka burgeni da naga ka ware gefe ba'a wannan shirmen da kai,” wani mutum wanda yake da kimanin shekara 35 ya fada lokacin da yake mikowa matashi Umar hannu. Murmushi kawai umar yayi gami da amsa sallamar wannan mutumin. “Nifa wannan shine zana jarrabawata ta shida, kuma abu daya kawai nake nema. "Maths...

SHUGABANCHI 1

                          SHUGABANCHI .... Sabuwar hanya na bi , don wayar da kan al'umma akan halin da suke ciki a rayuwar yau . Na tsara bayanin nawa ta sigar labari ta yadda yan'uwa zasu karantashi cikin nishadi da kuma walwala . Ina fatan hakan bazaisa yan'uwa su kasa gane darussan da yake dauke da su ba .                           **         **          ** Farko Duk da iskar da take kadawa mai karfi hakan bai hana mutane fuskantar inda suka saka gaba ba. Mafi yawansu zaka iske cewa matasa ne kuma an zana kalmar FUSHI a fuskokinsu.... Suna tafe wasu basa ko magana yayinda zakaga wasu suna musayar magananganu a tsakaninsu.....

FUTURE WIFE

All seas of the world tumbled about my heart... I am always thinking and praying for my future lady... It seems like the type of lady i want, i like, i love... Is no longer exist.... I am not sure if they exist.... May be 3% out of 100%. There was a friend of mine whose eyes always teary sometimes watered, when it comes to our future topics. He told me that; finding a good lady right now is difficult. Although speaking personally (in my view) it's easier compare to finding a good boy for a girl. Nobody will deny that bad boys are well-out of order and culture than girls. To cut a long story short, let me say finding a partner nowadays either boy or girl is difficult. What's the way out? May Almighty guide us. Naseeb Auwal.

WAIWAYE ADON TAFIYA. (1 - 5)

Tatacciyar sirar Ma'aiki ( S.A.W ) Waiwaye Adon tafiya (1) Tatacciyar sirar Ma'aiki ( S.A.W ). Sakamakon buqatuwar yan uwa ga sirah , naga ya kamata in gabatar musu da ita tun lokacin jahiliyyah har zuwa inda Allah ya nufe mu da tiqewa . Tabbas jama'a suna buqatar sanin tarihi , domin kuwa da tarihine zasu san asalinsu , da manufarsu , da kuma hanyar dayafi kamata subi . Tabbas babu wani zamani da ake buqatar tataccan tarihi kamar wannan zamani . Saboda dalilai kamar hka . * Tarihin musulunchi yanà buqatar inganchi don tabbatar da abinda ya tabbata da kuma abinda aka farar dashi . * Tabbas akwai chanje chanje a tarihi da wasu masu son zuciya sukayi , duk Dan cimma wata manufa tasu . Kamar Yan Shi'ah , yan haqeeqah wahdatul wujudi , dadai sauransu . * Akwai labarai da kafirai ne suka qagosu suka sanyasu cikin musulunchi , daga baya kuma suke amfani dasu wajen suka ...