LIKITAN ZUCIYA...





LIKITAN ZUCIYA.... 

BABI NA FARKO

Me yake damuna?
Anya kuwa ina da imani irin wanda mutanen kwarai suke da shi?

Wayannan sune tambayoyin da suke kai kawo a cikin zuciyata. A wasu lokutan idan na roki Allah ina jin nauyi, domin ina tsananin neman tallafinsa, alhalin ni kuma bana sadar da abubuwan da ya umarceni da in sadar, hakanan bana nesantar da dama daga cikin abubuwan da yace in nesanta da su... Kunyar da nake ji tana ƙaruwa idan Allah ya biya min buƙatuna, duk da cewar ni bana aikata abubuwa da dama da yake so kuma ya yarda dasu...

Gashi inayin iyaƙar ƙoƙarina domin kaucewa abin da Allah mai girma da ɗaukaka ya haramta, amma wani lokacin sai son zuciya yayi rinjaye a kaina in keta alfarma da girman Allah, in gudu inda nake ganin babu mai ganina, in saɓawa Allah wanda shi yana ganina a kowane lokaci, a kowane yanayi a kuma ko ina... tabbas malamai sun yi gaskiya da sukace wanda yafi karfin zuciyarsa, yafi wanda yake iya rusa birni shi kaɗai jarumta..

Wai menene yake damun zuciyata?
Tabbas akwai wata cuta wadda tana bukatar likitan da zai yaye min ita. Likitan da zai bani maganin da zai sa zuciyar tayi laushi ta kuma dace da abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi. Zuciyar da zata kyamaci zunubai kamar yadda take kyamatar wuta... zuciyar da hutunta zai zama saboda ambaton Allah ne da nutsewa cikin abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi.

Wanene wannan likita?
Tambayar da na fara bijirar da ita kenan zuwa ga wani ɗan'uwa, wanda shi kuma ya turani wajen wani hamshaƙin malami... a wani gari nesa da mu kaɗan.

"Tabbas kana bukatar likitan zuciya."
A cewar malamin bayan ya saurari dukkanin bayanin da nayi masa. Sannan ya cigaba da cewa "Naji daɗi, domin kuwa wannan shi yake nuna Allah yana sonka da rahamarsa. Domin wasu sukan tsinci kansu a irin halin da kake ciki amma su a nasu shirmen suna ƙudurce cewa ai Allah mai gafara ne don haka basu da damuwa don suna afkawa zunubansa, sun manta cewa Allah wannan mai rahamar shi ne dai Allah wannan da ya tanadi wuta, shi ne wanda yakewa mutane talala kuma shi ne mai azabtar da bawa tun daga rayuwar duniya har zuwa ta lahira..."

Nayi shiru ina sauraronsa, yayin da nake ƙara tuno wasu laifukan da nayi waƴanda ni kaɗai nasan da su, sai kuma Allah wanda ya halicce ni. Hankalina ya kuma tashi lokacin dana tuno gudummuwata a ɓangaren hirar mutane, gulma, ƙarya da sauransu.

"Kana ji na?" Babban malamin ya ambata.
Na gyada kai alamar ina jinsa.
Sannan yaci gaba da cewa, zan turaka wajen likitan zuciya, sai dai baya kusa, yana can Bahagon Daji..."
"Bahagon Daji?" na tambaya cike da mamaki.
"Kwarai kuwa Bahagon Daji... Dajin tafiyar kwana uku ce daga nan zuwa can.... sai dai dajin yana da mutukar hatsari da abubuwa masu tsoratarwa... abin da nake so da kai shine ka sani zaka tafi neman ilmi ne, don haka ko mutuwa kayi a hanya ka mutu ne a hanyar neman ilmi. Sannan a hanyarka banda karya banda cin amana. Duk lokacin da wani abu ya shige maka duhu ka roki Allah..."

Malamin ya ja bakinsa yayi shiru.

"Mallam sai na koma gida nayi shiri kenan?" Na tambaya
"Daga nan ga hanyar dajin can." Ya faɗa yana nuna min wata hanya miƙaƙƙiya.
"Tohm, bari naje gida na debo kayan tafiyar..."
"Idan har ka sanar a gida baka buƙatar komai, Allah zai ciyar da kai zai kuma shayar da kai."

Jin haka nace masa "Eh na sanar musu cewa zanzo ɗaukar karatu."
Harna miƙe zan fara tafiya, sai ya kira sunana, na waigo ina kallonsa, fuskarsa cike da farin gemu, fuska mai annuri... "Gwargwadon ƙaryar da za kai gwargwadon wahalar da zaka sha...." ba tare da ya jira nace komai ba ya mai da kansa kan littafin hannunsa ya cigaba da karantawa.



BABI NA BIYU
Na tsaya ƙiƙam na kasa gaba na kasa baya.

"Akwai abin da kake bukata ne?"
Malamin ya tambaye ni.
"a'a" na fada cikin rawar murya.

"Aikuwa akwai muhimmin abin da ka manta" Mallam ya faɗa amma a wannan karon murmushi ne yake kaikawo akan leɓɓansa waƴanda su ne kariya tsakanin mai kallonsa da giɓinsa. Yayi shiru kamar yana nazarin wani abu a fuskata, wanda hakan ya tilasta min sunkuyar da kaina ƙasa. Kamar daga sama sai naji sautinsa yana cewa "Ba ka tambayeni a ainihin inda zaka iske wannan malamin ba, amma duk da baka tambaya ba zan maka bayani dalla-dalla, domin tafiyarka bata da ma'ana idan baka san wajenwa zakaje ba, idan kuma kasanshi amma baka san inda zaka sameshi ba to namma tafiyar tana zama wahala kawai babu biyan buƙata..."

Bai jira nace wani abu ba sai kawai ya cigaba da cewa "Bayan kayi tafiyar kwana uku idan har baka samu tangarɗa ba zaka iske wani fili mai yawan dogayen bishiyu da kuma ƙoramu... sai dai yana cike da muggan halittu... kuma za suyi ƙoƙarin hallakaka.... wanda zai fara cetonka daga hannun wannan halittu shi ne malamin da zan turaka wajensa... Ko ince nake ƙoƙarin turaka wajensa..."

Yana faɗin haka sai ya ɗora da cewa "Allah ya kiyaye hanya."

Nace Ameen, daga nan na ɗauki hanya har nayi nesa sai ya ƙwalamin kira, na juyo na kalleshi, sannan yace min "Kada kayi ha'inci domin ha'inci yana tattare da rashin nasara... Idan kana neman taimako ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa rijiyar da babu ruwa ko an jefa guga ciki ba zai ɗebo komai ba... kada ka dawo har sai ka haɗu da malaminka, sannan ka taho da shi nan wajena..."

Nayi shiru ina jinjina al'amarin duk da bansan wanne malami ba ne, amma ina tunanin anya zai yarda ya biyo ni?

Nan dai mukayi sallama, bisa ga mamakina sai naga Mallam yana zubar da hawaye.

Nayi jim kamar in tsaya, amma sai yayi min inkiya da babu komai in tafi kawai.

★     

Tun ina tafiya ina ganin mutane jefi-jefi har na dai na cin karo da su. Ina tafe ina tunane-tunane kala-kala. 

Bayan tafiya mai nisa da nayi na tsaya nayi sallar la'asar na dan kashingida sai kawai bacci ya ɗauke ni. Ban farka ba sai ganina nayi a wani tsiburi a tsakiyar teku.

Gabana ya faɗi firgigit na mike zaune, inka dauke tekun da yake kewa da tsuburin babu abin da zaka iya hangowa..... sararin samaniya yayi duhu lokaci zuwa lokaci kuma walkiya tana haskawa rugugin aradu ya rinƙa kaikawo a cikin kunnena. Tabbas wannan shi ne mafi abin tsoro da na gani a rayuwata...

Cikin ƙarfin hali na tashi zaune, abinbda na gani ya kara sanya razani da tsoro a cikin zuciyata... ko kunsan me na gani?
Wani mahayi ne akan doki da takobi a hannunsa tsirara ya tunkaroni da tsananin gudu kamar zai bangajeni... cikin razani na ambaci sunan Allah... kamar daga sama sai kawai naga tsuburin da tekun sun bace sannan sai gani a inda na kwanta bacci...

Nayi hamdala na godewa Allah. Na cigaba da ambaton Allah har asuba ta doso. Nayi sallah sannan nayi azkar naci abin da na samu daga  tsirrai.

Ina shirin cigaba da tafiya kawai sai na hango wasu gungun mutane da makamai sun nufo inda nake... babu mai cikakkiyar sutura a cikinsu yanayinsu tamkar arnan daji....

Tsoro da razani suka cika cikin zuciyata amma sai na dake na tsaya ƙiƙam.

Da isowarsu sai wani wanda da alama shi ne shugabansu ya matso kusa da ni cikin murtukewar fuska yace "Menene ya biyo da kai ta wannan yanki mai tsananin hatsari? Tabbas zan ɗanɗana maka azabar da wani daga cikin mutanenku ma'abota sanya sutura ba zai ƙara sha'awar biyowa ta nan ba..."
Kafin inyi wani yunƙuri tuni wasu zabga zabga guda biyu sun cakumeni sukai baya da hannuna suka ɗaureshi tamau.


BABI NA UKU
Nayi yunkurin cewa wani abu amma sai kawai naga wani kato ya kwashe ni kamar kayan wanki ya azani bisa kafaɗarsa suka wuce da ni...

Zuciyata ta rinƙa saƙe-saƙen abin da waƴannan mutane suke ƙoƙarin yi da ni ko kuma inda za su kai ni..... 
Ni dai ina tunanin zuci kawai sai tsintar kaina nayi a wani ginin ƙasa an yashar dabni gaban wani ƙaton mutum.

Duk inda ake neman kato wannan mutum ya kai, zaune kusa da shi kuma wata mata ce wadda bata kaishi girma ba. Dukkaninsu babu cikakkun sutura a tattare da su inka dauke fatar namun daji da suka rufe wasu sassa na jikinsu babu abin da zaka iya ƙirgawa a matsayin tufafi a jikinsu.

Mutumin ya ƙura min idanu daga bisani ya bushe da dariya, sannan yayi gyaran murya, ya lalubi wani ƙaho a kugunsa ya daga sama ni kuwa kawai sai na rintse ido ina jiran jin saukar wannan kahon a sashen jikina. Amma sai naji shiru sai wani wari kawai da ya mamaye ilahiran wajen.... na buɗe ido a hankali sai naga wannan ƙatoton mutum yana shan wani abu ne daga cikin wannan ƙahon. Daga bisani ya kawar da ƙahon daga bakinsa yana siɗe ragowar abin shan da ya rage a leɓɓansa har da wasu ƴan tsutsotsi da suke wutsil-wutsil.

"Zan maka adalci," ƙaton ya ambata. "Zan sa a shayar da jininka ga abin bauta yanzun nan, kayi godiya ga ubangijin ababen bauta wanda gareshi abin bautar mu yake miƙa buƙatunmu...."

Duk da ina cikin tashin hankali amma sai na daure nace da shi "Ina neman tsarin Ubangijin ababen bauta da masu bauta daga sharrinku domin jinina yafi ƙarfin abin da kuke yankawa..."

Wannan ƙato a fusace ya zare wata takobi da niyyar raba kaina da gangar jikina amma sai wannan mace ta kusa da shi ta dakatar da shi gami da jefo min tambaya.

"Kana nufin kana da tsarkin da za ka iya miƙa buƙatunka ga ubangijin ababen bauta?"
Ni kuwa nace mata kwarai kuwa "Ai ubangijin ababen bauta mai jin komai da kowa ne, kuma yana ganin kowa da komai babu abin da yake ɓoyuwa a gareshi... kuma koda yaushe ƙofarsa a buɗe take yana amsa roƙon masu roƙonsa......"

Ban kai gaɓa ba, wannan ƙaton ya daka min tsawa yace "Kai yaro karka raina mana wayo mana, wanene ubangijin ababen bauta?"

Cikin ƙwarin gwiwa na ba shi amsa "Ku ne kuke kiransa da wannan sunan, Amma sunansa Allah, shi ne wanda ya halicci sammai da ƙassai, shi ne wanda ya halicci rana da wata, kuma shi ne yake saukar da ruwan sama kuma shi ne yake fitar da tsirrai... ko a cikinku akwai wanda ya taɓa ganin wani matokari da ya tokare sama daga faɗowa?"
Ƙaton yayi shiru yana kallona cikin bacin rai, amma ga mamakinsa sai yaga da wannan mace ta kusa dashi da dukkanin mutanen da suke wannan waje sun amsa "Bamu taɓa gani ba...."

Naci gaba da cewa "To ikon Allah shi yake riƙe da saman. Kuma shi ne ya hanata faɗowa......"

Suka jinjina kawunansu a wannan karon har da shi ƙatoton. 

Akayi shiru tsawon wani lokaci.

Na rasa me zance, sai kawai wata dabara ta fado min. Sai nace ina so a kawo min abin bautar nasu in ganshi.
Wannan macen tayi inkiya ai kuwa take aka bijiro da shi... sai gashi wani dan guntun gunki ne wanda bai wuce zira'i uku ba, an sassakashi da itace.

Suka ajiye shi a gabana. Na kalleshi nace ina so ka kwanceni daga daurin da sukai min...
Gaba ɗayansu suka bushe da dariya suka cemin ai ba ya motsi ballantana ya kwanceka...

Ni kuwa sai nace "Kuma a hakan kuke miƙa bukatunku zuwa gareshi?"

"Idan kai wanda kake neman taimakon yana taimaka maka ai sai ka nemi taimakonsa yanzun indai har yana taimakawar zamu gani..."
Wani tsoho cikin wayannan mutane ya ambata cikin ɓacin rai.

Take gwiwata tayi sanyi, na tuno da tarin laifukan da nake aikatawa tabbas bana cikin bayin da zasu iya kuɓutar da waƴannan mutane daga cikin duhun da suke ciki.

Wannan katon ya kyalkyale da dariya, yace min "Ba zare idanu zakayi ba, cewa akai ka nemi ubangijinka daya kubutar dakai daga kullin da mukai maka....."

Na sunkuyar da kaina ƙasa ina mai jin nauyin abin da zan roƙi mahaliccina da shi.
"Ya ubangiji ni nasan na zalunci kaina.. ina neman gafararka da afuwarka... Ya Allah babu wanda zai iya fitar da ni daga halin da nake ciki sai kai, Ya Allah ka kuɓutar da ni wata ƙila waƴannan mutane su karɓi addininka... ya Allah ka kuɓutar dani...." ban gama rufe baki ba sai wannan mugun daurin da sukai min ya kwance.....

Kowa ya saki baki a cikinsu ni kuwa kunyar mahaliccina ta sake kamani domin ya fitar da ni kunya duk da irin laifukan da nake aikatawa a gareshi. Wani hawayen farin ciki gami da jinjina karramawar mahaliccina ya kwaranyo daga idanuna....

"Yaro munyi imani da ubangijinka, dama mun daɗe muna jin labarinsa. Yanzu daganan zamu koma cikin gari don bin addinin naku sau da ƙafa muna fatan za kai mana jagora..."

"Ni ina kan hanya yanzu haka zanje wajen wani malami don neman magani...."
"Idan ka amince zamu haɗaka da masu rakiya zuwa wajen malamin daga nan in kun dawo sai mu wuce tare da kai..... domin dajin yana da ababen tsoratarwa da dama....." ƙaton ya fada yana mai sakin fuska.

"Bana son wani a cikinku ya wahala don haka ku zauna ku jirani cikin ƙasa da kwana biyu zan dawo gareku da yardar Allah."

Duk ƙoƙarin da za suyi akan na yarda sunyi amma na bijire bisa dole suka ɗorani a hanya suka nuna min hanyar da ya kamata na bi domin na kwatanta musu inda aka ce zanga malamin da nake nema.

Naci gaba da tafiya na barsu a tsaitsaye suna kukan rabuwa da ni.

Sai da na shafe tsawon lokuta ina tafiya kafin inyi arangama da wani ƙaton zaki wanda ganinsa yasa numfashina ya yanke, bugun zuciyata ya koma rige-rige yayin da tunanin hanyar gudun tsira daga hallaka ya rinƙa cin karo a cikin kwakwalwata....

Zakin yayi gurnanin ya ɗaga kafafuwansa na gaba sama yana dukan kirjinsa da su yana girgiza kai cikin yanayi mai tsoratarwa. Fiƙoƙinsa suka fito cako-cako masu tsananin tsini da kaifi...
Ina ma dai na yarda a bani abokan tafiya daga wayancan mutanen...



BABI NA HUƊU
Hasken rana yana dukan haƙoran wannan zakin wanda hakan ke sanya su sheƙi da daukar ido... abin gwanin ban sha'awa ga wanda baya cikin tashin hankali irin nawa wannan zakin yayi tsalle ya dira a kaina ya turmusheni yana wani gurnani.... bansan lokacin dana ambaci sunayen Allah ba....

Ina ambatonsu bisa ga mamakina sai naga wannan zakin yaja da baya, ni kuwa na mike...

Zakin ya kara daga kafafuwansa na gaba ya daki kirjinsa dasu yana gurnani gami da girgiza. Ya sake bazamowa gareni........ abin daya fara dawowa cikin kwakwalwata shine labarin sahabin nan na Annabi (S.A.W) wanda Annabi ya aikeshi, a hanyarsa yaci karo da zaki kuma ya sanar da zakin cewa shi dan aiken dan aiken Allah ne..... da jin haka sai zakin yayi masa jagora...

Cikin zuciya mai cike da jarumta da miƙa al'amura ga Allah na kalli zakin nan na daka masa tsawa nace "Kai halitta ne daga halittun Allah, kamar yadda nima halitta ne daga halittun Allah. Idan har kana goyon bayan in isa zuwa ga inda zanje don haɗuwa da malamin da zai gyara tsakanina da Allah to ka barni in wuce, idan kuwa har kana gabatar da cinka da shanka akan son mahaliccinka to na halatta maka dukkanin jikina..."

Bisa ga mamakina sai naga wannan zakin yayi wani gunji gami da gurnani mai tsoratarwa ya taho gareni a guje, bugun zuciyata ya qaru na fara tunanin mutuwa, hakoran nan nasa masu tsini suka kara tayar min da hankali, idanuwansa kalar zuma suka dawwama akan fuskata yayinda yake kusantoni... yana karasowa inda nake sai kawai ya rungumeni... yana lashe fuskata cikin yanayi na nuna soyayya.... tabbas sai a lokacin na tabbatar mun zama abokan juna ni da shi.

Ya durƙusa ƙasa yayi min inkiya da in hau bayansa. Ai kuwa na hau bayansa ya tafi da ni cikin wannan daji mukaci gaba da tafiya tare... 

Haka mukaita tafiya tsawon yini ga sanyi mai ratsa sassan jiki tamkar kankara zata sauko daga sama.... 

Bayan tafiyar kwana daya da wuni guda sai muka zo wani waje, nesa damu kadan wasu manyan bishiyu ne, ga koramai da suke gudana ta kowace fuska..... muna zuwa wannan waje sai zakin yayi nin inkiya na sakko daga bayansa. Sai naga ya samu waje ya zauna. Tare dayi min inkiyar cewa in cigaba da tafiyata....

Nayi jim ina tunanin cewa wannan wajen da nake hangowa anan ne mallam yace zan hadu da malami wanda zai zamo likitan zuciyata...

Na nufi wannan hanyar, ina tafiya ina waigowa ina kallon wannan zakin..... har na kule a cikin dogayen bishiyun nan. Babu abin da ke damuna sama da sanyin wannan waje.

Ina cikin tafiya sai naji an jefe ni da kwakwa. Na waiga banga kowa ba, na cigaba da tafiya zuwa can sai naji an kuma jifa na da wata kwakwar, na sake waigawa banga kowa ba..... na cigaba da tafiyata can sai ganin wasu gungun birarrika nayi sun biyoni a baya suna jifana da kayayyaki kala-kala, wasu da duwatsu wasu da kwakwa wasu lemo wasu kankana da dai sauran kayan tsirrai nanfa muka kasa tsere da su... sai da na dauki tsawon lokaci ina gudu sannan muka riski wajen wani kututturan bishiya, bisa ga mamakina sai naga basa iya zuwa kusa da kututturan bishiyar..... don haka sai na matsa kusa da wannan kututture.

Akan wannan kututturen bishiyar akwai wata jakar fata, ɗaya daga cikinsu ya jefo min lemo, sai lemon nan ya sami wannan jaka, bisa ga mamakina sai naga sun rufeshi da duka..... da kyar ya samu yasha. Suka cigaba da jifana, sai na ankara da cewa wato duk wanda ya sami wannan jakar suna rufeshi da duka.... don haka sai na dauki jakar nan. Ina daukarta sai naga sum-sum-sum suna zamewa suna barin inda nake.

Anan na zauna ina ta jiran inga malamina amma shiru, abu kamar wasa saida nayi sati guda babu malamin babu alamarsa.

"Wataqila ya mutu" zuciyata ta ambata.
Don haka saina tashi nabi hanyar komawa inda na biyo bayan doguwar tafiya sai na iske wannan zakin a inda na bar shi yana jirana.

Na sake hawa bayansa bai ajiye niba sai a wajen wayannan mutanen dajin da nayi musu alkawarin zan dawo mu tafi tare dasu. Ya ajiyeni nesa kadan da su ya sake rungumeni sannan ya sumbaci goshina.

Har yanzu ina tare da wannan jaka, tare da cewa bansan menene a cikinta ba.

Da ni da su muka shirya tsaf don zuwa gurin mallam da ya aikeni. Sai dai tafiyar tawa babu nasara domin ban sadu da likitan zuciya ba. Ko da yake me yafi wannan daɗi ace mutane sun samu shiriya ta dalilinka?


BABI NA BIYAR
Muna tafe muna kusantar gidan Mallam amma ni zuciyata ta kasa samun nutsuwa saboda muhimmin abin da aka turani in yishi bai samu ba.

"Amma wata ƙila idan mallam yaga na musuluntar da waƴannan Mutanen Dajin zai ji daɗi..." Zuciyata ta ambata tare da cewa babu jin daɗi a cikinta saboda rashin nasara a wannan tafiya, duk da bakar wahalar da na sha.
A wani ɓangare na zuciyar kuwa ina jin cewa ai kuwa akwai babbar nasara tunda na musuluntar da alƙarya guda, sannan ga tsuntuwar jaka da nayi wadda Allah ne kaɗai yasan abin da ke ciki....

Muna tafe ni da shugaban mutanen Alkaryar da matarsa akan gaba, yayin da daukacin jama'arsu waƴanda sun doshi mutum dayri suna biye da mu.

Tun daga nesa na hango gidan mallam cike da Jama'a anata sharar kwalla, da alama wanine ya rasa rayuwarsa. Gabana ya fadi, a zuciyata nace "Babu mallam babu likitan zuciya..."

Muka ƙarasa ƙofar gidan mallam jama'a aka bimu da kallo, na tambaya shin ina mallam?
Wani dattijo cikin sheshshekar kuka yace min "Ai mallam rai yayi halinsa a daren jiya, yanzun nan ma daga makabarta muke."

Bansan lokacin dana durƙusa bisa gwiwoyina ba, na fashe da kuka na kuma rungume tsintacciyar jakata ƙamƙam. Wani sanyi ya ratsa har cikin zuciyata.

"Amma wanne mallam kake tambaya? Mallam babba ko dansa mallam karami?"
Wannan dattijon ya jefo min tambaya.

"Ma... Mal... Mallam Babba, dattijo mai farin gemu..."
Na ambata cikin rawar murya.

"Allah sarki, kayi haƙuri" tsohon ya ambata yana mai ƙura min idanu kamar ya sanni, daga bisani yace "Mallam ƙarami shi ne ya rasu, mallam babba gashi can a ƙarƙashin waccan rumfar sai ka je kayi masa gaisuwa...."

Tunda nake a rayuwata ban taba jin farin ciki irin na wannan lokaci ba.

Muka ɗunguma muka nufi mallam ni da mutanen daji, yayi murna matuƙa da ganinmu jama'a aka taru ana kallon ikon Allah, yaro karami ya musuluntar da alƙarya guda...
Su kansu Mutanen Daji, sunji mamakin yadda aka tarbesu da karramasu da akai..... masu gidaje suka rinƙa basu kyautar gidaje, wasu kuma suka rinƙa yankar musu filin noma daga gonakinsu, sutura kuwa ba'a bar wannan wajeba har sai da kowa a cikinsu ya samu sutura mai kyau...

Mallam cikin taron jama'ar nan yayi gyaran murya akayi tsit. 
"Ina likitan zuciyar?" Ya tambaya yana mai kallona.
Ni kuwa na sunkuyar da kaina kasa domin bani da amsa, lokaci guda hawaye ya fara kwaranyowa daga idanuwana.

Mallam maimata wannan tambayar, amma nayi shiru na kasa bashi amsa. Ya sake maimaita tambayar a karo na uku wannan karon cikin yanayin tsawa ya tambayeni.

"Ban haɗu da shi ba." Na bashi amsa cikin dakiya.
"Menene a hannun damanka?"
"Jaka ce, wadda na samo a cikin daji, da ita ne na tsira daga sharrin birirrika..." na bawa mallam amsa.
"Aina gaya maka" mallam ya fada, "zaka sadu da likitan a waje mai yawan dogayen bishiyu da kuma koramu masu gudana, kuma shi ne zai tseratar da kai daga sharrin miyagun wajen... ko ban gaya maka ba?"
Na gyada kai alamar ya gaya min.

Mallam yace "To wannan jakar ita ce likitan zuciyar."
Nace "Ta yaya jaka zata zama likitan zuciya?"
Mallam yace "Abin da ke ciki shi ne likitan ba jakar ba".

Cikin gaggawa na buɗe jakar wani haske ya daki idanuwana ƙamshi ya tashi ya mamaye ilahirin wajen..... me zan gani?
Sai kawai naga maganar ubangijin sammai da ƙassai, naga igiyar Allah wadda bata tsinkewa, naga kundin hikima, naga littafin nan mafi darajar littafai, Ko kunsan me na gani..... shine AL-QUR'AN.

Mallam yaci gaba da cewa "Wannan shine likitan zuciya, a cikinsa akwai waraka daga cututtukan zuciya, yana gyaran zuciya, yana shiryarwa, ba'a taɓa amfani da shi don warkar da wata cuta ba face ya kawar da ita, wanda ya nemi shiriya daga waninsa ya ɓata, wanda yayi girman kai ya barshi haƙiƙa ya taɓe, wanda ya riki wani littafin sama da shi haƙiƙa ya kauce hanyar tsira..."

"Mallam me yasa tun farko baka gaya min shine likitan ba?" Na tambaya ina tuno irin gwagwarmayar da nayi a hanya.
"Mu mutane munfi kimanta abin da muka sha wahala kafin mu sameshi." Mallam ya bada amsa.

Wani tsoho daga cikin mutane yace "Mallam nina iya karantashi amma ban san ma'anoninsa ba."

"Kaci gaba da karantashi domin yana sanya nutsuwa da tsarkake zuciya da kuma maganin cututtuka, sannan kayi kokari ka san ma'anoninsa, domin gwargwadon saninsa dakai, gwargwadon amfanin da zai maka."

Wani dattijo mai kimanin arba'in yace "Mallam sunana mallam jatau, ni ban iya karantashi ba...."

Mallam yace "Ka yawaita biya abinda ka haddace, sannan ka cigaba da neman ilmin abinda ya rage maka."

Haka aka watse da ni da al'ummar dana musuluntar muka rinqa zuwa daukar karatu wajen mallam, abin gwanin sha'awa.

Bayan shekara ashirin.
Girma ya kamani lokacin nine nake jan sallah a babban masallacin garinmu. 
Wata ranar juma'a bayan an idar da sallah sai aka zo min akace ga wani mutum ya mutu, ya kuma bada wasiyyar cewa ni zan masa sallah. Mutane sukai ta yabon wannan mutum, suka gaya min cewa kaf unguwar da yake zaune babu mahaddaci kamarsa, yanzu hakama ya mutu amma gawarsa kamshi take.
Na tambaya wanene sai akace min ai Mallam jatau ne.

Ko kun tuna shi? 
Mutumin nan da ya miƙe ya gayawa mallam cewa shi bai iya karanta likitan zuciya (Qur'ani) ba.

Wannan shine abin da ya sawwaka daga wannan labarin.

Sai kuma kun sake jinmu ko a kusa ko a nesa, idan da sauran kwanaki kenan.

Allah ya bamu ikon kusantar babban kundi.
Ameen

Writer.
Abu Umar Alkanawy.

Comments

Popular posts from this blog

EYE OPENER... (SIWES)

MUTUM DA HANKALI

LIFE LESSONS FROM CELL BIOLOGY