Posts

SHUGABANCHI 2

Tun bayan fitowar matashi Umar daga dakin jarrabawar yake ta sake-sake a zuciyarsa gami da tunanin makomar wannan jarrabawa tasa, amma abinda yafi damunsa shine dubu dayar da aka karba daga hannunsa. “Idan naje gida me zan cewa Baba, tunda dai da ita suka dogara a matsayin cefanen gobe.” saurayin ya fada yana mai zurfafa tunani akan mafita. Duk da wasu daga yan'uwansa masu zana jarrabawa suna ta iface-iface domin kuwa yaune ranar kammala jarrabawar, yayinda wasu masu adadin shekaru basa wannan iface-iface, wasunsu ma tuni sun bar harabar makarantar... Tabbas wayanda suke baki a wajen zana wannan jarrabawar sunfi kowa murna da hauka gami da wauta. “Gaskiya ka burgeni da naga ka ware gefe ba'a wannan shirmen da kai,” wani mutum wanda yake da kimanin shekara 35 ya fada lokacin da yake mikowa matashi Umar hannu. Murmushi kawai umar yayi gami da amsa sallamar wannan mutumin. “Nifa wannan shine zana jarrabawata ta shida, kuma abu daya kawai nake nema. "Maths...

SHUGABANCHI 1

                          SHUGABANCHI .... Sabuwar hanya na bi , don wayar da kan al'umma akan halin da suke ciki a rayuwar yau . Na tsara bayanin nawa ta sigar labari ta yadda yan'uwa zasu karantashi cikin nishadi da kuma walwala . Ina fatan hakan bazaisa yan'uwa su kasa gane darussan da yake dauke da su ba .                           **         **          ** Farko Duk da iskar da take kadawa mai karfi hakan bai hana mutane fuskantar inda suka saka gaba ba. Mafi yawansu zaka iske cewa matasa ne kuma an zana kalmar FUSHI a fuskokinsu.... Suna tafe wasu basa ko magana yayinda zakaga wasu suna musayar magananganu a tsakaninsu.....

FUTURE WIFE

All seas of the world tumbled about my heart... I am always thinking and praying for my future lady... It seems like the type of lady i want, i like, i love... Is no longer exist.... I am not sure if they exist.... May be 3% out of 100%. There was a friend of mine whose eyes always teary sometimes watered, when it comes to our future topics. He told me that; finding a good lady right now is difficult. Although speaking personally (in my view) it's easier compare to finding a good boy for a girl. Nobody will deny that bad boys are well-out of order and culture than girls. To cut a long story short, let me say finding a partner nowadays either boy or girl is difficult. What's the way out? May Almighty guide us. Naseeb Auwal.

ABOKIYAR ZAMA

"Kafin in kara aure ban fuskanchi wata matsala da uwargida ba, asalima ita take min kwalliya ko kuma ta zabo min kayan da zan saka idan ta fuskanchi zanje zance." Matashin mutaumin mai kimanin shekaru 35 yake fada a dai-dai lokacin da nake gab da shi a cikin keke napep. "Ranar daurin aure ma ita tayi min kwalliya, mukayi hotuna daga bisani na tafi wajen daurin auren, da safiyar washe garin daurin auren ita tazo har bangaren amaryar ta shirya mana kayan breakfast gamida wasu lemuka data ajiyewa amarya wanda ni banma san ta tanade suba...." Ya dan dakata yana mai lalubo hotunansa da matan nasa gamida da nuna mini. Yaci gaba da cewa; "lokacin da nakuda ta zowa amaryar, uwargidan ita ta kaita asibiti a motarta, bananan lokacin sai kawai waya tayo min tace amarya ta sauka suna asibiti kaza, dana je asibitin abinda na gani ya burgeni domin hatta yan'uwan amaryar duk yan kallo suka zama duk abinda ake bukata kafin suyi uwargida tayi... Hatta kayan da aka sanyawa...

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU

ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU. Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. 👉🏼Lokacin da akace musulmi ana nufin wani mutum wanda ya mika wuyansa ga Allah, ya hakura da son zuciyarsa, kuma ya zabi yayi rayuwa yadda musulunchi ya tsara masa. 👉🏼Idan akace Musulunchi, to wani addinine wanda bai bar komai ba saida yayi magana akansa, tun daga kan bautar Allah har zuwa shiga bandaki, cin abinci, kallon madubi, taje kai da kuma yanayin tsarin kwalliya. 👉🏼In kuwa hakane musulmi yana da kyau ya zama musulmi, kuma yana da kyau ya zama mai bin koyarwa addinin musulunchin. Bana mantawa da wani umarni da ubangiji ya bayar cewa _A shiga musulunchi gaba daya, kada abi hanyoyin shaidan_. Wato dukkanin tsarin rayuwa ya zama yadda Allah ya tsara bisa koyarwar sunnar masoyi (S.A.W) ba tare da an karkace anbi hanyar shaidanu ba. 👉🏼A watan azumi ana kokari mutuka wajen bauta, da kuma komawa ga Allah, saidai k...

RAMADAN SERIES

RAMADAN SERIES 01. "Mai gida ka tashi lokacin sahur fa yayi.... Ragowar abinda ya rage bai wuce minti 15 ba...." Maryam ta fada lokacin da kokarin ficewa dauke da abinci. Umar ya mike zaune, yana mai furta addu'ar tashi daga bacci. Bayan nan yayi maza ya fice daga daga dakin. A gaggauce ya wanke bakinsa gami da daura alwala dama kuma fitowarsa daga wanke kenan bacci ya dauke shi. Yana gamawa ya nufo dakin da suke ya zauna don cin abincin sahur tare dasu. "Hanan, Humaira da Aliyu ina yaya Usman?" Mai gida umar ya fada lokacin dayayi turus a bakin kofar dakin. "Yace shi bazai sahur ba yau", Hanan ta bada amsa. Wadda dama ita take biyewa Usman wanda yake da kimanin shekaru 20, sai ita da take da 17 sai kuma Humaira kanwarta mai shekaru 12 biye da ita kuma dan autansu ne Aliyu mai shekaru 8. Tana gama furta hakan dattijo Umar ya juya ya nufi dakin Usman ya taso shi. Bayan sun hallara dukkansu, sai Dattijon arziki umar ya fara da cewa.... "An...