Posts

ILMI KAFIN AURE.

Image
Ilmi shine ginshikin ko jigon da yake jagorantar rayuwar mutane zuwa ga inda ya dace a lokacin da ya dace. Da ilmi ne al'umma take samun cigaba, hakanan da shine abokan adawa suke cin galaba akan kishiyarsu, da kuma shine din dai al'umma take samun kariya daga sharrin abokan adawarta. Ilmi nada mutuqar muhimmanci...... Idan muka juyo da idanuwanmu zuwa ga  rayuwar mu a cikin gidajenmu, zamu ga cewa ilmi na taka muhimmiyar rawa wajen nuna mana yadda zamu tafiyar da rayuwarmu data abokan zamanmu..... Mu dauki rayuwar aure wadda a yanzu tana daga cikin manyan matsaloli anan kasar hausa, duba da yadda mace-macen aure yake kara yawaita da kuma rashin zaman lafiya. Wanda idan kayi nazari kayi bincike a karshe zaka tarar da cewa 90% na matsalolin ana samu ne saboda karancin ilmi, ragowar 10% dinma idan ka tsawaita yawatawa da tunaninka tofa zaka tabbatar da cewa rashin ilmin dai ba wani abuba. Kafin aure akwai abubuwa da dama daya kamata mutum ya sani dangane dashi auren, amma haka...

INA HANKALIN YA TAFI?

Idan aka samu bambamcin shekaru masu tazara, tabbas za'a samu bambamcin fahimta da kuma yanayin yadda kowa tsakanin babba da karami suke kallon rayuwa...... Ka tuna lokacin da kake hakikancewa abu kaza da kaza daidaine, yayinda iyayenka da sauran magabata suke nuna maka cewa ba dai-dai bane..... In kuwa hakane ina hankalin maza da yawa yake tafiya lokacin da suka auro yarinyar da aqalla tazarar shekarunsu yakai 8 ko goma sha..... Kuma suke tunanin samun tunanin ta irin nasu? Da zarar tayi wani abu wanda ke dauke da yarinta kuma sai kaga an fara samun matsaloli a haka sai kaga matsala tana ta barkewa. A lokacin da kake tare da yaro, kaima saika koma yaro wani lokacin ba don komai ba sai don ku zauna lafiya kuma ku samu fahimtar juna..... Ka dubi rayuwar Annabi (S.A.W) da Nana Aisha... Shin daya aureta hana ta komai na yarinta yayi ko kuwa? Sign Abu Umar Alkanawy.

MU FARKA YAN NIGERIA

Bugun zuciyar yana tafiya da sauri tamkar karar kofaton ingarman doki lokacin dayake sharara gudu a dandaryar kasa, yayinda ruwa ya taso daga cikin ido ya cike saman idon wanda hakan ya bada damar ganin komai dishi-dishi.... Kafin daga bisani ruwan ya rikede ya zama hawaye sakamakon satatowa da zaiyi ya wanke wadataccen filin fuskar...... A zahiri kenan, a badini kuwa bakin ciki cike yake da zuciya wanda sanin ciwon kai da kishin al'umma su suka haifar da wannan bakin ciki.... Ba imani, ba kudi, ba ilmi, ba tarbiyya, ba shugabanchi, ba tausayi, ba jinkai, ba...ba...ba........ Abin da yawa, bawai babu su bane gaba daya, akwai su amma sunyi karanchi... Wanda wani sashen ma babu wasu gaba daya. Ta yaya al'ummar da jahilanta suke mulkarta zataci gaba? Ta yaya al'ummar da manyanta basa tausayawa kanana, kuma kananan basa girmama na gaba zataci gaba? Tayaya rashin tsaro, rashin tsari, rashin tarbiyya, rashin imani, rashin ilmi zasu cakuda basu haifar da abinda yake barazana ...

MAGANIN BACIN RAI

Sau d dama za a gaya maka wata kalma mara dadi, ko kuma a aikata maka wani aiki mai bata rai...... Wannan abu kuwa zai iya zamowa daga mahaifi ne ko mahaifiya ko mata ko miji, Aboki, Dan uwa da sauransu. Hakan kwarai yana sanya rai ya baci. Amma idan ka kawar dakai ana kiran wannan da "Tausayi ko Afuwa" amma fa wannan tabon da bacin ran yana nan damfare a cikin zuciyarka. To ta yaya zaka tafiyar da wannan radadi na bacin ran? Tayaya zaka bawa zuciyar kariya saboda kada cututtuka su shige ta irinsu gillu (kullata) hassada ko hawan jini da waninsu? Bari muji babban likitanmu me yace akan hakan (QUR'ANI)💡 1⃣ A cikin suratul hjr Allah yana cewa "kuma hakika mu munsan cewa kirjinka yana kuntata saboda abnda suke fada (na munanan kalamai)# Kayi tasbihi da godiya ga ubangijinka sannan ka zamo daga cikin masu sujjada" 2⃣ A karshe karshen suratu Daha Allah yana cewa "Kayi hakuri dangane da abinda suke cewa, ka kuma yi tasbihi da godiya ga ubangijin...

MISALI ZUWA GA MA'AURATA

MADUBI ZUWA GA MA'AURATA... (Muhimmam misalai) By Naseeb Auwal Umar Maigida Bilal ya shigo gidan jikinsa a sanyaye, ya lallaba ya leka dakin uwargida safiyya ya ganta zaune ta tafka tagumi tana kallon yayanta guda uku da suke kwance suna bacci... Ganin haka yasa idon Bilal ya ciko da kwalla yayi maza ya share kwallar sannan ya kira sunanta a hankali ta yanda wayannan yara bazasu farka ba, tayi saurin dagowa tayi murmushi tana mai boye damuwarta ta taso tazo inda yake cikin fara'a tace "Sannu da zuwa". "Yawwa" ya amsa, sannan ya dora da cewa "kiyi hakuri, wallahi yau ban samo komai ba, don haka na bibiya ta wajen wayanda nake tunanin zan samu rance, amma kowa saina gama gaya masa sirrina saiyace min bashi da kudi.... A hanyata ta dawowa ne na samu ana wani aikin karfi, na tsaya na nemi alfarma na danyi shine suka bani wannan kudin..." ya nuna mata naira dari, "da itane na siyo garin kwaki don ke da yaran nan kusha saboda nasan kuna jin yu...

GWAJIN HAUSA

Kana jin hausa ko kuwa har fahimtarta kanayi? Karanta don bawa kanka amsa. Daga Naseeb Auwal (Abu Umar) Tsananin tsantsar tsabagen tsayuwar tsayin daka da iyaye nagari suke wajen bada tarbiyya shine ya bambantasu da malalatan iyaye masu malalaciyar tsayuwa akan yayansu. Wawa da wawaso zuwa ga abinda turawan yamma sukai watsi-watsitsinsa yasa wasu suke kallon rayuwa da ido guda na bangaren hagu, yayinda jahilchi yayi bake-bake ya banke kishiyar idon hagun. Makarancin mutum wanda ya kammala karanta littafai dubu ko fiye da haka, zaka sameshi baida ilmin sisi bare ma ya bawa wani.... Yayinda zaka samu wanda ya karanta littafai cikin yatsun dake dauke a tafukan hannu na dama, zaka sameshi da ilmi harma yana iya gamsar da wani..... Tabbas tsakanin na farko dana biyu akwai banbanci tamkar tsakanin jirgin sama da kuma wanda ke kan laulawa a hanya mai gargada, kai bari madai zaka iya kamantashi da gajiyayyen yaron da yake rike da filfilwa yana rangaji da taga-taga kamar zai fadi. Sassa...

FRUITFUL OR FRUITLESS ATTEMPT?

Image
FRUITLESS OR FRUITFUL ATTEMPT? "Naseeb, that's a fruitless attempt", she said, "... we are tired of your everlasting and never-ending complaints about manyan yara, when you can't change a situation, it is either you keep quiet or join the majority". She smiled a little; her eyes and teeth gleamed in the dark. Sometimes, silence is the best answer; that is why I kept silent, even though she said it jokingly, but I'm not tolerating this kind of mockery in my Da'awa life. Sometimes they used to say "We can't read your screed, but we like your thriller, especially one of Jatau's bag of magic". What a misplaced priority! My long writing about religion and culture is one I like most, and I could never convince them to read it all, and I knew they needed it too much, but they didn't know. Their hubby and obsession were always watching films and reading useless Hausa novels, like Hajjo Gano, a character in Aliyu Kamal's Hausa ...