WAIWAYE ADON TAFIYA (36-40)

WAIWAYE ADON TAFIYA (36) 
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)

A dai wannan yaki da akai a banu musdalik wani babban al'amari ya faru. Kamar yadda muka nuna a rubutun daya gabata cewa ba'a samu yakin da kafirai suka fita da yawa ba irin wannan yaki. Ba don komai ba sai don kudirinsu na ganin sun tarwatsa musulunchi sun shiga tsakanin Annabi da sahabbansa, sun kunna wutar adawa tsakanin sashen sahabbai. Har ma suna ganin idan sun samu dama don zubar da mutunchin Annabi zasu kulla kullalliya don yin wani abu wanda zai zamo aibu a cikin gidansa. Saidai Allah bai basu iko ba.

Nana Aisha da kanta take bamu labari. Cikin hadisi ingantacce wanda Bukhari da Muslim suka fitar dashi. Zamu kawo a takaice.

Kamar yadda muka sani idan Annabi zaiyi tafiya yakanyi kuri'a a tsakanin matansa, wadda ta fada kanta to da ita za'a fita. A wannan lokaci sai akayi sa'a sunan Nana Aisha ya fito. Sai Nana Aisha ta shirya aka tafi. A wannan lokaci kuwa an saukar da ayar hijabi.

Wani dan daki ne mai kama da akwati ko keji wanda ake dora matan manya a ciki mazaje su daga Kodai su dorashi bisa kafadunsu, ko kuma su azashi bisa rakumi. 
Wayanda suke kallon india zasu iya tuno irin wannan abu, wanda zaka iske ana saka amarya a ciki mazaje hudu su hadu su dagata. Amma a wannan kissa ta nana Aisha idan suka dagata akan rakumi suke ajiye wannan akurki da take ciki.

Bayan Annabi ya kammala wannan yaki sai aka juya don komawa madina, a hanyarsu ta komawa sai bukata irinta dan Adam ta kama Nana Aisha, ai kuwa saita nesanta da mutane kamar yadda addini ya koyar don biyan bukatarta, bayan ta dawo, saita tarar sarkarta ta fadi. Don haka saita koma don dubawa. 

Su kuwa acan, sai Annabi yayi umarnin da a ci gaba da tafiya. Aka tashi cikin hanzari da rige rigen yin biyayya ga Annabi aka tashi akayi gaba. Wayannan mutane kuwa masu daukar akurkin Nana Aisha sai suka zo suka daga shi suka dorashi akan rakuma, a tunaninsu kamar kullum yauma tana ciki. Tunda ba kasafai take fitowa ba. Kuma babu wanda ya ankara cewa bata ciki. Musamman saboda bata da nauyi...

Ita kuma da taje can ta duba tana ta lalube, har a karshe taga wannan sarkar ta ta. Tana tafe tana gaggawa don komawa inda rundunar musulmai take, amma bisa ga mamakinta saita dawo ta iske an tafi an barta.

A zuciyarta ta cika da mamaki. Garin yaya hakan ta faru. Kodai babu wanda ya kula bata nan? 
Sai tayi duban duniya taga bata ga inda suke ba, ta hanga iyakar hangenta amma babu su babu dalilinsu. Sai kawai ta samu waje ta zauna. Tace idan aka fuskanchi bata nan tasan za'a biyo baya a dauketa. Tunda bata san hanya ba bata san kuma ina zatai ta tarar dasu ba. Tananan zaune kawai saiga sarkin barayi, ya lallabo ya saceta. Ina nufin sarkin barayi bacci.


Safwan Assalamiy yana can baya yana tafe yana nazarta hanyar ko zai tarar da wani abu da aka bari ya dauka ya riski rundunar dashi.

Yayin da Nana Aisha kuma ke kwance a kudundeni bacci ya dauketa kawai sai taji ance "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un", tana farkawa ta bude ido sai taga Safwan Bn Mu'addalin Assalami. Baice mata komai ba, sai kawai ya durkusar da rakuminsa. Ita kuma saita sake gyara abin lullubinta ta hau safwan yayi mata jagora suna masu bin bayan rundunar domin shi yasan hanyar. Babu wanda yayiwa wani magana a cikinsu. Basu riski rundunar Annabi ba sai dare. Inda Annabi ya yada zango.

Babu wanda yace 'kala akan wannan abu daya faru.

Su kuma munafukai sai sukace to ai wannan dama ce tazo musu. Dama sunata neman hanyar da zasu soki manzon tsira ta fuskar iyalansa amma sun rasa. Kamar yadda rigimar da suka so hadawa tsakanin sahabbai taki haduwa. Sai shugabnsu Abdullahi ibn Ubayyu Bn Salul ya rinka jujjuya wannan magana.

Lokacin da aka isa Madina Nana Aisha bata da lafiya, don haka saita zauna a dakinta kawai tunda babu lafiya ba damar yin aikace aikace kamar koda yaushe. 

Can cikin gari kuwa munafukai sun samu abinyi har suna yadawa cewa Nana Aisha da Safwan sun aikata alfasha. 
Muna neman tsarin Allah daga furuci irin wannan. 

Har magana taje kunnen Annabi Muhammad (S.A.W). Ya kasance idan yazo wucewa ta dakin Nana Aisha baya karawa akan tambayarta "yaya kuke?" Sai kawai ya wuce. Abin ya damu Annabi sosai...

Ita kuwa Nana Aisha bata san abinda ke faruwa ba, ita dai taga kamar Annabi ya chanja mata. Har saida wata rana wata jikar Abdulmuddalib mai suna Ummu misdahin sai ummu misdahin take sanar da ita abinda ke faruwa. 

Nan take rashin lafiyar Nana Aisha ta qaru matuka, bata da aiki sai kuka. 
Da gari ya waye sai Manzon Allah yazo wucewa ta dakinta saiyace da ita yaya kuke? Ita kuwa cikin kukan sai tace dashi ka bani izini in tafi wajen iyayena. A wannan lokacin tana son jin gaskiyar labarin ne daga kunnensu. Sai Annabi ya bata izini ta tafi gida. 

Tana shiga gidan kuwa ta sake fashewa da kuka, ta tafi wajen mahaifiyarta hawaye yana satatowa daga kumatunta, bakin ciki ya cika zuciyarta, duniyar tayi mata zafi... Tana kukan ta tambayi mahaifiyarta tace "Ya ke mahaifiyata, wai me mutane suke cewa ne." 
Mahaifiyarta tayi kokarin kwantar mata da hankali ta hanyar nuna mata cewa duk macen da mijinta yake mutukar sonta tana faruwa da irin wannan jarrabawar domin akwai wayanda suke bakin cikin hakan.

Hakan data fada kuwa sai Nana Aisha ta sake samun tabbas akan abinda mutane suke cewa. Haka ta kwana tana kuka hawaye ko tsagaitawa baya yi.
Annabin Allah, mutumin da tafi so akan kowa kuma mijinta amma munafukai sun shiga tsakaninsu...
Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu.

Al'amarin ya damu Annabi Muhammad mutuka, ya rasa yadda zaiyi ya warware matsalar. Kamar yadda zamu fahimta duk lokacin da abu ya shigewa Annabi duhu abinda yake shine neman shawarar sahabbai. To haka wannan karon ma saiya nemi shawararsu. Amma kasancewar wannan abune na sirri, saiya kirawo mutum biyu daya dan uwansa na jini Aliyu bn Abi Dalib dayan kuma Usama bn Zaid. Hana neman shawararsu akan iyalinsa.

Shi Usama dan zaid sai yace "Iyalinka ne ya ma'aikin Allah, kuma bamu san komai akansu ba sai alheri.
Shi kuma Aliyu Bn Abi Dalib sai yace "Ya ma'aikin Allah, kada ka takurawa kanka akanta, akwai mata da yawa bayan ita. Ka tambayi baiwarka (Barirah) nasan zata gaya maka gaskiya."
Sai manzon Allah ya kirawo Barira ya tambayeta sai tace "Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya, ni dai bani da wani abu da zan iya aibunta Aisha dashi. Kawai dai ita mai kananun shekaru ce, takanyi bacci yayi girki har akuya tazo ta cinye..." 

A wannan lokaci kuma ga babban abinds zai fayyace komai ya yanke, wato wahayi ya tsaya cak. Don haka Annabi sai ya hau mumbari yace bai san komai dangane da iyalinsa ba sai alheri... Yayi jawabi akan wannan sharri da ake yadawa.
Dajin haka sai sahabbai suka mike suna neman a gaya musu mai yada wannan sharri yanzu su sare kansa... Nan take hayaniya ta kaure wasu suna goyon baya wasu basa goyon baya a tsakanin su mutanen madina. Haka Annabi yayi ta kokari ya kwantar da tarzoma tsakaninsu.

Nana Aisha take cewa a wannan lokaci saida tayi kwana biyu da wuni guda kuka kawai take. Iyayenta suna tare da ita. Tana cikin wannan hali kawai sai wata mata daga cikin Ansarawa ta shigo ta zauna tare da ita itama tana kuka. 

Suna cikin wannan hali sai sukaji sallamar Annabin Rahama (S.A.W) ya shigo ya samu waje ya zauna. Wata guda cur ba aiwa Annabi wahayi ba.

Annabi yayi shahada, sannan yace "Bayan haka, Ya ke Aisha, hakika kaza da kaza ya riske ni akanki, idan babu ruwanki kin barranta daga abinda ake jingina miki, hakika da sannu Allah zai barrantar da ke. Idan kuma ki  aikata wannan zunubi to ki tuba izuwa ga Allah, domin bawa idan yayi zunubi yayi nadama ya tuba Allah zai yafe masa..." Kwana biyu da wuni hawaye ban yankewa Nana Aisha ba, amma da Annabi ya kammala wannan maganar sai hawayenta ya tsaya. 
Nana Aisha uwar muminai ta kalli mahaifinta ta bukaci ya bawa Annabi amsa, amma sai yace bai san me zaice ba. Ta maida kanta zuwa ga mahaifiyarta, itama tace bata da ta cewa. 
Nana Aisha na da kananun shekaru a wannan lokaci, don haka sai tace "Ni wallahi nasan kunji abinda mutane suke ta fada, kuma nasan kun yarda, abin ya zauna a zukatanku. Kuma kun gaskata shi. Idan nace muku ni banyi ba. Kuma Allah yasan na barranta (banyi din ba), ku ba zaku gaskata ni ba. Kuma da ace zance muku na aikata kuma Allah yasan ban aikata ba da gaskata ni zakuyi. Ni dai bani da wani misali da zan iya kawowa tsakanina da ku face misalin mahaifin Annabi Yusuf lokacin da yake cewa "Sai hakuri mai kyau, Hakika Allah shine mai kawo agaji a bisa abinda kuke siffantawa..." Sai nana Aisha ta juya akan makwancinta. 
Nana Aisha take cewa ban taba zaton lamarina yakai girman a saukar da wankeni a cikin Qur'ani ba, ni abinda nake ta buri shine Allah ya gayawa ma'aiki a mafarki cewa ni ba mai laifi bace.  

Manzon Allah bai bar wannan waje ba, sai kawai sukaga launin Annabi ya sauya, fatarsa tayi jajur, gumi yana tsatstsafo masa saboda nauyin abinda ake sakko masa na daga wahayi. 

Manzon Allah kawai sai akaga yana dariya ta farin ciki, ya kalli Nana Aisha yana murmushi hasken fuskarsa yana walwali yace da ita "Yake Aisha ki godewa Allah... Ina miki bushara, Allah ya wankeki..." Annabi yana farin ciki mara misaltuwa.

Mahaifiyar Nana Aisha kuwa sai tace mata ki tashi zuwa ga Manzon Allah mana, kiyi masa godiya. Nana Aisha tace "Bazan mike gare shi ba, kuma babu wanda zan godewa sai Allah, tunda dai Allah shine ya wanke ni..."

An saukar da ayoyi a jeri na wanke ta, ba biyu ba, ba uku ba, ba hudu ba... Saida aka saukar da ayoyi goma sukutum. Duk don wanke mafi darajar mata. Nana Aisha yar mafi darajar sahabbai kuma matar mafi darajar Annabawa.

Zamu dakata anan
Sai kuma a rubutu na gaba. 

WAIWAYE ADON TAFIYA (37)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Kamar yadda mu ka ji, wahayi ya sakko daga sama ayoyi goma sukutum don wanke Aisha...

Jarrabawa tana kara darajar mutum, don haka wannan jarabawar ba komai bace face karin daraja ga Nana Aisha. Bama itaba harda makusantanta. Akwai wani girma da daraja da Allah zai bata a cikin matan Annabi don haka akai mata wannan jarrabawar. 
Anan duniya an saukar da ayoyi goma akanta don wanketa.
A lahira kuma Allah kadai yasan abinda ya tanadar mata. Na daga matsayi, mukami, daukaka da babban lada.


Dangane da karin bayani, akwai littafin Nabiyur Rahma na sheikh Sani Umar Rijiyar lemo. Tabbas ya fito da bayanai da yawa masu ratsa zuciya cikin wannan kissar ba don gudun tsawaitawa ba. Da zamu ambata.


Tsarkakakkiya ce, kuma yar gidan mmafi tsarkin sahabbai, matar mafi tsarkin Annabawa. Wanda yaci gaba da aibatata bayan ayoyi sun kareta babu kokonto wannan mutum ya kafircewa kur'ani kamar yadda yayi soka zuwa ga tsarkin Annabi Muhammad. Domin tsarkin iyalinsa ai tsarkinsa ne.

Ko kasan saboda tsarkin matan Annabi akwai malaman da suke ganin ko mafarki mutum yayi mafarki da wani matan Annabi basa yi?
Bisa duba da wani hadisi da wata mata take tambaya shin idan mace tayi mafarki zatai wanka, sai wata daga matan Annabi da take wajen take jin mamaki take cewa "dama mata suna mafarki ne?" 
A karkashin wannan wasu malaman sai sukace saboda tsarkin matan Annabi basa yin mafarki irin wannan.
Wallahu A'alam

Wannan wannan yaki haka Annabi ya rinka tura sahabbai gurare da dama, kuma suka rinka samun nasara, Wani garin kuma kafin suje an gudu, wani garin kuma sai an taru an tsaya kowanne cikin kafirai yana jin tsoro amma ya dake don kada yayi abin kunya. Amma sa sunga alamun rundunar sahabbai yan gatan Allah saisu tarwatse kowa yasan inda dare yayi masa.

A irin hakane wani aike da Annabi yayi, sahabbai suka samu nasara suka kamo wasu kuraishawan makka da dukiyoyin kuraishawa a tattare dasu. Cikinsu harda Abul Ass ibn Rabi'i mijin Zainab yar ma'aiki (S.A.W). 

Saita turo aike tana neman fansarsa, nan ma sai musulmai suka sakeshi kuma aka saki wayanda aka kama tare da shi. Aka kuma basu dukiyoyinsu. 


Kaga karamchi na musulmai, mu tuna sufa munji yadda sukewa musulmai idan sun kama su, amma dubi su nasu yanzu an kama kuma an sakar musu a bagas.

Abul'ass bayan ya koma makka ya rabarda dukiyar zuwa ga ma'abotanta sai kawai yayi hijira daga makkah zuwa madina yana zuwa madina ya musulunta.

A watan DhulQada ne cikin shekara ta shidan dai, Annabi (S.A.W) yayi mafarki shida sahabbai suna shiga makkah kawunansu a aske cikin kwanciyar hankali. 

Don haka sai ya gayawa sahabbai, su kuwa sukaita murna saboda zasuyi umara. Muhajirun kuwa wannan soyayyar da dan gari yake yiwa garinsu saita baibayesu. Suka rinka shaukin zuwan wannan lokaci. Ai kuwa sai Annabj ya umarchi cewa a shirya. 

Aka sanar da larabawan kauyuka da sukai imani da Annabi amma sai sukaita bada uziri. A karshe Annabi ya fita tare da sahabbai 1400.  

A matansa kuwa ya tafi da ummussalama ne, haka nan tunda umara aka dauki niyyar yi. Annabi bai fita da makami ba. Sahabbai ma haka. Saidai irin makamin da ba'a rasa matafiyi dashi kamar wuka. Haka nan dabbobin yanka da Annabi ya tafi dasu guda saba'in ne. 

Annabi da sahabbai suka tsaya a Dhulhulaifa inda nanne mikatin yan madina. Annabi ya sanya ihraminsa. Suma sahabbai suka aikata hakan 

Can Makkah kuwa har labari ya riskesu cewa Annabi ya taho da runduna don yakarsu, don haka sai suka tashi tasu rundunar karkashin jagorancin Khalid Bn Walid. 

Annabi suna tafe tare da sahabbai sai labari ya iskeshi cewa kafiran Makkah sun fito da shirin yaki.

Annabin tsira kamar koda yaushe saiya tattara sahabbai ya nemi shawara. Sai sahabi Abubakar ya bada shawarar cewa ai sudai ba yaki suka fito ba, don haka su ci gaba da tafiyarsu. Babu ruwansu da kowa. Saidai wanda ya tare musu hanya ya takalesu da fada to sai su yakeshi.

Haka suka ci gaba da tafiya, saida aka kusa haduwa tsakanin kafirai da musulmai sai Annabi ya sauya hanya. Don dai gudun keta alfarmar makkah. Shi kuwa can Khalid bn Walid da yake masanin yaki ne, saiya fuskanchi tabbas Annabi Muhammad da sahabbai sun sauya hanya. Don haka shima saiya juya ya koma kurkusa da makkah.

Annabin tsira yana daf da hudaibiyya sai taguwarsa ta durkushe. Sahabbai wasu suka ce ta fusata ne, wasu sukace ta gaji... Annabi yace ba haka bane, kuma wannan ba halinta bane. Wanda ya tare gida daga shiga Makkah, shine ya tare ta daga nufar Makkah. Yana nufin Allah, lokacin da Abrahata yazo rushe ka'aba.

Annabi ya shirya tura dan aike don yaje Makkah ya gaya musu abinda ke tafe dashi, cewa shi baizo don yaki bane. Ai kuwa ya tura mutum na farko. Amma sai suka so su hallakashi banda wasu makusantansa sun tashi tsaye. 

Daga nan sai Annabi ya tashi sahabi Umar, amma sai sahabi Umar ya bada shawarar cewa a tura Usman domin kuwa Usman kusan masu fada aji a makka dukansu yan uwansa ne. Saboda haka idan aka turashi ba zasu cutar da shi ba, kuma wata kila saboda alfarmarsa a wajensu a samu su fuskanchi abinda ake fada musu.

Ka duba wannan hikima daga wajen Umar (R.A) kai kasan Allah bawai jigari-jigarin mutane yan tamore ya zagaye Annabi da su ba. 
Sau nawa wani zaiyi magana mai kyau amma saboda kiyayya a kasa fahimta ko kuma a dauketa mara muhimmanchi.
Sau nawa kuma wani zaiyi magana mara tasiri amma saboda soyayya sai kaga wannan maganar ta zama abar yabawa da son barka?

Hakan akai, Annabi ya tashi Usman (R.A) ya turashi. Ai kuwa sai kafiran Makkah suka karbeshi hannu bibbiyu suna murna da karramashi.

Suka tambayeshi dame yazo?
Yace musu ya zo ne ya kirasu zuwa musulunchi da bautar Allah. Sannan ya sanar dasu umara aka zo ba yaki ba.

Me kake tunani da waninsa aka tura? Yadda suke kiyayya da musulmai ace wani ne ya shiga har garinsu ya gaya musu irin wannan maganar cewar yana kiransu zuwa musulunchi... Ai sai sunyi kasa-kasa da mutum. 

Amma sai suka kasa bada mummunar amsa, sai sukace masa ya zauna zasuyi shawara. Shi kuwa dama manzon Allah yace dashi ya biya ta gidan musulman da suke makkah ya yiyyi musu bushara. Don haka saiya nausa don aiwatar da wannan aikin.
Ka duba wata baiwa. Duk rashin kunya irinta kafirai amma sun kasa yiwa Usman mummunar magana. Wato suma suna jin kunyar mutumin da Allah ke jin kunyarsa. Amma yanzu saimu samu wani bahagon mutum wanda ko karatun larabchi babu wasali bai iya ba yana kokarin yin suka ga Usman bn Affan. Muna neman tsarin Allah daga masharranta irin wannan.

Bayan tafiyar Usman sai labari ya zowa Annabi cewa an kashe Usman. Hankalin Annabi ya tashi nan take ya aje hannu sahabbai suka rinka yi masa mubayi'a kan jihadi har mutuwa da rashin juya baya.   

Sahabbai 1400 ne sukai mubaya'a kuma hadisai da dama sunzo na nuna cewa an gafarta musu zunubansu, cikinsu babu dan wuta, sannan kuma sune mafi alherin mutane.

Usman da baya nan, Sai Annabiya dora hannunsa daya kan daya yace wannan hannun na Usman ne. 
Don haka duk da sahabi Usman baya nan sai Allah ya daukaka darajarsa. 
Na farko hannun Annabi ne a matsayin hannunsa.
Na biyu wayanda suka samu darajar ma sun samu ne ta dalilinsa.

Zamu dakata anan
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy

WAIWAYE ADON TAFIYA (38)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Baya ga wannan sai larabawan makkah suka turowa Annabi mutane wannan bayan wannan don suji menene yazo da Annabi. Cikin yardar Allah duk wanda ya koma saiya gaya musu magana mai kyau akan zuwan Annabi. Wani daya koma yace lallai ya ziyarci fadar manyan sarakan duniya. Ya ziyarci fadar masu manyan dauloli na duniya amma bai taba ganin wasu mutane da suke girmama shugabanninsu ba kamar yadda suhabbai suke girmama Manzon Allah (S.A.W) ba. Kuma ya umarcesu dasu kyale Annabin rahama ya aiwatar da wannan umara.

Wani kuma daya koma sai yace dasu lallai ya kamata abar mutanen nan suyi abinda ya kawo su, shima ya fadi irin abubuwan daya gani na kyautatawa da girmamawa tsakanin sahabbai da Annabi. 

Daga baya sai suka turo Suhail bn Amru sai kuwa akai sulhu. 
Manzon Allah da Suhail sukai yarjejeniya aka rubuta, Manzon Allah yace a rubuta Bismillahir Rahmanir Rahim, sai suhail yaki yarda saidai a rubuta bismikallahumma... Sahabbai sukai caa suka ce sai an rubuta yadda Annabi yace a rubuta yadda Suhail din ya bukata. Aka rubuta.
Sannan da Annabi yazo fadar sunansa sai Yace "Muhammad Manzon Allah..." Sai Suhail yace bai yarda ba saidai a rubuta Muhammad Bn Abdallah domin kuwa da sun yarda Annabi manzon Allah ne aida ba zasu yi musu ko jayayya da shi ba, ko kuma su hanashi shiga makka ba.  

A karshe dai aka karkare da wani sulhu cewar duk wanda yazo wajen Annabi ya musulunta daga mutanen makkah ba tare da yardarsu ba Annabi zai dawo dashi garesu. Su kuma duk wanda yaje wajen su daga wajen Annabi koda yardarsa ko babu zasu rike shi. Annabi yace ya yarda. 
Anan take wannan Suhail ya bukaci a mayar masa da wani nasa. Annabi ya bashi uzurin cewa yanzu ake rubuta wannan yarjejeniyar fa ba'a gama ba. Sai suhail yace kodai a bashi abinda ya bukata ko kuma a fasa yin sulhun sai Annabi ya damka masa wannan mutum da yake nema a dawo masa dashi. Shi kuwa wannan mutum cikin tsananin bakin ciki yace yaku taron musulmai shin baku ga irin yadda suka azabtar da ni ba. Domin a wannan lokacin kafin ya gudo wajen Annabi sun gana masa bakar azaba...

Abin ya yaiwa Sahabi Umar da sahabbai da dama ciwo, amma babu yanda zasuyi domin Annabin rahama ne ke hukunchi. 

A dai wannan zama sukace Annabi bazai Umrar ba, sai shekara mai zuwa... Nan ma dai abin ya yiwa sahabbai ciwo da sukaji Annabi ya amince da hakan. Musamman an lasa musu zumar shiga garin makkah. Amma babu mai tankawa a cikinsu. Sannan kuma akai yarjejeniyar za'ai zaman lafiya tsawon shekara goma ba tare da yaki ba.

Sahabi Umar bai iya rike abin a ransa ba, har saida yazo ya tambayi Annabi. 
Umar: Shin ba kaine Annabin Allah na gaske ba?
Annabi: Kwarai kuwa nine.
Umar: Shin ba mune akan gaskiya ba?
Annabi: kwarai mu ne.
Sayyadina Umar ya tambaya to don me za'ayi wannan sulhu haka. Domin a zahirinsa idan mai karatu ya kula larabawa sun so kansu da yawa.
Sai Annabi ya bashi amsa mai kyau mai nuna cewa wannan sulhu daga Allah ne kuma Annabi baya sabawa Allah. 
Umar ya sake zuwa wajen Abubakar ya sake masa tambayoyi irin wayanda yayiwa Annabin rahama. Sai Abubakar ya bashi amsa irin wadda Annabin rahama ya bashi. 
Sahabi Umar yace bai gushe ba yana sallah yana azumi yana yanta bayi saboda wannan magana da yayi da Annabi har saida yaji ya samu kwanciyar hankali. 

Shi Sayyadina Umar abinda yake hange shine wannan sulhu da akai maimakon a kaskantar da kafirai tunda sune akan bata amma sai akayi amfanin da son ran da sukazo dashi. 

Ran sahabbai ya baci kafin su gano hikimar da take cikin wannan sulhu da akai. 
A hanyar Annabi ta komawa aka saukar masa da suratul fath, wadda take maganar Allah yayiwa Annabi budi budi bayyananne. Sannan a surar dai akace an gafaratawa Annabi abinda yayi dama wanda baiyi ba, aka kuma dai gaya masa Allah zai cika ni'imarsa a gareshi. Da wasu bayanai da dama. Wanda suka faranta ran da dama daga cikin sahabbai.


Wata hikima ta Allah itace kafin ayi wannan sulhu, an kasance ba'a haduwa face a filin daga idan ta kama ayi yaki, amma sakamakom wannan sulhu saiya zamana musulmai suna zuwa makkah don kasuwanci da ziyara kamar yadda kafiran suma suke shiga madina.Sai hakan ya bada hanyar yin hira a tsakanin sashen biyu. Hakan yasa aka rinka jan ra'ayin kafirai sai suka rinka musulunta kamar wutar daji, domin babu wanda keda ingantaccen hankali da yake bautar gunki da za'a zo masa da maganar musulunchi kuma yaki karba. Don haka a kasa da shekara biyu sai aka samu adadin wayanda suka shiga musulunchi sun ninninka adadin wayanda suka shiga kafin afkuwar hakan. Kuma har ila yau mutanen da suka shiga musulunchi cikin rashin son ransu zaka iske su yan kadan ne. Idan wani yana musu saiya kawo mana mutunen daya sani da aka ci su da yaki suka karbi musulunchi muji ko zasu kai daya bisa goman wayanda suka shiga saboda mu'amala...

Wannan sulhu bai tsallake wata goma sha takwas ba sai kafirai da kansu suka warware yarjejeniyar da sukai. 

Ayi mana hakuri zamu dakata anan
Sai kuma a rubutu na gaba.

WAIWAYE ADON TAFIYA (39)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)…

Mu dan koma baya kadan...
Bayan an zartar da sulhun Hudaibiyya, sai Annabi ya umarchi sahabbai dasu yanka abin yankansu da kuma aske kawunansu duk da kuwa basu samu damar yin umara ba. 

Rashin Umarar da kuma hukuncin da aka yanke a wannan sulhu bai yiwa sahabbai dadi ba. Don haka Annabi daya umarcesu babu wanda ya iya tashi dukkaninsu jikinsu yana sanyaye... 
Annabi da yaga haka sai ya shige zuwa wajen Nana Ummussalama matarsa. Inda yake gaya mata wannan bakon al'amari. Domin kuwa kamar yadda ya saba idan ya umarchi sahabbai suna rige rige wajen aiwatar da abu, amma yau gashi yayi umarni dukkaninsu suna zaune...

Sai ma'abociyar hikima Nana Ummussalama ta bashi shawarar cewa ya kirawo mai aski ya fara yi masa aski. 

Aikuwa take ya umarchi Khirash bn Umayya daya yi masa aski. Da ganin haka sai sahabbai kowa ya zabura suka rinka rige-rigen koyi da Manzon tsira (S.A.W).

Yayinda Annabi da sahabbai sukai aski sukai yanka suka kuma koma madina, saiyake sanar dasu cewa Suratul Fathi (Inna fatahna laka fathan mubiina) itace mafi soyuwa a gurinsa daga duniya da abinda ke cikinta. Malaman tafsiri sun hadu akan cewa surar ta sauka akan Sulhun Hudaibiyya.

Anyi shekara goma sha uku kafin ayi hijira, aka kuma dora shekara shida bayan hijiri, anyi shekara uku ana musayar gumurzu tsakanin musulmai da mushrikai kenan, amma munji adadin wayanda akai wannan tafiya ta umara (Hudaibiyya) dasu mutum dubu daya da dari hudu ne. 
Daga sulhun hudaibiyya da aka ajiye makamai zuwa fathu Makkah shekara biyu ne, amma saida Annabi ya koma da mutum dubu goma.

Kai ka duba kaga banbanci tsakanin yaduwar musulunchi ta hanyar aiki da karfi da kuma ta hanyar mu'amala da kira cikin hikima.

Bayan wannan sulhu sai Annabi ya turo wasiku zuwa ga manyan sarakunan duniya, wayanda sune duniyar take karkashin mulkinsu a wannan lokaci, kuma ake mutukar shayinsu. 

Kamar yadda masoyina Anas bn Malik yake cewa "Annabi ya tura wasiku zuwa ga Kisra, 'Kaisar, da Najashi da dukkanin wani ji da mulki ko isa a doron kasa, yana kiransu zuwa ga Musulunchi."

Najashi ya karbi musulunchi, 'Kaisar wanda muka fi sani da Hercules da sauran manyan sarakai duk suka girmama sakon Annabi, cikinsu harda masu turowa da Annabi kyauta, wadda Mariya (R.A) wadda ta haifawa Annabi Ibrahim tana ciki. 

Masana tarihi sukace yanayin sarakunan da Annabi ya zaba ya turawa sarakunan idan akayi la'akari da karfin mulkinsu to tabbas za'a gane wannan aike da Annabi yayi ba aiken dan'adam bane. Domin aike ne mai cike da lissafi da kuma hikimomi. Ga mai son karin bayani saiya duba littafin Muhammad Rasulullah. Banda ina gudun tsawaitawa da na ambaci darusa masu girma saidai idan akwai sauran kwana da tsawon rai nasan mai karatu wata ran zaici karo da hikimomin kodai daga gareni ko daga wani wajen wanda yafi nawa. 

 Cikin sarakunan nan akwai Kisra, shi da wannan sako yaje masa saiya yayyagashi yace ya za'ai bawansa ya turo masa da sako?

Daga nan ya umarci gwabnansa na Yemen daya kamo masa Annabi, suka tura wasu mutane karfafa guda biyu. 

Labari ya koma kunnan Annabi, Annabi yayi mummunar magana akansa akan Allah ya daidatashi da mulkinsa, ai kuwa sai aka wayi gari dansa ya kasheshi. Su kuma yan aiken nasa da suka zo sai Annabi ya basu labarin cewa ai wanda ya aiko sun ma ya mutu. Suka musa, da suka samu labari sai suka cika da mamaki haka suka koma cikin borin kunya da tabewa.

Haka Annabi ya sake tura wasu sakonnin zuwa ga shuwagabannin larabawa, wasunsu suka musulunta, wasunsu kuma suka 'ki musulunta.

Mutanen Khaibar sune yahudawan da suka rage, kuma suna nan cike da haushi da fushin Annabi Muhammad, musamman domin yayi buju-buju da yan'uwansu, wasunsu kuma gudaddu ne. Sune kuma wayanda suke kara kunna wutar kiyayya tsakanin Annabi da kafiran Kuraishawa. 

Lokacin da Annabi ya shirya zai fita Yakin Khaibar, sai munafukai suka taso, sai Annabi ya hanasu, domin da za'a tafi Makkah a fitar data wuce wadda akai sulhun hudaibiyya, kin yarda sukai su bishi. Don haka sai Annabi ya hanasu, ya kuma ce babu takura wanda yaga dama ya zauna.

Don haka wannan yaki na khaibar adadin mutanen da suka halarci sulhun hudaibiyya sune dai nafsin mutanen da suka tafi izuwa Khaibar. Shi kuwa khaibar gurine mai mutukar tsaro domin garin katanga-katanga ne, sannan sunada kayan yaki gami da karfafan mayaka. Amma a haka Annabi ya nufi wannan gari tare da sahabbai 1,400.

A wannan lokaci Aliyu bn Abi Dalib bashi da lafiya. Annabi ya tambaya ina yake, akace ai yana ciwon ido ne, a wannan lokaci Annabi tuta zai bayar, dukkanin manyan Sahabbai sunata kwadayi, kowa yana so a bashi wannan tuta, domin Annabi kafin ranar ya kambama darajar wanda zai bawa tutar. Amma sai Annabin tsira yace a kira masa Aliyun, aka kirashi, Annabi yayi masa tofi a idon nasa, take idon ya warke, sannan Annabi ya bashi wannan tuta.

Lokacin da aka isa Khaibar, sai wani kakkarfan mayaki daga yahudawa ya fito ya nemi fito na fito. Kafin wani ya ankare tuni Aliyu Bn Abi dalib ya kaddamar masa, ya turashi wani gari wanda ke kurkusa, amma muna hangensa a nesa.  Ma'ana dai ya sheka shi lahira.

Haka aka wanzu ana yanki Sahabbai suka rinka bude kofa bayan kofa har saida sukaci karfin yahudawa, yahudawa suka mika wuya. 

Bayan Annabi ya shiga garin sai suka kawo masa abinci, yaci bayan yaci saiya bukaci a tattara masa yahudawan yanki aka tattarosu.

Yace musu ku yayan wanene?
Suka gaya masa wani suna sai yace karya kuke ku yayan wanene, ya fada musu sunan mahaifinsu na asali... Suka cika da mamaki, a karshe Annabi yace dasu, shin zaku fadi gaskiya idan na tambayeku akan wani abu? Sai sukace masa eh.
Sai Annabi ya tambayesu shin kun saka guba a cikin wannan naman?
Sai sukace Eh sun saka.
Sai Annabi yace dasu me yasa kuka aikata hakan?
Sai sukace muna so idan karya kake mu huta, idan kuma da gaske kake gubar ba zata cutar da kai ba.

Aka bijiro da matar da tazo da naman, aka tambayeta me yasa ta kawo, ita kuma kai tsaye sai tace so nake na kasheka. Ta fadi hakan zuwa ga Annabi Muhammad. Sahabbai suka nemi izinin su kasheta, Annabi yace su kyaleta.

Wannan nama kuwa wanda ya cishi tare da Annabi shine Bashar bn Bara'u. Kuma ya mutu sai Annabi yayi umarni aka kashe wannan matar. 

Ka duba kiyayyar yahudawa ga Annabi. Burinsu shine su kasheshi. Kamar yadda burinsu shine su kawar da koyarwarsa daga doron kasa. Musamman ta hanyar aibata matansa da sahabbansa. 

A wannan khaibar dai Annabi ya auri Safiyya. An kamata a matsayin baiwa, Annabi ya yantata kuma yancinta ya zama sadakinta. 

Acan baya munji cewa Ja'afar Bn Abi dalib yayi hijira zuwa Habasha, to bayan dawowar Annabi sai gashi, tare dashi akwai abokan hijirarsa da kuma wayanda ya hadu dasu a hanya mutum hamsin da yan kai yan kabilar Ash'ariy dukkaninsu suka taho zuwa ga Annabi Muhammad (S.A.W). 
Annabi yayi murn mara misaltuwa, harma yake cewa baisan me yafi faranta masa ba, nasara akan khaibar ko kuma dawowar ja'afar.

Wayannan mutane duka suka musulunta, musulunchi mai kyau.  

Zamu dakata anan
Sai kuma a rubutu na gaba.


WAIWAYE ADON TAFIYA (40)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)…

Aka ce, gyara ado ne.
Annabi Muhammad yana Khaibar Ja'afar dan Abi Dalib ya dawo, haka ma zuwan kabilar Ash'ariyya, kamar yadda Daus suma sunzo sun samu Annabi kabilar kusan dukansu, wanda ba don tsawaitawa da kuma karancin lokaci ba da saimu ambaci kowace da dalilan daya sanya ta ta musulunta. 

Su Kabilar Ash'ariyawa a cikinsu muke da Abu Musal Ash'ariy. Kamar yadda Abu Huraira yake cikin kabilar Daus. Kabilar Daus shugabansu tun Annabi yana makka ya musulunta, kuma yaje yayita kiran kabilarsa amma sai suka ki amsa masa. Face wasu yan tsiraru cikinsu harda Abu Huraira, a karshe shi shugaban kabilar Dufail bn Amru ya taso takanas tare da Abu Huraira ya kawo kukansa cewa mutanensa sunki suyi imani dashi. Annabi ya daga hannu zai musu addini, Abu Huraira ya tsorata domin tunaninsa Annabi zaiyi musu addu'ar azaba ne tunda sunki imani, amma sai Annabi yayi musu addu'ar shiriya. Don haka sai suka rinka musulunta. 

Yahudawan khaibar bayan sun mika wuya sai Annabi yayi nufin ya koresu domin zamansu a tsakiyar larabawa babu abinda ke jawowa sai fitina wannan bayan wannan. Amma sai suka nemi alfarmar cewa a barsu su rinka yiwa musulmai aikatau, idan yaso sunada rabin abinda suka aikata. Sai akayi musu wannan alfarmar. Sukaci gaba da zMa har zuwa lokacin halifancin sahabi Umar Dan khaddabi, inda suka kashe wani musulmi kjma suka ki fadar wanda yayi kisan cikinsu, dalilin haka sai Sayyadina umar ya koresu duka daga jaziratul arab suka koma can yankin Sham. Sayyadina umar shiya kauda fitinarsu.

A watan zulqida na shekara ta bakwai bayan hijira Annabi ya shiga makkah kamar yadda akai yarjejeniya a sulhun Hudaibiyya, tabbas Annabi yayi mutukar murna yau gashi a mahaifarsa, yau gashi a garin daya taho, yau gashi a garin da duwatsun garin suke masa sallama idan zai gifta su. Farin ciki ya mamaye zuciyarsa. Yayi cikakken umara, saidai bai shiga ka'aba ba, saboda gumakan da suke ciki da kuma zane. Tare da Annabi akwai mutane, domin mutum dubu daya da dari hudu da suka halarci sulhu duk suna tare dashi saidai wanda ya mutu. 

A hanyar Annabi ta dawowa ya auri maimuna wadda itace matarsa ta karshe. 

A farkon shekara ta takwas Babbar yar Annabi Zainabu ta rasu. 
A watan safar na shekarar dai Khalid da Amru bn Ass suka zo wajen Annabi har madina suka karbi musulunchi, Annani yayi maraba da su. Kuma yayi mutukar farin ciki.

A jumada ula na shekara ta takwas din dai akai yakin Mu'utatul Azima tsakanin Musulmai da kafiran Gassan. 
Su kuwa Annabi ya tura musu da sako, sai suka yankewa Dan'aiken Annabin hukuncin kisa. Don haka Annabi ya tattara rundunar mutum dubu uku, wadda itace mafi karfin rundunar daya hada kafin ita.

Saboda sanon hadarin inda zasu je, sai Annabi ya nada kwamandodi guda uku, idan an kashe na farko na biyu ya dauki tuta  idan an kashe na biyu na uku ya dauki tuta.

Zaida bn Harisa shine kwamanda na farko, haka aka shirya aka fita, suna daf da karasawa sai labari yazo musu cewa kafirai sun samu dauki daga Rum mafi girman masarautu a duniya. Don haka sunada mayaka mutum dubu dari daga Rum qari akan wayanda suke dasu. Don haka sai suka tashi da rundunar mayaka zarata dubu dari biyu.

Rundunar musulmai su dubu uku da sukaji haka sai suka yada zango suna tattaunawa, wasu suka bada shawarar ai aikawa Annabi a gaya masa, ko za'a karo musu mutane...
Abdullahi Bn Rawahah ya tashi yayi musu jawabi mai ratsa jiki, yace dasu mu bada karfin yawa muke nasara ba, hakika mu muna nasara ne da karfin addinin dake zukatanmu...

Ai kuwa maza sai sukaci gaba da tafiya, ai kuwa suna zuwa garin masharif sai suka iske rundunar kafirai. 

Nan fa aka tsaya ana kallon kallo abinma a wajen kafirao abin dariya domin mutum dubu uku ne kawai sahabban su kuma su dubu dari biyu ne. 

Don haka sai suka taso da niyyar yiwa musulmai kwaf daya. Nan take musulmai suka ja tunga Zaid bn Harisa na rike da tuta.

Aka gauraya akai wata haduwa, Zaidu na gaba yana sara da sukan kafirai babu kakkautawa sukai masa rubdugu yayinda suhabbai suke kakarin dannawa don gamawa da kafiran...

Aka jiwa Zaid muggan raunuka, yayi shahada.  
Annabi yana can madina, amma Allah yana nuna masa abinda ke faruwa shi kuma yana sanar da sahabbai. Da sukaji an kashe kwamandan farko sai sukayi jimami.

Ja'afar Bn Abi Dalib ya dauki tutar ya rinka yaki cikin jarumta da bajinta babu ji babu gani.  Shima aka kasheshi. Annabi ya gayawa sahabbai da suke tare dashi, sukai jimami.

Sai Abdullahi bn Rawaha ya yi caraf da tutar yana kan dokinsa ya danna ya kutsa ya afka ya kifu akan kafirai musulmai suna yaki a tare dashi sara yake babu ji babu gani. Musamman saboda ganin cewa shine kwamanta na karshe...

Akaji masa muggan raunuka shima ya rasu, yayi shahada. Yayinda Annabi ya bawa sahabbai labari sai jikinsu yayi sanyi duk da Annabi ya gaya musu irin falala da wayannan masu shahadar zasu samu.

Tutar musulunchi ta fadi! 
Sabit Bn Aqram cikin jarumta ya dauki tutar musulmai suka dawo bayansa. Sai ya duba shin wanene wanda zai iya dagewa, wanene jarumin sadaukin dazai iya yaki ya kuma tseratar da rayukan musulmai, ya duba shin wanene wanda yake gwani wajen iya yaki da shugabantar yaki.  Sai kawai idonsa ya kai kan Khalid bn Walid, wanda wannan shine yakinsa na farko daya halarta a matsayin musulmi. Ai kuwa saiya mika masa tutar. 

Khalid ya miko hannunsa mai albarka cikin shauki da wata zuciya mai cike da imani, ya karbi wannan tuta ya damketa. Musulmai suka koma bayansa, bai gushe ba yana yakar wannan rundunar har saida Allah ya kawo budi ta hannunsa. Kamar yadda Annabi da kansa ya fada ga sahabbai cewa "...  Sai wata takobi daga takubban Allah (Khalid) ya dauki tutar, sai Allah ya basu nasara a hannunsa...”

Khalid a wannan rana saida ya lalata takubba har guda tara, idan yayi yaki yayi yaki sai takobin ta karye kota dakushe saboda yawan sara da kare sara, saiya dawo ya karbi wata. Da dare ya gabato kowa ya gaji don haka aka kafa sansani donjira sai washe gari.

Khalid dake gwanine, saiya umarchi wasu daga cikin mutanensa suka koma nesa da inda rundunarsa suke. Da wayewar gari sai wayannan wayanda khalid ya ware suka fara hargowa da ihu irin na yaki, da jin haka sai kafirai suka tsorata, sukace tab, mutum dubu uku kacal ma sun wahalar damu muna dubu dari biyu ballantana kuma yanzu da aka karo musu wasu sababbi... Sai tsoro ya shiga zukatansu.

Haka Allah ya taimakawa musulmai kafirai suka gudu yan Rum suka koma kasarsu.

Su kuma sahabbai suka juyo zuwa ga madina, kafin su karasa tuni Annabi da sauran sahabbai sun fito tarbarsu. 

Wasu daga jama'ar madina suke ihun cewa Sun gudo daga filin yaki, Sai Annabi ya hana yace su ba masu guduwa bane, su mayaka ne da yardar Allah. 
Su mutanen madina sun fadi hakane saboda ganin cewa Sahabbai da sukai wannan yaki basu shiga cikin garin ba, da sukaga Allah ya taimaka musu akan kafirai sun tarwatsasu sai kawai suka jiyo.

Wasu malaman kuma suna ganin cewa anyi nasara, kuma harma anci ganima, akwai dai wayanda suka dawo kafin a gama yakin don tsananin tsoron daya kamasu, to a kansu Annabi yake fadar wannan magana. 

Koma dai menene munji Annabi ya basu kariya, hakanan khalid ya iya tsare rayukan musulmai ta inda ba'a karkashesu ko kaskantar da su ba.

Wallahu A'alam.

Bayan wannan yaki sai Annabi ya kirawo Amru bn As yace dashi zan turaka gari kaza da sojoji ka yakesu abinda ka samu na dukiya ganima ce. Sai Amru yacewa Annabi ya ma'aikin Allah, hakika ni ban shigo wannan addini don tara dukiya ba, hakika nina shigo shine don jihadi saboda Allah.

Maganar ta farantawa Annabi matuka.

Aka hada Amru bn As da mazaje dari hudu, yaje kuma yayi nasara, ya dawo da mutanen daya tafi dasu cif cif ko rauni babu wanda ya samu. Amru da Khalid sune irin Kwamandojin da kowane mayaki zaiso yayi yaki a karkashinsu.


A cikin yarjejeniyar da akai tsakanin Annabi da Kuraishawa munji babu yaki. Kuma kabilar Khuza'a sun shiga karkashin tutar Annabi. Amma sai banu bakar da kuraishawa suka kashe kusan mutum ashirin a cikin banu Khuza'ata, ai kuwa sai labari ya jewa Annabi. Kuma ya samu tabbaci akai.

Can kuwa kafiran makkah sai sukaji tsoron warware wannan sulhu da sukai, don haka sai suka turo Abu Sufyan don ya jaddada wannan alkawari da Annabi. Amma bai samu nasara ba.

Annabi ya umarchi sahabbai dasu tashi, ya kuma umarchi kowace kabila da tazo a hadu da ita a nufi Makkah. 

Zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

Tare da ni
Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy!

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.