MUHIMMANCIN ADDU'A A RANAKUN JUMA'A DA LARABA.
INGANCIN AMSA ADDU'A RANAR JUMA'A KO RANAR LARABA.
Dangane da ranar Juma'a hadisai ingantattu sun tabbata waƴanda kai tsaye Annabi Muhammad ya faɗi cewa a a ranar juma'a akwai wata sa'a da mutum idan yayi addu'a babu makawa sai an amsa masa.
Akwai ruwayar Abu Huraira (R.A) cikin Sahihul Bukhari (935) da Sahihu Muslim (852), da kuma ruwayar Abdullahi Ibn Salam (R.A) cikin Ibn Sunan Majah (1138) da Musnad Imam Ahmad (23458). Cikin wannan ruwayoyin biyu hadisan sun nuna duk wanda ya kasance yana sallah a wannan sa'ar kuma yayi addu'a to babu makawa za a amsa masa wannan addu'ar.
Akwai kuma ruwayar Jabir Ibn Abdullahi (R.A) a Sunan Abi Dawud (1046), Sunan Nasa'i (1389) da kuma Sunan Ibn Majah (1139). Wanda shi kuma a tasa ruwayar ya nuna cewa lokacin shi ne bayan sallar La'asar, sannan bai ambaci cewa sai mutum yana sallah ba.
Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa lokacin amsa addu'a a Ranar Juma'a shi ne bayan Sallar La'asar, wannan shi ne ra'ayin Imam Ahmad, Ibn Qayyim, Ibn Hajar, Imam Nawawiy da mafi yawan malamai.
★ Dangane da amsa addu'a ranar Laraba kuwa akwai wani lokaci da sahabbai suka lura da shi, wato ranar Larabar tsakanin Azahar da La’asar...
Wannan kuwa ba daga bakin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kai tsaye ba ne, daga abin da su sahabban suka gani ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi addu'a ranar Litinin da ranar Talata, ya kuma ƙara yi a ranar Laraba tsakanin Azahar da La'asar, sai kuma suka ga alamun bushara a fuskarsa alamar an amsa masa a ranar Laraba ɗin.
An ruwaito daga Jabir Ibn Abdullahi (R.A) cewa: “Manzon Allah ya yi addu’a a Masallacin Fathu sau uku: ranar Litinin, Talata, da Laraba. Sai aka amsa masa addu’a ranar Laraba tsakanin salloli biyu, sai farin ciki ya bayyana a fuskarsa.”
Jabir ya ce: “Tun daga lokacin, duk lokacin da wani abu mai muhimmanci ya taso mini, sai in nemi wannan lokacin in yi addu’a, kuma koda yaushe ana amsawa.”
An rawaito hadisin a Musnad Imam Ahmad, Musnad Bazzar, Dala'ilun Nubawwa na Baihaƙi, kuma malaman hadisi sun ingantashi kamar Ibn Hajar, Ibn Rajab da Kuma Albany a Sahihut Targheeb (1185).
Malamai kamar Ibn Rajab, Imam Shaukaniy, Ibn Hajar da sauransu suka ce: “Kalmar 'tsakanin salloli biyu' tana nufin tsakanin Azahar da La’asar. Saboda haka suka ƙara da cewa ana son mutum ya yawaita addu’a a wannan lokaci, domin ana sa ran amsawa kamar yadda Jabir (R.A) ya yi.
★ Don haka duka lokuta biyun nan ana sa ran amsa addu'a a cikinsu.
1. Lokacin cikin ranar Juma’a (wanda Manzon Allah ya tabbatar da shi daga bakinsa mai tsarki)
2. Da kuma Laraba tsakanin Azahar da La’asar, wanda sahabbai suka tabbatar da shi a aikin Annabin Rahama Sallallahu Alaihi Wasallama.
Kuma duka hadisan isnadinsu ingantacce ne. Kuma babu cin karo a cikinsu.
★ Samun lokacin amsa addu'a a ranar Juma'a ba ya kore samun lokacin amsa addu'a a ranar Laraba. Domin ita addu'a a dukkanin lokacin da aka yi ta to ana karɓarta, kawai dai wasu lokutan sun fi wasu lokutan falala.
Sayyadina Umar (R.A) yana cewa: “Duk lokacin da na roƙi Allah wani abu to nasan lallai zan samu, saboda Allah shi ya ba ni ikon roƙarsa.” ko kamar yanda yace.
Allah ne mafi sani.
Allah ya ƙarawa rayuwarmu albarka, ya azirtamu, ya inganta lafiyarmu, ya amintar da mu, ya bamu ilmi mai amfani, ya shirya mana zuri'a, ya kuma sadamu da Annabin rahama da salihan bayi a cikin Aljanna maɗaukakiya.
✒️
Abu Umar Alkanawy
12th Nov 2025
Comments
Post a Comment