TAFIYA A SALLAH!!!
TAMBAYA: Mutum ne yana sallah, sai yaji an kwankwasa ƙofar ɗakin da yake, sai yayi taku uku zuwa biyar ya buɗe ƙofar. Sallarsa tana nan ko ta ɓaci?
AMSA:
★ Hukuncin mutum yana sallah, sai ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofa.
★ Shin ya halatta ya je ya buɗe ƙofar, ko ya ci gaba da sallarsa?
Asali shi ne:
👉 Mutum ya ci gaba da sallarsa, kuma bai halatta ya katse ko ya yi motsi ba idan babu wata buƙata ta shari'a.
Sai dai idan: Akwai buƙata ta gaske, ko rashin buɗe ƙofar zai haifar da lahani, asara, ko matsala, to an yi rangwame kuma Shari'a ta yarda mutum ya yi motsi kaɗan ya buɗe ƙofar, sannan ya dawo ya ci gaba da sallarsa, matuƙar bai fita daga yanayin sallah ba.
Abin lura a wannan taƙaitacciyar amsa ko bayani:
1. Idan babu buƙata ko babu ƙaƙƙarfan dalili:
Bai kamata mai sallah ya je ya buɗe ƙofar ba. Ci gaba da sallah shi ne mafi alheri kuma shi ne dai dai.
2. Idan akwai buƙata:
Ya halatta ne ya taku kaɗan ya buɗe ƙofar. Amma da sharaɗi.
Sharadin shi ne: motsin ya zama kaɗan, ba tafiya mai yawa ba.
3. Idan ya fita daga yanayin sallah:
Misali: Idan ya fita daga ɗaki, ya je wani wuri, ya dawo, tofa sallarsa ta ɓaci, babu shakka.
Dalilai daga Sunnah
1. Buɗe ƙofa a cikin sallah.
“Annabi ﷺ yana sallah, sai ya buɗe wa A’isha (R.A) ƙofa, sannan ya koma ya ci gaba da sallarsa.”
Abu Dawud (922), Tirmizi (600)
Hadisi ne ingantacce
★ Wannan hadisi hujja ce cewa motsi kaɗan saboda buƙata ba ya ɓata sallah.
2. Ɗaukar Umama a sallah, kamar yanda ya zo a Bukhari (516) da Muslim (543)
★ Ɗaukar yaro motsi ne, amma ba ya ɓata sallah.
3. Amsa sallama da ishara, wato ɗaga hannu. Kamar yanda ya tabbata a Sunan Abu Dawud (927)
★ Ishara motsi ne kaɗan, amma sallah tana nan.
Maganganun Malaman Mazhaba Huɗu
1. Hanafiyya:
Sallah ba ta ɓaci da motsi kaɗan; tana ɓaci da motsi mai yawa a jere.
2. Malikiyya:
Motsi kaɗan halal ne idan akwai buƙata; amma motsi mai yawa yana ɓata sallah.
3. Shafiʿiyya:
Motsi kaɗan ba ya ɓata sallah, ko da babu buƙata; mai yawa yana ɓata ta.
Ḥanabila:
Motsi kaɗan ana yarda da shi idan da buƙata; mai yawa yana ɓata sallah.
★ Ashe dukkanin mazhabobi sun yarda da wannan ƙa’ida.
Maganar Shaykh al-Islām Ibn Taymiyya
“Motsi kaɗan a cikin sallah idan da buƙata, ba ya ɓata ta bisa ijma’in malamai. Abin da ke ɓata sallah shi ne motsi mai yawa wanda ke fitar da mutum daga yanayin sallah.”
Majmū al-Fatāwā (22/559)
Misalin Aikace-aikacen da za a iya yi a sallah.
★ Ɗaukar waya a saka silent
★ Ɗaga hannu don amsa sallama
★ Tafiya kaɗan, Amma fa tafiya mai yawa, kamar fita daga ɗaki tana ɓata, wanda yayi haka to sallah ta ɓaci...
✒️
Abu Umar Alkanawy
DOMIN SAMUN KARATUKANMU, SAI A BIBIYEMU A WANNAN LINK NA KASA...
https://whatsapp.com/channel/0029VaAlG584yltOSfbGOS2b
Comments
Post a Comment