WAIWAYE ADON TAFIYA (41-45)

WAIWAYE ADON TAFIYA (41)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Kuraishawa sun san sun tafka kuskure, don haka suka rasa zaune suka rasa tsaye, a karshe sai suka yanke cewar gwara su aika wani daga cikinsu don yaje ya sabunta yarjejeniya da Annabi Muhammad (S.A.W) ta sulhun Hudaibiyya. 

Ai kuwa saiya dauki hanya ya nufo madina, haka ya wanzu yana tafiya har ya sadu da  madina, da zuwansa saiya zarce gidan yarsa wadda take matar Annabi Muhammad (S.A.W) Ummu Habiba.  

Bayan ya shiga wajenta ga gajiyar hanya sai yayi yunkurin zama ya akan gadonta amma bisa ga mamakinsa saita hanashi zama akan wannan gado tace mishi bazai zauna ba domin shi ba mai tsarki bane. Ya cika da mamaki, yau ga yarsa tana daukaka darajar wani mutum sama da tasa...

Daga nan saiya nufaci wajen Annabi Muhammad (S.A.W), a zuciyarsa yana tuno irin rashin kyautawar da suka yiwa Annabi tun daga farkon fara da'awarsa zuwa yanzu. Ya tuno irin kisan gillar da suka rinka yiwa sahabbai, da kuma irin cutarwar da suka rinka yiwa Annabi. Ya tuno farkon al'amarin Annabi lokacin da suke jifansa da cewa shi ba wani bane face mahaukaci ko kuma mai sihiri, wani lokacin ma har suna gaya masa cewa yaje ya nemi magani domin tabbas aljanu ne suke damunsa, ya tuno lokacin da Annabi yake aibata bautar gumakan da suke da kuma yadda suka juyar da al'amarin Annabi daga abin dariya a wajensu zuwa wani mataki na dabam. Ya kuma tuno lokacin da takura ta kai takura har hakan ya tilastawa Annabi da Sahabbai yin hijira daga makkah mahaifarsa zuwa madina. A hakan ya lallaba ya daure yaje wajen Annabi yana tunanin abinda zai tarar... Yana ta sake-sake, a karshe dai ya yanke cewar bari kawai yayi ta maza, amma lokacin daya hango Annabi sai gabansa ya qara fadowa. Domin Annabi yana da kwarjini. Haka dai ya daure yafi karfin zuciyarsa yaje gaban Annabin rahama ya furta bukatarsa cikin yanayi na lumana, amma sai Annabi yaki yace masa komai.  Da yaga alamar Annabi baida niyyar biya masa bukatunsa na sabunta wannan yarjejeniya saiya tashi yana sake-saken wanene mafi kusanci da Annabi Muhammad. Caraf sai tunanin aminin Annabi yazo masa, wato Abubakar. Ai kuwa sai yayi tattaki zuwa ga Abubakar. Kai tsaye Abubakar (R.A) yace bazai iya zuwa wajen Annabi ya nema musu ceto ba. 
Ya sake tashi ya tafi zuwa ga Umar Ibn kkhaddab, cikin fushi Umar (R.A) ya kalleshi yace "Ni zan cece ku a wajen Annabi? Da'ace bani da wani abu sai kwayar zarra wallahi saita yakeku da ita...".
Dukkanin wayannan sahabbai suna sane da laifukan da kuraishawa suka aikata na kurkusa akan kashe mutanen aminchi da sukai, kamar yadda suna sane dai da irin adawar da take cikin zukatan kafirai. Don haka wannan bukatar da kafirai suka zo da ita abune mai mutukar nauyi, irin nauyin da ba zasu iya nufar Annabi da wata magana ba, don rai ashirin da karya alkawari ba kananun laifuka bane. Tare da cewa wannan sulhu da akai su kansu kafirai sun san cewa sune suka tsara abinda suke so kuma aka ginashi akan abinda suka tsara din. 

Abu sufyan saiya rinka tunanin yanzu wanene bayan Abubakar da Umar wanda zai iya zuwa da bukatarsa zuwa ga Annabi? Tabbas bayan su bai san wasu ba, sai yayi tunanin Aliyu Ibn Abi Dalib, ya tafi zuwa ga Aliyu. Amma dai sai abu ya gagara, saidai dama dama shine Aliyu ya bashi shawara, cewa ya nemawa yan gidansu ko tsaginsu aminchi. Don haka sai ya koma masallacin Annabi ya shelanta cewa yana sanar da aminchi tsakaninsa da musulmai sannan ya hau abin hawansa ya nufaci Makkah. 

Ai kuwa da shigarsa, sai kuraishawa suka taru zuwa gareshi suna son jin abinda ya wakana tsakaninsa da Annabi Muhammad (S.A.W). Daya gaya musu sai sukace tabbas ya aiwatar da wani abu wanda baida riba a ciki suma basu da riba babu wanda hakan zai amfanar ba, sannan wannan shawara da Aliyu (R.A) ya bashi raina masa hankali kawai yayi tunda ba'a wajen Annabi ya nemi wannan aminchi ba.
 

Ka duba kaga, wayannan kafiran sune da za'ai sulhun hudaibiyya suka rinka takalo da kirkiro abubuwa na rashin mutunchi ciki harda kin yarda a yakarda a rubuta Arrahmanur Rahim saboda sunce basu san shi ba, kamar yadda basu yarda an rubuta Muhammad Rasulullah ba, baya ga haka suka gina sulhun da wasu abubuwa na son rai wanda saida ran sahabbai duka ya baci domin suna ganin ta yaya Annabi zai yarda da wannan rainin hankalin. Saidai ance abinda babba ya hango...


Can Al'amarin Annabi Muhammad kuwa ya gayawa suhabbai cewar su shirya amma ayi komai cikin sirri. Kuma sahabbai duka suka rike wannan sirri, banda wani guda daga cikinsu wanda ya tashi wata mata ya aiketa don taje ta sanarda kafiran kuraishawa game da zuwan Annabi. Allah ya sanar da Annabi inda ya tura wasu zababbun sahabbai ya gaya musu a waje kaza da kaza zasuga mata kaza tana dauke da sako zuwa ga kafirai. Hakan akai kuwa, sun risketa kuma a karshe suka kamata da wannan sako. Kuma ta bayyana wanda ya sakata wannan aiki. Bayan labari ya iski Annabi sai wani sashe na Sahabbai suka nemi a basu dama su kashe wannan sahabi amma sai Annabi ya hanasu domin ya halarchi Badr, su kuwa wayanda suka halarchi badr wankakku ne a wajen Allah. Sannan baya ga haka wannan sahabi ya bada uzurin cewa iyalansa suna hannun kafirai kuma bashi da mai kula dasu don haka shine ya zabi wannan hanya don saboda hakan watakila ba zasu cutar da iyalinsa ba...

Haka Annabi ya nufi Makkah tare da sahabbai adadin mutane dubu goma.

Zamu dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba.

WAIWAYE ADON TAFIYA (42)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)

Duk a cikin azumi ne, amma haka Annabi da sahabbai suka nufi hanyar makkah. Annabi yasan sahabbai da dama suna wahala saboda ga tafiya ga azumi, kuma an umarci wanda bazai iya azumi ba daya sha ruwa tunda matafiya ne, amma wasunsu sai suka dage suka jure suka ci gaba da azumi. Kamar yadda zamu fahimta a wannan tarihi, sauda dama Annabi yakanyi wani abu don jin kan sahabbai ko don saukaka musu, domin yanda muke jin irin soyayyar da suke masa tofa shima haka yake musu wannan soyayyar kai harma ya fi su karfin soyayyar. abin sani dama shine soyayyar da uwa takewa danta, sama take da soyayyar da 'dan yake mata. 

Don haka sai Annabi (S.A.W) ya sha ruwa ya kuma ci gaba da karya azumi, ganin haka yasa harma wayanda suke jurewa suma suka karya.

A hanyar dai akwai wani mutum mai cutarwa ga Annabi, sai aka hadu dashi, Sayyadina Aliyu ya bashi shawarar cewa yaje wajen Annabi ya nemi tuba akan abubuwan daya aikata. Ai kuwa yaje ya nemi gafarar Annabi, Annabi ya yafe masa sannan wannan mutumi ya musulunta. Shima kuma wannan mutum sunansa Abu Sufyan ibn Harisu (Ba wancan Abu Sufyan din ba). Tun daga ranar daya musulunta bai kara dago kai ya kalli fuskar Annabi ba saboda kunya. Allahu Akbar.
Yanzu wayannan mutanen har akwai wanda zaice ba Allah ne ya zabowa Annabi su ba?

Hakanan lokacin da zai mutu, mutane sun hadu anata kuka, saiyace musu su daina kuka domin wallahi tun daga ranar daya musulunta bai kara aikata wani zunubiba. 
Allahu Akbar!


Annabi ya yaada zango a kusa da makkah, dama baffansa Abbas da iyalansa sun silalo zuwa gareshi. Sun hadu dashi kuma a hanya. Abbas yayi farin ciki kuma ya bayyana musulunchinsa, wasu kuma daga malamai suna cewa Abbas ya karbi musulunchi tun da dadewa. 

A wannan dare dai Abu sufyan ya fito don ganin irin abinda Annabi ya taho dashi, ai kuwa sai Abbas ya ganshi, nan take ya kwalla masa kira, to sai Sahabi Abbas yayi tunanin cewa idan sahabbai suka ankara da Abu Sufyan kasheshi zasu yi, don haka saiya dorashi akan abin hawan manzon Allah, sukai goyo akai, suka nufi inda manzon Allah yake.

Haka suka rinka wuce sahabbai, duk wanda ya tsayar dasu idan yaga taguwar manzon Allah sai ya barsu su wuce, kuma musamman anga Abbas baffan manzon Allah ne akanta. Saida sukaje wajen Umar, saiya bincika da kyau, sai yaga Abu sufyan don haka saiya tasam masa, a karshe suka dunguma suka nufi wajen Annabi. Abbas yayi gaggawa suka qarasa, da shigowar Umar saiya zare takobi yace "Ya ma'aikin Allah ka bani dama in sare masa kai..." 
Nan suka fara cacar baki tsakaninsu, shi Abu Sufyan yana nunawa umar cewa adawar umar gareshi don shi ba dan'uwansa na kusa bane ba. Shi kuma Umar ya bashi amsa da cewa wallahi musuluntar Abbas itace mafi soyuwa a gareshi akan mahaifinsa ya musulunta, ba don komai ba sai don yasan musuluntar Abbas zatafi faranta ran Annabi Muhammad (S.A.W). 
Kai ka duba kaji soyayyar gaske, bama tsakaninsa da Annabi ba, har yana gabatar da baffan Annabi akan mahaifinsa saboda soyayya. Allah ka yiwa Umar gafara.
Sahabbai suke cewa Annabi idan zai bada labari yana cewa Na shiga tare da Abubakar da Umar, Nafita tare da Abubakar da Umar, Na aikata kaza da kaza tare da Abubakar da Umar... Shige da ficensu mafi yawan lokuta tare suke yi. Tabbas matsayi irin nasu babu.

Annabi da yaga hayaniya tana shirin afkuwa saiya umarchi Abbas daya tafi da Abu Sufyan su dawo daga baya.

Bayan sun dawo gareshi. Da isarsu abinda ya fara fitowa daga bakin Annabi shine "Shin har yanzu lokaci bai yi ba da zaka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah?"

Abu Sufyan da yake jiran mummunar kalma ko mummunan hukunci sai yaji tayin addinin musulunchi, zuciyarsa ta cika da tunani shin wannan mutumin ya manta da cewa shine Abu Sufyan, shin Annabi ya manta da cewa shine wanda yake gaba wajen jagorantar runduna a yakin uhudu da yakin khaibar don rusa musulunchi ba?
Abu Sufyan sai yace "Mahaifina da Mahaifiyata fansa ne a gareka" daga nan ya yabawa Annabi bisa wannan yafiya tasa da kawar da kai, daga bisani yace "Tabbas da ace akwai wani abin bauta da gaskiya bayan Allah da yau zai tseratar da ni."

Annabi ya sake cewa da shi "Shin har yanzu lokaci baiyi ba da zaka shaida babu abin bautawa bisa ga chanchanta sai Allah ba?"
Abu Sufyan ya bada amsar cewa tabbas shifa akwai shakku a tattare da shi. 

Abbas dake gefe ya daka masa tsawa sannan ya sake maimata masa gami da ce masa ya karbi musulunchi ya kuma yi imani da Allah da Manzon Allah. Ai kuwa take Abu Sufyan ya furta kalmar shahada sahabbai sukai maraba dashi, wannan kiyayyar saita juye zuwa soyayya.

Abu Sufyan suka zagaya tare da Abbas sukaga yawan mutunen da Annabi yazo dasu. Abu Sufyan yayita mamaki yana tambayar shin a ina Muhammad ya samu wayannan mutane haka. Ya tuno lokacin da musulman suke yan tsiraru ko arba'in basu kaiba. Shi da Abbas suka tabbatar da cewa wannan mu'ujiza ce.

Abbas ya samu Annabi yace dashi, Abu Sufyan mutum ne mai son fariya, saboda haka ayi masa wani abu da zai ji dadi. Don haka sai Annabi yace dashi Wanda ya shiga gidan Abu Sufyan ya tsira, wanda yaje masallacin ka'aba ya tsira, wanda ya rufe kofar gidansa shima ya tsira.

Abu Sufyan daya koma Makkah sai yayi shela, ya sanar da larabawa cewa Annabi Muhammad ya taho musu da wata runduna wadda ba zasu iya fukantarta ba. Don haka mai neman aminchi to yazo ya fake a gidansa.

Sai larabawa sukace amma dai ka fiya shashanchi shin gidanka zai iya daukarmu ne? Sai yace musu wanda ya kulle gidansa shima ya aminta, wanda yaje dakin ka'aba shima ya aminta. Don haka sai suka rinka rige rigen zuwa samun mafaka. Wasu suka rinka rufe kofofin gidanjensu, wasu suka tafi gidan Abu Sufyan, wasu kuma suka nufi masallacin ka'aba.

Annabi ya tasarwa makkah, yana tafe tare da sahabbai a wani salo wanda dole makiya su tsorata. Annabi yayi umarni da kada wanda ya fito da makami, kada a takali wani da fada, saidai wanda ya nufo su da fada.

Yauga wanda suke bi kwararo kwararo yana da'awa suna cewa karyane, yau ga wanda yana sallah suke masa izgili, yau ga wannan da suke kira da munanan sunaye, yau ga mabiyan nan da suka raina... Sun bar gari a matsayin korarru, sun kuma dawo a matsayin karfafa masu iko.

Kafirai na cikin matsanancin tsoro mutuka domin tunaninsu Annabi zai ramuwar gayya akansu, basu san cewa shi mai saka alheri ne ga wanda yayi masa sharri ba. 

Zamu dakata anan sai kuma a rubutu na gaba.
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy.

WAIWAYE ADON TAFIYA (43)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Manzon Allah ya raba mutane inda ya shiga Makkah ta wata fuskar, yayinda Khalid ya shiga ta wata fuskar. Abu Ubaida bn Jarrah kuma ya jagoranci mutane masu tafiya a kafa wayanda babu wani alama ta makamai a tattare dasu.

Duk da wannan karfi da musulmai suke da shi, da kuma irin tsorata da kafirai sukai amma hakan bai hana wasu daga kafirai haduwa don yakar musulmi ba, daga cikinsu akwai Ikrama bn Abi jahal, Safwan ibn Umayya da Suhail bn Amru. Sai sukai sa'a suka hadu da tawagar khalid bn walid har suka kashe mutum biyu cikin musulmai, aka bazama kansu aka kashe mutum goma sha biyu ragowar suka tarwatse suka arce. 

Duka wannan abu da yake faruwa su mutanen Ansar cikin fargaba suke, bawai fargabar kada kafirai su cim musu ba, domin babu hanyar wannan. Fargabarsu mai girma ce, fargaba akan kada Annabi ya zauna a Makkah ya kyalesu tunda Makkah ta zama gidan musulunchi itama kuma itace mahaifarsa. 

Masoyi (S.A.W) ya shiga masallacin ka'aba, tare da sahabbai yana kewayewa, yana tuno rabonsa da wannan waje, yayi ido hudu da hajarul aswad dutsen da akansa rigima taso ta afku tsakanin larabawa tun kafin Annabta. Daga nan ya rinka bin gumakan masallacin ka'aba yana tuntsirar dasu akan fuskokinsu da sandarsa...

Manzon Allah yayi dawafi takaitacce, lokacin daya cika 

DaGa nan aka bude Ka'aba, Annabi yayi umarni aka fito da kayan cikinta na daga hotuna da wasunsu, ya shiga ciki yayi sallah. 

Yana fitowa ya iske mutanen makkah sunyi sahu sahu sunajiransa, ya tsaya daga kofar su kuma suna kasa. Yayi godiya ga Allah ya bayyana musu cewa wannan aikin na Allah ne, shine ya taimaki bawansa, kuma ya rusa rundunonin kafirai... Yayi bayanai gamsassu har akan kabilanchi. Bayan ya kammala saiya bijirowa da Kuraishawa tambaya. Yaku taron Quraishawa shin me kuke tunanin zan aikata a gareku?" 
Sai suka hada baki suka ce "Alheri, domin kai din Dan'uwa ne mai karamchi dan gidan Dan'uwa mai karamchi."



Daga nan Annabi ya mayar da mukullin ka'aba izuwa ga wanda ya karba daga gareshi, sannan yace mukullin zai zauna a hannunsa har abada. Wato 'ya'yansa zasuyita gada.  

Abin lura. Abbas shine karshen wanda yayi hijira, domin kuwa ya fito yayi hijira a hanya sai Allah ya hadashi da Annabi Muhammad. Bayan fathu Makkah kuma babu hijira. 

Bayan Annabi ya tabbabata a makkah sai mutanen Makkah sukazo sukai masa Mubaya'a. 

Mutane sukaita musulunta, har sahabi Abubakar shima yazo da mahaifinsa ya musulunta. Allahu Akbar, sahabi Abubakar ya samu riba, wato mahaifinsa da mahaifiyarsa duka sun samu rahamar musulunchi. 

Mata ba'a barsu a baya ba wajen zuwa yiwa Annabi mubaya'a. 

Annabi yayi fatawa ta hana shan giya, cin mushe, cin naman alade da kuma bautar gumaka.

Kamar yadda ya hana abubuwa kamar kashe ya'ya domin tsoron talauchi da sauran laifuka.

Ko kasan yanzu ma ana kashe yara don tsoron talauchi.
Shin tallah da ake dorawa yara mata a aikesu dashi wani guri mai nisa sannan a bukaci kudin daya ninninka na kayan da aka dora musu daga garesu kansa ba kisa bani?
Banbancin shine waccan kisar lokaci daya rai zai fita mutum ya huta, wannan kuwa sai an tagayyara rayuwar mutum an kashe masa ita an cire dukkan wani jin dadi.

Allah ya kyauta.

Annabi ya zauna a makkah tsawon kwanaki goma sha tara. 
Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

WAIWAYE ADON TAFIYA (44)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Tabbas gaskiya ta bayyana zuwa ga larabawa da sauran kafiran makkah, domin kuwa sun riski wani abu wanda basu taba jin labarinsa ba a tarihi. Domin idan bamu manta ba a wannan zamani akwai manyan masarautu a manyan sassan duniya amma cikin wayannan masarautu babu wadda hankalinta ya karkatu izuwa makkah da madina don mai da su karkashin mulkinta, wanda su larabawa suna jingina hakan zuwa ga kiyayewar Allah, domin bawai ba'a san garuruwan nasu bane, ansan dasu domin kuwa ana zuwa kasuwanchi wajensu, suma kuma suna fita.

Maganar tasu ta cewa kiyayewar Allah ce, tabbas akwai gaskiya a ciki, domin Annabi Ibrahim ya roka musu aminchi da arziki, kamar yadda surar Quraish ta Qur'ani ta kara jaddadawa akan lallai Allah ya amintar dasu.

Hakanan shekarun da suka wuce suna sane da cewar wani sarki yazo don rushe ka'aba amma sai Allah ya sakko masa da ruwan duwarwatsu aka hallakasu. Amma kuma yau ga Annabin rahama ya shigo har cikin ka'abar ya kakkarya gumakanta amma babu abinda ya same shi, don haka sai suka yarda kwarai cewar wayannan gumaka ba ababen bauta bane. 

Haka Annabi ya aika wasu sahabbai suka rushe wasu gumakan na wasu garuruwan kusa da Makkah. Harma idan zasu rushe sai kafiran su taru don suga irin azabar da zata sakkowa mai ruguza gunkin amma sai suga babu abinda ya faru, don haka sai suka tsinke da lamarin musulunchi...

Kafirai suka wanzu suna tunanin ababuwan da sukaiwa sahabbai da Annabin kansa, suka tuno yanda suka killace Annabi da danginsa suka hanasu ci da sha, suka tuno yanda suke binsa hanya suna masa ihun mahaukachi, suka tuno yanda suke jifansa da yi masa habaici da duka... Suka tuno yanda suke korarsa, suka tuno yanda suka kora shi da sahabbansa, suka tuno bayan hijira yanda suka rinka kamo sahabbai suna musu kisan gilla, suka cigaba da tuno irin yaudarar da sukai masa cewa wasu kabilarsu sun musulunta, ya hadasu da sahabbai masu yawa amma sai suka karkashesu a hanya... Amma duk da haka sai Annabi ya yafe musu harma ya nuna musu cewa komai ya wuce ya so su kuma ya zauna zama mai kyau tare da su. 
Shin akwai wani mutum wanda jini ke gudana a zuciyarsa wanda zai iya yin butulchi ga wanda yayi masa wannan alheri?

Hindu wadda tana da hannu wajen kashe zakin Allah Hamza harda ita a zuwa don karbar musulunchi kuma Annabi ya karbeta karba mai kyau kuma har ta tsaya yi masa tambaya kuma ya bata amsa. Harma daya yi mata maganar kashe yara tace masa aisu basa kashe ya'yansu, shine dai idan yaran suka girma yake kashe musu su... Amma Annabi bai nuna wani nau'i na kullata ba. Domin yanzu ta shigo gidan aminchi, duba kaga yanda Annabi yake daraja da girmama duk wanda yake cikin sahabbai koda yayi laifi. Amma maimakon ayi koyi dashi sai muka iske wasu mutane da karatun tsarki ya kamata su koya amma sun kauce suna can suna lalubo laifukan sahabbai, da ace laifukan suke lalubowa da sauki, amma sharri da kage da kirkira suna suka dabaibaye lamarin nasu.  
Allah ya kiyashemu tabewa! 

Cikin wayanda suka musulunta harda wanda ya kashe Hamza, amma shima ba'a hanashi shiga musulunchi. Kuma haka kamar yadda yayi barna kafin ya musulunta haka yayi jihadi bayan ya musulunta domin shine ya kashe Musailamatul kazzab.  

Bilal da ake azabtar dashi lokacin da ake Makkah kafin hijira, sai Annabi ya umarceshi ya hau saman ka'aba yayi kiran sallah, ga masu azabtar dashi a kasa duk suna jinsa suna kallonsa. Wasu da basu musulunta haushi ya cika zukatansu, domin wannan bakin bawan ya za'ai ya hau saman wannan gida mai girma... 

Zamu dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba in Allah ya yarda.

Naseeb Auwal 
Abu Umar Alkanawy



WAIWAYE ADON TAFIYA (45)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Daga lokacin da aka ce anyi Fathu-Makkah, sai mutane suka rinka shiga musulunchi gayya-gayya. Inda zaka iske al'umma guda ta taso daga inda take tayo tattaki ba don komai ba, sai don ta riski Annabin rahama da kuma karbar musulunchi.

Wasu daga cikin mutane dama abinda ya hanasu imani shine karfin da makkah da Quraishawa suke da shi. To yanzu kuma gashi karfin ya dawo hannun musulmi don haka abinda suke tsoro ya kau. Wasu kuma suna tsoron fushin abin bautar da suke bautawa ne, to kuma sai sukaji labarin cewa hadda ka'aba wadda mafi girma da daukakar gumaka suke ciki wannan Annabi ya shiga ya rusa su ba tare da wani mummunan labari ya biyo baya ba. Bari ma dai akwai gumakan da yan aike ya tura suka rusa su. Kuma babu wani abu daya faru.

Annabi ya zauna a makkah tsawon kwanaki goma sha tara.

A makkah labari ya iskeshi cewa ga kafirai can na sassa sun hada wata gagarumar runduna a Hunain suna son suzo su kawowa Annabi hari don yakarsa da shafe sakon da yazo dashi.   

Da jin haka sai Annabi ya tashi rundunar mutane dubu goma sha biyu, dubu goman wayanda suka biyoshi ne daga madina, yayinda dubu biyun kuma mutanen makkah ne. Haka Annabi ya fuskanci Hunain, sannan ya shugabantar da Attaab ibn Husain a makkah, wanda shine farkon wanda aka shugabantar a Makkah bayan musulunchi.

Musulmai saboda yawasu sai suke tunanin babu makawa yau sai sunyi nasara. 

Babu hadi, tabbas rundunar kafirai tafi yawa domin su dubu ashirin da doriya ne, yayinda rundunar musulmai suke dubu goma sha biyu. Saidai kasancewar sun saba cin galaba koda kuwa an fisu yawa hakan yasa suke ganin wannan karon babu wata kafa da za'a ci galaba a kansu. 

Sune wayanda suna dari uku suka ja da mutane dubu. 
Sune dai wayanda suna dubu uku suka ja da mutane dubu goma.
Sune suke da zaratan jarumai irinsu Umar, Aliyu, Khalid, Bara'u da wasunsu(R.A).

Kasancewar suna jin cewa sunada karfi sai Allah yaso ya jarrabesu, inda ana fara yakin aka fara cin galaba a kansu. Duk karfi da jarumta irinta Khalid bn Walid amma saida aka fado dashi daga kan dokinsa aka ji masa mummunan rauni jini ya rinka zuba.  

Sahabbai sunga tashin hankali wannan rana, ana rinka yi musu ruwan kibbau da sara da suka da jifa da masu ta kowane sashe. Suka fita daga hayyacinsu. Suka tarwatsa don barin wannan tarko da suka fada, kai kuwa duk tashin hankalin da zaisa mazan da suka tsaya badar, suka tsaya uhudu, suka tsaya a gurare mabambanta su tsere don neman mafita kasan ba karamin tashin hankali bane...
Kuma duk hakan jarrabawa ce, domin Allah yana so ya nuna musu da kuma yan bayansu cewa karfi da nasarar ba daga garesu take ba, tabbas daga Allah take.

Yan'uwa mufa duba, Sahabban nan sune wasu abubuwa da Allah yake amfani dasu don ajiye mana darasi, ba don komai ba sai don su zamo mana madubin dubawa. Shin idan bamu so wayannan ba wa zamu so?

Sahabbai suka tarwatse suka bar Annabi sai tsiraru cikinsu akwai Abubakar, Umar da Aliyu da wasu tsirari. Allah ya kara musu yarda.

Da Annabi yaga haka sai kawai ya kutsa cikin kafiran, maza suna gudowa suna neman matsera yayinda shi kuma namijin maza yake kara kutsa kai cikin kafiran yana nanata musu cewa.
"Nine Annabi ba karya ba, Nine dan AbdulMuddalib"

Sahabi Aliyu (R.A) yake cewa sun kasance idan gumurzu yakai gumurzu... suna komawa bayan manzon Allah...
Kaji Namijin Duniya.

Ana wannan yanayi Annabi yaga yadda sahabbai suka rarrabu, yaga yadda suka fita daga hayyacinsu, yasan cewa tabbas aka tafi a haka tofa za'ayi musu babbar asara... Kuma hakika shi baya son abinda zai taba lafiyarsu don haka sai hankalinsa ya tashi... Shin me zaiyi wayannan wayanda suka fita daga hayyacinsu su dawo hayyacinsu... 

Sai kawai ya kirawo Abbas, yace masa yayi shela ya kirawo sahabbai ya janyo hankalinsu. Aikuwa Abbas dama mutum nd mai sauti daya daga murya yayi kira ya kuma ce kiran na manzon Allah ne, ya tunowa da sahabbai abubuwanda da suka wakana. Nan take sai suka dawo hayyacinsu. Ta yaya ba zasu dawo hayyacinsu ba, alhalin wanda suka bada rayukansu fansa ga nashi shine yayi kiran?

Ai kuwa sai sahabbai suka amsa, wasu daga cikinsu suka juyo da akalar ababen hawansu suka taho inda Manzon Allah yake, yayinda wasunsu kuma da sukaga ababen hawan zasu bata musu lokaci sai kawai suka sauka daga abin hawan suka nufo Annabi don amsa kiran...

Sahabbai dukda ana cikin yaki amma saiya zamana burinsu ba shine rayukansu ba, burinsu shine su amsa kiran Annabi. Shi kuma Annabi burinsa ba shine su rasa rayuwarsu ba, burinsa shine ya tseratar da rayuwarsu.

Bayan sun hadu, Sai Annabi (S.A.W) ya daga hannunsa ya roki Allah nasara, sannan ya cika da cewa "Ya Allah idan kaga dama ba za'a kara bauta maka ba bayan wannan rana..."

Daga nan Annabi ya debi kasa yayi jifa da ita cikin tafin hannunsa, ai kuwa sai wannan kasar ta tafi ta cika bakin duka kafiran da idanuwansu... 
Kasa cikin tafin amma ta cika baki da idanuwan mutum dubu ashirin... Wanene mai wannan aikin indai ba Annabi mai mu'ujiza ba?

Daga nan musulmai sukai dauki kan kafirai suna masu galaba, kafirai suka juya suka arce aka kama wasunsu. 

A wannan yaki an samu ganima mai yawa, bayan an gama Annabi ya duba baiga Khalid ba, ai kuwa take ya tambaya, sai aka gaya masa yaji ciwo yana can rai a hannun Allah.

Annabi yayi masa tofi a ciwon take wajen ya warke tas fyas.

Daga wannan guri Annabi yayi nufin nufar Da'if domin wayanda suka gudu da yawa can sukaje suka fake. Amma sai Annabi yayi mafarki cewa ba'a umarceshi da bude Da'if ba, don haka saiya koma.

Bayan anyi rabon ganima sai Ansarawa wasunsu sukaita surutun cewa Annabi ya raba ganima amma bai basu komai ba. Domin rabon da aka tashi sabbin shiga musulunchi aka bawa rabo mai tsoka wasu rakuma dari wasu wani abin makamancin haka.

Da kokensu ya koma kunnen Annabi, saiya tattarasu yayi musu bayani mai ratsa zuciya a karshe yace "Yaku mutanen madina, shin ba zaku yarda ba, ace mutane suna tafiya da akuyoyi da tumaki ku kuma kuna tafiya da Manzon Allah?...

Sai Ansarawa sukaita kuka suna farin ciki, ashe dai Annabi zai sake komawa garinsu ya zauna tare da su.

Takwas ga zhulqida Annabi (SAW) ya koma madina.

Zamu yada zango anan. 
Sai kuma a rubutu na gaba.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.