WAIWAYE ADON TAFIYA 16 - 20
WAIWAYE ADON TAFIYA 16 Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W) Munji cewa Sahabi Umar ibn Khaddab (R.A) ya musulunta, kuma muka ambaci cewa Annabin tsira da Aminchi ne yayi addu'ar cewa Allah ya karfafi addinin musulunchi da Umar... Wannan shine abinda ya tabbata a ruwayoyi wayanda na riska, saidai guda daya wadda Nana Aishatu uwar muminai take cewa abinda ya tabbata shine Annabi yace “Allah ka daukaka umar da addinin musulunchi...” dalilinta kuwa shine, tace “Shi musulunchi wani baya iya daukaka shi, saidai shi ya daukaka mutum.” Wannan fahimtarta ce. Allah ne mafi sani. ★ Kafirai da sukaga musulunchi yanata daukaka kuma sukaga duk matakin daya kamata su dauka sun dauka amma abu yaki ci yaki cinyewa sai suka sauya shawara. Suka nemi a basu Annabi, a sallama musu shi, su kasheshi, zasu musanya shi da wani daga cikinsu, sannan zasu biya dukiya mai tarin yawa... Abu Dalib da yaji bukatarsu sai yace amma gaskiya wannan abu nasu ya bashi mamaki, wannan wanne irin shirme ne, ya basu dan...