SHARHIN HADISI NA 19
Daga Ibn Abbas Allah ya yarda da su yace "Wata rana na kasance a bayan Annabin rahama, sai yace da ni "Ya kai yaro, ka kiyaye (dokokin) Allah, zai kiyaye ka. Ka kiyaye (dokokin) Allah, za ka same shi a gabanka. Idan za kai roƙo, ka roƙi Allah. Idan za ka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah. Kuma ka sani, lallai da al'umma za su taru don su amfanar da kai da wani abu, ba za su amfanar da kai da komai ba, sai da abin da Allah ya rubuta a gareka. Kuma haka nan da za su taru don su cutar da kai da wani abu, ba za su iya cutar da kai ba, sai da abin da Allah ya rubuta a gareka. An ɗage alƙaluma, kuma takardun sun bushe...
Wannan ruwayar Imam Tirmidhi ce, kuma sanadin ingantacce ne.
Wannan hadisi ya tattare bayanai da fa'idoji da yawa wanda kowace fa'ida a ciki abar ayi rubutu mai zaman kansa ne akanta, amma inshaa Allah zamu taƙaita a rubuce rubuce masu zuwa.
A cikin wannan hadisi a jimlace za mu gane sauƙin kan Manzon Rahama, domin dukkanin wayannan muhimman maganganu da yayi ya yi su ne ga ƙaramin yaro. A nan zamu gane cewa ashe yara tun suna ƙanamu ake koyar da su ilmin sanin Allah, da kuma tsoron Allah.
Dangane da faɗinsa (S.A.W)
Ka kiyaye Allah, Zai kiyayeka.
Yana nufin Ka kiyaye dokokin Allah, idan ka yi haka to lallai Allah zai kiyayeka.
Daga cikin sunayen Allah akwai Alkareem, wato Mai Karamci, a irin karamci na Allah, bawa ba ya taɓa yin wani abu dominsa face ya maidawa bawan da mafi alheri ninkin-ba-ninkin, tun kuwa a nan duniya, kafin kuma a je lahira wanda a nan bawa zai gane lallai wannan suna na karamci bai dace da kowa ba sai Allah.
Ayoyi da yawa sun nuna cewa "Wanda ya ji tsoron Allah...Allah zai ba shi mafita, kai bama iyakar mafita ba, bayan mafitar Allah zai sauƙaƙa masa al'amuransa..."
Hadisai da dama sun tabbata da cewa wanda ya bar wani abu saboda Allah, Allah zai musanya masa da wanda ya fi shi.
Rashin sanin wannan ya sa gama-garim mutane suke mamakin bayin Allah na kwarai da irin sadaukarwar da suke yiwa addinin Allah da Manzonsa, su kuwa bayin Allah nagari suna sane da cewa akwai sakamako gami da ƙari akan abin da suka aikata daga gurin mahalicci mai karamci.
Bayan gajeran bayani akan jimlar Ka kiyaye Allah, Zai kiyayeka.
Zamu ƙara bayani a taƙaice kafin mu tafi zuwa jimla ta gaba, za mu ƙara bayanin ne saboda buƙatuwar al'umma da irin waƴannan bayanai musamman a irin wannan zamani da mutane sukai nisa da fahimtar nassoshin shari'a, sai yawaitar karatu amma babu fahimta babu ilmi.
Allah (S.W.A) yana cewa
{من عمل صالحاً من ذكر أو أنثى وهو مؤمن فلنحيينه حياة طيبة} [النحل:97].
Ma'ana: Wanda yayi aiki nagari daga cikin masu imani maza da mata, lallai Allah zai raya shi rayuwa mai kyau. Kenan kiyaye dokokin Allah yana kawo kyakkyawar rayuwa, kyakykyawar rayuwa kuwa ita ce rayuwar da za a yi ta ƙarƙashin jagorori nagari, zaman lafiya, wadata, da kuma al'umma nagari.
Duk da haka, za ka iske wani yana da bakin magana lokacin da malamai masana sukai kiran mutane cewa su nemi sauƙi a wajen Allah ta hanyar gyara mu'amalarsu da shi da kiyaye dokokinsa... Sai ka ji mutum yana musu ko yana nuna babu alaƙa tsakanin tsananin rayuwa da kuma saɓawa Allah. Allah ya kyauta.
A wata ayar kuma Allah Maɗaukaki yake cewa:
{وما أصابكم من مصيبة فبما كسبت أيديكم} [الشورى:30].
Ma'ana: Abin da yake samun bayi na daga masifa da bala'o'i yana afkuwa ne sakamakon abin da suka aikata ma laifi.
Ayoyi irin wayannan a cikin Qur'ani suna da yawa, kuma hadisai da wannan ma'anar suna da yawa, haka nan wanda ya san rayuwa zai gane haka cikin rayuwarsa ta yau da kullum, sai dai idan talala Allah yake masa.
Muna neman tsarin Allah.
Allah ya shiryar da mu, ya kuma kawo mana sauƙin rayuwa, ya azurta garuruwanmu da arziki da aminci.
Mu sake dubawa mu ga cewa lokacin da Annabin Allah Yunus (A.S) ya faɗa cikin kifi da ya nemi taimakon Allah me Allah ya ce akansa...
{فلو لا أنه كان من المسبحين للبث في بطنه إلى يوم يبعثون } [الصافات:143-144]
Ma'ana; Ba don ya kasance daga cikin masu tasbihi ba, da (zamu bar shi) ya zauna a cikin (kifin) har zuwa ranar tashi (ranar lahira).
A nan kenan, ambaton Allah da yake shi ne silar da ta janyo masa aka tseratar da shi, aka sauƙaƙa masa rayuwa a cikin kifin, kuma aka fito da shi daga duhu zuwa haske, sannan aka ba shi tukuici na imanin al'ummarsa ba ki ɗayansu.
Ƙarkashin wannan zamu gane cewa Allah yana amsa roƙon baya ya kuma biya masa buƙatu tare da bashi kariya gwargwadon shi ma yanda ya bawa addinin Allah kariya, kuma gwargwadon yanda yake kiyaye dokokin Allah.
Mu tuna lokacin da fir'auna ya faɗa cikin teku, har da ya ga hallaka ta zo masa sai ya kada baki ya ambaci Allah, amma hakan bai amfanar da shi ba, Allah maɗaukaki yana cewa dangane da lamarin Fir'auna...
{آمنت أنه لا إله إلا الذي آمنت به بنو إسرائيل...... الآن وقد عصيت قبل وكنت من المفسدين} [يونس:90-91].
Ma'ana
Lokacin da Fir'auna yaga hallaka sai yace "Na yi imani, lallai babu abin bautawa bisa ga chanchanta sai ubangijin da Banu Isra'ila suka yarda da shi (Allah)..." Sai Allah ya bashi amsa ta hanyar mala'ika... "Sai yanzu kuma (da kaga halaka ƙiri-ƙiri) bayan ka riga da ka yiyyi saɓo kuma ka kasance daga cikin masu fasadi..."
A nan zamu ga shi Fir'auna saboda ba ya kiyaye dokikin Allah bai tsira ba, shi kuwa Annabin Allah Yunus (A.S) tun da mai kiyaye dokokin Allah ne sai aka tseratar da shi, tare da cewa tseratar da shi yafi zama abu mai wahala, domin shi Fir'auna a cikin ruwa ne kawai, shi kuma Annabi Yunus (A.S) a cikin ruwa ne, kuma a cikin kifi.
Allah muna roƙonka da ka bamu ikon bin dokokinka, tare da bin sunnar Annabinka, lallai kai mai iko ne akan komai.
Abin lura...
Da Annabi Yunus (A.S) da Fir'auna dukkaninsu sun faɗa cikin ruwa, kuma sun tabbatar da cewa sun hallaka, dukkaninsu sun kira Allah suna ma su neman agaji...
Sai Allah ya tseratar da Annabi Yunus (R.A) saboda shi mai tunawa da Allah ne a cikin yalwa, shi kuma Fir'auna sai aka hallakar da shi saboda shi mai mantawa da Allah ne a cikin yalwa.
Wannan shi zai sake fito da ma'anar wannan hadisi da Annabin Rahama (S.A.W) yake cewa "Ka tuna da Allah lokacin da kake cikin yalwa, zai tuna da kai lokacin da kake cikin tsanani."
A gaɓa ta biyu sai Annabi Muhammad yace da Ibn Abbas "Ka kiyaye (dokokin) Allah, za ka sameshi a gabanka (yana maka jagoranci)."
Abin nufi shi ne idan ka kiyaye dokokin Allah, to kamar yanda ka aikata abin da Allah ya ke so, haka shi ma zai yi maka jagora a al'amuranka cikin baka abubuwan da zasu gyara maka duniyarka da lahirarka, a irin wannan yanayi ne za ka iske wani lokacin kana tsananin son wani abu alhalin wannan abun cutarwa ne a wajenka, sai Allah ya hanaka wannan abin don kada ka cutu, sai ya musanya maka da mafi alheri, wani lokacin mutum da kansa yana gane hakan wani lokacin kuma Allah kaɗai yake riƙe sanin a wajensa.
Sanin wannan ne ya sanya wasu bayin ba sa taɓa damuwa don suna tsananin son wani abu amma Allah bai basu ba, saboda sun san cewa babu alheri a cikin samun wannan abin shi yasa Allah ya hana su.
Idan muka lura za mu ga hanyar da Annabi ya bi don koyar da Ibn Abbas hanya ce mai cike da jan hankali...
Na farko; Ya goya shi akan abin hawansa, wanda wannan falala ce ace Ibn Abbas (R.A) ya hau abin hawa ɗaya da Annabin rahama, wanda ɗaiɗaikun sahabbai ne suka samu wannan falalar.
Na biyu; Ya kirawo shi da lafazi mai jan hankali da kuma ba samar samar da nutsuwa, Yaa kai yaro...,
Na uku; Kasancewa an halicci mutum da son abin da zai amfanar da shi, da kuma son kansa, sai Annabin rahama ya fara kwaɗaitar da Abdullahi Ibn Abbas da cewa Ka kiyaye (dokokin) Allah, shi ma zai kiyayeka (kareka). A nan bayan an bashi umarni sai kuma aka gaya masa abin da zai samu shima, idan ya kiyaye dokokin Allah, to shi ma Allah zai kiyaye shi... Idan bayanin bai gama fito masa ba sai Annabin rahama ya ƙara fito masa da bayanin da kuma alakoro akan wancan sakamakon na farko, Ka kiyaye (dokokin) Allah, za ka same shi yana maka jagoranci... Shin akwai wani jagora sama da Allah?
Babu!
Sai Annabin Rahama rahama ya ƙara koro masa wani bayanin "Idan za kai roƙo, ka roƙi Allah..."
Wannan bayani dole zai ratsa zuciyar wannan Sahabi kuma ya riƙe maganar gagam, domin anyi gini mai kyau da maganar za ta zauna.
Addu'a ibada ce, don haka ba a roƙon kowa sai Allah.
Nassoshi da yawa sun zo akan haramcin roƙon wani ko neman biyan buƙatu a wajen wani wanda ba Allah ba, sai dai a irin abubuwan da Allah ya ƙaddara suna iya samuwa a hannun wasu bayi, kamar neman taimakon mai ƙarfi yayin da yake da ikon hana wani ya zalunceka, ko neman tallafin kuɗi a wajen mai wadata ko wanin haka...
Duk da haka dai neman wani abu a wajen bayi yana zubar da ƙimar mutum kuma abu ne da ba a so, don akwai sahabbai da sukai wa Annabi mubaya'a, cikin abin da sukai masa mubaya'a har da ba za su rinƙa tambayar mutane komai ba, don haka ɗayansu yana kan raƙuminsa bulalarsa za ta faɗo amma ba zai tambayi wani ya miƙa masa ba, ya gwammace ya zaunar da raƙumin ya sauka ya ɗauko bulalar sannan ya sake hawa kan raƙumin ya tashe shi sannan ya cigaba da tafiya.
Allah ka wadata mu, ka ka raba mu da ƙasƙanci, ka ɗaukaka mu, ka sa mu fi ƙarfin buƙatunmu.
Ameen
Idan za ka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah`
Bayan yiwa Ibn Abbas bayani akan kiyaye dokokin Allah da kuma kwadaitar da shi akan ribar kiyaye dokokin sai Annabin Rahama (S.A.W) ya sake jan hankalinsa akan roƙon Allah shi kaɗai da kuma neman taimakon Allah shi kaɗai.
Wannan kuwa don tabbatar da shi akan tauhidi da kaɗaita Allah akan dukkanin dangogin bauta, ta yanda ba zai roƙi wani wani abu wanda Allah ne kaɗai mai iko akai ba, haka nan ba zai nemi taimakon wani akan wani abu wanda Allah ne ke da ikon taimakawa ba.
Qur'ani cike yake da ayoyin da suke hana roƙon wani ko neman taimakon wani wanda ba Allah ba, sai dai a irin nau'in abin da Allah ya ƙaddara cewa ana iya samunsa a wajen bayinsa, kamar neman magani wanda zai saɓawa shari'a ba, kamar neman tallafi idan mutum zai wani abu da bashi da iko da sauransu.
Idan mutum ya yarda da cewa Arziki, haihuwa, Aminci, dacewa, shiriya, kariya da dangoginsu duka ana samunsu a wajen Allah mahalicci, to ba zai damu kansa da faɗawa hanyar bin bokaye ko malaman banza ba.
Allah ya karemu daga faɗawa cikin halaka, Allah ya shiryar da mu, Allah ya ƙarawa rayuwarmu albarka, ya kuma sadamu da alheran da Annabinsa kuma masoyinsa (S.A.W) ya nema a wajensa, ya kuma kiyayewa daga dukkan sharri, haƙiƙa shi mai iko ne kuma mai karamci.
Cigaba da bayanin hadisin Ibn Abbas (R.A)...
Har yanzu muna gaɓar da Annabin Rahama yake cewa Masoyinsa kuma ɗan uwansa na jini wato Ibn Abbas `Idan za ka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah`.
Tabbas neman taimakon wani a hurumin da Allah ne mai taimakawa wannan shirka ce, saboda idan mutum yana neman kariya, arziki, waraka, sa'a da sauransu duk a wajen Allah ake nema.
A nan za mu gane rashin dacewar maganar da wasu suke su rinƙa cewa Shehu kana gani.
Misali, Rayuwa ta yi tsada, shehu kana gani... Maƙiya suna so su ga bayana shehu kana gani, Shehu kana gani bani da kuɗi...
Wannan duk maganganu ne na shirka, kuma tsaf za su iya fitar da masu yinsu daga musulunci... Wani zai ce ai mu wasa mu ke yi abin ba wai har zuciyarmu ba.
To sai muce, ai wasa da Allah, ayoyinsa ko manzonsa shi ma aikin kafirci ne, kuma yana fitar da mai shi daga Musulunci, Allah maɗaukaki yana cewa:
(وَلَئِن سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ (65) لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ.. (66)) [التوبة].
Ma'ana: Kuma da za ka tambayesu sai suce ai mu wasa da zolaya kawai muke yi. Kace musu: Shin yanzu da Allah, da ayoyinsa, da Manzonsa ku ke yin izgili? Kada ku bada uzuri, lallai kun kafirta bayan imaninku. (Suratul Tauba)
Haka nan wasu za su ce ai kamun ƙafa mu ke da bayin Allah na kwarai. To suma wayannan shin sun manta akan wannan kamun ƙafar akaita dambarwa da kafiran Makkah?
Shi yasa a ƙa'idar addinin musulunci shi ne kada mutum ya aikata wani aiki, har sai yasan hukuncin Allah a cikinsa.
Annabi (S.A.W) ya cigaba da ce masa...
"...Kuma ka sani, lallai da al'umma za su taru don su amfanar da kai da wani abu, ba za su amfanar da kai da komai ba, sai da abin da Allah ya rubuta a gareka. Kuma haka nan da za su taru don su cutar da kai da wani abu, ba za su iya cutar da kai ba, sai da abin da Allah ya rubuta a gareka. An ɗage alƙaluma, kuma takardun sun bushe..."
Cikin wannan gaɓa akwai darussa masu girma wayanda duk wanda ya fahimcesu to fa babu shi babu damuwa, babu shi babu jin tsoro, babu shi babu neman yardar ababen halitta wajen kaucewa mahalicci.
★ Idan da dukkanin duniya za su taru don su cutar da mutum, ba za su iya cutar da shi sai dai idan Allah ya rubuta hakan, wannan kuwa shi ake kira da ƙaddara. Ƙaddara kuwa sananniyar aba ce, Allah ya rubutata tun kafin a haifi mutum, tun kafin a kafa garinsu, kai tun ma kafin a halicci kakanmu Annabi Adam (R.A).
★ A ƙarƙashin wannan za mu gane ma'anar cewa idan za kai roƙo ka roƙi Allah, ko idan za ka nemi taimako ka nemi taimakon Allah. Domin gashi kuwa nan an gaya mana cewa babu abin da al'umma za su iya yi don cutar da kai ko amfanar da kai, su kansu suna tafiya ne akan abin da aka ƙaddara musu. In kuwa haka ne to wanne dalili ne zai sanya in nemi taimako a wajen wanda shima ba shi da iko?
★ Har ila yau wannan kalmomi mu tuna ana gayawa Ibn Abbas ne a lokacin yana yaro, ashe kenan tun mutum yana ƙarami ake koyar da shi tauhidi da kuma dasa masa jarumta da rashin tsoron bayi a zuciyarsa.
★ Ka duba lokacin da Fir'auna yake da ƙarfin iko, ƙarfin mulki, ƙarfin runduna, ƙarfin dukiya... Amma duk da haka sai ya kasa hallakar da Annabi Musa (A.S) shi sai aka hallakar da shi.
★ Ka tuna lokacin yaƙin Badar, kafirai suna da duk wani sababi da zai iya ba su nasara, amma sai tsirarun mutane wayanda ba su gama ƙoshi ba, wasunsu ma suna zazzaɓi sukai galaba akansu...
★ Ka tuna lokacin da aka tattaro matasa aka jibge a ƙofar gidan Annabi (S.A.W) don su hallakashi, amma haka ya zo ya wuce ta gabansu ba su iya koda yi masa kallon banza ba.
★ Kamar yanda Hausawa suke cewa ƙaddara ta riga fata, to haka abin yake, ƙaddarar bayi a rubuce ta ke, kuma babu abin da yake juyar da ƙaddara sai addu'a.
Allah muna roƙonka kada ka jarrabemu da abin da ba zamu iya ba. Allah ka azirtamu, ka amintar da mu, ka bamu daga kyawawan wajenka.
Comments
Post a Comment