Posts

Majalisar Mallam Jatau

0️⃣1️⃣ Sakamakon kowa yana zaman gida, hakan yasa majalisar kullum take cike da mutane tare da cewa ba wani yawan kirki ne dasu ba. Domin a unguwar akwai wayanda suka yarda dasu killace kawunansu kamar yadda gwabnati ta bukata, wasu kuma suna fita don yin harkokinsu. Amma shi mallam jatau da wasu tsirarun mutane sai suka zabi cewa zasu rinqa zaman majalisa da tattauna matsalolin rayuwa na yau da kullum. Ranar farko abinda aka fara tattaunawa shine matsalar gidan aure.  Inda a karshe matsayar da suka samu shine; ana samun matsala bayan aurene saboda irin soyayyar da ake nunawa a waje kafin aure ba a nuna koda makamanciyarta a gidajen aure. Don haka sai mallam jatau yayi musu huduba a ciki yake cewa _Kamata yayi ku rinqa taya matanku ayyukan gida da rainon yara da girki........_ yayi musu bayani sosai suka gamsu. Bayan majalisa ta tashi. Mutum na farko ya koma gida, shigarsa keda wuya ya iske matarsa tana harhada kayan shan ruwa. Yana ganinta yayi murmushi yace “Zee baby” Ta dago cik...

INGANTACCIYAR MAGANA AKAN SIFFOFIN DA AKE SIFFANTA ALLAH (S.W.A) DA SU.

INGANTACCIYAR MAGANA GAME DA SUNAYE DA SIFFOFIN ALLAH. Babu wanda yasan hakikanin siffofin Allah da sunayensa sai shi ubangijin daya barwa kansa sani...... To in kuwa hakane babu wata siffa wadda zamu yarda da cewar ta Allah ce sai wadda muka san cewa daga gareshi take.  Mun kuwa san cewa babu wani abu daga Allah wanda ya wuce Qur'an da hadisi. In mun yarda da hakan to a Quran da hadisi kawai zamu dauko siffofi da sinayen Allah.... Wanda kuma yayi da'awar cewa shima yasan wasu wayanda babu su a Qur'an ko sunnah to saiya zo da hujja bayyananniya...... Dangane da maganar sunaye da siffofi gaba dayansu zamu iya rabasu zuwa kamar gida hudu. 1. Abinda Allah ya tabbatarwa da kansa, kamar ji, gani, ilmi da izzah. 2. Abinda Allah ya korewa kansa kamar rauni, nakasa da bacci. 3. Abinda Allah bai magana akansa ba amma saboda abin yana nuni da rauni dole a koreshi ga Allah. Kamar bakin ciki da kuka. Akwai bambanchi tsakanin fushi da baƙin ciki. Shi fushi anayinsa ne akan abin da ake d...

Darkest Era

We are living in the time of poverty and ignorance, and the age of darkness.... the best way to describe the era was the darkest era ...... Remember, We are like travellers with a guiding Map, which guides to the right path.... this map named Qur'an. Its unfortunately majority of us, think negatively and count theirselves as wise enough to know the way by their wrong and filthy mind...... Some people refuse to read the map, some read it but fail to apply the information, only few did both. Finally, remember, we still have a time, and our unstopable hard work will lead us to the right path and our wishes will come to fruition. Sign Naseeb Alkanawy 17/11/2019

THE MOST POWERFUL WEAPON

QUR'AN is a book, and BIBLE is also a book. Therefore, books are the most powerful weapons... and the most important and useful communicator...... The power of the brain, brain carrying capacity and thinking capacity of a person is depend of the books he read.... books are like food, you read them, and in return they build you, promote you and make you a man of education and standing and of a amazingly great stature....... Remember inside our hearts there are lions, non-readers lock their lions in a small cages, while readers let their lions out to chase their dreams....... Readers never giver-up. No matter how severe the failure.... they adapt, they overcome, they try again and move forward.... That's what they believe.... why not if its true that books turn zero to hero? With good books, nothing you can not do, nothing you can not have... and when heart of your hearts limit you, its the books that tell you "You are limitless"..... Books are more than to descri...

IYAYEN KO MALAMAN?

ƊALIBAN, MALAMAN KO IYAYEN? Rubutawar Naseeb Auwal (Abu Umar Alkanawy)                     Da Shifaa Khamis Adam    ★      ★       ★     ★       ★ Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin rahama, shugaban farare da baƙaƙe. Bayan haka. Taɓarɓarewar ilmin addinin musulunchi da kuma rashin ganin girmansa abune daya samo asali daga wasu abubuwa da zamu tattaunasu a wannan rubutu, kafin nan yanada kyau muyi waiwaye wanda ake cewa adon tafiya. WAIWAYE ADON TAFIYA Lokacin zuwan turawan mulkin mallaka, sun tarar da sarakuna na wancan lokaci suna kula da alarammomi da sauran dalibai masu neman ilmin addini, sa'annan masu ilmin ababen girmamawa ne da kuma girma da kima a idon mutane. Da ...

MERCY FOR THE WORLDS

Image
MERCY FOR THE WORLDS... By Naseeb Abu Umar Alkanawy “And we have sent you not but as a mercy for the worlds.” Did you know that;  Never in the history of human conflict had any conqueror shed so little blood and was crowned with such remarkable success, than a prophet Muhammad (S.A.W)? (Muhammad rasulullah p.361) The number of his battles was 27, while he is reported to have sent out 60 forays and expedition, estimated by my beloved author Ibn Qayyim in his incomparable book 'Zad-al-ma'ad'. Although no fighting had taken place in many of them. To make long note short; on all these battles only 1018  persons, Muslims as well as non-muslims, lost their lives. Qadiy Muhammad sulaiman mansurpuri gives this figure after a detailed study. (Rahmatulil Alamin). Surprisingly, within a berief period of ten years more than a million square miles  was won for ISLAM. Brig. Gulzar Ahmad in his book 'The battles of the prophet of Allah' 1975 p. 28, stated that...

SHUGABANCHI 3

Umar ya nufi waje daga cikin gidan yana rike da takardar da mahaifiyarsa ta bashi. Soron cike yake da kashin dabbobi wayanda suke kiwatawa, tare da cewa kullum sai an share soron amma hakan bai hana kasar wajen cakuduwa da fitsari gami da kashin dabbobin ba, sanadiyyar haka yasa zakaji yanayin soron wani iri. Ya sanya hannunsa ya jawo kofar gidan wadda take a sakaye, duk tayi tsatsa. Tayi wata kara gami da tirjewa, amma sai gogan naka ya sanya karfi ya fincikota, karfin jan dayayi mata ya sanya kofar ta sallama ta budu tare da cewa tana tirjewa game da kartar kasa tamkar bata son motsawar. Ya kalli layin nasu wanda yake cike da ledoji barkatai, dududu fadin layin ko keke napep bazai iya shigowa ba. Tsakiyar layin kuma wata kwata ce wadda gurbataccen ruwa ya dankare ya tsaya a cikinta, a haka yaci gaba da tafiya kansa a kasa daga bisani ya samu guri kebantacce a gefen layin inda aka ajiye wani kututture, ya zauna akai. Ya kalli dama da hauni, yaga babu kowa inka dauke tatta...