WAIWAYE ADON TAFIYA (31 - 35)

WAIWAYE ADON TAFIYA (31)
Tatacciyar Sirad Ma'aiki (S.A.W)

Safiya bnt Abdulmuddalib yar uwar Hamza ibn Abdulmuddalib ce, labari kuma ya riga ya risketa cewa an kashe dan'uwa don haka ta taso don ganin gawar dan'uwanta shugaban shahidai Hamza (R.A). Annabi baya son taga gawar don kada hankalinta ya tashi saboda irin kisan da akaiwa dan'uwanta, don haka saiya umarci danta Zubair Bn Awwam daya hanata karasowa inda gawar Hamza take. Dan nata yayi maza ya tare ta ya gaya mata cewa Annabi  baya son taje don ganin wannan gawa. Budar bakinta ke da wuya sai tace "Saboda me? Ai nasan an yiwa dan'uwana kisan wulakanci, sai dai akan tafarkin Allah ne kuma ina burin Allah zai saka masa da mafificin alheri, ni kuma insha Allah zan zama mai hakuri." Daga nan taje taga Hamza tayi masa addu'a. Bayan nan Annabi yasa aka binneshi anan filin Uhud kabarinsa har yau yananan. 

Mus'ab wanda ya daukarwa musulmi tuta a wannan yaki na Uhudu, ya kasance mafi kwalliyar mutane a makkah, kafin musulunchi. Domin kuwa dai dai da turaransa ya fita dabam. Shima a wannan yaki na Uhudu aka kasheshi. Kuma dai dai da tufafin da aka binneshi dashi bai iya rufeshi gaba daya ba. 

A hanyar Annabi da Sahabbai ta komawa madina, sahabbai suka hango wata mata ta bazamo hankalinta a tashi... An gaya mata mijinta, babanta da dan'uwanta duk sun rasa rayuwarsu a filin daga. Abinda ta fara tambaya shine shin ina Annabi Muhammad (S.A.W)? Aka gaya mata yana raye.  Nan ta godewa Allah. Amma sai zuciyarta ta kasa samun nutsuwa. Sai tace to indai yana raye tana so a kaita wajenshi. Ai kuwa sai aka kaita. Sai tace tunda yana raye ai dukkanin kuncinta yanzu ya yaye. Damuwar data shiga saboda tunanin an kasheshi yanzu babu ita. 
Jama'a mu kula da kyau. An kashe mijinta, babanta da dan'uwanta. Amma ita Annabin dai shine abinda yafi damunta.
Tabbas sahabbai sun cancanci yabo da addu'a.

Ka duba irin wahalar da Sahabbai suka sha, da kuma irin raunukan da suka ji a wannan yaki, amma washe garin ranar Annabi ya sake bada umarnin a fita abi bayan kafirai. Haka sahabbai suka dunguma suka bi bayan kafirai. Dalilin wannan bin baya kuwa shine akwai yiwuwar kafiran zasu farwa madina. Domin burin da suka zo dashi shine suyiwa musulmi kaca-kaca su kuma shiga har madinan. Amma tun a farkon yaki da akaci galaba a kansu sai suka tsorata, tare da cewa bayan sabawa umarnin Annabi da sahabbai sukai sai kafirai suka samu karfi akansu bisa taimakon Khalid bn Walid. Musulmai suka shiga rude da tashin hankali daga bisani kuma suka sake hade kawunansu a waje daya. Don haka ganin musulmai sun sake hadewa sannan kuma da kiran da Abu Sufyan yayi yaji cewa lallai tabbas Annabin rahama da Abubakar da Umar duka suna raye shine ya sake jefa tsoro a cikin zukatansu inda suka kasa aiwatar da wani abu face ikirarin sake haduwa a wata shekarar a filin BADAR, suka kuma bar wannan yaki a matsayin fansar yakin badar ne, suka kuma yi da'awar cewa anyi kare jini biri jini da su da musulmai. Amma sai gwarazan musulunchi suka nuna musu akwai bambanci. Domin mamatan musulmai suna Aljanna, mamatan kafirai kuwa suna wuta.
Allah ne mafi sani.

A shekara ta uku bayan hijira wasu kabilu biyu suka turo wakilai cewar suna so Annabi ya hadasu da wasu daga sahabbansa don su koyar dasu addini. Annabi kuwa saiya basu mutum shida. A hanya sai kawai suka kame wayannan sahabbai zasu daddauresu. Wayannan sahabbai suka fito da makamai don kare kansu. Wayannan kafirai suka gayawa sahabbai cewa ba zasu kashe suba. Su kuwa uku daga sahabban suka ce ba zasu yarda da wannan abu daga kafirai ba. ai kuwa sai kafiran nan suka kashe su, suka tafi da ragowar ukun, a hanya suka sake kashe daya. Ragowar mutum biyun kuwa sai suka sai da su ga Kuraishawa. Hujair bn Abu Ihab ya sayi Khubaib bn Adiy (R.A), Safwan Bn Umayya kuma ya sayi Zaid bn Dasinna (R.A). Dukkaninsu sun siye su don daukar fansar yan'uwansu.    

Aka tara mutane don a makkah don suga irin kisan da za'a yiwa Zaid bn Dasinna. Kafin kisan suka tambayeshi shin yanzu baya burin ace Annabi aka kama ba shi ba, shi yana can wajen iyalansa? Sai yace musu. "Na rantse da Allah, bana burin kaya ta caki Annabi, alhalin ni ina cikin jin dadi nida iyalina."
Abu Sufyan yana wajen ya cika da mamaki, yace shi bai taba ganin mutumin da akewa irin wannan soyayya ba sai Manzon Allah.  Daga nan suka kashe zaidu. 

Shi kuwa Kubaib, da aka zo za'a kasheshi, sai ya nemi a barshi yayi sallah raka'a biyu. Ai kuwa sai suka barshi. Bayan ya idar sannan ya juyo ya kalli kafirai yace ba don kada kuyi zaton na tsawaita sallar don tsoron mutuwa ba da sainayi sallah mai yawa. 

Daga nan kafirai cikin rashin imani suka dauko wukake suna yankar naman jikinsa suna tambayarsa "Shin kana so a kama Annabi a maimakonka kai kuma a sake ka?" 
Jini na zuba radadi da zafin yanka yana ratsashi inda aka zabtari namansa yana zubar da jini amma a hakan cikin juriya da imani zai rinka bada amsa yana cewa "Wallahi bana burin in zauna lafiya alhalin kaya zata soki Annabi Muhammad..."

Haka suka rinka yankar naman jikinsa suna bijiro masa da wannan tambayar, shi kuma yana maimata musu wannan amsar a karshe har saida suka gaji suka karasa kasheshi, kafin ya mutu ya daga kansa sama yayi musu mummunar addu'a.

Ba zaka gane munin irin kisar da sukai masa ba sai kaji daga bakin wanda ya halarta.
Bari mu kawo daya daga cikinsu.

A wata ziyara da Sahabi Umar yakai garuruwan Sham lokacin kalifancinsa, ya shiga Himsa, sai mutanen garin suka kawo masa karar sarkinsu mai suna Sa'id bn Amir akan wasu abubuwa guda hudu. Laifin farko yafi na biyu...
Sai Umar yasa aka kirawo sarkin alhalin suma suna nan zaune, saiya tambayesu me kuke kokawa akan sarkinsu.

Suka ce: Baya fito mana har sai rana ta dago.
Umar yace da shi, me zaka ce akan haka?
Sai Sarki sa'eed (R.A) yayi shiru, daga bisani yace: Bana son fada wallahi, sai dai babu makawa saina fada. Iyalina basu da dan aiki, ni nake tashe na nika musu garinsu, sannan in kwabashi sannan inyi musu gurasa, sai inyi alwala in fita inyi sallah.
(Ina maza masu kin taya mata aiki, to ga abin koyi).

Sai Umar yace: Sai kuma me kuke kawo kara akansa?

Sukace: Baya amsa kiran kowa da daddare.

Umar ya sake cewa: To kai Sa'id me za kace?
Sai Sarki Sa'id yace: Wallahi wannan ma bana son fada... Ni na sanya rana garesu da bukatunsu. Dare kuma na barwa Allah ina bauta masa.

Sai Umar (R.A) ya kuma cewa: Sai kuma me kuke kawo kara akansa.

Sai suka ce: A wata, akwai wata rana guda da baya fitowa garemu baki daya.

Sai Umar ya tambayeshi dalili.

Sai Sarki Sa'id yace: Bani da mai yi mini hidima, kuma bani da wani kayan bayan wanda ke jikina, saboda haka ina wankeshi sau daya a wata, sannan in jira har sai ya bushe don haka bana fitowa gare su sai yamma likis.

Sai Khalifa Umar ya sake tambayarsu sai kuma wacce matsala.
Sai suka ce: Wani abu mai kama da Suma ko farfadiya, saiya fita daga hayyacinsa baya sanin wake tare dashi ko a ina yake. don haka saiya boya ga wayanda ke wajen zamansa...

Sai Umar ya tambayeshi dalili.

Sai yace: NA HALARCI KISAN DA AKAIWA KUBAIB IBN ADIY LOKACIN INA MUSHRIKI, QURAISHAWA SUNA YANKAR NAMAN JIKINSA SUNA TAMBAYARSA...(irin tambayar da muka fada a baya)... HAKIKA NI BANA TUNA WANNAN RANAR, DA KUMA KIN TAIMAKONSA DA NAYI FACE NAYI ZATON ALLAH BAZAI TABA GAFARTA MIN BA... SHINE NAKE WANNAN SUMAN.

Ka duba fa, yana kafiri abin ya faru, amma har bayan ya musulunta idan ya tuno saiya suma kai kuwa wannan wacce irin kisa akayi?

Bayan wayannan wasu mutanen suka kuma zuwa suka nuna sha'awarsu ga musulunchi, suka nemi a basu malamai su koyar dasu, Annabi ya zabi mutum saba'in ya hadasu dasu. Suka tafi dasu da sukazo wani guri mai suna Bi'r Ma'una kabilar Banu Sulaym, Usayya, Ri'il da Zakhwan sai sukaiwa musulman nan rubdugu. Jarumta Musulman suka rinka kare kansu a karshe aka kashesu kakaf, Ka'ab Bn zaid ne kawai ya tsira ya dawo ya bada labari.

Zamu tsaya anan
Sai kuma a rubutu na gaba! 

WAIWAYE ADON TAFIYA 32
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Munji irin ta'addancin da akaiwa sahabban ma'aiki da cin amanar da akaiwa Annabi domin an bukaci ya bada makaranta masana don suje su koyar da addinin musulunchi amma sai aka kashesu, bayan Annabi saida ya fitar da zababbu mutum saba'in, cikinsu babu wanda ya iya dawowa wajen Annabi sai mutum guda kawai. Ya dawo ya bada labarin abinda ya afku. 

Tabbas wannan abu ya girgiza Annabi. Domin tunda batu akai masa na koyarwa dole ya zabi mutane na musamman ya turasu. Don haka sahabbai suka dugunzuma suka zamo cikin tashin hankali.   

Dama haka Allah yake lamarinsa, yana jarraba mutane don ya tantance mai kyau daga mara kyau. Haka nan jarrabawa itama wata alama ce ta cewa akwai gagarumar nasara da zata wanzu.

A watan muharram na shekara ta hudu bayab hijira Annabi ya aiki Abu Salama tare da wasu mutum hamsin zuwa ga Dulaihatu ibn Khuwailid wanda ya tara abin tarawa don kawai ya yaki Annabi muhammad. Amma kafin Abu Salama ya karasa sai tsoro ya mamaye kafirai suka gudu. 

Bayan Abu Salama Mijin Ummussalama ya dawo sai ciwon da yaji a yakin uhudu ya famo, wanda sanadiyyarsa ya rasu.

Annabi yaji mutuwarsa mutuka kuma yayi masa addu'o'i na alkairi kuma ya rarrashi matarsa. 

A dai Muharram na wannan shekarar Annabi Muhammad ya tura Abdullahi Bn Unais don kashe Khalid bn Sufyan Alhuzaliy. Shi kuwa wata runduna ya hada mai girma don yakar Annabin Rahama. Ka duba kaga fa, rundunace mai tarin yawa, amma an tura mutum gudu don ya kashe shugaban rundunar. Amma da yake sahabbai imanin gaske garesu sai Abdullahi Bn Unais yaje yayi shiri ya kintsa sannan ya wuce don zuwa aiwatar da wannan gagarumin aiki. Haka ya tafi shi kadai har zuwa inda wannan runduna da ake hadawatake. 

Da zuwansa sai Huzaliy mai hada rundunar ya tambayeshi shin daga ina yake?
Shi kuwa Abdullahi Bn Unais yace daga Khuza'a yake. Naji ance kana hada runduna don yakar Muhammad. Huzaliy ya amsa alamar hakane. Sai Abdullahi yace to ina so in zamo cikin wayanda zasu yakeshi. Huzaliy yayi maraba dashi.

Abdullahi ya zauna a cikinsu yanata tunanin hanyar da zaibi don kashe wannan mutum, sai kawai dabara ta fado masa. Ai kuwa cikin dare an fara watsewa sai Abudullahi ya dirarwa mutumin nan ya kasheshi, cikin gaggawa kuma ya biyo hanyar dawowa madina. 

Su kuwa can sai suka tarar an kashe shugabansu, don haka sai suka biyo bayansa kasancewar basu san daga ina ya fito ba sai nemansa ya zama abu mai mutukar wahala domin babu inda za'ai ace shi aka tafi nema. A haka dai rundunar ta tarwatse.

Al'amarin Abdullahi bn Unais kuwa bai gushe ba yana tafiya har saida ya karaso Madina.  Annabi ya ganshi yaga cewa tabbas wannan jan gwarzo ya aiwatar da abinda ake bukatarsa da yayi, sai murna ta kama Annabi don ganin ran Abdullahi da lafiyarsa basu samu tangarda ba. Sannan kuma gashi ya kashe makiyi da makiya musulunchi. Saboda murna Annabi ya bashi sandarsa yace masa "Wannan ayace tsakanina da kai ranar Alkiyama." Wato alama ce da Annabi ya bashi. Haka kuwa akayi lokacin da wannan sahabi ya mutu tare da sandar aka binne shi.

A watan Rabiul Auwal ne yahudawan Banun Nadhir sukai nufin kashe Annabi, su kuwa sunada kwarewa wajen kera makamai ga kwarewa a filin daga. Amma hakan bai tsorata Annabi da Sahabbai ba. Su kuwa yahudawa sai tsoro ya kamasu, nan take suka nemi sulhu da sharadin cewa zasu kwashe komai nasu subar wannan yanki. Amma banda makamai.
Suratul Hashr akan wannan lamari ta sauka. 

A watan sha'aban shekara ta hudun dai Annabi ya fita izuwa badr don cika alkawarin da sukai na haduwa da sake gwabzawa da kafirai karkashin Abu Sufyan. Annabi ya fita ccikin mutum 1500, yayinda su kuma kafirai tawagar Abu Sufyan su dubu biyu ne. Tun farko Abu sufyan a tsorace yake don haka fitowarma ba'a son ransa ya fito ba. Annabi (S.A.W) yana can filin Badr tare da sahabbai sunata jiran kafirai su karaso. Amma yayinda kafirai suka zo wani da ake cewa Usfan sai suka juya rundunar ta tarwatse kowa ya kama gabansa saboda tsoro daya mamayesu. 

A watan Shawwal na shekara ta hudun dai Annabi ya auri Ummussalama matar Abu salama. Sunanta Hindu bnt Abu Umayya ibn Mughira. Annabi ya aureta bayan ta gama idda. Ta kasance mai tsananin zurfin tunani da kaifin hankali. Kuma itace ta karshen rasuwa a matan Annabi Muhammad (S.A.W). Ta rasu a shekara 61 bayan hijira. 

A shekarar dai Annabi ya auri Zainab matar Zainab. Bayan zaidu ya saketa Annabi ya aureta bisa umarnin Allah. Ita kuwa har alfahari take zuwa ga matan Annabi. Tace ku iyalanku ne suka aurar daku ga Annabi, ni kuwa Allah ne da kansa ya aurar dani zuwa ga Annabinsa.

Ayi mana hakuri zamu dakata anan. Sai a rubutu na gaba.


WAIWAYE ADON TAFIYA (33)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

 Adawar Yahudawa da Annabi tsohuwar adawa ce, dauki wannan takaitaccen tarihi tabbas a cikinsa zaka ji sunansu yanata maimaituwa...

Idan muka koma can baya kadan zamu iske cewa Yahudawa sune masu yiwa larabawa gori akan bautar gumaka da suke, harma suna tutiyar cewa idan Annabin karshen zamani yazo zasu hade kai dashi su yaki kafiran larabawa yaki mai tsanani. Saidai kuma abin mamaki lokacin da Annabin ya bayyana da sakon sai suka bijire saboda hassada. Ka duba kaga yadda Annabi ya sakko ya nuna musu a shirye yake daya karbesu a matsayin musulmai harma yana daura alkawari dasu akan zaman lafiya da taimakekeniya amma duk da haka sai hassada ta hanasu yin imani alhalin sunsan Annabi kamar yadda suka san kawunansu, sun kuma san alamominsa da siffofinsa kamar yadda suka san siffofin yayansu. Saidai inaa duk wannan bai zamo musu izina ba kuma basu yarda da wannan Annabi ba. Tare da cewa a zukatansu sunsan cewa kwarai shi din Annabi ne.

Ina ma'abota karatu? Yana da kyau su koma sudu duba littafin Sunan Darimiy a babi na biyu ko na uku ya zayyano hadisai da suke bayanin ayoyi a cikin littafan Ahlul Kitaab da suke nuni akan zuwan Annabi. Shin wannan kadai bai isa yasa muji tsoron cutar hassada ba?
Shin akwai abinda ya hana shaidan yiwa Adamu sujjada in ba Hassada ba?

Lokacin da Yahudawa suka ga nasarar Annabi akansu, da kuma yadda aka korasu suka bar garuruwansu sai wasu wakilai daga cikinsu daga kabilar Banun Nadir da Banu Wa'il, suka wuce Makkah inda suka riski kafiran kuraishawa suka rinka basu shawarar cewa su taso a hada karfi da karfe don rusa Annabi Muhammad (S.A.W). Da fari Kuraishawa basu amsa wannan kiran ba, saboda sunyi yake-yake tare da manzon tsira (S.A.W), amma wayannan wakilai suka rinka zuga su tare da nuna musu ai suma tare da su za'ai wannan yakin mai tsanani. Yahudawan basu gushe ba suna masu yiwa kuraishawa dadin baki hat saida kuraishawa suka yarda zasu fita. Daga nan kuma yahudawa suka tafi wajen kabilar Gadfan itama suka bijiro mata da wannan kudiri nasu suma suka aminchi inda su kuma yahudawa suka ce dasu zasu basu amfanin gonar khaibar na wannan shekarar sukutum.

Yahudawa, Gadfan da Kuraishawa suka tashi rundunar zaratan jarumai. Kuraishawa dubu hudu, Gadfan kuwa suka taho da zaratan mutane dubu shida. Tabbas basu taba hada runduna irin wannan ba.

Abu Sufyan shi aka nada kwamandan wannan yaki.

Lokacin da Annabi yaji wannan kuduri na kafirai, sai nan da nan ya kirawo sahabbai taron gaggawa inda ya nemi shawarinsu. Ai kuwa sai nan take shawara ta fara gudanuwa, a karshe suka tsaida magana cewa zasuyi yakin kare kai, domin basu da karfin da zasu fuskanchi abokan gaba. anan wajen dai sai Sahabi Salman Farisiy ya tashi ya bada shawarar cewa a haka katon rami ta fuskar da kafirai zasu zowa madina tunda ta kowace fuska babu hanya saita bangaren arewa kawai. Aka kuwa amshi shawararsa. 

A wannan lokaci mayaka zarata mutum dubu uku ne, tsayin da ake so a haka ramin shine zira'i dubu biyar, fadinsa zira'i tara, zurfinsa kuma daga zira'i bakwai ne zuwa goma. Aka rarraba cewa duk mutum goma zasu haka zira'i arba'in.

Haka sahabbai suka dukafa ga yunwa ga kishiriwa ga tsanani sanyi. Dadin dadawa ga tsoro mai tsanani. Sun gaji likis da wannan aiki Annabin rahama tare da shi ake wannan haka, yana kallon masoyansa sahabbai a zuciyarsa soyayyarsu da kuma tausayinsu yana qara shigarsa. Gami dayi musu addukar nasara. 

Annabi yaga yadda suke aiki babu ji babu gani, babu ci babu sha gashi karfinsu ya fara karewa, sai kawai dabara tazo masa don zuwar musu da kuzari. Nan take ya sabi wata magana da kari irin na baituka yana rera cewa 
Ya Allah babu rayuwa sai rayuwar lahira,
Ka gafartawa Ansarawa da muhajira.

Cikin nishadi sahabbai suka fara rera nasu baitukan
Munai mukai mubaya'a ga muhammada, 
Akan jihadi bamu bari har abada.

Haka akaci gaba da aiki ga yunwar ga kishiriwan amma har basa so su nuna sun gaji saboda su burge Annabi sannan basa son sakashia damuwa. Domin idan yagansu a wani yanayi yana shiga damuwar da tafi tasu yawa (S.A.W).

Can ta bangaren da Bara'u Bn Azib yake haka tare da abokan hakarsa, sai suka ci karo da wani katon dutse a kasar da suke hakawa, sukai sukai su fasashi amma wannan dutse yace bai ma san ana yi ba. Da sukai sukai suka rasa sai suka ce aje a gayawa Annabi. akaje aka gayawa Annabi Muhammad, ai kuwa saiya taho bigiran ya karbi abin hakar da suke hakar dashi. Ya daga sama yayi bismillah ya doka akan wannan dutse wani tartsatsi ya tashi ai kuwa take daya bisa uku na dutsen na fashe. Annabi yayi kabbara yace an bani madubin Sham, wallahi yanzu haka a wajen nan da nake ina hango jajayen gine-ginenta.
Annabi ya sake bismillah ya doka madokin akan dutsen a karo na biyu. Nan ma sai rabin abinda ya rage na dutsen ya farfashe, Annabi yayi kabbara yace an bani mabudin farisa hakika ni ina hango biranenta.
Daga nan ya sake kabbara ya daki dutsen sai ragowar dutsen ya farfashe, Annabi yayi kabbara yace an bani mabudin Yemen hakika daga nan ina hango kofofin San'a'a.

Su kuwa munafukai suka ce me zasuyi inba dariya ba, har sashensu yana cewa sashe "Ji mutum muna fama da yunwa dayanmu baya samun abincin da zai ci amma yana can yana cewa an bashi manyan garuruwa." Su kuwa sahabbai sai sukai imani da abinda Annabi ya fada kuma hakan ya zamo musu kwarin gwiwa.

Daga sahabbai akwai Jabir, kuma a wannan lokaci yana da wani dan guntun abinci wanda mutum uku zasu iya maleji dashi. Saiya cewa Annabi akwai abinci a gidansa, don haka so yake Annabi ya taho masa da mutum daya ko biyu wayanda zasuci abinci. Shi kuwa Annabi sai yayi shela ya cewa Sahabbai su taho aje gidan Jabir, akwai abinci a can. Haka suka taho sukayo gayya sai gidan Jabir.

Kunya ta kama Jabir (R.A) shi ba abin ya cewa sahabbai abincin dan kadan bane ba. Sai kawai yayi ta maza aka rankaya harshi. Amma sai yayi gaggawa ya rigasu zuwa gidan ya gayawa matarsa abinda ke faruwa cewa Annabi fa da gaba dayan mutanensa ya taho abincin mutum uku na maleji an kuma taho da mayunwata dubu uku. 
Matar ta tambayeshi shin ka gaya masa cewa abincin mutum uku ne? Mijinta ya tabbatar mata daya gayawa Annabi sai tace masa babu damuwa.

Anan zamu gane irin son da Annabi yakewa sahabbai, ta yanda yaki zabar wasu yabar wasu, hasalima saiya taho dasu dukkansu. Ka iya kwatanta soyayyar da soyayyar uwarnan da bata iya cin abinci ta kyale yayanta.  

Wata mu'ujiza ta Annabi shine, haka ya rinka debo abincin nan yana rabawa sahabbai har saida duk sukaci suka koshi. Kuma aka bar ragowar ga jabir da matar tasa.
Ka duba wani ikon Allah, abincin mutum uku, amma mutum dubu uku mayunwata sun ci harma sun bar ragowa. Lallai sahabbai sunga abubuwan mamaki.

Akaje aka ci gaba da haka, yayinda kafirai suka karaso musulmai sun gama hakar da suke. Kafirai da suka zo da zummar yiwa musulmi kwaf daya sai suka tarar da wangamemen rami a gabansu. Basu taba ganin irin wannan al'amari ba, don haka sai sukai cirko cirko suna kallon juna gami dayin shawarar ta ina zasu afkawa musulmai.

Sai ya zamana wawakeken ramin shine a tsakiya gefe da gefensa kuwa rundunonin biyu ne. 

Kamar yadda muka sani Bani Quraiza yahudawa ne, kuma akwai yarjejeniya tsakaninsu da Annabi cewa, ba zasubbada kofa a cutar dashi ba, kamar yadda zasu taimaka wajen tsare madina. Amma sai Huyay bn Akhtab wanda dashi aka harhado wannan runduna, kuma shugaban kabilar Banun Nadir yashiga ya fita tun shugaban Banu Quraiza yana kin yarda da kudurinsa har dai a karshe yaci karfinsa ya yarda zai mara baya a yaki Annabin tsira ayi kaca kaca da sahabbai. Nan fa labari ya iskewa Annabi cewa Banu Quraiza sun karya alkawarin dake tsakaninsu da Annabi, ya kuma tura Sa'ad Bn Mu'az da Sa'ad Bn Ubada don suje su jiyo gaskiyar wannan lamari, suka je suka dawo suka tabbatarwa da Manzon Allah cewa gaske ne lallai Banu Quraiza sun janye alkawarin dake tsakaninsu da Annabi. Amma sai suka bar abin a matsayin sirri tsakaninsu domin yadda sahabbai suke cikin tashin hankali idan labari ya sake zuwar musu irin wannan tabbas tashin hankalinsu zai karu. 

Kafirai da bakin naci haka suka tsaya suka kafa suka tsare suna ta neman sai sun samu inda zasu afkawa musulmai, duk sanda sukayi yunkuri sai Sahabbai su fara yi musu ruwan kibbau da masu don haka dole su hakura.

Munafukai kuwa sai suka rinka neman izini suka rinka komawa gida wasunsu suce sun manta basu kulle gidajensu ba, wasu kuma suka rinka fadar uzururruka makamantan wayannan.  

Bayan tsoro, sanyi matsananci, yunwa da kishirwa data addabi musulmi ga kuma gajiyar da take tattare a jikinsu, hakan tasa tausayin sahabbai ya zauna daram a zuciyar Annabi, ya rinka tunanin hanyar da zaibi don ya tseratar dasu, a karshe duk karfin izza irinta Annabi akan kafirai amma don ceto rayuwar sahabbai musamman mutanen madina wayanda a kowane yaki anfi kashe mutanensu sai Annabi ya kirawo sahabbai yana mai neman shawararsu akan cewa yana son yin sulhu da mutanen Gadfan ta hanyar basu daya bisa uku na dabinon madina...
Ai kuwa nan take Sa'ad Bn Mu'az da Sa'ad ibn Ubada sukace ya ma'aikin Allah idan umarni kake bamu, bamu da zabi dole mu bi. Amma idan shawara kake bamu hakika ko lokacin da muke mushrikai muna bautar gunki da mu da mutanen Gadfan din basa cin dabinon mu sai dai idan sunzo mana bakunta ko kuma idan sun siya. Shin yanzu kuma haka siddan saimu dauki dabinonmu mu basu bayan Allah ya shiryar damu ya bamu izza da musulunchi da shiriyarka? Wallahi ba zamu basu komai ba sai takubbanmu don yakarsu har sai Allah yayi hukunchi a tsakaninmu... Annabi da yaji haka sai ya yarda da abinda su Sa'ad suka ce. 

Kaji shugaba, mai adalchi wanda yake aiki da shawarar mabiyansa take mutukar shawarar bata banza bace. Kuma daga cikin abubuwan da suka sanya sahabbai suka zartar da wannan hukunci akwai 
1. Sun san Annabi saboda tausayinsu ya kawo wannan shawarar, da kuma tunaninsa ko sun karaya saboda ganin yadda munafukai suketa bada uzuri. Su kuwa sahabbai sai suka nuna masa indai sha'ani na Allah da manzonsa ne to hakika basa karaya ko mika wuya don kuwa a shirye suke su bada jinin jikinsu don tutar musulunchi taci gaba da kadawa.
2. Sun dabi'antu da izza ta musulunchi wadda sun koyota ne daga shugaba jaa gaba (S.A.W).

Ana tsaka da wannan al'amari kawai sai wani da ake kira Amru bn Abdu'wud ya bazamo tare da wasu mahaya ya dako tsalle da dokinsa ya dira gaban rundunar musulmi, yayi gunji gami da kururuwa. Shi Amru mutum ne kakkarfa domin shi kadai yana iya bugawa da mahaya mutum dubu. 

Yaci gaba da gurnani kamar yaci babu, kuma ya nemi fito na fito daga cikin musulmai.

Cikin hanzari Aliyu zaki dan Abi Dalib yayi fitar burtu zuwa gareshi yana mai kiransa zuwa ga musulunchi, amma sai Amru ya aibata musulunchi yace babu abinda zai amfanar dashi domin musulunci baida amfani a wajensa. 

Aliyu yace dashi to ina gayyatarka zuwa gareni don yin fito na fito, Amru ya bushe da dariya yace da Aliyu ya kai dan dan'uwana, ni bana son in kasheka.

Aliyu ya katse shi ta hanyar daka masa tsawa yace "Sai dai kuma ni, ina son kashe ka."

Maganar ta yiwa Amru ciwo mutuka, ya fusata mutuka, yayi gurnani kamar wani zaki ya daga hannunsa ya mari dokinsa a fuska gami da zaburar dokin zuwa ga Aliyu Ibn Abi Dalib. 

Akai wata haduwa, musulmi sunata addu'a da burin Allah ya tseratar da Aliyu daga sharrin wannan shirgegen kafiri, su kuwa kafirai sunata shewa gami da yiw wannan katon kafiri kirari. 

Kur ta turnuke sararin samaniya, yayinda su kuma kafirai sukaita shewa.

Kamar daga sama filin yayi tsit, sakamakon abinda aka gani. Aliyu tsaye rike da takobinsa yayinda gawar Amru ke gefe, kansa ma kuma yana wani gefen dabam yana gwagwiyar kasa...

Wayanda suka marawa amru baya kuwa sai suka tarwatse suka koma cikin kafirai a mutukar razane.

Ai mana hakuri. Zamu dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba.

Naseeb Auwal 
Abu Umar Alkanawy!

WAIWAYE ADON TAFIYA (34)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)...

Kafirai har yanzu sunanan sunja tunga jefi-jefi kuwa ana musayar jifa da masu da harbin kibiya. 

Kafirai sun fusata ainun sakamakon kashe musu Amru da akai. Aminchin da musulmai kuwa suke dashi ya ragu domin banu Quraiza da suke makotansu sun janye yarjejeniyar da ke tsakaninsu, kuma suna bada gudummuwa ga kafirai don haka koda yaushe za'a iya amfani dasu wajen cutar da Sahabbai. Saidai kafirai sukai kusan wata guda cur a wannan waje.

A irin wannan musayar jifa da ake ne aka damu Sa'ad Bn Mu'azu inda ya zubar da jini mai yawa amma saiya roki Allah da cewa kada Allah ya kasheshi har sai yaga rushewar Banu Quraiza. 
Abinda yasa kuwa shine, tsakaninsa da Banu Quraiza akwai soyayya mai karfi amma sai gashi sun watsa masa kasa a ido.

 Akwai ranar da Sayyadina Umar (R.A) ya shigo wajen Annabi a firgice yana zagin kafirai yana cewa sun shagaltar dani daga sallar la'asar. Annabi yace dashi "Wallahi ni ma ban sallaceta ba." Haka aka tashi akai sallar gab da faduwar rana ana idarwa kuma lokacin magriba yayi don haka sai aka dora. 
A wannan lokaci ba'a shardanta sallar tsoro ba.

Sahabbai sun jigata mutuka. Gashi babu abinci, su kuwa kafirai suna samun abinci daga ko'ina harma Banu Quraiza suna yo musu tallafi.

Annabin Allah mai jin kai ne, kuma rahama ne ga talikai don haka saiya daga hannunsa sama yace "Ya Allah mai saukar da littafi, ya mai tafiyar da girgije, ya mai rusa runduna, ka rusa su...".

Ko ta ina daukin zaizo?

Ana cikin wannan hali na tsoro Annabi ya tambaya cikin sahabbai wanene zai iya zuwa cikin kafirai don gano sirrinsu, kowa yayi shiru. A karshe Annabi ya tashi Huzaifa tare da cewa yana jin tsoro amma saiya amsa kuma yaje cikin kafiran harma ya samu damar da zai kashe Abu Sufyan amma saiya tuno idan ya kasheshi ya sabawa umarnin Annabi domin Annabi bai bashi damar yin kisa ba. Don haka ya dawo ya bawa Annabi labarin abinda ya gano, Annabi ya lullubeshi da bargonsa saboda murnar dawowarsa da kuma bayanan daya kawo. 

Nu'aim bn Mas'ud mutumin Gadfaan ne, shine yazo wajen Annabi, ya cewa Annabi hakika shi ya musulunta. Amma mutanensa basu sani ba, saboda haka shin akwai wani aiki da zai iya yiwa musulunchi?

Sai Annabi yace dashi ai shi kadai ne... Amma saiya haska masa abinda ya kamata ya aikata.

Nu'aim daya tashi bai tsaya ko inaba sai wajen Banu Quraiza yace dasu  kunyi alkawari da Muhammad, kuma akan wasu mutane wayanda suka taho daga nesa kun karya alkawarin dake tsakaninku, wayanda a karshe zasu tafi su barku tare da shi, kumga saiya dauki hukuncin daya ga dama a kanku alhalin su babu abinda zai shafesu. Saboda haka idan suka sake neman wani taimako a wajenku kuce musu ba zaku basu ba, har sai sun baku wasu mutane daga cikinsu a matsayin ku rike su. (Kamar a matsayin jingina kenan). 
Sai Banu Quraiza sukace wannan ra'ayi naka mai mutukar kyau ne. Kuma suka dauki wannan shawara daya basu.
Nu'aim baiyi kasa a gwiwa ba, saiya kara zuwa wajen Kuraishawa yace dasu, Quraiza fa sunyi nadamar hadewa da sukai da ku, don haka yanzu sun shirya wata dabara ni kuma naga yadda muke aminchi da ku bazan bari a cutar da ku ba... Zasu nemu ku basu mutane daga cikinku, idan kuka basu zasu damka su zuwa ga Annabi ko hakan zaisa ya yafe musu...
Daga nan yaje ya sake gayawa kabilar Gadfaan abinda ya gayawa kuraishawa. 

Sai shakka ta shiga cikin rundunar kafirai, kowanne sashe yana kokarin gwada sashe.

A karshe Gadfaan da kuraishawa suka nemi wani abu daga yahudawan Quraiza, amma sai yahudawan nan sukace ai ba zasu kara taimakonsu ba, har sai sun basu wasu mutane daga cikinsu. 
Da jin haka sai kuraishawa da Gadfaan suka ce lallai abinda Nu'aim ya fada gaskiya ne, suka kuma ki su bawa, Quraiza mutane a matsayin jingina.  Suma Banu Quraiza da suka ga haka sai sukace, lallai abinda Nu'aim ya fada gaskiya ne. Don haka sai suka janye jikinsu.

A wannan dare Allah ya taro da wata iska mai karfin gaske, ta rinka jifa da tukwanen kafirai da tantinansu, sannan dabbobinsu suka rinka nutsewa a cikin sahara. Babu shiru Abu Sufyan ya hau abin hawansa har yana mantawa bai kwanceshi ba. Ya umarci kowa daya tashi su gudu. Haka suka arce suna kaskantattu.

Annabi kuwa da sahabbai bayan sun gama shirin komawa gidajensu, sai Mala'ika jibril ya zo masa yace masa wai ka ajiye yakin ne? Annabi ya amsa masa da cewa kwarai ya ajiye tunda kafirai sun gudu. Sai jibril yace "Malaiku basu ajiye ba, sannan Allah yana umartar Annabi daya je wajen mutanen Quraiza domin..."

Duk da gajiya dake tare da sahabbai da rauni dake jikin wasu amma babu yadda za'ayi Allah ya sakko da umarni. Don haka Annabi yace kowa la'asar tayi masa a yankin banu Quraiza. Ai kuwa hakan akai. A karshe dai suka mika wuya akai musu hukuncin kisa. Aka maishe da matansu bayi. 
Wannan shine hukuncin wanda yaci amanar Manzon Allah ko aka hada kai dashi don kashe mmanzon Allah.  Kuma Allah ya karbi addu'ar Sa'ad Bn Mu'azu domin shi sukace suna so yayi musu hukunchi domin shine masoyinsu tun a jahiliyya, hakanan yan uwansa wasu a madina suka rinka yi masa magiya cewa yayi musu hukunci mai sauki tunda abokanansu ne, amma saiyayi hukunchi bisa abinda ke dai dai.

Kashe su shine kawai mafita domin kuwa kuwa suna dakile tafiyar Annabi Muhammad, sannan a shirye suke da idan sukai karfi su kawar da shi.  
R.V.C Bodley cewa yayi ba don wannan kisan da akai musu ba da musulunchi ba zaije ko'ina ba. Domin zasuyita dakile shi ne ta bayan fagge. Kuma Annabi zai zama baida cikakken karfi. Duba littafin don samun wasu dalilai kwarara daya kawo.
(The messenger, the life of Muhammad p.217)

Haka nan Dr Israel Wellphenson shima ya tabbatar da cewa tunda Annabi yanke wannan hukuncin sai munafukai suka daina yi masa kutse cikin lamarinsa. Da kokarin jayayya dashi idan ya fadi abu.
(Alyahud fi biladil arab p.155)

Hakanan Annabi yasa akaje can Najd aka kamo masa shugaban Banu Hanifa Sumamatu ibn usal, aka daureshi a masallachi. 
Annabi ya fito gareshi sannan yace dashi "Me kake tunanin zai faru ya Sumama?"
Sai Sumama yace "Idan ka kashe ni ka kashe wanda za'a dauki fansar kashe shi, Idan ka nuna min karamchi to ka karrama ma'abocin karamchi ne, idan kuma kudi kake nema to hakika za'a baka adadin da kake so."
Duba kaga yana daure amma yake gayawa Annabi wayannan maganganu, amma ko harararsa Annabi baiyi ba.
Rana ta biyu Annabi ya sake tambayarsa amma wannan amsa dai ita ya sake bayarwa.
Rana ta uku Annabi ya sake zuwa, sai yasa aka saki Sumamatu.

Ai kuwa Sumama yayi tafiyarsa, ashe ba tafiya yayi ba, sai kawai yaje yayi wanka ya dawo. Ana zaune a majalisar ma'aiki sai akaga fursanan da aka saka kyauta ya dawo. Anan take ya furta shahada. Sannan yace na rantse da Allah, a da babu wata fuska da nafi tsana sama da fuskarka, amma yanzu itace mafi soyuwa a gareni. Na rantse da Allah babu wani addini mafi muni a wajena sama da addininka amma yanzu shine mafi soyuwa a gareni... Abinda ya faru dani shine na fita zanje makkah don yin Umra, sai aka kamoni aka kawoni nan wajenka. 
Annabi ya taya shi murna sannan ya bashi umarnin yaje yayi umararsa.

Ai kuwa ya tashi ya nufi makkah, da yaje da sukaga yadda yake umararsa, sai sukace ko dai kaima kabar addini ne, sai yace musu ba barin addini nayi ba, saidai na karbi addini daga wajen Dan'aiken Allah ne. Kuma ina rantse muku da Allah babu wani kayan abinci da zai kara zuwar muku daga Yamama face sai da umarnin Annabi (S.A.W).

Haka kuwa yayi daya koma, saiya datse hanya ya hana kawowa makkah kayan abinci, ai kuwa sai kafiran makkah suka shiga matsi. A karshe suka rubuta wasika zuwa ga Annabi cewar suna so yayi umarni ga Sumama daya bude musu hanya abinci ya rinka zuwar musu...

Ka tuna ya kai mai karatu, mutanen makkah sun sha duka, zagi da kisa ga musulmi duk a lokacin da musulmai suke tare da su.
Ka tuna sune suka hana bawa banu Hashim abinci ko abinsha tsawon shekaru, har ya zamana suna cin ganyen bishiyu sabida yunwa.
Ka tuna Annabi a Makkah aka haifeshi amma saida suka takura masa ya tashi ya bar garin.
Ka tuna duk da ya barsu a hakan farautar rayuwarsa suke.

Me kake tunanin ya dace ayi musu tunda ga damar ramuwa tazowa musulmai?

Amma Annabi sai ya tausaya musu cikin gaggawa ya bada umarnin da'a cigaba da kai musu kayan abinci. (S.A.W)

Shin akwai tausayin da ya kai wannan?
Shin akwai mai kyautatawar da ya kai wannan?

Tabbas Annabi Rahama ne ga talikai.

Ayi mana hakuri zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba in Allah ya yarda.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy!


WAIWAYE ADON TAFIYA (35)
Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W).

Ba'a jima ba, sai bayani ya zowa Annabi cewa Banu Mus'dalik wayanda su din mazauna ne tsakanin makkah da madin, saidai sun fi kusa da madina. Dama kuma tun daga yakin Khandaq ko Ahzab an samesu da hannu dumu-dumu wajen yakar Annabi Muhammad (S.A.W). 

Wannan lamari ya faru a watan sha'aban shekara ta biyar bayan hijira, wasu kuma suna cewa shekara ta shida. Saidai malamai mafiya yawa sunfi nasabta yakin da shekata ta biyar.

Kamar yadda ya bayyana, tun zuwan Annabi madina ya samu karfi mai girma, da kuma tarba ta karamchi, don haka mutanen da basa goyon bayansa suke ta kulle kulle wajen ganin sun hallaka shi, ko kuma dakile da'awarsa zuwa musulunchi. To hakika sunyi abubuwa da dama ciki kuaa harda aika sirrikansa zuwa ga makiyansa don dai a samu a kawar da shi amma babu inda suka samj nasara. Dalilin haka yasa suka sauya dabara, dabarar kuwa itace zasu shigo da rikici da rabuwar kai a tsakanin mabiya wannan Annabi mai girma. Da kuma shigar da rudani da rikici cikin gidansa tsakaninsa da iyalinsa. Domin muddin sukai haka to tabbas sunci karfin yin nasara a kansa.

Don haka lokacin da Manzon tsira ya kira mutane zuwa musdalik sai aka samu munafukai sunyi fitar da basu taba yi ba domin yanzu babban burinsu shine su shiga jikin Annabi su haddasa fitina.

Su kuwa Banu Musdalik dama suna cikin tanadi ne, tare da su akwai wayanda suke taimakonsu daga cikin larabawa. Banu Musdalik suka tashi yan aike suka turasu don ganin sirrin Annabi da kuma irin tanadin da yayi. Saidai kash sai sukai rashin nasara, domin kuwa caraf aka kame yan aiken aka karkashesu. Lokacin da labarin kisan yajewa Banu musdalik sai hankalinsu ya tashi mutuka. Kabilun larabawa da suke tare dasu sai suka rarraba kowa ya kama gabansa. 

Yakin ba'a sha wahala ba, aka gwabza aka ci galaba akansu, aka ribaci matansu a matsayin ganima da dukiyoyinsu da yayansu.

Cikin wayanda aka kama harda yar gidan shugabansu, da sahabbai suka ga cewa yaf gidan shugaba ce kuma akwai tausayi daga yar sarki ki koma baiwar wani daga cikin gama garin mutane marasa sarauta sai suka kaiwa Annabi ita.

An kama mutane da yawa, kuma dukkaninsu zasu zama bayi, sannan kuma tsakaninsu da musulmai akwai wani kulli na adawa, domin suna da hannu tsamo-tsamo wajen yakar Annabi Muhammad da Sahabbansa. Don haka idan suka zamo bayin musulmai in ba wanda Allah ya shiryar ba cikinsu zaka iske akwai wannan wutar adawar dai a cikin zukatansu. Shi kuwa Annabi baya goyon bayan ci gaban adawa, abinda yake so shine haduwa da zama tamkar yan'uwa da kuma taimakekeniya wajen biyayya. Shin me zai aiwatar don kawar da adawar da take cikin zuciyoyin wayannan mutane da aka kamo su? Wasu an kashe musu yan'uwa, wasu daga masu mulki zasu koma bayi.
Idan kaine yaya zakayi ka cire musu wannan kiyayyar?

Annabi dake hikimarsa daga Allah take, lokacin da aka damka masa wannan yar sarki da ake kira juwairiyya, sai yace ya yantata kuma ya aureta.

Da jin haka sai Sahabbai suka rinka yanta bayinsu da suka kama suna masu koyi da Annabi suna cewa wayannan mutane sun zama sirikan manzon Allah. Kai kuwa kasan yadda Sahabbai suke da Annabi akwai kunya ace baiwar mutum ko bawansa sirikan manzon Allah ne... Don haka sai sahabbai sukai ta yan tasu.

Su kuma ta fuskarsu kamammun banu musdalik sai suka ga cewa lallai wannan mutumin yanada karamchi, suka tuno cewa sune suke bada kansu da jinanensu don a yakeshi amma gashi yayi musu karamchi irin wannan. 
Bawai kuma yantasu yayi kawai ba, harma da auren yar sarkinsu kaga suma sunada uwa a bakin murhu kenan!
Kaga kiyayya ta juye zuwa soyayya!

Nana Aisha uwar muminai da kanta tana cewa "Bansan wata mace mai albarka ga mutanenta ba kamar juwairiyya."

A hanyar dawowar Annabi da sahabbai da munafukai, an yada zango, sai wani daga cikin mutanen makkah muhajirai ya daki wani daga cikin Ansarawa da kafarsa. Sai wannan na Ansarawan ya taso sai kowannensu ya kirawo mutanensa donsu kawo masa dauki. Nanfa hayaniya ta fara, cikin hanzari Annabi yazo ya tsoratar ya nuna musu cewa wannan irin da'awar jahiliyya ce.

Yayinda labari ya jewa Abdullahi Bn Ubayyu bn Salul shugaban munafukai saiya hakikice yanata nanata magana gami da gori ga sahabbai yana cewa lallai sun samu dama, dama ance idan ka ciyar da karenka ya girma to kai zai ciza... Mu muka basu kariya muke ciyar dasu amma mu zasu wulakanta... Mun daina basu abinda muke basu. Kuma idan muka koma madina sai mun kaskantar da su.

Sahabi Zaid bn Arqam yaji abinda Abdullahi ya fada, nan take yaje ya gayawa Annabi. Umar Ibn Khaddab yana jin haka ya fusata ya mike yace ya ma'aikin Allah a bani umani in saro kansa. 
Sai Annabi yace a kyaleshi kada ace Muhammad yana kashe mutanensa. 

Aka kirawo Abdullah bn Ubayyu aka tambayeshi amma saiya rantse yace Zaidu karya yake. Zaidu yayi bakin ciki, bai daina bakin ciki ba sai lokacin da aka saukar da suratul munafikun Annabi ya turo masa bushara cewa Allah ya gaskata shi.

Da ace Annabi yaga dama zai bari a kashe Abdullahi Bn Ubayyu ibn salul, amma sai yayi amfani da siyasa domin kashe Abdullahi zai jawo rabuwar kai da gasken gaske da kuma kirkirar shubuha ga wasu da dama daga mutanen madina.  

Kafin Annabi yakai madina dan gidan shugaban munafukai yaje ya tare hanya, saida ya bari babansa yazo wucewa saiya tsareshi yace naji abinda kace, kace zaka kaskantar da Annabi. To babu inda zakaje har sai ka gaya mana wanene kaskantacce a tsakaninku. Saika tabbatar da cewa kaine makaskanchi sannan zan barka ka shige.

Annabi yazo ya tarar da wannan lamari, amma Annabi mai Karamchi saiya umarchi dan shugaban munafukai daya kyautatawa mahaifinsa tunda ana tare. Sannan kuma ya barshi ya shige.

Karkashin wannan zamu gane cewa lokacin da kakeda iko ba kowane abu ake amfami da karfin ikon ba, wani abun amfani da karfin iko saidai ya kara lalatashi.

Ayi mana afuwa, zamu dakata anan.
Sai kuma a rubutu na gaba.

Naseeb Auwal
Abu Umar Alkanawy!

Comments

Popular posts from this blog

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

EYE OPENER... (SIWES)

AUREN DOLE.